{9..}
💛 HAJAR 💛
Da yake glass din motar tint ne yasa Hajar bata ga drivern ciki ba. hannun yaron ta riƙe still dai tana kallon glass din motar, kawai jira take drivern ciki ya fito, few seconds passed amma babu alamar wanda yaso aikata ta'asar zai fito, Zainab da ta toshe kunnuwanta har tayi jarumtar juyowa ta hango Hajar tsakiyar titi tare da yaron, Hajar taja hannun yaron ta tsaya bakin ƙofar driver ta shiga knocking glass, a hankali glass din yayi ƙasa ya zuge gaba ɗaya, wani sanyi da ƙamshi suka fara sirnanowa suna dukan fuskar Hajar da ta yaron. ta haɗe gira tana kallonsa tace "malam wai baka san darajar rai bane iyeee?, ya za ai ka kusan bige yaro amma ka wani hakimce a mota bazaka fito ka dubasa ba", Zainab ce ta tsallako kan titin itama tace "zo mu tafi ai Allah ya kiyaye tinda dai bai bigesa ba", Hajar tace "ke kinga mutumin nan fa ko a jikinsa, idan da ace ya bige yaron nan fa sai fa yadda Allah yayi", shi kam Nurain mamaki da firgicin da ya ziyarcesa ne ya hanasa magana, Hajar ta sake kallon cikin motar tace "Allah ya isan sa kuma a ringa sanin darajar ɗan Adam", Zainab ta zaro ido tace "Hajar mene haka?", Hajar taja hannun yaron ta tsallar dashi titi tace "maza gida kaji", yaron ya kyalla da gudu ƴan uwansa suka take masa baya. wajen da suke jiran napep ta koma ta tsaya fuska a haɗe, mutanen yanzu basu da kirki ace ka kusan aika yaro lahira amma ka zauna ko a jikinka sai kace wanda ya kusan bige akuya yo ko akuyar ce aika fito ka duba idan kasan darajar rai, Zainab ta dawo gefenta ta tsaya tace "Hajar yanzu me kika aikata haka, Allah ya isa fa kikai masa, dubi fa har yanzu bai tafi ba", Hajar ta kalli motar da har yanzu take tsakiyar titi ta yamutsa fuska tace "me kwa na aikata, ya shekara a wajen kar ya tashi". a hankali ya juya kan motar ya gyara parking a gefen titi, Zainab ta damƙi hannun Hajar ta fara janta ganin ya fito daga motar ya tunkarosu, Zainab tana janta tace "Hajar kizo mu gudu kar yayi mana wani abun", Hajar ta fuzge hannunta tace "wllh bazan gudu ba", Zainab tayi tsam ganin har ya iso gabansu yayinda wani ƙamshi mai daɗi ya fara busowa a hancinsu, yana kallon Zainab speaking calmly yace "Assalamu alaikum young lady", a ɗarare ta amsa kana tace "bawan Allah kayi haƙuri dan Allah", Hajar da ta juyar da fuskarta ta juyo ta ɓalla mata harara jin abinda tace, girgiza kai yayi yace "ba komai, tell your friend itama tasan darajar ɗan Adam cause ba tayi hali ko kama da mutanen da suka san darajan mutum ba", da sauri Hajar ta juyo ta kallesa, and that look makes her brain to boot on, she saw this calm and charming face familiar, but where and when??, walking fast ya koma ya shiga motarsa ya kunna ya fita daga street ɗin da reverse. gida ya koma sbd wannan incidence ɗin da ya faru yasa yama manta da wani batun fruit salad, yana parking motar Garba ya taho wajensa, ko kashe motar baiyi ba ya fito cikin sauri ya shiga cikin gida, Garba ne ya shiga motar ya kashe sannan ya zare key ya fito. har lokacin Noor da Khausar suna zaune a palour, Noor tana kallonsa tace "yaya ina fruit din ko basu ka fita nema ba", shiru yayi mata ya haye stairs, Khausar ta taɓota tace "he is weird", Noor ta sauke ajiyar zuciya tace "ina jin an ɓata masa rai ne", she knows her brother in and out kuma she is very sure rai aka ɓata masa.
★Hajar ta shiga gida sai gunguni take, Mu'azzam da yake alwala a bakin rariya yace "toh jarababbiya", ta zumɓuri baki tayi ɗakin umma, Maama da take talgen tuwo Nabila na mata tankaɗe tace "kin ji ba ɗan uwanta ma yasan jarababbiya ce", Nabila ta doka tsaki ta cigaba da tankaɗenta, Umma ta kalli Hajar da take ƙoƙarin cire hijab tace "ke kuma lafiya kike wani cin mur", Hajar tace "wai a duniyar nan Umma mutane basa son gaskiya, wai wani mutum ne ya kusan kaɗe wani yaro a titi amma ko a jikinsa, wllh ko fitowa ya duba yaron ƙi yayi", Umma tace "Allah ya kyauta bai dai bigesa ba ko??", Hajar tace "saura ƙiris fa, amma wllh mutumin nan yadda kika san gunki haka ya zauna a mota yaƙi fitowa ya duba yaron", Umma tace "ke kuma shine kike kumbura akan hakan", Hajar tayi shiru kawai tuno abinda yacewa Zainab take wai batayi hali ko kama da mutanen da suka san darajan ɗan Adam ba. kiran sallar magrib ne ya fitar da ita tsakar gida tayo alwala ta dawo ɗaki tayi sallah, bayan ta idar da Sallahr isha'i tana zaune akan darduma Sabra ta ajiye littafi a gabanta tace "Adda ki koyamin", Hajar ta janyo littafin ta duba kana ta fara gaya mata abinda zata rubuta. Umma ta shigo da wata warmer ta abincin da tayi tazarce ta ajiye a gefe guda, Hajar na kallon Sabra tace "yanzu ke Sabra mosquito din ne baki iya spelling ba, ƙwaƙwalwar dusa ne dake ko me??" ta zuba mata rankwashi aka, Sabra ta riƙe kai tace "ashhh Adda fa na iya", Hajar tace "to rubuta mana", Umma tace "kiyi mata a hankali dan Allah". washe gari Hajar taje islamiyya tayi screening dinta na ƙarshe, kuma a yau ne aka fayyace musu kuɗin sauka da walima, kwanaki uku bayan haka ranar Alhamis da yamma, Baba bai jima da dawowa daga wajen aiki ba yana zaune a ƙofar ɗakinsa yana cin abinci, wani yaro ne ya shigo gidan yace "wai ana sallama da mal Adamu", Hajar da take shanya kayan da ta gama wankewa tayi wuf ta shiga ɗaki, jikinta ne ya bata cewa ya sayyadi Nura ne yau yazo wajen Baba daman ya gaya mata zaizo, Baba ya ɗauki kofin ruwa ya sha sannan ya rufe ragowar abincin ya miƙe ya saka takalmi yayi soro, yana zuwa ya tarar da wasu mutane su uku, biyu zasu kai sa'anninsa ɗayan kuma matashi ne, matashin ne ya russuna yace "Baba barka da fitowa", Baba ya kallesa ya amsa, shi dai bai shaida su ba, Baba ya miƙa musu hannu su kay musabaha, ɗaya daga cikin manyan yace "daman munzo da wata magana ne", Baba yace "toh" ya koma cikin gida ya amso tabarma a wajen Umma, tinda Maama taga ya fita soro da tabarma taji hankalinta bai kwanta ba, ta kalli Maimuna da take zaune akan dokin ƙofa tana shan rake ita da Nabila tace "Maimuna leƙo mana su waye suka zo wajen Babanku", Maimuna ta ɗauki rakenta ta ɓalla sai kace sabuwar kamu ta wuce ƙofar soro ta laɓe, leƙawa ta farayi ta hango su a zazzaune, da sauri ta dawo da kanta tace "ya sayyadi Nura" sai kuma ta kasa kunne, kaf abinda suka zanta karaf a kunnuwanta tana naɗa, taɓe baki tayi ta dawo cikin gida tana zabga tsaki, Maama ta dakata da sharar da take tace "su waye??", Maimuna ta zauna dokin ƙofa ta ɓalli rage tace "wai neman izini suka zo yi a wajen Baba na neman waccan shegiyar", Maama ta saki tsintsiyar hannunta tace "neman izini kamar ya??", Maimuna ta hura buɗaɗɗen hancinta tace "ni dai a yadda na fahimta sunzo nemawa ɗansu auren shegiya ne", Maama ta zaro ido tace "aure??", Nabila ta zubar da tuƙar raken bakinta tace "Hajarar??", Maimuna ta kallesu duka tace "meye naga kun wani firgita ne??, bafa wani mai arziƙin ne yake nemanta ba, Nabila kin tuna ya sayyadi Nura??", Nabila tace "kwarai ma kuwa", Maimuna tace "toh shine fa yazo tare da iyayensa", Nabila ta daka wata shewa tace "waii tsiya ta ɗakko tsiya, da wannan ruɓaɓɓen shagon nasa zai riƙeta", Maama tace "kun sansa ne??", Nabila tace "farin sani ma kuwa, ya sayyadin islamiyyar mu da muka dena zuwa ne, wllh bashi da komai, matsolo ne ainun", Maama ta gasa mata harara tace "dalla gafara can, da bashi da komai ɗin ke kin taɓa kawo kamarsa ne eyee ko wanda bai kaishi matsolontaka ba?, wllh kun bani kunya duk irin samarin da kuka tara babu wanda ya taɓa zuwa gidan nan da maganar arziƙi, kuna zaune sai kace tsumammun kayan wanki waccan shegiyar zata cigaba", Maimuna tace "chaɓ, ina wani cigaba wajen Nura, wllh ci baya daii", Maama tace "ja can amma dai ta fi ku ko??", Maimuna tace "wllh bata fini ba nida nake da Alhaj, kuma yace aurena zaiyi, lokacin zuwa wajen Baba ne kawai bai samu ba". Baba ne ya dawo ciki ya naɗo tabarma a hannunsa, kan dardumarsa ya koma ya zauna ya kirawo Umma, Umma ta fito ta tsugunna tace "mal gani". Baba ya wassafa mata kaf abinda ya faru ya ƙarƙare da cewa "da har kuɗin aure suka ce zasu bayar na dakatar dasu sbd inaso na binciki yaron kuma a tabbatar da yarinya itama tana so", Umma tace "to mal Allah ya tabbatar da alkhairy". Maama da tayi karaf da kunnenta ta rangaɗa wata shegiyar guɗa ta cigaba da shararta.
★Nurain zaune a farar kujera a compound ɗin gidansu Ruqayyah yana jiran fitowarta, wayarsa yake latsawa a hankali, saida ya jingine 20mins amma bata fito ba abinda bai taɓa faruwa ba, dialing numbernta yayi, tana yin picking speaking keenly tace "ina zuwa dearest" ta katse kiran, after like 5mins ta fito sanye da hijab da riga da skirt na atamfa, taja kujera ta zauna tana facing ɗinsa tace "sorry na saka jira", wayarsa ya kashe ya saka a pocket yace "na ɗauka ma kwalliya aka tsaya tsara min", murmushin gefen baki tayi tace "ka jira lokaci, kwalliya har saika gaji da ita", ya ringa kallonta sai kuma yace "ehen ina jinki you said you want to talk to me", wasa ta farayi da fingers ɗinta tace "kana ji dearest", yace "all ears", ta sunkuyar da kanta tace "ina so a ɗaga lokacin bikin mu"............✍️