FreeArewaPen original
ALƘALAMIN SO
- 1views
- 15chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · Page 1
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah. Ina mika godiya ta ga Allah daya bani ikon fara rubuta sabon littafi na cikin koshin lafiya, yadda na fara lafiya Allah ka bani ikon gama sa lafiya.Fatan alkhairi ga masoyana a duk inda kuke, Ina miko gaisuwa ta tare da muku albishir din sabon littafi na, Ina fatan zamu fara tafiyar nan tare daku mu gama tare In sha Allah. Ku sani Ina kaunar ku sosai masoyana🤌😂 fatan zaku cigaba da bani goyan bayan ku darı bisa dari. Ku biyo ni a cikin sabon littafi na wanda nasan In sha Allah zaku so shi sosai, wannan salon na daban ne da ban taba zuwar muku da irin sa ba muje zuwa dai domin na nishadan tar daku hadi da fadakar wa a cikin wannan labarin namu. ALKALAMIN SO BYDIJAHAM(Oum Amani)Page 1 Turo baki nayi gaba cike da shagwaba Ina kunkuni na mike badan Ina so ba zuwa toilet, sai da nafi 5mins a ciki sannan na fara wankan ina yi Ina zumbura baki badan yadda Uncle ya tsani kazanta ba kuma nasan yana gidan yau da ba abinda zai sa nayi wankan nan sosai da dakile kawai zan yi abuna kamar yadda na saba wasu lokutan in baya nan sbd sanyi.Shirya wa nayi tsaf cikin uniform dina riga fara mai dogon hannu sai straight skirt black color, kaina sanye da hula baka na rike socks dita fara kal da black karamin Hijab dina, dan kallan kaina nayi a mirror naga yadda fuska ta tayi fayau gashi ko kwalli ban sawa ido na ba duk nayi wani kala, fayau din dana yi sai hakan ya karawa fuska ta kyau sosai.Jakata na goyo a bayana na fito daga dakina Ina dan lumshe lulu eyes dina sbd baccin nan Sam baya İsa ta nidai, Mami ce tsaye a jikin dinning table tana hada min tea dagowa tayi ta kalle ni sannan ta kalli katon watch din dake manne a dinning area din, girgiza kai tayi tace "yi sauri mana kin tsaya kina tafiya kamar wacce Kwai ta fashe a ciki, tun dazu Sultan da Maryam suke zarya ke kawai suke jira ke dai kullum sai kin sa kun kusa makara ko?".Kara narke wa nayi Ina turo baki gaba idona suna sheki kamar hawaye zasu zubo min nace "ai Ya Kausar ce bata tashe ni da wuri bafa Mami"Harara ta kawai Mami tayi tana cire spoon din data gama juya min tea din tace "maza dauki ki shanye sa ynxun nan na saka miki toasted bread koza kici nasan halin ki ba hankali ya gama ishar kiba Maimakon in an fita break ki siyi Abu mai dan nauyi kici to baxa kiyi ba sai dai kawai ki ta narka wa cikin ki zaki".Nidai kallon ta kawai nake da manyan idanuna Ina Shan tea dina, ban yadda na cire cup din a baki naba sai da ma shanye sa tas, kitchen na kai na ajiye na fito da sauri na sa hijab dina da takalmi na sosai uniform din yamun kyau bama yadda hijab din ya Kara haska fuska ta sosai.Jakata na goya bayan nasa karamin conta...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.