ALƘALAMIN SO

Page 6

by @djham20

ALƘALAMIN SO




DIJAHAM(OUM AMANI)



Page 6



BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


 

  Dariya yake sosai jin yadda take masa magana muryar ta a shaƙe shi dama yasan halin ta shiyasa yana jin su Daddy na maganar yayi saurin kiran ta ya fada mata.


Ni kuwa jin shirun sa yasa naji rai na yana ƙara ɓaci kawai na kashe wayar, numbern Maryam nayi dialing sai da ta kusa katse wa sannan ta ɗaga. Ban ko tsaya mata sallama ba na ce "Maryama mai nake ji haka ne? Ynxu Sultan ya kira ni yana fada min wai boarding za'a kai mu.."

 Murya kasa kasa ta ce "eh nima haka Mummy ta ke fada min dazu da safe".


Rai na daya gama ɓaci gaba ɗaya na ce "ko kin ce musu kina son zuwa boarding school ne dan ni dai bamu taba maganar da kowa ba".


Murmushi tayi wanda har Ina jiyo sautin sa a kunne na ta ce "ni ma yadda kika ji maganar haka naji ta, kuma kam dai yanzu sai dai kawai muyi hakuri sauƙin ta ma SS2 za'a kai mu kin ga mu seniors ne balle kiyi tunanin ko za'a yi bullying din mu".


Tsaki nayi kawai na ce "ni dai ba makarantar kwanar da zani haka kurin sai ka ce waɗanda aka gaji da su". Katse waya ta nayi na shiga neman numbern Mami, sai dai abin bakın cikin ita ma tabbatar min tayi da cewa eh da gaske ne, ba wanda ban kira na har Dada amma kowa ce min yake muyi hakuri don gobe ma su Ya Haidar zasu je mana registration.


Kuka na zauna Ina yi wa Hajja wacce ta goya min baya da cewa kar na damu bara Dada ya zo anjima da daddare zata sa a fasa kai ni, da wannan na dan kwantar da hankali na, sai dai har wajen 11 na dare ba Dada ba labarin sa.


Hankali na bai gama tashi ba sai washe gari da Sultan yace min an gama mana komai uniform ne kawai da books suka rage mana suma kuma sai mun je school din zasu bamu, ni fa don bakin ciki ko sunan makarantar ban tambaya ba.


Ni da zan yi wa Hajja sati daya sai da nayi sati biyu ya rage saura sati daya kawai zamu tafi school din, yau dai na hada kaya na tsaf na wuce gida don duk fushin da nake yi nayi missing din su Mami, ga Uncle baya nan shi da ya wuce Italy yin sati daya sai gashi wai sun zarce UK daga nan za'a gyara jirgin kafin su taho wanda zasu iya yin month ko fiye kun ga kenan har mu tafi baxan gan sa ba.


Kullum dai muna tare a waya in ya samu time yana lallashi na da fada min yana dawo wa zai zo school din ya gan mu, a bakın sa ne ma nake jin sunan makarantar QUEEN SCIENCE ACADEMY.


 A kofar babban gate din gidan mai adaidaita ya sauke ni, hand bag dita na bude na basa kudin sa sai da na tsaya na karbi chanji na sannan na shiga tura madaidaiciyar akwati ta Ina turo baki gaba.


Baba mai gadi yana ganin shigowa ta ya saki fuskar sa sosai yana min Murmushi ya ce "Barka da dawowa A'isha sai yanzu kika tuno da mu ke da kika ce sati daya zaki yi ki dawo".


Kan table din da yake zaune na nufa na zauna kusa da shi nayi tagumi kafin na dago na kalle sa na ce "Baba kai baka san abinda aka shirya min a gidan nan ba, na tafi muna farin ciki da juna wai kwana na hudu da tafiya ashe har an yi cuku cuku an gama magana za'a kai ni makarantar kwana". Sai kuma na fashe da kuka, cikin kuka na cigaba da cewa "ni dai nasan ba wanda na bata wa rai kafin na tafi amma sai kawai labarin kai ni makarantar kwana nake ji".


Murmushi Baba mai gadi yayi ya ce "ban da abinki A'isha ai nasan su Abba baza su kai ki inda zaki sha wahala ba, kuma ai ana zuwa wa yan makarantar kwana ziyara ko?"


A dan fusace na ce "Baba baka fahimci mai nake nufi ba har yanzu ni Ina wani ruwa na da ana zuwa visiting ko ba'a zuwa kawai abin da na sani shine an gama da ni kawai".


Baba mai gadi dai bai gaji ba sai dan nasiha yake min ni kuwa nayi tagumi Ina sharbar kuka, muna zaune a haka Sultan ya shigo gidan, dan turus yayi gani na zaune Ina kuka kamar wacce aka aiko wa da sakon mutuwa.


Kara so wa yayi ya zauna a kusa da ni ko kallon sa ban yi ba sai dai kukan dana dai na, bamu yi wa juna magana ba har kusan minti 5 ya wuce.


Tsaki nayi ba tare dana kalle sa ba na ce "meye kuma zaka zo ka zauna anan ai ni tuni na fahimci cewa kai ashe ba masoyi na bane na gaske, in ba bakin hali ba wannan mummunan abun ya same ni amma ace kai zaka fara fada min kuma da murnar ka, ni Sultan daga yau kar ka sake min magana ma hanyar dani bi kar kabi don ba abinda zan yi da maciya amana irin ka".


Ajiyar zuciya ya sauke yana kallon fuska ta data yi jajir sbd kuka ya ce "kiyi hakuri A'isha wallahi lokacin dana ji su Baaba na magana na dauka ko basu yi serious sosai bane shiyasa na fada miki don na tsokane ki sai washe gari nake ji a bakin Ya Hamza wai har sun yi muku registration, ni tun da naji haka na rasa me yake min dadi kin fi kowa sanin dai bani da kamar ki, in kika tafi makarantar kwana ya zan yi da rai na".


Dan kallon sa nayi ido na yana ciko wa da ƙwalla ganin shima nasan idon da ƙwalla a ciki yasa ni sa hannu biyu na dafe kai na Ina rushe wa da kuka, shima kukan ya saki muka hada kai waje daya muna kuka.


Cikin kuka na ce "kayi hakuri Sultan kaddarar muce wannan kuma zamu cinye ta İn sha Allah, kar ka damu kamar yau ne zaka ga mun gama duka duka term biyar ne fah shikenan, in bana nan dai kayi min alkawarin ba zaka yi budurwa ba nafi so kayi karatun ka kar yan mata su dinga cinye maka savings din ka.


Shima cikin kukan ya ce "wani maganar budurwa kuma bayan ba kwanciyar hankali, in kika ga na kula wata mace ai sai kin dawo na gan ki garau cikin koshin lafiya, ni ba wannan bama yanzu dan abincin da muke ci da daddare in kika tafi shikenan ko?".


Kuka na sake fashe wa dashi har wani juya kai nake Ina kuka shima yana taya ni.


Baba mai gadi daya saki baki yana kallon su dariya da tausayi suka basa a lokaci daya sai dai ya daure yaƙi dariyar sai Murmushi kawai da yake. Horn da aka yi a gate din yasa shi mike wa da dan sauri ya bude gate din.


Ya Haidar ne yake tuka Abba, tun da ya danno hancin motar cikin gidan idon sa ya sauka akan su A'isha dake kuka kamar wadanda Iyayen su suka mutu, shi dariya ma suka basa sanin dalilin kukan nasu bazai wuce makarantar da su Aishan zasu je ba.


Sai da yayi parking a inda Abba ke ajiye motocin sa sannan ya fito ya buɗe ma Abban ƙofa, fito wa Abba yayi idon sa akan su A'isha da har a lokacin kuka suke.


Ɗan murmushi Abba yayi ya nufi gurin su, ɗan tsaya wa yayi yana kallon su ganin yadda suna ganin tahowar sa a tare suka rufe idon su suna cigaba da kuka.


Cikin taushin murya yace"kukan ya İsa haka to kar kuyi ciwon kai".


Sai a lokacin muka raba kan mu dake haɗe, cikin kuka na ce "Abbaaa Ina wuni, na same ku lafiya don ni dai Ina cikin tashin hankali"


Sultan ma cikin kuka ya ce "barka da dawo wa Abba, ka ga dai halin da muka tsinci kan mu ni da A'isha ko wa zuciyar sa suya kawai take yi da tiririn tashin hankali"


Cikin wani sabon kukan na ce "ai ni Sultan tawa zuciyar har ɗan maiko maiko take"


Ya Haidar da tun da yazo yake dariya ya dan saita fuskar sa ya ce "to zuciyoyin naku su ƙone mana saboda bacin ciki".


Juya wa nayi na kalli Sultan shima ya kalle ni kawai muka tashi tsaye muka rungume juna muna sake sabon kuka.......






DIJAHAM

***