018
*MAI ƊAKI...!*
Fitattubiyar
©️ *Nana Haleema.*
*Book 1*
*Page 18*
A tare dukkan su suka kalli juna gaban Yusuf yayi mugun fad’uwa ya fara zare idanu ya sunkuyar da kai yana shafa kansa hankalin sa ya tashi sosai, yasan Ameena baza ta ya dake ta ba maganar Ammah ce baya so. Amma ta sake kallo Ameena da ita kanta fuskar ta ta nuna alamun rashin gaskiya tace, "Amina me nake gani a wuyan ki haka? Da gaske duka ne?." Bata iya amsa mata ba dan bata san me zata ce ba Ammah ta sake cewa, "Kalli yadda wuyan ki yayi Ja fa, Yusuf ne ya dake ki?."
Yadda gaban Yusuf yake fad’uwa haka ita kanta Ameena din dan bata san abinda zata ce ta kare kanta ba, a tare gaban su yake faduwa shi tsoron kar ta tona masa asiri shine rashin hankalin sa ita kuma rasa abinda zata cewa Ammah shine yake d'aga mata hankali ita kanta Ammah burin ta kar taji ance Yusuf ne yayi dukan. "Kai Meya same ta haka?". Ta fad'a Tana kallon Yusuf ya dago kai ya kalli Ameena kafin yayi murmushi yana tattaro abinda zai fad’a yace, "Mayafi ne, ta nad'a jiya a wuyan ta da tazo cirewa sai taja shi da karfi shine yayi haka."
"Da yake mafayin qusoshi ne a jikin sa?" Ta tambaya tana kallon sa.
Kafin yayi magana Ameena tace, "Haka ne Amma, kin San wani lokacin baka yi tsammanin abu ba sai ya faru. Ni kaina ban San wajan yayi ja haka ba zai d’azu dana gani.”
Da mamaki Ammah take kallon su duka biyun kafin tace, "amma wannan baiyi kama da abinda kika ce ba da zanen abin duka yayi kama." Murmushi tayi tace, “Amma waye zai dake ni?.” Ta kalli Yusuf da yake kallon Amina Ammah tace, "ka fada mata zancen tsayar da ranar bikin naka?." A firgice ya kalli Amma ya kalli Amina da take kallon sa ya sake kallon Amma yace, "Ban sanar da ita ba Amma."
"Meyasa?."
Tashi tsaye yayi yace, "rashin Lafiyar da take fama da ita ya saka ban fad’a mata ba, ban San ta inda zan fara fad’a mata ba shiyasa na bari sai ta samu Lafiya. Ammah ana kira a store Sai na dawo" yana gama fad'a ya fita daga d’akin da sauri.
Amma ta kalle ta tace, "An tsayar da lokacin bikin sa sati takwas mai zuwa." Amina ta girgiza kai tace, "Allah ya nuna mana lokacin."
"Amin Amina. Kar ki saka komai a ranki kar komai y dame ki kinji ko?." Murmushi tayi tace, "To Amma in sha Allah." Humairah da take gefe har lokacin bata ce komai ba tausayin Amina take ji sosai a zuciyar ta tana kuma tabbatar da ba wani mayafi dukan ta kawai aka yi.
Kalamai masu dadi Amma ta dinga amfani dasu tana kwantar mata da hankali har sai da taga ta saki jiki suna hıra da Humaira sannan ta basu waje Amina zuciyar ta cike take da tsoro wani b’angren kuma cike take da Jin dadin uwa da ta samu bayan rasa wacce ta haife ta da tayi, badan Amma da take kwantar mata da hankali ba tabbas da zuciyar ta zata iya bugawa ko wanne lokaci.
Tunda ya zauna ya dafe kai baiyi magana ba itama kuma bata ce masa komai ba dan Tunda taga yanayin da ya shigo tasan akwai babban abinda yake damun sa sosai. Musamman da yayi tattaki yazo gidan ta duk da mutum ne mai zumunci amma bai cika zuwa ba sai da dalili. Shirun taji yayi yawa ya saka tace, "İbrahim Lafiya wai?."
Sai sannan ya d’ago ya sauke numfashi ya kalle ta yace, "Ina zan kai damuwar Fiddausi ne?." Murmushi tayi tana kallon sa tace, "Ikon Allah yau kuma da kanka kake tambayata inda zaka kai damuwar Fiddausi masoyiyar ka?." Kai ya girgiza ya lumshe ido zuciyar sa na bugawa sosai dan Allah ya sani yana son Fiddausi so mai tsanani abubuwan da take masa bai saka son ya ragu da yawa ba, damuwar daren jiya ce ya kasa jurewa sai da ya garzayo gidan Yayar tasa abokiyar shawarar sa ya furta mata abinda yake zuciyar sa ko zai ji dadi.
Ganin ya sake yin shiru ya saka tace, "Me Fiddausi tayi maka?."
"Meye ma bata yi ba?, sam Fiddausi ta canja akwai Wanda yake zuga ta ko kuma aljanu sun shafe ta."
"Ba wata zuga ko aljanu wallahi, ita kad'anta itace aljanar kanta. Tun yaushe nake fad’a maka yarınyar kanta yana rawa nan gaba bazata zauna da kai ba kace min kai ba haka ba?. Tana da hange ne İbrahim Tana kai kanta inda Allah bai kaita ba, gasa take da k’awayen ta wanda suka fita auren masu kudi. Ita kuma gasa duk wanda yace zaiyi wallahi yana tare da wahala.”
Sake kallon ta yayi yace, "Nasan da wannan halin nata tun ba yau ba, amma na yanzu yayi yawa abubuwa take yi kamar wacce bata cikin hankalin ta. Ni wallahi zargi nake anya ba aljanu ne suka shafe ta ba?." Wacce take amsa sunan Yayar tasa wacce yake bi ta kalle tare da tab'e baki tace, "Hmmm! To me tayi maka a wannan karon?." Bud'e Baki yayi zai yi magana sai kuma ya fasa ya kawar da kansa gefe yace, "Ki cigaba da taya ni addu'a kawai Allah ya daidai ta tsakanin mu."
"To amin, addu'a kayi ai babu abinda yafi k'arfin Allah. Amma matar nan taka sai dai kayi hak’uri dan kai kasan bazan ‘boye maka ba na fad’a a bayan idanun ka ba, in da tana sonka yanzu bata sonka hangen wani wajan take yi. Kaga ban san me tayi maka ba ko? Amma a jikina nake Jin babban abu ne tunda gashi har ka kasa jurewa kazo ka same ni da batun ta, Allah ya shirya ta in tana da rabo in kuma babu Allah ya kawo karshen auren naku kawai."
Kallon ta yayi fuskar sa dauke da firgici yace, "Haba Mariya wannan wacce irin magana kike yi haka?." Hannu ta wara tace, "To akwai wacce ta fita ne?."
"Taya zaki fatan mu rabu bayan mun fara tara zuri'a nida ita? Kodan Amir bai kamata kice haka ba gaskiya."
"Ko babu ita Amir zai taso cikin gata da kuma tarbiyya, ko babu Hajiya akwai ni ga yayyen mu babu wands bazai rike Amir ba."
Numfashi ya sauke a sanyaye yace, "Duk da hakan dai bai kamata kice haka ba." Ta girgiza kai tace, "To naji, Allah ya daidaita ku." Ya
amsa da amin suka fara hira dai sama-sama kafin ya tashi ya tafi ko babu komai ya samu saukin abinda yake ji a zuciyar sa.
Fiddausi kuwa tun da abin ya faru take cika tana batsewa ita k’adai koda taji fitar sa tsaki tayi ta koma ta kwanta a fili tace, "Tun kafin kasan akwai ciki a jikina ya kamata na zubar dashi dan bazan sake haihuwa da kai ba, talakan banza da wofi kawai." Wayar tace tayi k'ara ta fara kallon agogon wayar taga karfe goma na safe sannan ta kalli mai kiran ganin Zakiyya ya saka ta dauka daga can bangaren tace, "Ke Lafiya babu wani feedback ne?."
Fiddausi taja tsaki tace, "Ban San ya zanyi masa ba Kiyya, nayi duk abinda ya kamata amma mutumin nan kamar mata zuciya. Jiya Ruky na gidan nan a gaban ta nayi masa rashin mutunci amma bawan Allah nan kalmar saki ya kasa furtawa sai huci da yake kamar wani zaki."
Zakiyya tayi dariya tace, "Kice kin sha wa'azi a wajnan Rukayya.”
"Kamar kin sani, ta saka ni a gaba tana fad’ar wannan ta k’arasa da wancan, dan munafurci harda kuka wai ita da take neman mijin nida na samu ina wulakantawa nace in ya sake ni ya aure ki kinga shikenan kin samu miji a sama.”
"Banza ce ai yarinyar nan zata iya auren nasa fa, ita bata gudu abinda ake gudu.” Fiddausi tace, "Ai ba cikakken hankali ne da ita ba, Ana gudu wahala tana so ta saka kanta a ciki."
Zakiyya tayi dariya tace, "Ya batun cikin?."
"Ban zubar ba har yanzu kuma bai sani ba, kamar yadda kika ce na fison saki da zubewar sa kinga shikenan na huta da idda." Zakiyya ta sake yin dariya tace, "Shegiyar kaya kice kin matsu dai ki ganki an America ana honey moon ko?." Itama dariyar tayi tace, "Waye yak'i dad'i?."
"Ke ina so na fad’a miki wani abu.”
“Ina Jin ki.”
“wai ashe Yusuf din Ameena aure zaiyi bata fad’a mana ba?."
Daga kwance Fiddausi ta mik’e zaune ta wara ido tace, "Kece wallahi?." Zakiyya tace, "Wallahi da gaske wai aure zaiyi, har an saka rana ma nan da sati takwas bikin."
"Innalillahi wa’inna ilahiri raji’un, y’ar uwa kinji yadda k’irjina yake bugawa kuwa?. Daman Yusuf zai iya yiwa Ameena kishiya?, duk wannan soyayyar da yake yi mata zai iya had'a ta da wata macen a duniya?. Kai lamarin rijalu sai Allah, duk soyayyar da Amina take masa yanzu wata zai kawo mata?."
Zakiyya tace, "Bari kawai kedai, wallahi ni kaina naji abin a zuciyata fiye da tunanin ki, in a tuna waye Yusuf a wajan Ameena sai naji kamar nayi kuka. Yaushe ma akayi bikin nasu da zai yi wani aure dan Allah?."
"Abinda na gani nima kenan ai Kiyya, an ina kika ji labarin?."
"K’awar wacce zai aura ce take fad’a min, da farko ban gane ma Yusuf take nufi ba sai da ta ce min ke mijin k’awar ku fa Ameena. Ashe shi da irin yaudarar nan yaje neman auren ai kuwa suka kamo shi caraf ya haukace akan amaryar. Gashi tace min basu da tarbiyya yaran ko kad’an basa girmama kowa, sai dai muyi addu’ar Allah ya zaunar dasu Lafiya.”
Fiddausi tace, "Allah sarki Ameena, ya kamata muje gidan nata muyi mata jaje."
"Banza wai jaje kamar wacce aka yiwa sata? Kawai zamu je ne matsayin mu na k’awayen ta kuma y’an uwan ta mu kwantar mata da hankali. Nasan halin ta yana nan a tashe ko Baka son miji yace zai k’aro aure sai kaji a jikin ka balle kana son sa, ko da yake sai nake ganin kamar ma bai dame ta ba harkar ta kawai take." Fiddausi tayi dariya tace, "To indai da kud’i meye wani abin kishi Kiyya? Ai in kika ji ana d’aga murya akan miji wallahi talauci ne." A tare sukayi dariya kafin Zakiyya tace, “Kedai kudi kawai matar Alhaji.” Dariya itama tayi kafin suyi sallama ta kashe wayar.
^^^^^^
Rukayya kuwa haka ta tashi babu kuzari a jikin ta gabadaya, abinda ya faru a gidan Fiddausi ne yake dawo mata sai kuma d'an shaye-Shayen da yazo da sunan wai yana neman auren ta har cikin gidan su, komai yin sa take a sanyaye har ta kammala ta koma d’aki tayi wanka ta fito ta ci abinci har lokaci Umma tak’i yi mata magana tun jiya take fushi da ita akan tace bata son wanda yazo jiya.
Kasa jure hakan Rukky tayi bayan Umma ta shiga d’aki tabi bayan ta ta dur’kusa a kusa da ita tace, "kiyi hak’uri Umma da b’ata miki da nayi jiya, ki yafe min." Umma kamar jira take tace, "Ai in kinga na yafe miki kawai kin amince anyi auren nan, ke haka kike so ki ta zama kowa yana aure yana barın ki?. A haka kike so ki tsufa a gida? Ki duba tun da kyaun ki sai ya disashe sannan kika so ki tashi?.”
Rukky ta sauke numfashi tace, "Umma aure ai lokaci ne in nawa lokacin yazo zanyi."
"Sai na buge miki baki keda lokacin, ni zaki fad’awa aure lokaci ne? Nifa na sani kika yi ko me?."
"Kiyi hak’uri."
"K’anwar ki tayi aure ta barki kina yawo da hijjabi a titi da lunguna. Duka k’awayen ki uku yara ne dasu amma ke kina nan sai dai kici kiyi bacci ko samarin nan irin na waya baki dasu. Wallahi ni na gaji da ganin ki a gabana jinina hawa zaiyi, kamar a kanki aka kawo bak’in jini duniya? Kanwar ki ta biyu gata nan aure zatayi amma ke kowa yazo kice bakya so kashe ni kike so kiyi Rukayya?".
Yadda Umma ta k’arasa maganar kamar zatayi kuka y saka Rukayya ta girgiza kai tace, "A'a Umma Kiyi hak’uri dan Allah, in lokacin yayi zanyi auren.” Umma tace, "Na gaji da ganin ki haka aure nake so naga kinyi shine hankalina zai kwanta."
"To Umma zanyi."
"Yaushe?."
"Nima ban sani ba Umma."
"In kika fita samari basa tare ki?."
"Babu wanda yake min magana har naje na dawo."
Umma tace, "Taya kike so hankalina ya kwanta ama irin haka?." Rukayya ta fashe da kuka mara sauti Ummw tace, "Ba kuka zaki ba amsar duk wanda yazo yana sonki zakiyi ayi auren nan kema ki huta. Kin wuce lokacin da za’a ce sai kin zab’a ai Rukayya, lokacin zab’en miji a wajan ki ya wuce.” Kai ta girgiza alamun to kafin Umma ta sake cewa, "Ki dai yiwa kanki fad’a ki daina tsayawa zab’e, ai tunda kika wuce shekara ashirin da biyar zab’e ai ba naki bane kawai da anzo ki amince bana son wani wasa da hankali. Ki bar yara suce zasu yi zab’e amma bake ba."
Nan ma kai ta d’aga kawai sabida kuka bazata iya magana ba Umman tace, "in ma dan shaye-shaye ne kuna tare albarkar aure sai kiga ya daina, balle ke mai ilimi da wuri zaki nusar dashi ya daina yin abinda yake yi. Amma da yake ke ga kareena kapoor gaki benu sarkin yarinta kice sai kinyi zab’e ana rok’o Allah ya kawo ya kawo kuma ke kina cewa bakya so." Murmushi takaici Rukayya tayi tana cigaba da hawaye Umma ta kalle ta tace, "Tashi kije ki d’ora girkin rana amfanin ki kenan daman ai." Jiki a sanyaye ta mik’e ta fita zuciyar ta kamar zata buga sabida bakin ciki da takaici, har tana ji a ranta zata amince da duk wanda aka sake kawo mata matsayin miji ko wanne irin hali ne dashi zata karb’a kodan Umma.
#Comments
#vote
#Share