{6..}
💛 HAJAR 💛
Da sauri Hajar ta miƙe daga kan kujera ta juya taga wane ne yayi mata wannan azababben ɗaɗen na rashin imani, Maama ta gani tana mata wani kallo mai cike da tsantsar tsana, Hajar ta ja da baya idonta na kawo ruwa tace "me nayi miki??", Maama tace "uwarki kikay min, uban waye yace ki zauna min a kujera?, ko so kike ki shafamin baƙin fentin da ke tare dake", Hajar bata ce komai ba darajar Naseer da Huzaifa yasa take ragawa Maama, Sa'adatu ta ɗingiso tana ƙoƙarin buɗe idonta na hagu da ya kanne tace "chaɓ wannan ɗan dukan, ai da kin sani dundu kikay mata wanda shegiyar za tay aman wahala", Hajar ta tsotse kumfar bakinta ta tofar ta zabgawa Sa'adatu harara tace "ke dalla malama ja can da ruɓaɓɓen bakinki, wllh kika sake magana saina naushi ɗayan idon kinyi duka babu", umma daga cikin ɗaki ta jiyo muryar Hajar ai kam ta fito da sauri, tana ganin Hajar tsaye ta riƙe ƙugu ga Maama da Sa'adatu tasan ba lafiya, daga bakin ƙofa ta tsaya tace "Hajara zo nan yanzun nan", Hajar ta ɗauki buta ta kuskure bakinta ta ɓallawa Sa'adatu harara ta shiga ɗakin umma. Maama ta kalli fuskar Sa'adatu tace "keda nace karki fito, me za kiyi a wajen?", Sa'adatu tace "bayi zan shiga ne", Maama tace "toh ina Maimuna da nace ta taimaka miki kafin anjima a karɓo miki magani a chemist", Sa'adatu tace "uhmm Maimunan ce zata temaka min" ta ɗingisa ta ɗauki butar da Hajar ta ajiye mai ruwa ta shiga bayii. Maama ta bita da kallo sai kuma ta nufi ƙofar ɗakin su Naseer, bubbugawa ta shiga yi da ƙarfi, Mu'azzam ya buɗe, ta ɓalla masa harara tace "ban hanya", ba musu ya matsa mata ta tura kai ɗakin, Naseer da yake kwance a katifarsa ya rufa har ka ta tsaya tana kalla, ta yaye rufar tace "Nasiru tashi", ya buɗe idonsa da kyar ya miƙe zaune yace "Maama lafiya??", tace "ka gaida babanku kuwa?", ya juyar da kai yace "Tin asuba muka gaisa aii", tace "toh maza yanzu ka fito ka sameni a tsakar gida karka ɓata lokaci" ta fita a ɗakin. Umma ta kalli Hajar tace "waike Hajara mai yasa kike da kunnen ƙashi ne iyee, ba nace ki dena shiga sabgar su ba", Hajar tace "Allah umma ban shiga harkar su ba, kawai fa ina zaune ina goge baki shine Maama tayi min ɗaɗe a baya wai na zauna mata a kujera", ta kwashe rigarta tace "kinga wajen", Umma ta zabga wani uban salati ganin yatsu biyar cif raɗa-raɗa a bayan ƴarta, wajen yayi Jajur tamkar ka taɓa jini ya fito abinka da farar fata, Umma tace "wllh Allah ya isa ban yafe ba", Sabra da take shafa Vaseline a ƙafafuwanta ta miƙe da sauri tace "Adda nagani", Sabra ta zaro ido tace "lalala chaɓ", Hajar ta sauke rigarta ta kalli umma tace "Umma ki bani kuɗi na siyo brush nawa ya faɗi a gefen kwata", Umma tace "kije wajen babanku ki karɓa", Hajar tace "tom, daman yanzu zanje na gaishesa" ta fita waje, a ƙofar ɗakin Baba ta tsaya tayi sallama sannan ta yaye labule ta shiga, ta durƙusa tace "Baba barka da safiya, an tashi lafiya??", Baba yace "lafiya ƙalou Hajara Allah yayi albarka", tace "Ameen Baba", yace "yaushe zaku fara jarabawar??", tace "banda wannan satin wani mai zuwa zamu fara", yace "toh Allah yasa a fara a sa'a, saiki dage da karatu", tace "Tom Baba" sai kuma ta fara murza hannunta tace "Baba dan Allah ka tahomin da brush idan ka fita aiki nawa ya lalace", ya karkace ya ciro ɗari biyar daga aljihunsa yace "gashi ki sayi brush ɗin, ragowar canjin kuma kiyi kuɗin makaranta dasu na gobe", tasa hannu biyu ta karɓa tace "nagode" ta miƙe zata fita daga ɗakin, Naseer ne ya yaye labule ya shigo fuskarsa duk kumburin bacci, Maama ce ta kunno kai ta wani rirriƙo Sa'adatu, Hajar dai ta koma gefe tana kallon ikon Allah sai kuma tace "yaya ina kwana??", Naseer yana murje fuskarsa yace "lafiya" ya samu guri ya zauna, Maama ce ta tattagosa wai tana buƙatar ganinsa a ɗakin Baba, ita dai Hajar ta kama gabanta ta samfe a ɗakin, Maama ta zaunar da Sa'adatu itama ta zauna tana kallon Baba tace "barka da safiya mal, yaudai ga ɗanka nan na kawo maka shi kayi masa katangar ƙarfe da dukar min ƴaƴa, ni nayi masa magana yaƙi ji, kalli kaga yadda ya sauyawa Sa'adatu kamanni, Maimuna ma tana ɗaki ya kwaile mata baya, toh gashi nan dai kayi masa magana wataƙila kai yaji maganarka, nidai nan gaba idan ya sake dukar min ƴaƴa kamar haka to wllh saina kwashe masa albarka kaf ehee", Baba ya kalli Sa'adatu ya juya ya kalli Naseer yace "kai ka daketa ??", Maama ta ɗaga murya tace "yo ƙarya zan masa kake tambayarsa, kayi masa gargaɗi kawai mal", Baba yace "dakata Rabi ki bari na gama magana, Naseer ina jinka me ya faru", Naseer ya gyara zama yace "Baba yarinyar nan kullum akan hanyar fita take daga gidan nan da shigar da bata dace ba, da dare sai kaga an ajiyeta a wata ƙatuwar mota, kuma motar da take kawota daban-daban ce, nayi mata kashedi amma taƙi ji shine jiya na zaneta", Sa'adatu ta fashe da kuka tace "Baba wllh ƙarya yake min, ai Maama tasan inda nake zuwa wajen ƙawata kuma ni ba a taɓa sauke ni a mota ba a napep nake dawowa", Naseer yace "ni nake miki ƙarya?", Maama tace "yo yarinya da bakinta kana ƙoƙarin yi mata sharri ai dole ta ƙaryata ka, mal nidae daga yau sai yau kar Nasiru ya sake taɓa min ƴaƴa, tashi muje", Maama ta miƙar da Sa'adatu suka fice daga ɗakin, Naseer yace "Baba, Maama tana sakaci da tarbiyyar yaran nan, wllh yarinyar nan a mota ake ajiyeta kuma namiji ne ba mace ba, ai ko macen ce a zargeta duniya ta lalace", Baba yace "na yarda da kai Naseer, abinda nake so da kai duk wani hukunci da za kai ka fara sanar dani kafin ka wanzar dashi, tashi kayi tafiyarka Allah ya shiryesu".
★Nurain ya sakko down stairs yana gyara zaman rantsatten agogon hannunsa, bai samu kowa a main palour ba don haka ya wuce part din Mami, da sallama ya murɗa handle ɗin palourn Mami ya tarar bata nan sai ya nufi ƙofar bedroom ɗinta, a hankali yayi knocking, daga ciki Mami tace "come in", ya buɗe door ya shiga, Mami na zaune bisa prayer mat ta idar da sallar walha, ta kallesa tace "A'a fita za kai, yau ai ba aiki ko??", yace "yeah, wajen Anty Zulaiha zani, tace tana son gani na, and i have another appointment", tace "ohk, anjima Abba da su Salisu zasu je gidansu Ruqayyah aii", ya jinjina kai yace "ammm Mami kin yiwa Anty Zulaiha maganar ne??", tace "eh na sanar da ita jiya da daddare", yace "ohk i think that was the reason take nema na, Noor fa?", tace "ta fita Grocery shopping wai girki zata ma friends ɗinta zasu zo", yace "ohk, na wuce", Mami tace "wait" ta miƙe ta buɗe huge press ɗinta ta ɗakko wata paper bag ta miƙa masa tace "ka kaiwa zuhaiha", ya karɓa ya fice daga part ɗin, katafaren compound din gidan ya fito mai ɗauke da shuke-shuke masu kyau da parking lots na motoci ƴan ubansu, Garba ne ya taho da sauri ya russuna yace "barka da fitowa alhj ƙarami", Nurain yace "yawwa, an gama wanke motar", Garba na washe haƙora yace "Eh an gama alhj" ya ciro key daga aljihun rigarsa ya miƙa masa, Nurain ya karɓi key ɗin ya zura hannu a trouser pocket dinsa ya ciro wallet ya buɗe ya fello dubu goma ya miƙa masa, hannu bibbiyu Garba ya amsa yana washe haƙora yace "Alhj harda hidima haka, to nagode Allah ya saka da alkhairy yasa afi haka", Nurain ya nufi wajen wata dunƙulalliyar mota a parking lot ya buɗe ya shiga, yayi warming sannan ya mirgina ya fita daga gidan bayan mai gadi ya buɗe masa damfareren gate. Slowly yake driving yana waya da Ruqayyah, wani murmushi ya sake speaking calmly yace "why are you doing this babe?, mesa bazan zo yau ba?", from the other side Ruqayyah tace "haba dearest nidae kunya nakeji, ka bari sai gobe kazo", yace "naji cewa sai gobe amma mesa zakiji kunya bayan da kanki kika kaini gidanku kikace kina sona kuma zaki aureni...", ƙit yaji ta katse kiran yayi murmushi ya sake dialing amma taƙi picking, a hankali yace "shy girl". A daidai gate din wani gida Bungalow ya danna horn, Gate man ya buɗe masa ya shiga da Motar yayi parking ya buɗe ya ɗauki paper bag din da ya ajiye a kujerar mai zaman banza ya fito, direct Main building din gidan ya dosa, ya tsaya a ƙofar shiga ya ciro wayarsa daga pocket ya kira Antyn nasa, tana yin picking yace "I'm here Aunt", Anty Zulaiha tace "toh me kake jira come in mana", Nurain ya shiga palourn da ya ƙawatu ba ƙarya bayan yayi sallama ya zauna akan kujera ya ajiye bag din hannunsa a gefe, wata ƴar budurwa ce da bazata wuce 20yrs ba ta fito daga kitchen hannunta riƙe da serving spoon, zaro ido tayi ta ƙaraso cikin palourn tace "yaya Nurain sannu da zuwa", yace "yawwa Khausar, ina Anty?", tace "bari nayi mata magana" tabi wani corridor, tare suka fito da Anty Zulaiha, Khausar ta koma kitchen Anty Zulaiha ta zauna kan kujerar dake kusa da nashi tace "na taso Dr da sassafe", ya shafa sumar kansa yace "ai mun saba da fitar safe, ya gida Anty?", tace "lafiya, ya Noor ta dai ƙi zaman gidan nan", yace "ai Noor Mami's tail ce" ya ɗauki paper bag din ya miƙa mata yace "inji Mami", tace "toh me na samu haka wajen yayata haka" ta buɗe taga perfumes ne kala uku, Khausar ta fito daga kitchen da trayn mai ɗauke da drink da kuma snacks ta ajiye masa, ta buɗe lemon ta tsiyaya masa a glass cup sannan ta koma kitchen, ya ɗauki lemon yayi one sip ya ajiye, Anty Zulaiha tace "jiya Mami take gayamin abin arziƙi, ashe yau za a kai kuɗi da sa rana, toh Allah ya tabbatar da Alkhairy, Ruqayyahn ce dai koh??", yace "yeah", tace "tom, maganar lefe na gaya maka balance dai koh??", yace "yea, yanzu zan miki transfer ba 2m ba??", tace "Eh haka yake, Insha Allah zasu isa a gama harhaɗo abubuwan da suka rage..", yace "idan ma basu isa ba just Ping me". Khausar da take rakuɓe a ƙofar kitchen kaf hirarsu a kunnenta ta lumshe ido a hankali tace "what kuɗin Auren yaya Nurain za a kai".............✍️