YADDA KADDARA TA SO

05

by @salmaahmadisah

⭐️YADDA ƘADDARA TA SO⭐

⭐️ شاء القدر⭐️

*Magical love story*

©By Sai Kaska

Wattpad @Sai_Kaska

Phone number:***

Arewabooks @18saikaska

_________________________________

*Proud of my first novel*


★TAURARI WRITER'S ASSOCIATION★


*Yau babin naki ne Fateema Sa'id Haruna*


*BABI NA GOMA SHA BIYAR (15)*


HANAM POV.

Zaune take a office tana dudduba wasu yadika, yau Naani ɗin Arya bata zo ba, wai bata jin daɗi.

Dan haka ta saka aka ɗauko masa castle tent ɗinsa daga ɗakin da ake renon nasa zuwa office ɗin nata, ta saka shi a ciki, ta haɗa shi da wasu teddies da kayan wasa, saima ta manta dashi a office ɗin, dan sabgarsa yake, shi idan da kayan wasa babu ruwansa da kowa.

Sanye take da farin cargo pants, sai wata peach sweat shirt a jikinta, gashin kanta ta ɗaure shi a bayanta, ta saka masa farin bow ribbon clip, daga ƙasa kuma ta sakeshi ya baje a bayanta, duk da gashin nata ba wani tsayine dashi na tashin hankali ba, kuma kamar kullum daga ƙasansa tai masa kalar brown.

Haka zalika amar kullum fuskarta babu kwalliya, ko kwalli bata saka ba bare aje ga hoda da sauran kayan kwalliya, ta sofara pen a bayan kunnenta, wata ɗabi'a wadda tun tana makaranta take yinta, sofara biro a bayan kunne, kunneta karamar barima ce kawai.

A hankali take kaɗa ƙafarta ta dama ta na yi tana duba yadikan, kasan cewar kanta a ƙasa yake yasa bata lura da wanda yake tahowa daga waje ba, dan katangar office ɗin nata glass ne, saiji tayi ana ƙwanƙwasa ƙofar,kuma ba tareda ta ɗagoba ta bada izinin shigowa.

Shigowar yayi ta bashi damar zama, ya zauna a kan kujerar, ta aje ipad ɗin hannunta ta ɗago, ta ɗora idonta akansa, Damm!, gabansa ya faɗi da ganinta, tunainsa ya ɗauke shi can shekarun baya.


*2016, NEW PRIME ACADAMY, ABUJA*

Ɗaliban SS3 ke hayaniya sbd test ɗin da ake raba musu, kowa sai haƙilan samun tasa yake daga hannun ifeanyi, wanda ya kasance shine montan ajin nasu. Saida aka gama rabawa kowa ya koma seat ɗinsa ya zauna, sannan malamin geography ɗinsu, Uncle Bala ya ce.

“Kowa ya samu tasa ?” 

Suka amsa masa da eh

“To ɗalibai, kowa yayi ƙoari, kuma kun bani mamaki sosai, gaba ɗaya cikinku naga babu wanda ya samu ƙasa da 10, dan haka wanna abun alfaharine, but their is only one person who score below 10......”

Gaba ɗaya kowa yayi shiru yana jiran wa za'a ce, duk da sun riga da sun san ko wa za'a kira dan gaba ɗaya ajin ansan waye baya focusing kwata-kwata, kuma kamar yanda suka zata hakance ta kasance.

“Uchenna Franklin, stand up!”

Duka suka saka masa dariya, yana daga seat ɗin baya kansa a ƙasa ya miƙe tsaye, kallo ɗaya zaka masa ka gane cewa yafi duka yaran ajin a haife, dan da gani ba sa'ansu ba ne, a hakan da ya ke ma zai iya kaiwa 24.

“ Shut up my friend!!” 

Ɗif!, dariyar ta ɗauke, Uncle Bala ya kalli uchenna, wanda kansa yake ƙasa rai a haɗe kamar bai san wata kalma wai ita dariya ba, bayan inde barkwanci ne Uche yafi kowa iya shi a ajin.

“Kafi kowa girma amma kafi kowa koma baya, why Uchenna?, yanzufa kuna second term ne, before you know zaka ga har kun kai third term, kuma kasan cewa a third term ake zana neco da waec, haba Uchenna, ya kamata ace ka gyara, yanzu kai baka jin haushin yanda yara kannenka suke maka dariya ?, kaf nan nasan babu wanda bakafi a haife ba, ya kamata ace ka gyara”.

Da kyar ya gyaɗawa Uncle ɗin kai, yana kawar da kai gefe, Uncle ɗin bai san me Yake tunani bane shi yasa, bai san miye yake hanashi karatu ba shi yasa, kuma shi yanzu Hanam Muhammad Hakuɗau ce baya so taji ana masa faɗan shi yasa yake basarwa, kyakyawar balarabiyar ajinsu.

Kaf yaran ajinsu babu wadda ke burgeshi sai Hanam, saide kuma ita bata ma nuna ta san shi, bata nuna akwai kalarsa a ajin, bama shi kaɗai takewa hakan ba, kusan kowa takewa hakan, ƙawayenta biyu kaf ajin, daga Salma Sa'ad Gashuwa, wadda Suke kira Falaq, sai Iqra Muhammad Ilyas Raja, sukenan ƙawayenta.

Dubansa ya kai inda take zaune, ta kama kanta kamar bata san ana wani abu a ajin ba, ya ɗan cije leb'ensa a hankali, ya ƙudiri cewa yau-yau ɗin nan zai faɗa mata saƙon zuciyar sa.

Hakan kuwa akayi, bayan sun tashi break ya sameta zaune ita da ƙawayenta biyu, kallonsu kawai yayi suka watse, duk da ita i

Iqran bata tsoransa, dan jinin sojane ke yawo a jikinta, mahaifiyarta soja ce, Hanam ta bishi da kallo har yazo ya zauna kusa da ita.

Juyowa tayi ta kalleshi, ita bata tab'a masa kallon kullira ba ma sai yau, Baƙine amma kyakyawa, dan Uche bashi da muni sam, ga tsafta kamar ba Cristian ba, komai tsaf-tsaf, itama ɗin saide ta faɗa masa farin fata, amma ba kyau ba.

“ What ?”

“Au haka ma zaki ce ?, to shikenan let's go straight to the point, ina sanki Hanam, shine abinda nazo na faɗa miki, kuma ina fatan zaki karb'eni”.

Wani irin kallo na baka da hankali ta masa sannan ta miƙe tsaye.

“So you think we are joking ?” 

Shima sai ya miƙe tsaye, ta ɗan ɗaga kanta ta kalli fuskarsa dan Uche akwai tsayi ba laifi.

“What do you mean Haman ?”

“ I mean nida kai bazamu tab'a zama ɗaya ba, hanyoyunmu mabanbanta ne, ba addininmu ɗaya ba, muna da banbanci Uche, tun ba yau ba nasan cewa sona kake, amma kayi haƙuri soyyaya tsakaninmu abune mara yiwuwa, dan bazamu tab'a zama ɗaya ba”

Tana kaiwa nan ta tafi ta barshi a wajen.

*** 

Har yanzu bai manta ranar ba, dan daga ranar bai sake ganinta ba sai yau, to yama za'ayi ya manata ranar, nan take wani abu da ya daɗe da mantawa da shi ya dawo masa, wani hoto da yaso yayi deleting ɗinsa daga kwakwalwarsa ya dawo, yan da mahaiyarsa ke kuka a ranar

_“Na tsaneka Uche, Allah ya tsine maka”_ 

Sai kuma tsinuwar ta shiga dawo masa tunaninsa, yanda yake tsine masa a mabanbanta lokuta.

_“Kai tsinanne ne”_

_“Allah sai ya tsine maka”_

_“Ba zaka tab'a ganin daidai ba a rayuwarka”_

_“tsinuwata ce za tayi ta bin ka”_

*

“Hello!!”

Firgigit ya dawo daga tunanin, kamar wanda lantarki ta kama.

“Are you okay ?” 

Muryarta ce ta tambaya, shekaru kusan bakwai kenan, amma kammaninta na nan yanda suke, bata sauya komai ba sai girman da ta ƙara, to amma me yasa bai gane cewa Abba shine mahaifin ta ba ?, ko ta sunansa ya kamata ace ya gano hakan ?, shi yanzu ta tuna da shima ma ?, ba lalle ace ta tuna dashi ba, wata ƙilama tayi aure abinta.

Shi kuma tun bayan ita bai kara san ko wace yarinya ba, duk da ƴan mata da yawa sun sha kawo kansu gareshi amma baya kulawa, Hanam kawai ya so, kuma baya jin zai sake san wata bayan ta.

“Yeah i am okay” 

Muryar tasa ta fito cikin wani irin sauti wanda bazaka fahimci komai a cikinsa ba.

“ Mr. Uchenna Franklin right ?”

A hankali ya gyaɗa mata kai, Hanam ta shiga nazarinsa, tabbas ta gane shi, shine Uche wanda sukayi makaranta tare, wanda giyar yarinta tasa yazo yace yana santa, dan ita a ganinta kawai wannan yarinta ce ba komai ba, duk da ya sauya ya ƙara girma kammaninsa sun ɗan sauya kaɗan, amma ta gane shi.

Saide kuma ba wannan ne abun da yasa take nazarinsa ba, tana nazarinsa ne sbd muryarsa ta yanzu, kamar ta tab'a jin muryar a wani wuri, saide ta kawar da tunanin.

“Ok tam da fatan Abba ya yi maka bayani ?”

“e

“Eh ya yi min bayani, yaushe zamu fara dinkin ?”

“Zuwa gobe, yau zan sa a kaika ka zagaya fashion house ɗin kafin ka fara aiki”

“To....”

kafin ya faɗi wani abun, yaji wani dan karamin hannu ya riƙo ƙafarsa ta ƙasa, a hankali ya sunkuya ya kalleshi, Damm! wani bangaren na glashi ya fado a zuciyarsa, ganin wani yaro me tsantsar kama da matar dake zaune a gabansa, babu ta yanda za'ayi ka kalli yaron kace ba jininta bane. Yaron kamashi yayi yana jan kafarsa, a hankali ya kai hannu ya ɗauko yaron ya ɗora akan cinyarsa.

“Yaron ki ne ?”

Ya faɗi yana masa wasa

“Eh, yaro nane”

“Shine na farko ko na uku?”

Ta ɗanyi wani gajeren murmushi, har yanzu Uche bai sauya ba.

“Shine na biyar”

“Miye sunansa ?”

“ Muhammad aryaan, arya”

“Wow what a wonderful name”

Arya ya kama gemun uchenna yana ja

“Kai! kai! bari, wannan me tsada ne, hala babanka baya dashi, shi yasa kake tab'a min nawa” 

Ya faɗi yana kama dan karami hannunsa.

A karo na farko zuciyar Hanam ta motsa akan maganar mahaifin Aryaan, kowa kallon shege yake masa, babu wani wanda ya tab'a magana akan mahaifinsa kamar haka, wata ƙila shima Uchen dan be sani bane.

Yana kallon reaction ɗinta, kuma nan take ya fuskanci cewa akwai matsala game da yaron, kode mahaifinsa ya rasu, ko kuma dai akwai wata a ƙasa.

“Baaaabaaaaa” 

Daga Hanam har Uchenna kallon Aryaan suke da tsantsar mamaki, Hanam bata tab'aji yayi magana haka ba, saide gwaranci amma baya magana haka, ko Mama bai iya cewa ba amma gashi yana kiran wani Baba, Baba ?.

“Baba ?, kode ina kama da babanka ne ?”

“Kalisa zata zo ta zaga da kai, thanks for concern” 

Hanam ta faɗi dan ta dakatar da bugawar da zuciyarta ke shirin yi, sai Uche yayi murmushi, ya miƙe ya zagaya inda take ya bata Aryaan ɗin, sannan ya shafa sumar kansa me taushi.

“God bless you my boy”

daga haka kuma fice, Hanam tayi wata iriyar ajiyar zuciya tana dafe kirjinta.

“Ya'ani inta manak zau'u, bit ɗalla'a ala hada garib wa tuƙullu Baba, badal ma tafda'a ma'a ismi ana”

(Gaskiya kaikam baka da kirki, kawai sai ka kalli mutum ka kirashi Baba, memakon ka fara da kiran sunan).

Kamar wani Babba idan yayi abu haka take masa faɗa, harda wata harara, sai kuma ya bata dariya ganin yanda yayi lamoo yana kallonta, shima tanayin dariyar ya bangale nasa wawulon bakin, Hanam ta aje shi akan table ɗin kayan aikinta sannan tayi pecking kansa tana shafa sumar kan nasa.

”Abu ummu inti galiz”

(Baban mama baka jin magana)

A hankali ta rungumeshi.

MARYAM POV

Bata ankara ba har famfon sink ɗin ya cika robar dake hannunta har yana zuba, saurin kai hannu tayi tana kashe kan famfon, a hankakali ta juya ta kalli kitchen island ɗin, wanda ta cika shi da kayan kitchen ɗin, dan so take ta sauyawa komai ma'aji, amma gaba ɗaya ta kasa, tunani ne fal ranta, tayama zata iyayin wani ƙwaƙƙwaran aiki ?.

Tatuna abinda yace mata jiya, dan second daya...... biyu....... 

LA na ukun ne wayarsa dake kan coffee table tayi ringing, kusan tare suka kalli screen ɗin wayar, 'NEHA' shine abinda aka rubuta, a gaban sunan kuma akwai heart emoji, gaban Maryam yaci gaba da buga a lokacin, wayar ya ɗauka ya miƙe, har ya kai kan stairs sai ya juyo ya kalleta a inda ya barta.

“An kawo kayan abinci, suna kitchen kije ki duba ki gani, idan akwai abinda babu sai ki faɗamin” 

Cikin karfin hali Maryam ta gyaɗa masa kai. 

Tana jin ya ja kofar ɗakinsa itama ta miƙe harda gudu ta shiga kitchen ta ɗauki abuncin ta data dafa na dare, ta koma ɗaki ta kulle.

Sai kuma ta tsun duma duniyar tunanin cakuɗɗaɗun zatukansa, wanda babu abu ɗaya data tsinta a ciki, gaba ɗaya zantukan nasa sun ɗaure mata kai, wai me yake nufi da shi annoba ne ?, me yasa zai kira kansa da monster?, kuma beast?, dama mutum yakan zama dodo ?, kode yayi hakan ne dan ta nisance shi ?, to amma Fulani ta faɗa mata makamancin hakan.

Kode dan yana so ya auro wannan Neha ɗin ne yasa yace mata haka ?, kai bama haka bane, koma de miye shi yasani, amma kuma a can ƙasan zuciyarta a tsorace take, dan Maryam gwanar tsoroce, saide tunanin zata koma makaranta, dana kayan abincin daya ƙara cika store ɗin da shi sai ya kore wannan tunanin, tunda de har yace ta nisance shi, kuma yace ta riƙa kulle kofa ai shikenan.

Amma kuma duk da haka abincin data ɗauka bata samu ta ci ba, bacci ma da ƙyar tayi, daga ta ɗanji motsi zata farka, da haka har gari ya waye, kuma taji sanda ya fita masallaci, sai a lokacin ta sauƙo kasa ta mayar da abincin kitchen ɗin.

Sannan ta shiga store ɗin aje kayan amfani na gidan, ta ɗauko broom da squeegee da mop ta koma saman, ta share ko ina a ɗakinta ta goge, ta wanke toilet ma, haka balcony, ta buɗe curtains ɗin tana kallon yanda hasken rana ke baza duniya.

Ga tsirarin mutane na kai kawo, sannan ta dawo cikin ɗakin, kuma bata fita ba saida taji ya dawo daga masallaci, sannan ta fito, ta share corridor ɗin nan tayi moping sannan ta saka squeegee ɗin nan ta goge glass ɗin balcony ɗin.

A wajen taga abincin akun nan ta zuba mata harda ruwa, sannan ta ɗauko watering can, tayiwa flowers ɗin dake wajen bayi, kana ta sauƙo ƙasa, parlon ma ta gyarashi sosai harda wajen daning, dama store da ironing room, sannan ta shiga kitchen, kuma shi har yanzu bata gyara shi ba sbd so take sai ta gama shirya kayan cikinsa kafin ta gyara shi.

Da wannan tunanin ta ƙaraso island ɗin, ta ɗauko wasu gajerun kwalabe na glass wanda tasan cewa na species ne, ta riƙa juye kayan species ɗin har saida ta gama, sannan ta janyo wata cabinet guda haka ta jerusu.

Sai kuma ta dawo kan glass cups da smoothie jars da kuma mugs, suma ta jeresu a loka guda, tanayin aikin zuciyarta na washewa da farin ciki, plate da bowls ma nasu wajen da ban, sai kaysn stainless steel cooking utensil set, ta aje su kusa da stove, oil containers din data zuba mai a cikima ta aje su kusa da set din.

Knife set ma a wajen ta aje shi, sai frying pan, work, set ɗin tukunya duka ta aje su a waje guda cikin wata cabinet, blender, greater da juicers suma tai musu ma'aji, kayan shayima su bournvita da su lipton ta sauya musu mazubi zuwa wasu containers na glass. 

Sai da ta tabbatar da komai a killace yake sannan ta shiga share kitchen ɗin, kayan fridge ɗin ta barsu sai ta gama sharar.

Bayan ta gama sharar ta goge ko ina, sai kuma ta tsaya tana bin ko ina da kallo, wai ita zata nayin girki a wannan kitchen din, abun is un believable.

Fridge ɗin ta buɗe ta fitar da gaba ɗaya tarkacen ciki duka har karafen fridge ɗin, ta wanke su sannan ta meda su ciki. Ta ware kayan fruits ta sakasu a cikin wata roba wadda ta gani a cikin fridge ɗin, kayan ganyema ta ware musu gu.

Ta ɗauko ma'ajin ƙwai, duka ƙwan da aka kawo wajen cret biyu haka ta jereshi a wajen sai taga harda space, kayan miya ma ta ware su da ban, kayan drinks kuma su ta fara sakawa a sama, su miones, bread gesha da dai sauransu duk ta killace komai.

Sannan ta rufe fridge ɗin, ta koma store ɗin, tana duba gaba ɗaya kayan girkin, albasa, doya da dankali dama tun da farko saida ta ɗebo ƙasa a garden ɗin ta zuba a ƙasa sannan ta sakasu a kai.

Ta san cewa zai je aiki, dan haka ya kamata ace tayi masa girki, dan haka tayi niyyar dafa masa wani abun me sauƙi idan har zai iya cin abincin data girka.

Sai kawai tayi niyyar yin sandwich da pancake, babu b'ata lokaci ta shiga aikin, tana ganin abun kamar mafarki, girki na ɗaya daga cikin abinda take so kuma yake bata nishaɗi, dan haka gaba ɗaya ko wace damuwa ta nemeta ta rasa.

Ta meda hankali sosai akan aikinta, sandwich ɗinma a sandwich maker tayi, cikin ɗan ƙanƙanin lokaci ta gama komai, sbd akwai kayan aiki.

Tana haɗa hot chocolate taji alamun ana ƙoƙarin buɗe ƙofar. Gabanta ya faɗi, dan tasan ba kowa bane face shi, dan haka ta juyo da sauri, a dai-dai lokacin da shima ya buɗe ƙofar yana kallonta.

Kamar jiya sanye take da hijabi, kuma tun daga ƙofar kitchen ɗin ya soma sauraron abinda ya zame masa wajibi, bugun zuciyarta, yasan cewa tabbas yanzu bata da abin tsoro daya wuce shi, tunda har ya faɗa mata waye shi.

Bai damu da tunanin da zatayi akan sa ba, amma yasan abinda yayi shine dai-dai, dan ya zama dole ya faɗa mata gaskiya.

Kuma jiya bayan wayarsa tayi ringing ya ɗauka ya koma dakinsa ya daga, kanwarsa ce Neha, wadda take da aure a abuja. Sun jima suna waya har ya faɗa mata cewa yayi aure itama ta gama masa ƙorafi na yayi aure bai sanar musu ba, ya bata haƙuri kafin tace wai ya bawa matar tasa waya su gaisa, shi kuma yasan a lokacin ba lalle ta iya tsayawa a gabansa ba, wata ƙilama idan ta ganshi zuciyarta ta buga gaba ɗaya kowa ya huta, dan haka sai yace mata tayi bacci ta bari sai gobe zai haɗa su.

Bayan ta kashe kuma saiga kiran Daadi, kakarsa wadda ta haifi mahaifiyarsa kuma ita tana zaune ne a india, ita kuma faɗama ta shiga masa, kuma bama shi kaɗai ba harda me martaba take haɗawa.

Tana faɗin ai shine ya masa auren, dan bai basu muhimanci ba shi yasa bai faɗa musu ba, dan kar su aura masa ƴarsu shi yasa su suka aura masa tasu yar.

Saida ya fahimtar da ita cewa auren ya farune cikin gaggawa sannan ta kwantar da hankalinta, amma tace masa dole yazo india, ya faɗa mata cewa yana da aiyyuka da yawa, tace masa kada ya kuskura ayi bikin holi ba tare da yazo india ba, ya rantse tare da mata alkawari, kuma tace sai ya nuna mata alkawarin nasa, shi kuma yace zai tabbatar mata ta hanyar tara gashi a kansa bazai yi aski ba sai ranar daya zo india, da haka hankalinta ya kwanta, har tace ya gaida matar tasa daga haka wayar ta ƙare, kuma yayi mamaki daya ga wutar ɗakinta a kunne, dan kusan kwana yayi yana sauraron rabin ransa.

Kuma yauma da safe yaga wutar ɗakin nata a kunne, yananjin sanda take moping corridorn ma, yanzun ma ya fito ne cikin shirinsa na zuwa aiki, kuma shi bai iya riƙe yunwa ba.

Dan haka ya fito dan yaci abinci, a nan ne yaga ko ina na gidan ƙal ta share ta goge.Sai kuma gashi ya ganta a kitchen.

“Ina kwana” 

Muryarta ta fito cikin sanyinta, kuma haka kamar da tsoro a ciki, ya fara takowa cikin kitchen ɗin yana amsawa da

“Lafiya, fatan kin tashi lafiya ” 

Muryar tasa ta fito da wani irin sauti fayau, bazaka tsinci komai a ciki ba, Maryam ta miƙe tana faɗin.

“Lafiya” 

Store taga ya nufa, jim kaɗan ya fito sai ta ganshi da kayan girki, kenan abincin zai dafa, da ƙyar tayi ƙarfin halin faɗin.

“Ga abinci fa na girka maka” 

Cak ya tsaya da kunna wutar da yake, a hankali ya juyo ya kalleta yayin da ita take tsaye a jikin island tana hada hot chocolate a cikin wata jar, ya kalli plate ɗin dake kan island ɗin, abinci ta dafa masa?, shi ta dafawa abinci ?, wata kulawa da baya samunta sai idan yana india, amma a nigeria kam saide idan abuja yaje, dan tun yana yaro koda sau ɗaya Fulani bata tab'a masa girki da kanta ba, saide ta sa bayi su masa.

“Ke da kanki kikayi ?” 

Yayi tambayar ba tare da shi kansa ya san ya yi ta ba, kanta a ƙasa ta gyaɗa masa kai, sai ya fara takowa zuwa island ɗin, gaba ɗaya kamshin turaren sa ya cika mata hanci, kuma yauma kamar kullum sanye cikin kayan hausawa yake.

Wata shaddace a jikinsa Kansa kuma babu hula, wannan kyakyawar sumar tasa tare a kansa, saida ya kai hannu ya shafa sumar tasa yana kallon abincin, ashe a ƴan area irin tasu akwai wayyayu kamarta ?, gaskiya ta fita da ban.

“Nagode” 

ya faɗi yana zama akan ɗaya daga cikin kujerun dake zagaye da island ɗin, Maryam ta kasa gaskata abinda taje ji, godiya fa yake mata, gaskiya wannan abun azimun ne, kai kawai ta gyaɗa masa, bayan ta haɗa hot chocolate ɗin ta miƙa masa.

Sai yanzu ya kai hannu ya ɗauki sandwich ɗin ya kai bakinsa, saida ya lumshe ido, sannan yaci gaba da taunawa, daɗin abinci mara misaltuwa ne, ta iya girki sosai, ya cinye na hannunsa tas.

A lokacin ita kuma ta ɗauki nata ta bar masa kitchen ɗin bayan ta jere kayan da tayi amfani da shi a dish washer, dan bazata iya zama ga ta ga shi ba, yace su nisanci juna, to hakan take ƙoƙarin yi.

Tafida baisan ya cinye abinci ba saida yaga plate ɗin babu komai, sai kuma ya dawo kan hot chocolate ɗin, shima ya shanye tas, bai cika cin abinci da yawa ba, amma yau yaci sosai, ya miƙe ya buɗe dish washer ɗin sannan ya saka plate da jar ɗin a ciki.

Ya buɗe freezer zai dauki ruwa, ya tsaya yana kallon komai a tsare, a ransa yace gyara da daɗi, dan shi ba wani bi takan kitchen ɗin yake ba, ya ɗauki ruwan ya sha sannan ya rufe.

Fita ya yi, ya koma ɗakinsa ya ɗauki wayoyinsa da hularsa da key ɗinsa ya dawo ƙofar ɗakinta ya ƙwanƙwasa.

Maryam na cin abinci ta miƙe ta saka hijabinta ta buɗe masa ƙofar, kuma kamar kullum gabanta na bugu.

“Zanje asibiti ne” 

shine kawai abinda ya faɗi bayan kofar ta bufe maryam ta bayyana a gabansa, kamar zata tambayeshi me zaije yi asibiti sai ta tuna ashe likita ne.

“A dawo lafiya, Allah ya tsare”

“ Ameen, thanks for the meal”

Ya faɗi yana juyawa, kamar jiya yau ma maryam tabi bayansa da kallo, tana gode masa itama a ranta.

__________________________

_Ehem ehem, nace ba, kamar fa nima na fara zargin Hanam game da Arya, anya kuwa ba shege bane kamar yanda kowa yake fada?, ko dan, bari nayi shiru, kada nima a sammin mari😁_

_Hajiya Maryam, Barka dai, wai mrs zak's tace daga kinji birin ko fito ko duba kiga me ke goin😁_

_Nagode masoya, Allah ya kara mana son juna, Nagodr da addu'oin ku_

🌸-SAI KASKA CE✍️-🌸.


⭐️YADDA ƘADDARA TA SO⭐

⭐️ شاء القدر⭐️

*Magical love story*

©By Sai Kaska

Wattpad @Sai_Kaska

Phone number:***

Arewabooks @18saikaska

_________________________________

*Proud of my first novel*


★TAURARI WRITER'S ASSOCIATION★


*Wannan babin naki ne Habeebty*

*BABI NA GOMA SHA SHIDA(16)*

UCHENNA POV.

Yau kwanan sa uku da fara aiki a HANAM FASHION HOUSE, kuma aiki a wajen na masa daɗi, shi da Hanam suke zana ɗinkin da za'ayi, amma kullum tana faɗin nasa yafi kyau, kuma a kullum zeyi ɗinki cikin yabawa take.

Amma kuma ya lura da wasu sabbabin ɗabi'u da take da su, bata sakarwa kowa fuska, duk da dama can haka take, amma kuma na yanxu yafi na da ɗin, kuma a yanda ya lura bata da aure, hakan yasa ya tambayi wani Aminu a wurin, wanda yake kawo masa kayan aiki idan ya buƙata.

Kuma Aminu ya faɗa masa cewa, suma haka suka ganta da ɗan, daga tafiya USA na shekara biyu sai gata ta dawo da wa, kuma har yau iƙirari take kan cewar itace uban ɗan, abun yaso ya ɗaure masa kai, dan haka yayi niyyar tambayar Abba.

Yana zaune a office ɗin da aka bashi domin ɗinki, bayan ya gama dinka wata riga sai ya ɗauki break yana shan coffee, kawai sai yace bari ya kira Abba ya tambayeshi, tunda basa samu su hadu.

“Abbana”

Cewar Uche bayan Abba ya ɗaga kiran kuma sun gaisa.

“Na'am ɗana”

“Tambayarka na ke sanyi” 

Ya faɗi yana kallon windown daya buɗe, hannunsa na dama rike da mug.

“Faɗi ɗan Abbansa, ina jinka”

“Abba.....” 

Sai kuma yayi shiru, shi sam bai iya ƙunbiya-ƙunbiya ba, idan yana so ya faɗi abu kansa tsaye ya ke faɗarsa, amma yanzu sai ya ji nauyin Abban, sai ya tattaro ƙarfinsa ya furta abinda zai zama sanadiyyar sauyawar ƙaddararsa.

“Abba ni Hanam ta tab'a aure ne ?” 

Abba beyi mamakin tambayar ba, dan tun a ranar da Uche ya fara zuwa HANAM FASHION HOUSE ɗin ya faɗa masa cewa ai ya sana Hanam sun tab'a yin aji ɗaya a secondary.

“A'a haris, bata tab'a aure ba”

Uche yayi wata b'oyayyar ajiyar zuciya, amma duk da haka saida Abba ya ji, Abba yayi murmushi

“Haris”

“Na'am Abba”

“Next week zanje hakuɗau, kuma tare nake so muje” 

Hakuɗau shine mahaifar Alhaji Muhammad.

“Zuwa lokacin na gama aiki a nan, ba matsala zamu iya zuwa”

“Eh nasan zuwa lokacin ka gamawa Hanam aikinta, kawai na faɗa maka ne dan ka shirya”

“To Abbana, Allah ya kaimu”

“Ameen ɗan albarka na” 

Kuma daga haka wayar ta ƙare, Uche ya aje mug ɗin hannunsa akan wani table, sannan ya dawo ya ɗauki measuring tape, ya shiga auna wani yadi, zuciyarsa fal tunane-tunane iri-iri.

Kuka yaji, kuma yasan cewa babu me kukan bayan Arya, dan ɗakin da ake renonsa kusa da office ɗin sa ne, Allah ya sani tun daga ranar da yaron ya riƙe ƙafarsa ya shiga ransa, dan haka da sauri ya aje yadin da measuring tape ɗin duka ya fice da sauri ya faɗa ɗakin.

Ya iske Naani ɗin nasa ta na rarrashinsa shi kuma sai kuka yake, gaba ɗaya ya rikita Naani ɗin nasa.

“Kinga kawo shi” 

Ya faɗi yana miƙa mata hannu, miƙa masa shi tayi, shi kuma ya karb'eshi ya fice daga ɗakin.

Office ɗin nasa ya koma da shi, ya shiga rarrashinsa, amma yaƙi shiru, sai kawai Uche ya ɗauki wani zanin atamfa daya yanka ya goyeshi, yana jijjiga shi.

Tunda Aryaan yazo duniya ba'a tab'a masa goyo irin wannan ba, dan Hanam bata goyonsa saide ta sakashi a baby carrier, nan da nan yayi bacci.

Hanam taji kukan Arya hakan yasa itama ta fito domin taga abinda yake faruwa, sai Naani ɗin ta faɗa mata cewar ai wannan na ɗayan office ɗin yazo ya karb'eshi, dan haka Hanam ta fita, ta shiga office ɗin Uche.

Samunsa tayi yana kai kawo da Aryaan ɗin a bayansa, kuma gashi ya goye shi, wani abu ya motsa a kirjinta, wanda rabonsa da ya motsa tun shekaru biyu baya, sai ta kawar da tunanin, dan a ganinta abun ba meyiwuwa bane, ita sai abun ma yaso ya bata dariya, namiji da goyo, kuma ya iya goyon ko dan igbo ne oho.

“Yanzu Uche da atamfar dubbunan kuɗin ka goyi yaro ?” 

Ta faɗi tana shigowa ciki, shi sam ma bai kalleta ba.

“Me zai hana idan de boy ze yi shiru, idan yana kuka bazan iya aiki cikin kwanciyar hankali ba”

Hanam taji wanna abun yaci gaba da motsawa, kuma wannan irin wanda tavjine lokacin da ta haifi Arya ɗin.

“Naga ya yi bacci kawo shi, kar ya hanaka aiki”

“Ba dole yayi bacci ba, yaji goyo, nasan yanzu haka ba goyonsa kike ba” 

Ya faɗi yana ƙoƙarin since zanin goyon.

“Na miye zan wani zo ina goyonsa, ai baby carrier ɗin shine dai-dai shi”

Ta faɗi a lokacin da ya miƙa mata shi, daga haka kuma ta fice daga wajen, Uchenna yabisu da kallo su duka, yana murmushi ya dawo yaci gaba da aikinsa.


*ALARO CITY, BLOCK 3, HOUSE NO 122*

*Da misalin karfe 06:00pm*

Maryam ce tsaye a cikin kitchen ɗin gidan, meat pie take haɗawa, dan yau da safe Tafida ya faɗa mata cewar an gama komai na makarantar ta dan haka gobe za suje tare a ƙarasa sauran abubuwan.

Yanayin murnar da take ciki sam bame kwatantuwa bane, lokacin da aka ɗaura musu aure kowa faɗi yake cewa tayi sa'a duk bataga sa'ar da tayi ba sai yanzu, a yanda ta fahimta shima sam baisan da auren ba, amma kuma haka ya haƙura ya karb'i auren nasu hannu biyu.

Kuma babu abunda ya rageta da shi, komai yana mata, bata da wani abunyi sai godewa Allah da kuma shi Tafidan, data fusakanci baya san tana gode masa sai ta samo wata hanya ta gode masa da ban, Ta lura da yanada san cin abinci, kuma yana san abincin da take girkawa dan haka sai ta ke gode masa ta hanyar abinci.

Kullum da safe sai ta tsantsara masa girki na gani na faɗa, da yamma ma haka, dama na rana baya ci a gidan, duk girkin da take dashi a wayarta shi take masa, kuma dama ita gwanace wajen girki, kuma ta lura da yana jin daɗin girkin nata.

Sbd zata fara zuwa makaranta yasa yau ta yanke shawarar musi meat pie da cake, sbd koda zata makara da safe wata rana, Sai su samu su rage hanya.

Kuma shekaran jiya yace mata taje su gaisa da matar maƙocinsu, kuma taje ɗin dan harma ta ɗan jima a gidan dan matar tana da kirki, duk da ta girme mata a shekaru, dan zata iya fin Anti Fati ma.

So take tayi ta gama soya meat pie ɗin kafin magariba tayi, dan cake kam tuni ta riga ta gama shi, shima meat pie ɗin kaɗan ne ya rage. 

Kuma kafin magaribar ta gama soya shi tas, ta juye a wasu containers masu kyau, ta zuba cake biyar meat pie shida a wani ƙaramin kwano me murfi, wanda zata miƙawa Maman Ilham, kamar yanda matar tace mata shine sunan ƴarya ta farko.

Ta zuba gaba ɗaya kayan data b'ata a dish washer, dan bata wani wanke-wanke, komai cikin sauƙi take yinsa, ta goge duk inda ta b'ata, sannan ta ɗebi warmers ɗin data zuba abincin data girki, ta fita daga kitchen ɗin.

Ta jerewa Tafida nasa akan danning table, sannan tayi sama. Sallar magariba ta gabatar, sannan ta ƙara sauƙowa ƙasa ta ɗauki wayarta dake chargy a parlo, ta ɗauki wannan kwanon data zubawa Maman Ilham meat pie ɗin, ta janyo ƙofar parlon ta fito compound ɗin gidan.

Sai da ta kalli parking lot ɗin gidan, motocin Tafida ne guda biyu kawai, dan ya fita da guda ɗaya, ta buɗe ƙaramar ƙofar gare ɗin ta fito.

Bata damu da ta kulle gidan ba, dan a ganinta babu wanda zai iya shiga gidan bare har yayi sata, ta tsaya tana kallon kyakyawar unguwar tasu, yanda take da kyau da daddare, bata tab'a fitowa da daddare ba sai yau, dan last time data fito har ta shiga gidan Maman Ilham ɗin da rana ne, kuma shine fitarta na farko, sai kuma yau a gaba ɗaya zamanta a unguwar wurin kwana shida, saide ta ganta ta saman balcony.

A hankali ta shiga takawa har zuwa ƙofar gidan dake jikin nasu, wanda yake shima sak nasun yake, ita ranar data shiga gidan ma tayi zaton zata ga komai na ciki irin nasu ne, amma sai taga hatta da ginin cikinma irin nasun ne amma banda kayan cikin.

Kanta tsaye ta tura ƙaramar ƙofar ta shiga, dan ta lura da gaba ɗaya gidajen unguwar basubda masu gadi. 

Sai da ta ƙwanƙwasa ƙofar parlon gidan, sannan aka buɗe, Ilham ɗin ce ta buɗe mata ana gaisheta, itama Maryam ɗin ta amsa mata da fara'a

“Ilham waye ne ?” 

Muryar Maman Ilham ɗin ta tambaya daga cikin parlon, Ilham ɗin ta buɗe kofar gaba ɗaya tana faɗin.

“Anti Maryam ce”

“To ta shigo mana, sai ta tsaya a waje?”

Maryam ta shigo tana murmushi, Maman Ilham ɗince a parlon ita da sauran yaran nata biyu, aliyu da abdul, ta zauna a sanda suma suke gaishe ta, sannan suka gaisa da Maman Ilham ɗin.

“Maman Ilham meat pie ne nayi, shine nace bari na kawo miki a bawa yara”

“A'a to an gode” 

Maman Ilham ta faɗi tana karb'ar bowl ɗin

“Gobe zan fara zuwa makaranta”

“Tanan ALARO zaki fara zuwa ?”

“Eh” 

Maryam ta amsata kanta a ƙasa kamar yanda ta saba.

“To Allah ya temaka, Allah ya bada sa'a Maryam ”

“Ameen, ni zan koma” 

Take miƙe

“Har zaki koma?”

“Eh magariba ta yi, nasan ya kusa dawowa ”

“Hakane kam, Ilham tashi ki rife mana ƙofar”

Ta ƙarashe tana kallon ilham ɗin, lokacin Maryam har ta kai bakin ƙofa.

Tun daga fitar ta daga gidan su Ilham ɗin ta hangi motar Tafida sai kawai ta tsaya a ƙofar gidan har ya ƙaraso, ya buɗe gate ɗin da wayarsa sanna ya shiga da motar.

Amma bai kulle gate ɗin ba dan ya ganta shima, fitowa yayi daga motar ya dawo ƙofar gidan inda take, Kuma tun kafin ya ƙarasa inda take ya fara sabbaben nasa, wato sauraren bugun zuciyarta, wani abu da ya zame masa farilla a kwanakin nan, abun na mugun bashi mamaki, dan yanxu abun ya zame maza jiki.

Idan baya gidan har Allah-Allah yake ya dawo, dan yazo yaci daddaɗan girkinta, ga kuma daddaɗan sautin bugun zuciyarta, wanda yake saka masa nutsuwa a koda yaushe, a da daga asibiti sai gida sai kuma filin wasan cricket, bashi da wani abu na nishadi bayan cricket ɗin.

Amma yanzu an samu sauyi, zuwan Maryam rayuwarsa ya sauya abubuwa da dama, ya koma wani Tafidan da ban da na da, yanzu ya koyi yawan cin abinci, sab'anin da, da ba sosai ya cika cin abincin ba, sbd shi bai cika san cin abincin waje ba, yafi so ya girka da kansa, wani lokacin a makare yake tashi baya samun damar yin girkin.

Da yamma kuma ya dawo a gajiye wataran saide yaci bread kawai ya sha ruwa, amma yanzu a kullum so yake tace masa ga abinci, dan ya samu yaci daddaɗan girkinta, shi yana mamakin yanda kanta yake a waye, ga yanda ta iya girki, har tunani yake ma wata ƙila tayi makarantar koyon girki ne.

Ga kuma yawan sauraren waƙa da yake a da, amma banda yanzu, sam sauraren waƙarma baya gabansa, wannan bugun zuciyar tata, shine ya zame masa kamar waƙar, wani lokacin sai ya raba dare yana saurarensa, koda tana ɗakinta yana iya jiyoshi.

Saide idan tana ƙasa ne, amma middin tana ɗaki to zaiji yanda zuciyarta ke bugawa, kuma har yanzu idan yana tsaye a gabanta zuciyarta na bugawa cikin tsoro.

Sai kuma wani abu dake faruwa da shi, rabon da baƙin ruhinsa ya tashi tun yana haɗejia, kuma hakan ya bashi mamaki, duk da a wasu lokutan idonsa na sauya kala, duk da a da can baƙin ruhin baya tashi sai idan an b'ata masa rai.

Shi kuma abu mawuyacine ke b'ata masa rai, a kwanakin nan ne abun yayi ƙamari, amma kuma yanzu gashi ya tafi, Sannan har cikin ransa yake fatan Allah yasa ya tafi har abada. Sai de kuma shi da kansa yawan cewa yana nan, babu inda ya tafi, Dan akwai wannan super natural ɗin a jikinsa.

Ko kaɗan baya fatan wani abu da zai cutar da Maryam, musamman ma ace daga gareshi ne. Gaskiya Muktar ya faɗa, tabbas yayi dace, dan Maryam ɗayace tamkar da dubu, samun irinta a wannan zamanin sai an tona.

“Sannu da zuwa” 

Muryarta ta fito cikin sanyinta, kuma yaji sanda zuciyarya ta buga, ya samu kansa cikin irin yanayin da yake tsintar kansa a duk lokacin da ya saurari bugun zuciyar tata cikin tsoro ko nishadi koma murna.

“Sannu Daaso, gidan Mustapha ki ka je ?”

Daaso ?, shekaran jiya ya fara kiranta da sunan, wata ƙila dan nishaɗi yake kiran sunan, Mustapha kuma ta san sunan mijin Maman Ilham ne, dan haka ya faɗa mata ranar da yace mata taje gidan.

“Eh, nan naje, banma jima ba yanzu na shiga kuma na fito” 

Ya ɗan cije lips dinsa kaɗan, sannan ya gyaɗa kansa a hankali.

“Hira ki ma je ku kayi?”

“Ko kaɗan, nayi meat pie ne, shine na kai mata nace a bawa yara” 

Yanzu ma kansa ya gyaɗa sannan yace.

“Muje ko?” 

A hankali ta fara takawa zuwa cikin gidan, ya tsaya a wajen yana kallonta, sannan ya rufe gate ɗin, ya shigo gidan shima.

Bai sameta a parlo ba dan haka yayi saman shima, wanka kawai yayi dan yayi Sallah a hanya, ya saka wasu jogger set farare, ya rufe kansa da hular hoodie ɗin kayan, ya sauƙo ƙasa, cike da farin cikin zai ci girkin Maryam.

Kuma kamar yanda ya zata ɗin ne, ta aje masa komai akan danning, ruwan shansa da abincinsa yaga yau harda juice a wani jug na glass.

Bai san sanda murmushi ya sub'uce masa ba, to shi kuwa miye ba zeyiwa wannan innocent soul ɗin ba ?.

Kujera ya ja ya zauna, sannan ya buɗe plate ɗin da ta aje, ya buɗe warmer ɗin farko, wadda yake da tabbacin miyace a ciki, kamshin spices ne suka fara shiga hancinsa, kafin yayi arba da cabege sauce, kalar cabejin daya hadu da attaruhu da tattase sune sukafi ɗaukar hankalinsa.

Harda haɗiyar yawunsa, sannan ya aje murfin a gefe, ya janyo ɗayar ya buɗe ita kuma farar shinkafa ce a ciki, wadda ta dafata da carrots da kuma green beans.

duka ya juye shinkafar a plate ɗin, sannan ya zuba miyar, ya hauci yana ta lumshe ido, da ace yana da yawan magana da wata ƙila santi zeyi, dan abincin nata ya kai a masa santi.

Yana ci yana haɗawa da strawberry juice ɗin da ta aje masa, har ya cinye tas, dan dama bata tab'a zuba masa abinci ya rage ba. Tashi yayi ya shiga kitchen ɗin, ya buɗe dish washer sannan ya jere mata kayan a ciki.

Har ya juya zai fita kamshin wani abu ya bigi hancinsa, ya waiga ya waiga sai hango wasu containers guda biyu kusa da stove, beyi tunanin komai ba ya nufi wajen.

Ta farko ya buɗe yaci karo da meat pie, hannu yakai ya ɗauki guda ɗaya ya kai bakinsa, ya cinye shi tas, sai kuma ya rufe mata.

Ya buɗe ɗayar ita kuma cup cakes ne a ciki shikam guda biyu ya ɗiba ya cinye shi duka, a ransa yake faɗin, Maryam na so ta maida shi acici. (kujini da ɗan raini😁).

Rufewa yayi ya maida mata ya aje sannan ya fito, a parlo ya zauna, ya kunna wata tashar da ake nuna wasan cricket, ya kishingiɗa yana kallo, harda ture hular hoodie ɗin, ya shiga shafa sumarsa data fara taruwa, sbd alƙawarin da yayiwa Daadi, hatta wajen fade ɗin ma ya tara gashi.

Ko me ya tuna sai ya miƙe tsaye ya nufi ɗakinsa ya ɗauko wani abu ya dawo ƙasan, yana daga inda yake ya ƙwala kiran Maryam.

Maryam na zaune a ɗaki tana sauraren ƙira'a qur'ani, taji kamar Tafida na kiranta, kasan cewar kunne ɗaya ta saka.

Sai ta cire ear piece ɗin, ta shiga ƙoƙarin danna pause amma sam wayar taƙi bata haɗin kai, haka take mata kwana biyu, ta ɗan ja gajeren tsaki, sai ta tsayar ta jikin ear piece ɗin, ta miƙe hannunta riƙe da wayar ta saka hijjabinta ta fita.

A parlo ta sameshi, sai ta zauna a ƙasa.

“No seat here”

Maryam ta kalli inda yake nuna mata, gefen kujerar da yake zaune a kai ne, kasan cewar kujerar nada tsayi ita kuma sai ta zauna a can ƙarshen kujerar.

Kanta a ƙasa kamar kullum idan tana gabasa, gyaran murya yayi, bayan ya gama saurarar abinda ya saba.

“Kamar yanda na faɗa miki, an gama komai da kamai na makarantar ki, so gobe zamuje tare zamu ƙarasa abinda ya rage...... Nasan zaki buƙaci wani abun na amfanin makaranta, so ni bansan me kike so ba, dan haka na yanke shawarar kawai na baki kuɗin ki siyi kome kike so, dan akwai super market nan kusa da block ɗin mu, zaki iya zuwa ki siyi abunda kike da buƙata”

Ya ƙarashe yana mika mata kuɗin da Maryam bata san adadinsu ba, hannunta cikin hijabinta ta karb'a, kuma hannu biyu

“Nagode sosai, Allah ji ƙan mahaifa” 

Bai amsa a fili ba sai yaci gaba da cewa

“Kina da waya ne ?”

A hankali ta gyaɗa masa kai, tana fito da wayar tata daga hijabi ta nuna masa, saida Tafida ya kusa yin dariya, amma yasan idan yayi zata ji babu daɗi, amma wayar tata ta bashi dariya, like for real matar Tafifa da wannan wayar.

“Daaso wanna ai ba waya bace” 

Dama tasan za'a rina, taya za'ayi Tafida ya kalli wayarta da kima, yana riƙe waya biyu, kuma duk da ba sanin kuɗin wayoyin ta yi ba tasan masu tsadane.

Barinma iPhone ɗinsa, dan wayar ta burgeta ita kanta, musamman ma gefen wayar wani abune aka kewaye wayar dashi kamar gold

“Karb'i wannan, akwai numbers ɗima akai, idan na shirya zan karb'e su” 

Ya miƙa mata Samsung ɗinsa, ƙirar S22 ultra, Maryam ta kalli wayar, sai kuma a hankali ta ɗago ta kalleshi, shima ɗin ita yake kallo, kafin ta kai hannunta ta karb'i wayar, za tai masa godiya ya katseta da faɗin.

“No Miriam, you don't need to be”

Miriam ?, ita kuma haka za ta yi ta samun sauyin sunaye ?.

Ranar haka ta kusan raba dare tana ta shige da fice a cikin wayar, ita wayar tamafi burgeta akan kuɗin da bata ma samu TA ƙirga ba.

Duk da shima kuɗin ta ji daɗinsa, domin bata tab:a riƙe kudi kamar haka ba, ƙololuwar yawan kuɗin da take riƙewa a hannunta shine na registration ɗinta.

Amma ita wayar tafi yin gaba da ita, kuma taga babu sim a kai, saide wasu numbers da basu da yawa, kuma a ciki akwai ta Daadi, Neha, Chaacu Imran (Wato kawu Imran), Chaacu Irfan (Kawu Irfan).

Choti Gulzar (Sieger Gulzar), Ramesh, Arjit, Mahesh, da dai sauranau, yawancin number ɗin na india ne, hakan ke nuna mata cewar da yan uwansa na india Yake waya.

Sai kuma gallery data duba, tarin hotunansa ne birjit, abun har ya bata mamaki, ganin namiji da yawan hoto, ita da take mace ma bata da wasu hotuna na azo a gani, amma nasa kam sai baki take kamawa dan mamaki.

Kuma ciki taga na wadda take kyautata zaton itace Neha da kayan sojoji an musi shi da ita, abun mamakin shine kayan sojijin nigeria ne a jikinta, kuma gata ba india, hotuna dai sai wanda ya manta baiyi ba.

A ciki ma taga wani nasa wanda ya tara gashi a kansa har yayi parking ɗinsa, harda dariyarta, dan style ɗin hoton ya bata dariya.

“Eshaan Tafiida” 

Ta furta muryarta ɗauke da wani irin nishadi da bata san daga ina yake fitowa ba, a cikin daren gaba ɗaya ta ɗebe kayan wayarta ta maida kan wayar, amma bata tab'a masa hotonsa ba ko ƙwara ɗaya, dan wata ƙila ya buƙaci kayansa, amma taji daɗin samun wayar sosai ba kaɗan ba.


HANAM POV.

Cikin sati ɗayan da Uchenna Franklin yayi a ƙarƙashinta sun ƙara samun kusanci, duk da bata fatan ya haura harkar kasuwanci kawai, dan ita dan shi tasa aka kawo shi, bayan nan kuma bata fatan wata alaƙa daban, sbd kamar yanda ta faɗa masa ne a wancan lokacin sunada banbanci sosai.

Kuma cikin sati ɗayan ya gama mata aikin da zai mata, sannan taji daɗin aiki dashi sosai ba kadan ba, dan ya iya ɗinki sosai, kuma bayan sun gama aiki saida ta sake masa tayin karb'ar kuɗi kamar tun sanda suka fara aikin amma yaƙi, kamar de da farkon.

Yace ita ƙanwarsa ce, ba zai karb'i kuɗinta ba, yayi mata ne matsayinta na ƙanwarsa.

An ce komai yayi farko yanada karshe, gashi har yau Uchenna zai bar fashion house ɗin, ya shigo office ɗinta tana bawa Arya custard dan yau Naani ɗinsa bata zo ba, ta miƙe da Arya ɗin a hannunts, tana masa murmushin da ma'aikatan wurin suka faɗa masa shi kaɗai takewa irinsa, amma su dai kam basa samunsa.

“Har ka gama ?” 

Ta yi maganar tana kallon jakar hannunsa

“Eh wallahi na gama haɗa komai, zan kuma koma bakin aiki na”

“To Mr. Uchenna, Nagode, nagode sosai, thanks a ton”

“ you got it......my friend baƙo zai yi halinsa”

Ya faɗi yana ƙoƙarin karb'ar Arya daga hannunta ta sakar masa shi, ya karb'eshi.

“Muje na taka maka to”

Haka ta raka shi har parking lot, inda ya aje motarsa, ya bata Aryaan sannan yayi musu sallama ya tafi.

*Ma farin komai kenan😉*

_________________________

_Ah-Ah, su Daaso an shiga next level_

_Na fada ?, aa nayi shiru dai_

_Ina me mika muku dubbin godiyata, Allah ya temaki ko wannen ku🙏_

🌸-SAI KASKA CE✍️-🌸.


⭐️YADDA ƘADDARA TA SO⭐

⭐️ شاء القدر⭐️

*Magical love story*

©By Sai Kaska

Wattpad @Sai_Kaska

Phone number:***

Arewabooks @18saikaska

_________________________________

*Proud of my first novel*


★TAURARI WRITER'S ASSOCIATION★


*Babin yau sadaukarwa ne gareki Maman Eman*


*BABI NA GOMA SHA BAKWAI (17)*


HANAM POV.

Hanam ce kwance akan gadonta, daga gefenta kuma Arya ne zaune yana wasa, waya ce kare a kunnenta, tayi shiru tana sauraron matar dake iƙirarin cewa itace mahaifiyarta.

Wai mahaifiyarta?, matar da tun da tasa ƙafa ta bar nigeria kusan shekara ashirin da biyar bata ƙara waiwayowa ba.

Taje ta can ta haɗa wani sabon iyalin, ta manta da ƴarta dake nan cikin wani hali, hatta da date of birth ɗin yarta tata ta manta, tana da jika amma bata sani ba. 

Da ta ga hotonsa akan dpn Hanam ɗin ta tambayeta waye ?, Hanam ɗin tace mata ɗanta ne, kuma bata ƙara cewa komai ba, bata tambayeta ba shin aure tayi ?, tsintar yaron tayi ? ko kuwa.

Babu ɗaya data tambaya daga ciki. kuma sai tayi shekara bata kirata ba, itama kuma Hanam ɗin bata kiran nata sai de idan ita tayi niyya ta kira. Dan ta tica ta faɗawa kanta cewar bata dariya mahaifiya.

“Izan shu an shaglik ?”

(To yaya aikin ki ?)

Muryar matar wadda daga muryarta zaka tabbatar dacewa balarabiya ce, ta fito daga cikin wayar, sai da Hanam ta wani jujjuya idonta sannan tace.

“Kullu tamam..... kaif waladik?”

(Lafiya ƙalau, ya yaranki ?)

“kullun mnah, am ya sallumu alaiki”

(dukansu lafiya, sun cema suna gaisheki) Muryarta ta fito da fara'a, taji daɗi an tambayi yaya lafiyar yaranta, Hanam ta miƙe zaune tana cire wani zare a kan Aryan

“Biya'ar funi shi ?”

(sun sanni ne ?)

Saida tayi dariya sannan ta amsata

“Hinin biya'arfuki kitir”

(sun sanki sosai ma kuwa)

Hanam ta gyaɗa kai.

“Ibni bi hajati, salam”

(Ɗana yana buƙa tata, sai anjima)

“Oh ana asfe, kifu ibnik ?”

(Ohbyi haƙuri na manta, yaya ɗan naki yake?)

Ta manta ?, wai ta manta, taya za'ayi uwa ta manta da cewar yarta tanada ɗana?, ko da yake ba wani abun mamaki bane, hakan zata iya faruwa, tunda uwar ɗan ma manta ta ake, ai ba lefi dan an manta ɗan.

“Huwa mih, bitasil ma'ak ba'adain”

(Yana lafiya, zan kiraki daga baya)

Kuma bata jira cewar ta ba ta kashe kiran, kuma bawai dan Aryaan ɗin na bukatarta bane, wayarce ta isheta, komawa tayi ta kwanta tana kallon Aryaan, yana juyowa ya kalleta suka hada ido, his blue eyes ya tuno mata da shi.

Ta kawar da kanta gefe, a lokacin da shima yaron yaci gaba da buga motar wasan dake hannunsa, kuma jiyowa tayi taci gaba da kallonsa, wani abu na mata yawo a ka, tunanin shekarun baya suka su shiga dawo mata, waɗanan shuɗayen idanuwansu.

Ƙofar ɗakin aka ƙwanƙwasa, dan haka ta miƙe zaune, Abba ne ya buɗe ƙofar ya leƙo da kansa.

Kuma tasan babu me mata hakan sai shi, sai kuma Rafi'a ƴar gidan Hajjo, dan Allah ya haɗa jinin yarinyar da Aryaan, tana shigowa ɗakin idan Hanam ɗin tana gida, kuma itama bata hanata ɗaukarsa.

“Abba”

Ta kira sunansa bacin ya shigo ɗakin

“Na'am, Bannute (Babu girl) ” 

Ya faɗi yana kallon su ita da Arya, bayan ya tsaya kusa da su.

“Ki shirya jibine tafiya hakuɗau”

“Ai kuwa gwara da ka tuna min, dan na manta, tare da sauran yaran gidan zamuje ?”

“Eh mana, ba ƴan uwanki bane ?”

“Nima bance komai ba fa, zan tafi da motata ne ”

“To shikenan..... Kai ƙatoto bakayi bacci ba ?”

Ya ƙrashe yanawa Arya wasa, Hanam ta yi dariya, irin wadda take a duk lokacin da ɗaya daga cikin su yake tare da ita.

“Wasa ya ke, kace Abba sai ka fara bacci zanyi”

“Idan ya yi magana ai guduwa zanyi“

Yayi maganar yana ɗaukansa, gaba ɗaya suka saka dariya.


TAFIDA POV.

Ƙofar ɗakin Maryam ya dosa, kuma tun kafin ya ƙwanƙwasa ya tsinkayi muryarta tana karuntun ƙur'an, yaji wani dummm, idonsa yayi duhu, kamar ana so za'a zare masa ruhinsa ne, yaji kamar wani abu ne zai fita daga jikin nasa.

*

Yayinda a can cikin wani rami, wata wani baƙin hayaƙi ya shiga yawo a cikin kwalbar, yana girgiza kwalbar.

*

Gara ya buɗe ƙofar ya dakatar da ita daga karatun kafin ransa ya fita gaba ɗaya, irin wannan yanayin yake shiga a duk lokacin da zeyi sallah, daga ya tada kabbarar harama zaiji wani yifff, kamar abu ya faɗo daga jikin nasa.

Sai kuma yayi sallahr cikin nutsuwa, yanajinsa sakayau, yana jin tabbas wannan shine, shine yake controling kansa ba wani ke controling ɗinsa ba, Sannan daga yace assalamu alakum na sallamar da sallah, wannan abun zai faɗo masa a ka.

Sai yaji kamar wani dutsene ya danne shi, kamar an ɗora masa wani abu akan nasa, kamar wani ke controling ɗinsa. Kuma a kullum a cikin irin wannan yanayin yake, sai de idan sallah zaiyi. 

Ya kawarda ko wani tunani dake kansa ya buɗe ƙofar kansa tsaye, shi tunda ta zo gidan bai ƙara shiga ɗakin ba sai yau, bai ganta a cikin ɗakin ba, kuma dama ba daga nan yake jin sautin ta ke fitowa ba.

Yau cike da farin ciki Maryam ta tashi, dama ita bata saba baccin safe ba, dan haka tana tashi ta shiga yin aikace-aikacen ta data saba, ta gyara ko ina.

Sannan tayi girki me sauƙi, taci nata ta aje masa nasa akan danning kamar yanda ta saba, taga launch box har guda biyu a kayan kitchen ɗin, dan haka ta zuba musu cake da meat pie ɗin da ta yi.

Kuɗin daya bata kuma ta saka a cikin waya daga cikin jakukunan da fulani ta bata, sbd idan ta dawo daga makaranta zata tsaya a super market ɗin ta yi siyyaya, yau zata huta da zaman kaɗaici, wata ƙila ma sanda zata dawo gida shima ya dawo, dan haka kaɗaici ya ƙare.

Bayan da ta gama duk abinda za ta yi sai tayi wanka ta saka abaya a cikin kayan wajen Fulani, ta dauki ɗaya daga cikin hijabanta ta saka, ta zauna a ɗakinta tana jiransa.

Sai kuma taga da zaman banza ai gwara ta ɗan tab'a tilawa dan ta ɗan jima ba ta yi ba, ga azumin alhamis da litinin da take shima ta dena, ta ɗanyi tsaki kaɗan tana mitar sakacin da ta fara, kuma ta ƙudirce a ranta a cikin satin nan zata dawo da yin aziminta.

Bataji shigowarsa ba, sai da taji takunsa, da kuma ƙamshin turaren sa, zaune take a balcony akan wannan kejarar me kamada lilo, ta dakatar da karatun a lokacin daya karasa shigowa balcony din.

*

Kuma a lokacin ne wannan hayaƙin ya kwanta a ƙasa, kwalbar ta dena girgiza.

*

Miƙewa tsaye tayi tana gyara zaman hijabinta, Allah ya temaketa yasa dashi a jikinta, kanta a ƙasa ta gaisheshi dan yace ta dena tsugunnawa har ƙasa idan zata gaidashi, kuma kwata-kwata basu haɗu ba tun jiya da daddare. Ya amsa mata kadaran kada han, kamar yanda ya saba, fuskarsa babu fara'a bare walwala, ita tarasa meke damunsa haka.

“Kin shirya ?”

Muryar sa me zurfi da taushi ta tambaya.

“Eh na shirya”

Bai ce komai ba ya juya yana tafiya, Maryam tabi bayansa da kallo, kamar yanda ta san shi inde zai fita manyan kaya ne a jikinsa, yau wani yadine me kyau a jikinsa black color, hular kansa ma akwai ratsin baƙi.

Haka takalminsa, ita kam riƙon al'adar mutumin nan na bata mamaki, yanzu waɗanda suke hausawan ma gaba ɗa ba basa riƙe al'ada kamar haka, bare shi da ya kansace ruwa biyu.

Cikin ɗakin itama ta komo ta aje ƙur'anin a kan wata chest drawer, sannan ta ɗauki jakar data saka kuɗin nan a ciki da wayarta, itama ta fita.

A motarsa ƙirar Audi suka fita, Maryam kam yau tana cikin farin ciki, dan tunda tazo garin wajen sati ɗaya da kwanaki bata tab'a fitowa daga block ɗinsu ba sai yau, kuma ba su yi wata doguwar tafiya ba suka isa makarantar.

Komai shi ya mata babu abinda ta yi, kuma taji daɗi, daɗi sosai ta ji, dan hakama tun yanzu take tunanin abinda zata dafa masa idan ta koma gida, duk da ta koma baya abun bai dameta ba, aide zataci gaba da karatun.

*

“Miriam”

Muryar Tafida ta faɗi yana kallon Maryam yayinda suke tsaye a jikin motarsa, dan tafiya zaiyi ita kuma yau zata fara shiga aji, bata amsa ba sai ɗagowa da tayi ta kalleshi.

Kasa jurewa kallon idonsa ta yi sbd sun mata tsauri da yawa.

Shi ma be san me yasa ya kirata ba, kawai de yaji baya so su rabu, baya so ta tafi sautin bugun zuciyar tata ya yanke masa. Launch box ɗin hannunta ta miƙa masa.

“Miye wannan ?”

“Meat pie da cake” 

Ya tuna yanda ya ɗanɗana na jiya, kuma yasan cewa shine wannan ta zubo masa, sai kawai ya karb'a still yana kallonta.

“ Meri aakho ka tara hai tu Miriam ”

kuma yana gama faɗin hakan ya buɗe motar ya shiga ya tafi, Maryam ta tsaya a wajen kalaman na maimaita kansu a kwakwalwar ta, ita bata jin indianci, amma tana kallon fina-finan india, kuma ta ɗan san wasu abubuwan, amma wannan kalaman daya faɗa mata babu ɗaya data gane, sai de ta riƙe su gam a kanta, kuma zata tambayi Google me kalaman suke nufi.

***

Tafida ya shigo cikin corridorn da zai sada shi da office ɗinsa bayan ya fito daga elevator.

 Wasu nurses ne suka gaida shi, ya amsa musu, kuma bayan ya wuce sai yaji suna wata hira data ɗauki hankalinsa, dan haka ya motsa kunnensa yana ci gaba da tafiya.

“Ke naji an ce wai yayi aure” 

Ɗayar ta tambaya

“Eh mana, yayi aure kuma ance wai da yaje garinsu aka aura masa ita”

“Kenan itama ba'indiyar ce ?”

“Eh to bana ce ba, tunda ban ganta ba, kuma ai kinga yana saka kayan hausawa, wata ƙila hausace”

“Uhmm, ai ko idan ƴar masifar nan ta sani za'ayi bala'i”

“Wa kenan ?”

“HELEEN mana, ni bana ganinta ma, ta jima bata zo nemansa ba”

“Eh rannan tazo wai zata masa sallama, ta tafi abuja wani aiki, ke de bari kawai, Allah ya kawota musha kallo”.

Yayi wani gajeren murmushi yana buɗe ƙofar office ɗinsa, shi sai yanzu ma su ka tuna masa da wata Heleen, ya manta da ita gaba ɗaya. Heleen?, wata mata da zai iya cew.......

Ƙofar da khabir ya turo ce ta katse masa tunani.

Gaisawa sukayi kamar kullum kafin Khabir ɗin ya zauna.

“Ka kirani kace nazo”

“Eh, yanzu dama kai yaɗani ka yi ta yi a asibitin nan wai nayi aure?”

Khabir yayi dariya

“To ai abun farin ciki ne, lefine dan na faɗa ?, shine kaɗai dalilin kiran ?”

“A'a ba shi bane, hijabai muke so, kuma manya shine nake so a tambaya min Madam ina zamu samu?”

Yanzu ma Khabir ɗin dariyar ya sake yi

“ What's funny ?”

“A'a wai naga ka zama me gida ne shi yasa”

Ya ɗanyi murmushi kaɗan

“Shikenan zan tambaya maka ita, though ita bama saka shi take sosai ba”

“To godiya nake”

“Bari na je ”

Khabir ya faɗi yana miƙewa, sannan ya fice. 

Bayan wasu mintina wayar Tafida ta yi ringing.

Yana duba wasu files a cikin book shelf, ya ajiye wanda ke hannunsa ya jiyo ya ɗauki wayar. Muktar ne dan haka ya ɗaga ba jira, gaisawa sukayi kamar yanda suka saba kafin Muktar ɗin yace.

“Muna tare da su yanzu haka, godiya suke so su maka”

“Umhm bari ma kira vedio call”.

Daga haka ya katse kiran, laptop ɗinsa ya buɗe ya aikawa Muktar ɗin kira. Nan take Muktar ya ɗaga kiran, tare da seta wayarsa ga mutum biyun dake zaune a gefensa, Tafida na ganinsu ya tsinci kamarta a fuskarsu, duk da su sun ɗan fita kyau, duka a tare suka gaisheshi, ya amsa musu, ɗaya daga cikinsu ne yace.

“Mun gode sosai Yaya, Allah ƙara girma”

“Nop, kamar yanda kuka ce ni Yayanku ne, idan Yayar ku ta muku abu zaku mata godiya ?” A tare suka girgiza kai.

“Good to nima haka, we are all the same, ba kira nayi dan ku min godiya ba, kira nayi dan na ƙara jaddada muku cewa, ku kula da Mamanku sosai, kuma ku kauɗa kai daga abinda Abbanku yake, kada ku riƙa masa rashin kunya, musamman ma kai Hassan, nasan Hussain yana da haƙuri, amma karinƙa haƙuri kaima, kaga shi mahaifi ne, kuma mahaifa haƙuri ake dasu, dan Allah ku kiyaye”

“InshaAllah Yaya”

“Good boyz, yanzu ina asibiti, zamuyi magana daga baya”

“Dan Allah ka bamu lambara Yaya”

Ya ɗanyi jimm, shifa bashi da lambarta ma.

“Kawai ku turomin taku sai na bata”

“To zan turo maka” 

Cewar Hassan, daga haka yayi sallama da su ya ci gaba da aikinsa.

____________

_Ƙwan-ƙwan-ƙwan, nach ba, wacece wannan Heleen ɗin ?, nica ban gane ba, kamar.....😂_

_Nica maganar zuwa wannan hakuɗau ɗin ban gane mata ba, anya kuwa ?_

_Inye su Daaso an gayu, an fara zuwa makaranta_

_Na gode da goyon bayan ku🙏_

🌸-SAI KASKA CE✍️-🌸.



⭐️YADDA ƘADDARA TA SO⭐

⭐️ شاء القدر⭐️

*Magical love story*

©By Sai Kaska

Wattpad @Sai_Kaska

Phone number:***

Arewabooks @18saikaska

Facebook fage: Sai Kaska

_________________________________

*Proud of my first novel*


★TAURARI WRITER'S ASSOCIATION★


*Wannan babin na ki ne Zuwaira*


*BABI NA GOMA SHA TAKWAS (18)*


MARYAM POV.

* Da misalin 04:30pm*

Maryam ta fito daga ɗakinta, kamar kullum sanye cikin hijabi har ƙasa, ƙasa ta sauƙo hannunta riƙe da wayarta, yau ta samu ta siyi credit ta saka, kuma ba credit kaɗai ta siya ba ta siyo abubuwa da dama da kuɗin da Tafida ya bata.

Yanzu haka zuwa za ta yi ta jere kayan da ta siyo ɗin, dan bata jima da dawo daga makarantar ba, dan a ƙafa ta taho sbd babu nisa, kuma a yau ɗinma har ta yi ƙawaye biyu, wanda suka kasance hausawa kamarta, Dan yawancin aan makarantar yarabawa da igbo ne, sai fararen fata, kuma ƙawayen nata sun faɗa mata su suna block 4 ne.

Yanzun ma sallah ta yi shine ta fito, so take ta je ta gama gyara kayan sai tayi girki dan yau girkin ma na musamman za ta yi, sai kuma ta zo ta zauna ta siyi data ta ɗan hau tiktok ta duba sabbabin recipes.

Ta kuma kira Anti Fatifati da Badar, dan tun ranar da tazo garin da sukayi waya da Anti Fati basu ƙara ba, kuma tayi mamaki da har yanzu Badar ba ta kirata ba.

Amma de koma miye yau zata kirata, Dan tana soma ta kaiwa Maanmu su gaisa, ta ji ya suke.

Hannu takai ta kama handle ɗin ƙofar kitchen ɗin, ta murɗa sannan ta tura ƙofar, ledojin data aje akan kitchen islan ɗin suna nan, ledojin da suka gajiyar da ita, dan suna da nauyi ga yawa amma haka ta riƙo su niƙi-niƙi ta taho, dan ta shiga super market ɗin da ya faɗa mata.

Switch ta kukkuna ta ƙara hasken fitilun kitchen ɗin, daga wajen glass ɗin dake wajen stove ta kalli yanda neon strip light ɗin nan suka fara haske, wajen na matukar burgeta musamman ma da daddare ta yanda take hangosu ta saman balcony ɗin ɗakinta, kyanta ace ta zauna a wajen tana shan iska da daddare, amma tsoranta ba zai bari ta zauna a wajen ita ɗaya ba.

Ledojin ta shiga bubbuɗewa, sai da ta cire komai gaba ɗaya, wani kitchen trolly na ƙarfe data siyo ta fara haɗawa wanda take so ta fara jera kayan miya a kai.

A kusa da ƙofar baya ta aje shi ta, ɗebo sauran kayan miyanta dake cikin fridge ta jere akan trolly ɗin, hakama sauran su doya da kalin da suka rage.

Sannan sauran abubuwan da ta siyo irin su jan nama, naman kaza, nutella, fruits, yoghurt, butter duka ta saka a fridge.

Su chocolate, cookies, choco pie, oreo da sauran kayan kwaɗayi da ta siyo kuma ta ciresu a ledojinsu ta saka a wasu containers na glass, tana saka biscuits ɗin oreo tayi murmushi data tuna da Auta.

Ta ɗebi kayan da ta siyo na bukatar kanta ta kai ɗaki, sannan ta dawo ta kwashe sauran kayan da suka rage.

Ta yanke cewar zata gwada dafa masa abincin al'adarsa yau, sbd ta nuna masa jin daɗinta akan abunda ya mata tunda baya san godiyar.

Dan haka ta yi niyyar dafa masa chicken biryani, bata tab'a girkawa ba, amma sbd shi zata gwada kuma tana fatan yayi daɗi.

Bata gama girkin ba sai kusan shida, ita ba iya cin abincinsu za ta yi ba dan haka ta zubawa taliyar rice stick ɗiinta ruwan zafi.

Ta yanka jan nama ta dora a wuta, sannan ta yanka albasa, sosage, red paper, green bell pepper sannan ta soya ƙwai ta haɗasu gu ɗaya ta saka seasoning.

Kafin ta kawo naman data tafasa ta haɗa sannan Kuma ta ɗauko taliyar data zubawa ruwan zafi ta zuba, ta saka soy sauce, ta jujjuya, sannan ta juyeta a warmer dan ba zata ci yanzu ba.

Sai tayo sallar magariba dan an kusa ƙira, dan haka ta ɗebi kayan data girka masa ta aje a kan island dan yau da kanta take san ta zuba masa abincin.

Ta ɗauki wayarta ta nufi dakinta. Tana sallah taji sanda ya dawo, bai nemeta ba dan haka bayan ta idar ta ɗauki wayarta ta siyi data, sannan ta kira Anti Fati, suka gaisa ta tambayeta ya gida ta amsa mata da kowa yana lafiya.

“Badar fa ta koma kano”

“Wai da gaske ?”

“Wallahi ta koma gida, cewa tayi babu Maryam a haɗejia me zata zauna tayi”

“allah sarki kaunata, zan ƙira ta ai”

“Ke yanzu bata da waya, a bikinki aka sace mata”

“Me ?, tab ” 

Ta tuna yanda badar take ji da wayarta, kai mutane basu da kirki, yanzu a ɗan wannan taron da a kayi har aka samu zarafin zacewa mutum abunsa. 

Daga nan suka ɗan tab'a hira kaɗan, daga bisani Maryam ɗin ta mata sallama, Anti Fati ta rufe da cewa.

“Dama Maanmu tace idan kin kira na faɗa miki ki ta ya ta da godiya kan abinda Tafida ya yi wa su Hussain”

Girar Maryam ta haɗe waje guda alamun mamaki.

“Su Hussaini kuma ?, me ya musu ?”

Tana iya jiyo sautin murmushin Anti Fati daga wayar ga kuma hayaniyar lulu ƙasa-ƙasa.

“Bawan Allah kenan, ahse ma bai faɗa miki ba, to mijinki dai su Hussain yasa aka kira masa ya yambayi ko wannensu wani aiki yake so, dan yace aikin gareji bai dace dasu ba, Hussain yace shagon PS 5 yake so, shi kuma Hassan yace jari yake so zai fara saide wayoyi, yanzu de haka zancen da nake miki ya buɗe musu shaguna kusa da kusa, shi Hussain na PS5, Hassan kuma ya cika masa shago da wayoyi da su covers, kayan de harkar waya, ai in faɗa miki shagon Hussain yafi kyau, inda kika san a waje, kinga shagon ne ?”

Kamar wata sokuwa haka Maryama ta girgiza mata kai, itama Anti Fati kamar me jiran girgiza kan nata taci gaba.

“Wallahi shagon ya haɗu, a taya mu godiya”

“To zan faɗa masa”

Kuma daga haka wayar ta ƙare, Maryama ta yi shiru ta na jujjuya abun a ranta, wai ita kam wa take aure ne ?, ta kasa ganewa kan wannan bawan Allahn.

Sauƙa tayi daga kan gadon da take zaune tayi sujudi shukr, sannan ta ƙara godewa Allah a bayyane, dan saide godiya, Allah ya gama mata komai. 

Kalaman ɗazu ne suka dawo mata a rai, dan haka ta koma inda ta bar wayarta ta ɗauka, ta shiga Google ta rubuta ' Meri aakho ka taara hai tu'.

' You are the star of my eyes' 

Itace amsar data samu, Maryam ta kusa kaiwa ƙasa dan daɗi, kenan yana nufin tana da muhimanci a rayuwarsa haka ?.

“Oh Allah” 

Ta furta a bayyane, murmushi kwance a kan fuskarta, kuma har yanzu tana kallon wayar, ita kuwa me za ta yi dan ta sakawa wannan bawan Allahn.

Da sauri ta aje wayar ta fita, bata samu kowa a ƙasa ba dan haka kanta tsaye ta wuce kitchen. Abun da idonta ya fara arba da shi shine.

Tafida tsaye a jikin fridge yana shan ruwa a roba, shima jin an buɗo ƙofar yasa ya juyo hannunsa riƙe da gorar ruwan. Kallonsa kawai take, tana jin wani abu na yawatawa a kanta, ji take kamar taje ta rungumeshi ta faɗa masa cewar ta gode, amma bazata iya hakan ba sam. Faɗa kawai take.

“Sannu da dawo wa” 

Da kai ya amsa mata yana ci gaba da shan ruwan.

“Kaci abincin ne ?,naga kana shan ruwa”

Ta faɗi tana ƙarasa shigowa cikin kitchen ɗin, sai ya juyo ya kalli warmers ɗin.

“Da naga baki ajemin akan danning ɗin ba, shi yasa nayi zaton baki girka komai ba”

“Baka duba wanna ba?”

“Ummm”

“To ai shine abincin naka” 

Ya ɗan cije leb'ensa yana meda gorar cikin fridge ɗin, ya rufe fridge ɗin nasu me ƙofa biyu, sannan ya juyo ya kalleta.

“A ina kika siyo kayan nan ?” 

Ya tambaya ne dan yaga kayan da ba shi ya siyo ba a cikin fridge ɗin, kuma dama so yake ya sha ruwa sai ya buɗe warmers ɗin, dan ya san nasa ne, ƙishin ruwan yafi ji shi yasa. Tana ɗaukowa plate da ta bashi amsa

“Ɗazu a super market ɗin nan”

“But ai wannan na kayan buƙatar ki ne na makaranta”

Ta juyo tana aje plate da ɗin akan island ɗian sannan muryarta ta fito ba tare da ta kalleshi ba.

“Na sani, kawai ina buƙatar kayan ne, kuma kuɗin yamin yawa shi yasa na siya”

Ya ƙaraso inda take tsaye, hakan yasa ta tsaya da ƙoƙarin buɗe warmers ɗin da take shirin yi, gabanta ya shiga bugu, ashe da gaibu take, da tace zata iya rungumeshi, wasa ne kawai, a yanzu da yake tsaye a gabanta ma ta kasa ƙwaƙwaran tunani, ina kuma ga ace tana cikin jikinsa ne, sai yanzu ta kalleshi da kyau.

T-shirt ce a jikinsa, da sweat pants wanda ya bayyana baƙin zaren dake ɗaure a ƙafarsa ta dama, sai crocs sanye a kafarsa, gashin kansa na gaba kwance a goshinsa, duk da yana kawai hannu ya kawar time to time.

“Last time na faɗa miki cewar if you need anything, just talk to me, zan bawa Devid ya kawo miki, anything Miriam, i mean anything”

Da ƙyar Maryam ta gyaɗa kanta, ta san Devid shine drivernsa, drivern da baya tuƙa shi a mota saide aike. Ya lumshe idanuwansa yana sauraron bugun zuciyarta, wani abu da a yanzu ya zame masa rabin jiki, da baya iya sukuni idan bai ji shi ba.

Ƙamshin spices ne ya daki hancinsa, irin spices ɗin da yasan a girki ɗaya ake saka irinsa, biryani, dan haka ya buɗe idonsa dan yaga shin ita ɗince Daaso ta dafa masa ?, kode ta saka ne a wani girkin da ban.

Sai ya ga kuwa ita ɗince, saida ya haɗiyi wani yawu, shida yaci biryani sai idan yaje india, da akwai wani restaurant ɗin indians da yake zuwa yaci a can, amma yanzu me wajen ya rufe, hakan tasa ya daɗe baici ba.

Kuma shi ba wani samun time ɗin dafata yake ba. Ya dawo da dubansa kan Maryam, me yasa take da nasarar yin duk abinda yake so ne ?, ' hai fagban' (Oh god).

Ya faɗi bayan a zuciyarsa, yana kallo har ta zuba masa a cikin plate. Ya kalli abincin sosai, biryanin ta ji kwai ta ji kaza.

Kamar yanda yake sonta, sai yake jin kamar yana india ne, Daadi tayi masa ta saka shi a gaba tana faɗin maza cinye Eshaan, kuma kamar yana abuja gidan kawunsa Imran Neha ta dafo masa tana faɗin sai ka cinye tas Bhai.

A hankali yaja kujerar island ɗin ya zauna, yaja plate ɗin gabansa, kawai sai ya tsura musu ido yana kallo, kamar me nazarinsa, to ita wai a inama ta iya girki haka ?.

Maryam ta ɗebe sauran kayan data b'ata ta saka a dish washer, sannan ta buɗe fridge ta ɗauko masa milk shake ɗin da tayi ta zuba a cikin wata jar. ta aje masa a gabansa, sai taga har yanzu bai fara cin abincin ba, ya saka a gaba yana kallo, kamar me san gano inda tayi kuskere.

“Baka so ne ?”

Ya juyo ya kalleta, sai kuma ya kalli milk shake ɗin nan.

“No ba so ne ba nayi ba, biryani is among my favorite food, kawai de tambayar ki nake san nayi tun kafin na fara cin abincin, dan kar ki ce santi nake”.

Dariya ta so kwacewa Maryam, amma kawai sai ta yi murmushi.

“Ina jinka”

“A ina kika koyi girki ?”

Yanzu kam dariya ta ɗan yi, shi kuma bai tab'a ganin dariyarta ba sai yau, sai ya kafeta da ido yana sauraren bugun zuciyarta wanda yake bugawa cikin nishaɗi.

“Maanmu ce ta koya min, kuma ina ƙara sanin sabbabin girke-girke through social media, more especially tiktok da inster”

Ya gyaɗa kai yana jan plate ɗin gabansa.

“Me zai hana ki zama food blogger, tun da kinga course ɗinki na makaranta ma na yan tuwo ne”

“Inji wa ?”

“Inji Eshaan” 

Yanzu ma murmushin ta yi, a ranta take faɗin ashe yana magana haka.

“Haka mutane suke cewa wai home and rural economic na ƴan tuwo ne, amma ba haka ba ne, sana'o'i da dama ake koyarwa, kamar calabash decoration, tie and dye, fishing, farming ga kuma shi kansa girkin da dai sauransu”.

Ya gyaɗa kai yana kai loma wajen ta uku, dan shi baiji wani banbanci da na indian ba, kamar Neha ko Daadi ne suka dafa.

“Back to our business, ki zama food blogger, ina ga wasuma zasu ƙaru da abinda kike” 

Ta gyaɗa kanta ita ma, sun tab'a maganar ita da Badar, amma a lokacin dariya kawai ta yi mata, bata bawa abun muhimanci ba.

“Amma fa ba zaki nuna fuskarki ba, babu muryar ki kuma duk abinda zaki faɗi saide ki rubuta, waƙoƙi koma de wani abun da bam zaki ɗora a kai”.

Mamaki ya kusa kama Maryam, wai kishinta yake ?, dama ita takai namiji kamar Tafida ya yi kishint?.

To yanzu kawai tana tafiya a hanya ta haɗu da wani ta nuna masa Tafida tace shine mijinta ta tabbatar da dariya zai mata, dan ko kaɗan basu dace ba, Tafida irin mazan nan ne da ba'a ganin irinsu sai a film ɗin india, na film ɗinma idan har ya kasance director ɗin ya zab'o kyakyawa a matsayin actorn.

“Yaushe zaki fara ?”

“Ummm duk time ɗin da zanyi girkin gida”

“Wanne daga ciki zakiyi, tiktok ko inster ?”

“Duka biyu” 

Ya gyada mata kai, ganin kamar hirar ta ƙare kuma yana cin abinci ta tsaye masa a kai tana saka shi managa yasa Maryam ta ɗauki flask ɗin data zuba rice stick ɗinta, ta buɗe ta juye a plate, sannan ta ɗauki milk shake ɗin itama ta ɗora komai a tray ta fice.

Shima bai hanata ba, to idan ya hanata yace mata me?.

A parlo ta zauna ta fara ci, dan tasan yanda yake cin abincin sa cikin yanga, ba da wuri zai gama ba sai ta gama ma shi bai gama ba.

__________________

_umm wai nace ba, team Maryam zasu fara food blogging, to muna saka ido mu gani_

_She danin ruhin fa kamar yaji tsoro, yo naga kwana biyu yayi kwana, baya lekowa_

_A har kullum ina godiya gareku, Allah bar kauna mutane na🙏_

🌸-SAI KASKA CE✍️-🌸.


⭐️YADDA ƘADDARA TA SO⭐

⭐️ شاء القدر⭐️

*Magical love story*

©By Sai Kaska

Wattpad @Sai_Kaska

Phone number:***

Arewabooks @18saikaska

Facebook fage: Sai Kaska

_________________________________

*Proud of my first novel*


★TAURARI WRITER'S ASSOCIATION★


*Sadaukarwa zuwa ga Firdaus*


*BABI NA GOMA SHA TARA (19)*


*Titin ƙauyen hakuɗau*

*Da misalin 05:30pm*

Motoci ne guda biyar suka gangaro daga titin auyo suka hau kan jan b'irjin da zai kai ka har zuwa cikin ƙauyen hakuɗau, tun daga kan hanya yara ke binsu har sukayi parking a ƙofar wani gida me ginin bulo irin ginin zamani.

Gidan kamar ba'a ƙauye ba, hatta da fentin sa sabo ne, ƙofar gidan ma gate ne.

Yara da manya duka a ka firfito ana kallonsu, duk da ba wannan bane zuwansu na farko, suna zuwa lokaci-lokaci, saide kowa yasan cewa idande Alhaji Muhammadu ne yazo to kakarsu ta yanke saƙa, dan zai raba musu kuɗi, koma kayan abinci, dan shi kam ko bai zo ba yana aikowa.

Da gaba ɗaya yaransa ya taho, wajen su goma sha huɗu, mata da maza, matan sane kawai ba'a zo dasu ba, sai yaransa uku mata dake sa aure. 

Uche ne ya fito daga motar Abba ta mazaunin driver, da alamuma shine yayi tuƙin, sai miƙa yake, duk da sun sha zuwa tare da Abban.

Hanam ce ta fito daga tata motar, dan ita daga ita sai Arya da Rafi'a suka taho a motar ta, sanye take da atamfa, ɗinkin straight gown me tsaga daga baya, kuma kamar kullum babu kalliya a fuskarta, ta ɗaura ɗankwalin atamfar akanta, sai mayafin data yafa a kafaɗarta, front seat ta zagayo ta buɗe ta ciro Aryaan daga car seat, lokacin da Rafi'an ma ta fito daga bayan motar.

“Yaya kawo shi, sai ki ɗauki jakar taki” 

Miƙa mata shi ta yi tana ɗan murmushi, dan tun ba yau ba ita kaɗaice suke shiri a gidan, dan ma tana zuwa makarantar bodin a wancan lokacin yanzu kuma ta gama shi yasa zamanta ya dawo gida gaba ɗaya.

Booth ta buɗe ta ɗaiki jakarta data Aryaan, sannan ta sauƙo da su zata fara turawa.

“Kawo na ɗauka miki” 

Da sauri ta ɗago ta kalleshi, dama da shi aka taho ?

“Dama ka zo ne ?” 

Uche yayi murmushi yana karb'ar jakukunan hannunta.

“Eh mana, nine ma nayi deriving motar Abba” 

Abun ya bata mamaki, bata san ya biyo su ba. Hayaniyar da yaran gidan kakanin nasu keyi ce ta ɗauki hankalinsu.

“Muje ko”

Suka fara tafiya yana tura mata jakar bayan ya ɗauki ɗayar, suka zo wucewa ta gaban Kamal, Hanam na kallonsa yana hararar su, sai kuma ta lura da hararar ba tata bace, ta uche ce.

Sai tunaninta ya dawo mata da sanda taji shida uwarsa suna magana akan wani Uche, wai Abba yana sansa fiye da kamal ɗin, komai sai Abba yace shi.

 Ashe shine Uchen?, tayi murmushi kawai. A ƙofar gate ɗin ta karb'i kayan, ta masa godiya ta ƙarasa shiga ciki, gaba ɗaya mutanen gidan sun fito sai hayaniya ake ana murnar ganin mutan abuja, ta ƙaƙalo murmushi, tana gaida tsoffafin gidan, kada ran kada han suke amsa mata, ta sana da hakan dan haka bata damu ba.

“Ke kar ki zo min da wannna shegen kusa da ni!”

Hanam ta tsaya cak, ta karkata kallonta zuwa kan Inna Ai, kishiyar kakarsu, wadda a koda yaushe cikin hantararta take tun a baya ballan tana yanzu, ta kalli Rafi'a wadda take hawaye, dan a rayuwarta bata son taji Arya yana kuka, itama sai ta fara kuka kamar wata ƙaramar yarin.

Hanam ta haɗiye wani abu, lokaci ya wuce da zata zauna tana kuka, zuciyarta dakkakiya ce, tanada ƙarfi kamar karfe, ta daɗe da sanin cewa A strong woman will always turn pain into power.

Ta miƙa hannu ta karb'i Arya dake kuka, a lokacin data ƙarasa kusa dasu, ita kuma Rafi'an su Nabila sai zaginta suke sbd tana kuka akan wannan yaron, Inna Ai ta wurgawa Hanam harara tana faɗin.

“Gara ai, gara kizo ki fitar min da shege daga rumfa,daga ke har uwarki babu na kirki, Ai mu Muhammadu ya gama b'ata nan zuri'a, tunda har ya auri mana dangin ano ba”

Hanam ta tsaya daga fita daga cikin rumfar, ta juyo ta kalli tsohuwar, zuwa lokacin kowa yayi shiru yana san ganin yanda za'a kaya, dan dama can a gidan basa san uwar hanam ɗin.

“Iya Ai, ya.....isheki haka, kiyi magana a kaina babu damuwa, amma kada ki ƙara dangantani da waccan matar, ni bani da uwa.....”

“shi kuma ɗanki bashi da uba ko?” 

Inna Ai ta yi saurin faɗi, tana katse Hanam ɗin, harda wani miƙewa tsaye tana jijjiga,.

Hanam ta ɗaga kanta sama tana lumshe ido, tare da lasar lips ɗinta, bata so ta yi loosing temper ɗints, amma da alama yau Inna Ai tana so ta tunzurata, ga kukan Aryaan dake hawa mata kai, idonta ta buɗe.

“Lak kras wu laik!!”

(Kayi min shiru!!) 

Ɗif, kukan da Aryaan ɗin yake ya ɗauke, sbd gigitaciyar tsawar data daga masa, ita ba ta san damuwa, sai yayi shiru yana kallonta, ta juya ga Inna Ai.

“For the last time zan faɗa miki wannan maganar, babu ruwanki da ɗana, ta ya na sameshi ?, waye ubansa ?, daga ina yazo ?, duka bai shafe ki ba, sbd wannan damuwata ce”

Ta nuna kanta 

“Damuwatace ni ɗaya, sbd Arya ɗana ne ni ɗaya, ɗana, ina fatan kin fahimta?”

Tana kaiwa nan taja jakukunanta ta yi b'angaren Baabaa, matar kakanta ɗaya da duk gidan babu me ƙaunarta kamar ita. Dan mahaifiyar Abba ta rasu, kuma kakansu matanza uku yanzu.

Uchenna Franklin ya bar ƙfar gate ɗin gidan, bayan ya gama sauraren duk abinda ya faru, har cikin ransa yake tausayin Hanam, memakon su tambayeta cikin ruwan sanyi ta faɗa musu a ina ta samo yaron sai de kawai su riƙa jifansa da kalmar shege, me yasa ne haka ?, me yasa.....

“Ah-ah, Harisu ashe da kai aka zo ?”

Uche ya yi murmushi yana duban tsohon da suke tare da Abba.

“Ai kasan babu yanda za'a yi a zo ganinka babu ni, sbd nayi kewarka sosai”

“Ƙaryar banza, idan kana kewata ka dawo hakiɗau da zama, ka riƙi fatanya sai na yarda da kayi kewata”

“To ai ni ko ƙauyenmu ma bana zuwa sbd noma, haka kawai da kuruciya ta zan zo nayi ta maka noma kaida matanka da ƴaƴanka kuna ta ci ni kuma na tsofe na rasa me aure na ?”

Tsohon ya yi dariya irin tasu ta manya.

“Sai in baka ɗaya daga cikin jikokina”

Uche yayi dariya

“To ya Maman taka ta ke ?”

“Mamana lafiyarta ƙalau, tana Enugu”

“To idan kunyi waya kace ina gaishe ta”

“zakuwa taji”.

***

*Da misalin 08:00pm*

Hanam ce ke girki a ƙofar rumfar Baabaa, noodles take girkawa akan ƙaramin gas stove ɗin da ta taho da shi.

Hatta da noodles ɗin ma ita ta taho da ita, dan ita ba iya cin abincin gwana goma za ta yi ba, bawai abincin nasu ne ba zata iya ci ba, domin suna da cima me kyau, kawai de tsaftar masu girkin nasu ce bata yarda da ita ba.

Dan ta taso a cikin hausawa ne, amma wannan kyankyamin irin na larabawa a jininta yake, ko kaɗan bata san kazanta. Noodles ɗin ta juye a cikin plate sannan ta ɗorawa Arya baby feed ɗinsa.  

Data gama ta juye masa a baby bottle ( fida) ɗinsa me kan teddy, sannan ta kashe stove ɗin ta kawar da shi gefe, ta koma ɗakin.

Baabaa ta iske zaune tana lazimi ga Aryaan zaune a kan cinyarta, sai yunƙurin kamo carbin hannunta yake ita kuma Baabaan sai ɗaɗɗaga carbin sama take, sai ta miƙo masa kamar zata bari ya kama, kuma sai ta ɗga shi sama, shi kuma sai ya saba kansa sama sa hannunsa yana son ya kamo carbin.

Tayi musu dariya tana zama, hasken ƙwan lantarkin dake ɗakin ya haska ko ina, dan gidan kwana ake a yini da generator kamar ba kauye ba. System ɗinta ta cire a chargy, ta zauna ta shiga daddanawa tana cin abincin.

“Gashi ki bashi bulumbotin nasa ya sha”

Hanam tayi dariya

“saide na baki ki bashi da kanki”

Baabaa ta miƙa mata hannu, Hanam ta bata baby bottle ɗin.

“Amma fa da zafi”

“Bakya bashi abinci ne ?”

 Hanam ta girgiza kai, tana ci gaba da danna system ɗin gabanta.

“Ina bashi, saide bana bashi me yaji”

Baabaa ta gyaɗa kai.

“Hanam ya kamata ace kinyi aure”

Hanam ba ta kalli Baabaa ba, dan wannan sabbabiyar maganace a wajenta, ta yi murmushi me ciwo, tana kai cokalin noodles bakinta.

“Aure ?, Baabaa babu wanda zai aure ni a haka, babu wanda zai aureni da ɗa, kowa kallon shege yakema ɗana, to waye zai auri uwar shege ?”

Tausayinta ya ƙara rufe Baabaa, tun tana ƙarama bata samu wani farin ciki ba, sbd uwarta data tafi ta barta, yanzu ta girma lokacin da ya kamata ace ta yi aure tana gidan mijinta kuma wata ƙaddarar da ban ta sameta.

“Kiyi haƙuri Hanam, Allah yasan da ke, wasu lokutan ɗan adam bai san sanda ƙaddarorinsa zasu ƙare ba, ki yi ta addu'a Allah zai baki wami sabon fata da ban”

Yanzuma murmushin ta yi kuma tana ci gaba da danna system ɗin.

“Baabaa nayi wannan addu'ar a baya, sai Allah ya bani Arya, na ɗauke shi a matsiyin wannan sabon fatan, shi da Abba kaɗai sun isheni” 

Muryar ta fito cikin shaida abinda take faɗi gaskiyane, kuma haka ɗin ne bata buƙatar kowa ya shigo rayuwata, kullum cikin godewa Allah take daya azurta ta da Abba da kuma Arya.

“Salamu alaikum”

Sukaji sallama daga bakin ƙofa, Baabaa ta amsa. Uche ya leƙo ɗakin, Hanam tana mamakin yanda yake abu sai kace musulmi, ita dai bata amsashi ba, tanaga yanda suka gaisa da Baabaa kamar da suka saba sosai, abun ya bata mamaki.

“Hanam, Baba ne ke kira” 

Uchenna ya faɗi yana duban Hanam, a hankali ta gyaɗa masa kai, shi kuma ya fita.

Ta miƙe ta saka takalmanta, wata farar cardigan dress ce a jikinta, ta san yanzu ba a gida take ba dan haka ta ɗauki wani ƙaramin gyale ta yafa a kanta, sannan ta karb'i arya a hannun Baabaa, ta ɗauki wayarta da ruwan gorarta ta fita.

A tsakar gidan taga gaba ɗaya ƙannenta da yayanta kamal ga abba ga uc3he a gefe, ga Inna Ai dake aiko mata saƙon harara.

Hasken globe ɗin dake wajen ya temaka mata wajen kallon kowa gaba ɗaya, daga gefen kakansu kuma ɗaya matar tasa ce, da kawunnansu suma suna zaune a wajen, duka de gida an taru, Baabaa ce kawai babu, waje ta samu ta zauna a kusa da kakanta tana masa murmushi

“Kai ɗan kauye baka kira Baabaan ba ?” Baba ya faɗi yana duban Uche.

“Wannan ai matarka ce, kaje ka kirata da kanka”

“Ja'iri ɗan nema, jeka kira min ita”

Uche na dariya ya shiga sashen Baabaa, Hanam de kam kanta ya kulle, taga kowama na gidan ya saba da shi, to yaushe hakan ta faru ?.

Bayan ɗan wani lokaci sai ga uche ya dawo Baabaa na biye sa shi, hanyar ƙofa ya yi zai fita, Baba ya kirashi yana faɗin.

“Ina za kaje ?”

“Waje zan fita naga ka tara iyalanka ne, ban sani ba ko wasiyya zaka basu”

“Ɗan nema dawo ka zauna, ai kai ma ka zama dan gida”

Arya ya na ta ɗagawa Abba hannu Hanam ta miƙa masa shi tana faɗin.

“Abba gashi yana maka magana”

Abba ya karb'eshi yana dariya.

Nasiha Baba ya musu kamar yanda ya sabba musu idan aka taru irin haka, kuma ya ƙara da magana akan auren Hanam, ita de kawai jinsu take, dan ita tasa a ranta babu wani aure da za ta yi.


MARYAM POV.

*Da misalin 09:00pm*

Tsaye take jikin kitchen island, tana decorating cheesecake, ranta fes, bata da kowace duwa, domin yanzu duk tsoranta akan halin da su Maanmu ke ciki ya kau, tana jin kamar ko wani buri da take da shi ya cika, babu abinda ya rage mata sai godewa Allah.

Yau Sunday babu makaranta kuma babu aiki, tun bayan da Tafida ya ci abincin safe yayi wanka ya shirya cikin kayan wasan cricket yace mata Ya tafi filin cricket, Kuma har yanzu bai dawo ba.

Tunaninta ya katse lokacin da aka turo ƙofar kitchen ɗi, ta ɗago da kanta ta kalli wajen, duk da tasan babu me aikata hakan sai me iko da gidan.

Kamar yanda ta zata shiɗin ne kuwa, ya sauya kaya daga green Jersey da ya fita da ita zuwa wata blue, a gefen Jersey ɗin an rubuta india, hakan ke nuna mata cewar ta india ce, sai wani jeans dake jikin nasa, gashin kansa a jike ya sauƙo kan goshinsa, alamun de wanka ya yi, idonasa manne da wani baƙin glass me duhu, kamar kullum fuskarsa babu fara'a babu akasinta, sai ya fito kamar wani jarumin Bollywood.

Kamar yanda take kallonsa shima ita ɗin yake kallo, bai jima da dawowa daga filin wasanin ba, sbd Khabir da ya kirashi yace masa ansamu hijaba nan, kuma gashi nan a hanya zai kawo masa su, bayan ya fito daga wankan ne ya kalli idonsa a mudubi yaga ƙwayar idonsa tayi ja.

Shi kam ya fara tabbatarwa da maganar su Fulani, da suka ce masa wata ƙila Maryam itace maganin matsalarsa, dan kusan sati biyu kenan rabon da baƙin ruhinsa ya tashi, kuma duk ya danganta hakan ne da shigowar Maryam rayuwarsa.

Baya san ya riƙa tsorata Maryam shi yasa ya saka glass ɗin, Abinda ya saba ya shiga yi, wato sauraron bugun zuciyarta.

A hankali cikin takunsa na kullum ya fara takowa cikin kitchen ɗin, still idonsa a kanta, ita kuma sai ta kawar da idonta a kansa ta ci gaba da jera raspberry ɗin da take jerawa akan cheesecake ɗin data hada.

“Yaushe ka dawo ?” 

Muryar ta fito ba tare da ta kalleshi ba, tana ci gaba da abin da take, Tafida yaja kujera ɗaya daga tsallekin inda take tsaye ya zauna sannan ya amsa mata da.

“Ban jima da dawowa ba, saƙo za'a kawomin shi yasa na dawo da wuri”

Ta gyaɗa kanta tana saka raspberry ɗin na ƙarshe.

Shi kuma yaci gaba da kallon duk motsin da take, ya kalli hannunta, a hannunta na dama a yatsarta ta tsakiya akwai zobe, wata ƙila azurfa ce, dan yana kama da azurfar. A tsintsiyar hannunta na hagu kuma akwai wasu jerin abun hannu na ƙananun beads masu sheƙi, sai wal-wali suke a cikin hansken fitilun dake haskawa a kitchen din.

Maryam ta bar jikin island ɗin, ta nufi jikin cabinet ɗin da take aje ƙananun plates, kasan cewar cabinet ɗin a sama suke yasa sai ta yi tattage, kamar wani abun baki sai tsayinta ya kasa kaiwa, ko hannun cabinet ɗin ta kasa tab'owa bare ta buɗe.

“Matsa”

Ta tsinkayo muryarsa a bayanta, kuma cikin umarni, matsawar ta yi ta juyo tana kallonsa, daga inda yake ya ɗaga hannunsa saitin cabinet ɗin, ya motsa hannunsa daidai buɗewar ƙofar, Maryam ta juyo ta kalleshi ta jiya ta kalli cabinet ɗin data buɗe kanta.

“Me ki ke so ki ɗauka ?”

Maryam ta haɗiye wani abu, sannan ta lalubo muryarta tace.

“P...plate”

Saida yayi wani murmushi, sannan ya kuma motsa hannunsa, nan take plate ɗin ya fito daga cikin cabinet ɗin, kuma bai sauƙa a ko ina ba sai akan cabinet ɗin.

Duka a kan idon Maryam, wadda ta yi sumar tsaye, kamar mafarki take, kode tsafi yake ?, kuma ai yace mata he is monster saide kuma babu yanda za'ayi mutum ya zama dodo.

Kamar me tsoron taka ƙasa haka ta tako zuwa jikin island ɗin, hannunta na rawa tunani da yawa na yawo a kanta ta kai hannu ta ɗauki wuƙa.

Duka abinda take Tafida na lura da ita, so yake yayi dariya, amma kumma sai ya dake, yanzu iyaka wannan kawai ta gani ahse idan ta ganshi a wancan halin suman gaske za ta yi.

Da ƙyar Maryam ta samu ta iya yanka cake ɗin, ta ɗora akan ƙaramin plate ɗin da ke aje a gabanta, sannan ta ɗora karamin cokali a kan poate ɗin.

Ta tura plate ɗin gaban Tafida dake zaune a tsallakenta ya kafeta da ido, ya tabbatar da a halin da take ciki yana cewa kett!, zata saka gudu, dan ga yanda bugin zuciyarta ya sauya, tana bugawa da sauri-sauri.

Ya kai hannu yana jan plate ɗin gabansa, ya ɗauki ƙaramin cokalin ya guntsiri cake ɗin ya kai bakinsa, kamar kullum girkin Maryam 100% ne koma ya fi hakan, babu wata makusa. Yana ci yana kallon Maryam da ta masa nutsuwa.

“Ki zauna”

Maryam ta kasa ganewa umarni yake bata ko kuwa, tade kawar da komai dake kanta ta zauna, amma har yanzu ba a nutse take ba.

“Kin manta da abinda nace miki rannan ko?” 

Yayi maganar a sigar tambaya, saide be jira amsawarta ba yace.

“Miriam” 

Ya kira sunan daya raɗa mata ƙarfi da yaji, Maryam ta yi ƙarfin halin ɗagowa da idonta ta kalleshi, har yanzu idonsa sanye yake da glass, amma sai ya aje cokalin hannunsa ya kai hannu ya cire glass ɗin, 

Ƙwayar idonsa da ta yi ja ta bayyana a idon Maryam, gaban Maryam ya shiga bugu fiye da ɗazu, ta zazzaro idanuwanta gaba ɗaya tana kallonsa, tunda Maanmu ta kawota duniya bata tab'a ganin abu makamancin wanda take gani yanzu ba, zata kawar da kanta gefe ya dakatar da ita.

“No dont, keep looking at me” 

Babu yanda za ta yi bata iya musu ba, dan haka taci gaba da kallon nasa, saide zuwa yanzu ta fara hawaye, sai taga yayi murmushi.

“Ba tsafi nake ba Daaso, baƙin ruhi ne a cikin gangar jikina, yana controlling ɗin base on yanda yake so, kuma tun ina ƙaramin yaro na gamu da wannan abun, babu wanda yasan abinda ya haddasar min da wanna abun, su me martaba sunce akwai ɗaya daga cikin our forefathers da ya yi rubutu akan irin wanna abun nawa, kuma sunce wai ta yanda za'a dakatar da hakan shine ta hanyar aura min wata yarinya.... ni ban ma riƙe signs ɗin da sukace yarinyar tana da shi ba, shi yasa suka auramin ke, dan sunce wai kece yarinyar, Maryam a duk lokacin da baƙin ruhi na zai tashi bana ji bana gani, bana banbance masoyi ko maƙiyi, hatta da kaina ma bana ganewa, akwai abinda ban tab'a faɗawa kowa ba, amma zan fada miki.....”

Sai kuma yayi shiru, ganin yanda Maryam ke ta zubar da hawaye, miƙewa ya yi da ga inda yake ya dawo inda ta ke, ya zauna a kujerar dake gefen tata, ya miƙa mata hankin daya ciro daga aljihun wandonsa, Maryam ta karb'a tana share hawayen da suka ƙk tsayawa, kuka take da gasken-gaske, amma mara sauti, tausayinsa ya cika mata zuciya, Tafida ya gyara zamansa yana juyowa ya kalleta da kyau.

“Abinda ke jikina aljanine, kuma yana bani super natural, sannan yana kareni daga cin asiri, a duk sanda za'amin asiri baya cina, saide ya koma kan wanda yamin, kuma turoshi a kayi, idan ina mafarki ina ganin wanda ya turoshi, bansan waye shi ba, kuma bansan me yake nema a wajena ba, amma tabbas nasan shine yake cutar dani, rayuwata bata da wani amfani, dan sam bana iyayiwa ubangijina tasbihi, bana iyayiwa manzona salati, hatta da kalmar larabci ɗaya sometimes gagarata take, kuma kin san wani abun mamaki ?”

Ya faɗi yana kallon Maryam, ita de har yanzu kuka take, amma mara sauti, sai share hawaye take, bata iya ce masa komai ba shima kuma sai yaci gaba..........

________________

_Nace ba, wai a ina su Baba suka san Uchenna Frankline ?_

_Menene Abun mamakin da Ficar Yara yake SO ya rasa mana ?_

_A har kullum, ina me matuƙar godiya a gare ku, ngd sosai da goyon bayanku, me ƙaunar ku ce Salma Ahmad Isah_

_I LOVE YOU WUJIGA-WUJIGA❤😂_

🌸-SAI KASKA CE✍️-🌸.


⭐️YADDA ƘADDARA TA SO⭐

⭐️ شاء القدر⭐️

*Magical love story*

©By Sai Kaska

Wattpad @Sai_Kaska

Phone number:***

Arewabooks @18saikaska

Facebook fage: (Salma Ahmad Isah Sai Kaska)

_________________________________

*Proud of my first novel*


★TAURARI WRITER'S ASSOCIATION★


*Na sadaukar da wannan babin gare ki Bilkisu H Muhammad*


*BABI NA ASHIRIN (20)*


.........“A duk sanda zanyi sallah, dana na yi takbiratul ihram sai na ji kamar wani abu ya fita daga jikina, kamar akwai wani gingimemen dutsi a kaina da aka sauƙe min, kamar da a ɗaure nake sai aka sakeni, kamar kuma ina ƙarƙashin sarrafawar wani abune, bana tantance yanayin amma sai naji ni wasai, ina jin cewa nine, nine ni a karan kai na, inayin sallahta a nutse, amma daga zarar na yi sallama, wannan nauyin dake kaina da zai dawo, wannan ɗaurin da a kamin zai dawo, zanji kamar ana sarrafani, kamar bani bane, bani bane akaran kai na, rayuwata akwai wahala WIFEY, shi yasa nake ganin lefin su Fulani da suka sakoki a cikin rayuwata, rayuwata bata da alƙibla, rayuwa nake ba irin ta sauran mutane ba, na banbanta da sauran mutane, sam bana farin ciki, duk dariya ko murmushin da zan yi yakan tsaya akan lebena ne kawai, baya kaiwa har cikin zuciyata, ko kaɗan bana farin ciki, saide kuma inasan naga na saka wasu farin ciki, tunda ni bazan samu ba me zai hana na bawa wasu, amma kuma Maryam shigowarki rayuwata ya sauya wasu abubuwan, a da baƙin ruhina baya kusanta ta sai raina ya b'aci, amma a wattanin nan da muke ciki sai abun yayi ƙamari, ya dawo yana tashi kullum, saide tun daga ranar da aka ɗaura mana aure bai ƙara tashi ba, saide kl nayi wannan....”

Ya ƙarashe yana nuna mata ƙwayar idonsa.

“Kuma kece kaɗai kike sakani naji cewa bani kaɗai ba ne, ina da wani, duk da ina da ƴan uwa amma kullum cikin kaɗaice nake jina, abubuwa sunmin yawa akai na, banajin daɗi jikina kullum, ko kaɗan wanna ba rayuwata ba ce”

Sai yaji wani nauyi dake zuciyar sa ya sauƙa, kamar wani dutse aka ɗora akan kirjin sa kuma aka sauƙe haka yake ji, yaji shi free domin ya amayar da abinda ke damunsa tsawon shekaru, bai tab'a zama ya bajewa wani ciwonsa haka ba, ko Neha da yafi kusancin da ita fiye da kowa bai tab'a magana da ita irin haka ba, bai tab'a ba, amma kuma kullum abun na ci masa zuciya, har yana barazanar hanashi numfashi, kuma duk abinda ya faɗa mata haka ɗin ne, baya jinsa daidai, baya farin ciki, yanajin kamar rayuwar tasa ba tasa bace, kamar ana sarrafashi ne, yanzu haka sai da yayi kokawa da wani abu sannan ya iya amayar da wannan maganganun.

“Ke kalleni nan”

Maryam na goge hawaye ta kalleshi, har idonta ya sauya kala zuwa ja, matsowa kusa da ita yayi ya kai ɗan yatsansa ya goge mata hawayen, a tarihin zamansu karo na farko daya fara tab'a jikinta kenan.

“Ki dena kuka is not good for you”

Maryama ta gyaɗa masa kai, wayarsa dake tsallaken island ɗin ta shiga playin waƙar Teri meri khani, hakan ke nuna wa Tafida cewa kira ne ya shigo, dan haka ya miƙe, ya dafa kan maryam sannan ya ɗauki wayar tasa da glasses ɗinsa ya fita.

Bayan Maryam ta iya ƙarfafa kanta ta dena kukan ta ɗauki sauran cake ɗin da bai ƙarasa ci ba, dama wanda ta haɗa ɗin duka ta saka a fridge, ta tattare duk abinda ta bata ta saka a cikin dishwasher na cikin dishwasher ɗin kuma wanda ta wanke ta ɗebesu ta sakasu a inda ta saba ajewa.

Batajin ko cake ɗinma zata iya ci, dan haka ta fita daga kitchen ɗin, fitowar tata ta yi dai-dai da shigowar Tafida daga Ƙofar waje.

Ido suka haɗa sai ta ganshi da baƙin glass har yanzu, taji tausayinsa ya ƙara kamata, hannunsa ta kalla taga ledoji har biyu, bata ce masa ƙala ba ta yi hanyar hawa sama.

“Wifey tsaya mana”

Maryam ta tsaya da tafiyar da take, a hankali ta ɗaga kanta sama tana so ta hana hawayen dake san zubowa sauƙa. Sai da ta tattabar da bazasu sauƙo ba sannan ta juyo, a lakocin Tafida har ya zauna akan kujera, da hannu ya yafito ta, dan haka ta dawo cikin parlon.

Gefensa ya nuna mata alamun ta zauna, sai ta zauna ɗin tana kama hijabin jikinta, yayin da shi kuma yake fitowa da wani kwali daga cikin leda.

“Desktop led ring light ne, tunda zaki fara food blogging”

Ya faɗi a lokacin da yake ciro kwalin, Maryam kawai kallonsa take, tana mamakin yanda yake iya b'oye abunda ke ƙarƙashin ransa. 

Shi da kansa ya haɗa ring light ɗin, ya jona da wuta hasken ring light ɗin ya haske fuskar Maryam dan a setinta ya ajeshi, Maryam ta kai hannu ta tare fuskarta.

“Ha kawo ko ?”

“umm” 

Ta amsa shi da ƙyar, sai kuma ya zare shi daga socket ɗin, sannan ya dawo ya zauna a inda ya tashi.

“Kinga yanda yake working ko ?”

Maryam ta gyaɗa masa kai, sai kuma ya janyo ɗayar ledar, ita kuma bai buɗe ta ba ya miƙa mata kawai.

“Kije ki, a ina zan aje miki ring light ɗin ?”

Maryam ta karb'i ledar tana miƙewa, bata amsa shi ba, sai kama ring light ɗin da ta yi ta aje shi a kusa da TV stand sannan tayi sama.

A kan gadonta ta zazzage ledar daya bata, hijabaine kusan kala goma, Maryam ta zauna a bakin gadon tana kallon hijaban hawaye na cika mata ido, ya kamata ace tayi wani abu akan rayuwar bawan Allahn nan.

Bai kamata ace ta barshi cikin wannan halin ba, ya zama dole ta temaka masa, kamar yanda ya temaki rayuwarta, sam bai kamata ta zuba ido tana ganinsa haka ba, she need to do something.


*Hadejia Emirates*

*Sashen bayi*

*Da ƙarfe 05:30pm*


“Ke?, wai ina kika je ne ?”

Cewar Hasana tana duban Husainarta, Husainar ta zauna tana sharce gumi.

“Kede bari, wannan mara rabonce tasani binne mata wani asirin da suka ƙara yi akan Tafida”

Ido waje Hasana take kallon yar uwar tata.

“Ke inji de baki binne ba ?”

Husaina ta girgiza kai.

“Na binne mana, me zai hanani binnewa”

“To amma Hassana me yasa ?”

“Sbd inaso na nunawa Fulani Sadiya cewa mugunta sayin faƙo ce, idan baka iya ba ka b'ata jikinka, ita har yanzu Allah bai sa ta gane cewa abinda take ba daidai bane, ta yi, ta yiwa bawan Allahn nan asiri amma bai ci shi ba taƙi ta haƙuri”

 Hasana ta yi ƙasa da murya tana faɗin

“Ai wannan addiƙu mina diƙu inna hu ɗiɗif ce”

 Suka saka dariya suna tafawa

“Har yanzufa bata lura da cewa duk asirin da ta masa kan ɗanta ya ke dawowa ba, kinga na neman mata data saka aka masa kan ɗanta ya dawo, ta saka a masa na shayeye shima ya dawo kan ɗanta, yanzu haka Allah ne kaɗai yasan name ta sa aka masa wannan karon”

“Allah sarki bawan Allah Tafida,yana can yana fama da kansa ita kuma tana nan tana shirin ƙara masa wani zafin” 

Husaina ta dan daki cinyar Hasana tana faɗin.

“Me dallah nace miki asirin baya cinsa, wata ƙilama daya tafi bakinsa ƙofar garin hafejia yake dawowa” 

Suka ɗan dara kaɗan kafin hasana tace.

“Kome ya tsare mata?, oho ”

“Wata ƙila dan tanaga yafi ɗanta halin arziƙi ne, sbd kinga shi bashi da wani hali na kushe, amma ɗanta fa ?, yafi kowa lalacewa, wata ƙila tana ganin kamar idan sarki ya sauƙa shi za'a ɗora, ita kuma da ɗanta su tashi a tutar babu, shi yasa take wannan abubuwan”

Hassana ta tab'e baki.

“Ammafa Husaina lamarin Tafida abun a duba ne, bisaga dukkan alamu akwai wani a bayan lamarinsa” 

Husaina ta gyaɗa kai tana nazari.

“Ƙila hakane, to amma ke a ganinki waye ?”

“Yaya zan yi nasani, Allah shi ya barwa kansa sani”

Husaina ta aje kofin ruwan data sha tana faɗin

“Koma de waye muna fatan Allah kub'utar da shi daga sharrinsa, dan Tafida mutumin kirki ne”

“Ameen ƴar uwata”.


HANAM POV.


Saida sukayi sati ɗaya a hakuɗau sannan suka dawo abuja, Hanam saida tayi nadamar zuwanta hakuɗau wannan karon, dan basu tahoba saida Naba yace kada ta haura watan nan ba tareda ta nemi mijin aure ba.

Ta rasa yanda za ta yi ita bata da wanda take so, Jabeer ne kawai ta tab'a soyyaya da shi, bata da wata mafita dan Abba ma haka yasata agaba da nasa faɗan, ta laluba ta lalubo bata da wani tsayyaye sai Jabeer ɗin, shi kuma har yanzu yana santa.

Dan haka kawai ta cewa Abba ta amince da auren Jabeer ɗin, Abba yayi murna sosai kuma a ranar data faɗa masa cewa ta amince ɗin ya kira Jabeer ɗin ya sanar masa, Jabeer yazo sukayi magana basu wani ja abun da tsawo ba dan dama tun farko an fara maganar bikin.

Sbd haka suka yanke biki sati biyu, Hanam sam ba haka taso ba, ita bata ƙi a barta daga ita sai Arya da Abba ba, amma babu yanda za ta yi, ko kaɗan bata san Abba ya yi fishi ko ransa ya b'aci, tafi so a kullum ta ga yana farin ciki, inde har auren nata shine farin cikinsa to za ta yi auren.

**

“Wai yanzu mom bari za ki yi tayi auren nan?”

Muryar Kamal ta faɗi, yayinda yake zaune a ɗakin mahaifiyar sa, suna facing juna, Mero ta yi wani murmushi wanda za'a iya kira dana makirci.

“Kamal kenan, ai bazan tab'a bari ta yi auren nan ba, bade Jabeer bane ?, to ita da Jabeer sai a lahira idan ana haɗuwa, amma babu ita babu shi, bazan tab'a bari ta auri Jabeer ba”

Kamal ya bushe da dariya harda buga ƙafa.

“To yanzu miye shirinki ?”

“Kaide ka zuba ido ka gani, Allah ya kaimu ranar ɗaurin aure, ba de ita wannan shashashar taƙi yarda mu haɗa kai ba?, ni ɗaya zan yi abuna na gama”

“Wa kenan ?”

“Hajjo mana, wai ita me tsoron Allah”

ta ƙarashe da kwafa.

“Auren yar lele,bari muga to idan za'ayi”

gaba ɗayansu suka saka dariya.


UCHENNA POV.

Zaune yake a ɗakinsa, guitar yake kaɗawa cikin wani kiɗi me taushi da sanyaya ruhi, waƙar daya rubuta yake rerawa tareda ƙidan.

Waƙa na ɗaya daga cikin mafarkansa na rayuwa, kuma tun yana ƙarami yake so ya yi waƙa, dan haka yake rubuta waƙar yana ajewa, idan ya samu free time kamar haka sai yazauna yana rerawa, wata ƙila ya kore ƙunci damuwa da b'acin rai dake cikin zuciyar sa.

Labarin ɗaura auren Hanam a gobe ya dakeshi, hakan yasa yake cikin duwa, dan har yanzu yana santa, kuma dama bai tab'a dena santa ba, ita kaɗai ya so, kuma ya ƙudircewa ransa ita zai ci gaba da so har zuwa lokacin da zai rasata, wata ƙilla Allah baisa ta kasance tasa ba, wata ƙila ba shi da rabon samunta, wata k......

Wayarsa da ta yi ringing ta dakatar da tunani da kuma kiɗan da ya ke lokaci guda.

 Uchenna ya juyo ya kalli wayar tasa dake aje a gefensa 'MOM' shine abinda ya fito b'aro, b'aro akan screen ɗin, ya aje guitar ɗin yana murmushi kafin ya kai hannu ya ɗauki wayar.

“Mom” 

Ya kira sunanta, kuma yanajin sautin murmushin ta ta cikin wayar, kafin ta amsa

“Na'am Haris, ya kake?”

“Ina lafiya, and you ?”

“ I am fine also”

“How is zakiyya ?”

“she is fine, she went to school”

Yayi murmushi, yana shafa sumar kansa

“Zaki zo bikin ne?”

“Me zai hana Haris?, mutumin nan ya yi maka komai daya kamata ace mahaifin ka ne yayi maka, ya zama dole nazo na taya shi murnar auren ƴarsa”

Ya gyaɗa kansa kamar tana ganinsa.

“Yaushe za ki zo ?”

“Gobe inshallah, i call to inform you dama”

“Ok mom see you tomorrow”

“Take care of yourself, Allah ya maka albarka”

“Emeen” 

Daga haka wayar ta ƙare, ya lumshe idonsa yana jingina da jikin gado, yana azabtuwa, Allah ya sani yana azabtuwa sosai.


MARYAM POV.

Tsaye take a jikin lokarta tana shirya kayan data wanke kuma ta goge yau da rana, dan gobe monday, tun shekaran jiya take cikin damuwa, sam bata jin daɗin ranta, gaba ɗaya lamarin Tafida ya dagula mata lissaffi, tarasa wani mataki zata ɗauka akai, kuma gashi bata san kowa yasan halin da yake ciki, dan wannan sirrinsa ne, da tanemi shawarar Anti Fati......

Wutar da aka ɗauke ce tasa tunaninta yankewa, tunda tazo garin kusan sati biyu amma bata tab'a ganin wutar gidan y ta yi koda fari ba, balle a ɗauke, abun ya bata mamaki, tsoro ya mamayeta ganin duhun da ɗakin yayi.

 Allan ya yi ta da wani bala'in tsoro, tana da tsoro sosai musammanma na duhu, tana tsoron duhu shi yasa ma bata kashe wuta idan zata kwanta, yanzu gashi ita ɗayace a ɗakin bazata iya tuna inda ta aje wayarta bama balle taje ta ɗauko.

Taji kamar ana tab'a balcony ɗun ɗakinta, ta zabura ta yi waje, wajen ma babu haske, ko ina yayi duhu a gidan, dan wajejen karfe 10 ma ne na dara.

Maryam taci gaba da takawa tana bin corridor ɗin a tsorace, ji take kamar ta fasa ihu....., sai kuma gashi ta fasa ihun, saka makon karo dataci da abu kamar mutum, hannunta taji an ruƙo, ta kara rudewa tana fasa ihu, sai kuma taji ance

“Ssssshhhhhh!”

Ta ƙzra ruɗewa tana ƙoƙarin ƙwatar hannunta daga ruƙon da aka mata, tsabar ta kiɗime sam bata gane muryarsa ba.

“Ke !!, Miriam nine ”

Inaa, sam bata ta gane yaren da yake, tsoro ya cika mata ciki, tsalle kawai take da ihu tana haɗawa da kiran sunan Allah. 

Tafida yaga abun nata bana ƙare bane, shima yana waya da Fulani yaga wutar ta ɗauke shi yasa ya fito dan ya duba meke faruwa, shine yaci karo da ita.

Tafin hannunsa na hagu wanda be riƙeta dashi ba ya buɗe, nan take wuta ta bayyana tana ci, kuma bata tare da ta tab'a tafin hannunsa ba, maryam ta ƙara fasa ihu tana fadin.

“Wayyo Allah wayyo Maanmu, dan Allah karka ƙonani aljani, kayi haƙuri kaji, dan Allah kayi haƙuri, to wai ni me na maka wa ?”

Tafida yana murmushi ta ya ɗago da hannun setin fuskarsa ta yanda zata samu damar ganin fuskarsa, sai kuma tayi shiru ta tsaya da tirje-tirjen da take, yana murmushi har hakwaransa na bayyana yace

“Main hoon na (nine), nine Eshaan, Tafida”

Ya faɗa mata sunayen har guda biyu duk dan ta gane, babu abinda ya bashi dariya sai ganin yanda fuskarta take sharkaf da hawaye.

“Eshaan ne ?” ta tambaya kamar wata sokuwa, yana murmushin dake barazanar komawa dariya ya gyaɗa mata kai

“Eh nine” 

har yanzu wutar na setin fuskarsa, yayinda yake riƙe da hannunta ƙaya

“Ki koma ɗakinki ki zauna, zanje na duba wutar”

A kiɗime ta ƙankame shi daga gefe kamar side hug amma duka hayyaneta biyu kewaye daya shi, ita kanta bata san ta yi hakan ba, dan gaba ɗaya ta tsure ta ƙidime, ta shiga girgiza masa kai tana kuka.

“Ni a'a, bazan koma ɗakin ba, tsoro nake ji Eshaan, i am scared, Eshaan....Eshaan”

Dariya tana so ta kifecewa Tafida ya kai hannunsa ya ciro nata daga jikinsa, ya riƙo hannun nata.

“To muje tare”

Ya faɗi yana jan hannunta, a hankali suke taka stairs ɗin, ya riƙe hannunta da hannunsa ɗaya, ɗayan kuma har yanzu wutar na ci, yana haska musu hanya har suka shiga garden ta kofar dake parlo, kasan cewar makunnar wutar gidan gaba daya a garden ɗin take.

Koda ya buɗe wajen sai yaga layin wutar ne ya sauƙa, dan haka ya meda latin, nan take haske ya gauraye ko ina a gidan, Maryam ta sauƙe wata ajiyar zuciya ta kwanciyar hankali.

Bata ankara cewa hannunta na cikin na Tafida ba saida suka shiga parlo, aiko tana ganin haka ta yi saurin zame nata daga cikin nasa, ta kalle shi da idonta da har yanzu akwai sauran ƙwallar data taru mata a ciki.

Sai kuma ta ruga da gudu ta haye sama ta faɗa ɗakinta tare da banko ƙofa. A jikin ƙofa ta jingina tana maida numfashi kamar me asthma, hannunta akan kirjinta, idanuwanta a lumshe, sai yanzu duk abinda ta yi yake dawo mata daki-daki, da ace wani ne ya faɗa mata cewar zata iya riƙe Tafida kamar yanda tayi yau to da kuwa ko qur'ani ne zata dafa akan hakan bazata faru ba.

Hannunta na dama daya rike ta ɗago ta kalla, sai kuma ta yi murmushi sannan ta bar jikin ƙofar tana goge hawayen idonta, sannan ta koma taci gaba da saka kayanta a wardrobe.

Tafida ya bi bayanta da kallo yana murmushi har sanda ta shige dakinta, sannan ya tako zuwa saman shima ya shige dakinsa, gaba ɗaya ta haga bashi dariya yau ɗin nan, ga yanda yaji zuciyarta na bugawa a ɗazun, ya saka shi cikin nishadi.

___________________

_To fa, nima fa ina ganin kamar akwai wani a bayan wannan lamarin kamar yanda Hasana sa Husaina suka faɗi, to koma de waye Allah bayyana mana kai, dan mun gaji da ganin fidar yara 😁 cewar maryam yana shan wahala, ko ba haka ba ?__

_Jama'a Hajiya Mero ta ɗauki zafi, ko me ta tana sa ?_

_To kide biyo ni, Dan juga yanda zata kaya_

_Ina me muku godiya 🙏_

🌸-SAI KASKA CE✍️-🌸.