Page 12
by @djham20
🤎🤎🤎🤎
*ELHAJJ*
🤎🤎🤎🤎
Free page 12
Written by
Mrs A.M
Marubuciyar
*NOOR*
*TASWIRAR KADDARA*
Wannan book din na kudi ne akan farashi mai sauki 300, ki biya kudin ki, ki karanta cikin salama ngd.
Ga mai son biyan kudin book din ku tuntubi wannan number din.
***
*BABY BEAUTY LOUNGE*
*INA YAN GAYUN SUKE MASU BUKATAR GYARAN JIKI, HENNA BLACK AND RED, PEDICURE AND MANICURE, MAKEUP, SALON KU GARZAYO ZUWA BABY BEAUTY LOUNGE DOMIN SAMUN DUKKAN WANNAN ABUBUWAN, HAKIKA GYARA SHINE MACE KUMA KO WACCE MACE YAR ADO DA KWALLIYA CE*
*INA MASU BUKATAR KOYAR MAKEUP DA SALON DUK MUNA YI A BABY BEAUTY LOUNGE CIKIN FARASHI MAI RAHUSA ZAKU SAME MU A TUDUN MALIKI TITIN ALASURE NO.995*
PHONE NUMBER *** OR ***
*MUNA SIYAR DA MAGUNGUNAN MATA DANA MALLAKA DUK A BABY BEAUTY LOUNGE*
Kallon ta kawai yake yaga yana kallon abincin take tana fadin daure daure Dije.
Girgiza kai yai a ransa yana fadin dama nace yarinyar nan bata da kai Sam.
Da kyar na tattaro nutsuwa ta duk da so take ta kwace nace "Ina wuni Ya Ustaz".
Ban za ya Mata don yau miskilancin yana kusa sosai.
Ganin ya min banxa na Kara bude baki nace "ina wuni Ya Ustazu".
Dago lumsassun idanun sa yai masu ruruta yan mata yace "waye Ya Ustaz din?".
Turo baki nai nace "kai mana".
Kankance ido yai yana mata kallon kasa kasa, samun kansa yai kawai da ce Mata "shekara ki nawa?".
Zaro ido nai sai kuma nayi saurin juyawa cike da kunya nace "saura 5 months na shiga 16".
Da mamaki sosai yake kallon ta ganin bai yadda ba yasa shi fadin "ban yadda ba".
Mai da kallona nai kansa nai rau-rau da ido nace "Allah ya Ustaz da gaske nake, na Kusa shiga 16".
Hararar ta yai yace "na dauka kin yi 20 ai".
Turo baki nai na shiga bubbuga kafafu a kasa cike da shagwaba.
Idanu kawai ya zuba Mata Yana kallon ikon Allah, ganin abin nata bana ka re bane yasa shi mikewa Yana shafa gemun sa dake kwance yace "kee! Lafia kike?".
A shagwabe na turo baki na gaba na makale kaina da kafada ta nace "ba kaine kace min na Kai 20 ba bayan har ynxu baby ce ni".
Kallon ta yai tun daga sama har kasa, kaikace ido yai yana mata wani irin kallo, shi dai kallon mace bai dame sa ba amma wannan Yarinyar ko da tana cikin hijab ya gane tana da kayan harka sosai.
Da sauri yayi Istigfari ya kawar da kansa daga kallon ta, baya bukatar bata answer don sam bai son ya cigaba da mgana da ita, wannan kallon da yai masa kadai nema yake ya taso masa da dukkan wani hakurin sa.
Abincin Kan table din ya kalla yace dauki kije ki ci.
Da sauri na kalli abincin ina hadiyar yawu sai dai tuno maganar Mama yasa ni a sanyaye nace baxan ci ba ngd.
Da mamaki ya kalle ta yace why?
Rau-rau nai da ido nace "Mama ta min fada sosai da na ce Mata rokar ka nai, har tana cemin irin haka ne samari suke amfani da damar in sunga yarinya na karbar abinsu Suma su fanshe a jikin ta, ni kuma ba haka nake ba wallahi".
Shiru nai ina goge hawayen daya zubo min na cigaba da fadin kuma ni sam bana kwadayi Allah, tsautsayi ne yasa ni rokar ka bani don kazar ta birgeni kuma ina jin yunwa amma baxan sake ba kayi hakuri.
Tun da ta fara magana yake kallon ta, a ransa yaji dadi sosai Ashe tana da tarbiyya kuma ya jinjina wa Mama sosai sbd a zamanin da muke ciki ba ko wacce uwa ce take tsaye akan yar taba har ma taji yadda take gudanar da wasu Abu nata.
(Ynxu da ace Mama bata bincikar Dije da watakila haka zata cigaba kawai komai ta gani ta nuna tana so kunga daga haka sai buri ya shiga zuciyar ta, kuma tabbas wannan zai bawa saurayi damar fara kai hannu jikin ta don ya latsa ta tunda tana karbar abin hannun sa).
Murmushi yai min Wanda ya kusa zautar dani wannan shine karo na farko da ya min murmushi tun haduwa ta dashi, tabbas murmushin ya dake ni bama yadda dimples dinsa suka lotsa sosai, nima sai na samu kaina da murmushin.
A hankali yace "ki godewa Allah Maman ki tana iya kokarin ta ganin ta baki tarbiyya, ki kula sosai kiji tsoron Allah".
Rau-rau nai da ido nace "insha Allah Ya Ustaz".
Hade rai yai yace waye "ya Ustaz din wai?".
Da sauri nasa hannu na rufe bakin ina cewa "afuwan".
iPad dinsa ya dauka ya fita daga office din gaba daya yana Jin wani iri a ransa, maganar sa da Dije ta tuno masa da tasa mahaifiyar, haka take itama tana gudun ya karbi abun wani ko yayi roko sbd kar ya tashi da matacciyar zuciya na komai sai dai yace a a bashi.
Murmushi yai yana fadin "Allah ya Miki rahama ya haskaka kabarin ki Ummana".
Ni kam da Naga ya fita daga wa nai na shiga gyaran office din ba algus, lokacin da nake wanke masa toilet kamar na cire kayana nai wanka, a rai na ina fadin da irin wannan toilet din ne damu a gida so 10 Zan dinga wanka kullum.
Bayan na gama jakata na bude na dauko turaren wutan dana kullo a leda, burner na kunna nasa turaren wutan nan da nan kamshi ya fara zagaye office din.
Murmushi nai ina sa hannu na akan kuguna, ina kallon office din ya min kyau sosai komai fess.
Turo kofar da akai ne yasa na juya ganin waye ya shigo, Yasir ne ya shigo hannun sa rike da file da alama ajiye wa zai yi.
Bin office din yai da kallo ya jinjina kai yace "lallai kanwata kin iya gyaran office har da turaren wuta".
Murmushi nai nace "eh mana, ai kasan shi turaren wuta yafi su air freshener din nan kama daki, shiyasa na dan dibo na Mama".
Dariya yai yace "lallai kuwa naga kokarin ki, MD nasan baxai yi saken da zaki kubuce masa ba don wannan gyaran ba na biyun ki".
Dariya muka sa a tare dai-dai lokacin kuma Salim da Elhajj suka shigo.
Kallon su kawai Salim yake kishi yana nukurkusar sa, fuska a hade ya kalli Yasir yace "mai kake yi anan?".
Da sauri ya sunkuyar da kansa kasa yace "File nazo ajiye wa Sir".
Tabe baki yai yace "ohk zaka iya fita".
Ko kallon su Elhajj bai yiba don basa gaban sa amma yayi karya in yace bai ji dadin yadda ya samu office din nasa fess ba duk da ba datti dama yai ba ga kuma kamshin da yake tashi.
Daga jiya zuwa yau ya fuskanci yarinyar tana da tsafta kawai dai matsalar kamar bata tsaftar jikin tane sai ta muhalli.
Kallona Salim yai fuskar sa dauke da murmushi yace "Khady ba gaisuwa".
Ba yabo ba fallasa nace "ina wuni Sir".
Murmushi yai sosai yace "lafia qalau Khady ya aikin, fatan dai baya miki yawa koh?".
Dago wa nai na kalle sa Naga ya zuba min ido yana kallona, turo baki gaba nai alamun ni an takura min na juya na kalli Elhajj da yake danne dannen sa a waya cikin kwanciyar hankali.
Kamar xan kuka nace "Ya Ustaz na gama Zan iya fita?".
Daga min kai yai ba tare da yai magana ba, shiyasa nima kawai na fita.
Ko da suka gama magana da Elhajj daya fito sai da ya tsaya ya kara min magana sannan ya tafi.
Bin sa da kallo nai na tabe baki kawai ina ma Yasir complain din nifa bana son wanna Salim din dai dariya yake min.
Tare da Baba muka koma, yauma sai da na bawa Mama labarin komai kuma bata min fada ba sai dai ta kara min nasiha akan na Kula sosai.
Sati na biyu da fara aikin nan na saba da mutanen office din sosai, sbd barkwanci na nida Yasir kuwa mun zama friends duk inda zai je ina raka sa.
Tsaka Nina da Ya Ustaz kuwa iya kaci gaisuwa da sa aiki nayi Ko na bari, a yan kwanakin nan ma na fahimci Yana cikin damuwa sosai.
Duk da ba fitowa yai ya fada min na amma na fahimta, ya rage yawan magana dama kuma can shi din ba mai magana bane amma ynxu abin yayi yawa, zan iya zuwa office har na dawo ko A baxai ce min ba duk sai na damu kuma.
Salim kuwa kusan ko yaushe Yana floor din mu, ko yace yazo min hira dana nuna masa bana so sai ya tsiri zuwa gun Elhajj sbd ya ganni.
Nidai na kawo Ido na zuba masa don ba abinda ya shafe ni da lamarin sa.
Yau sai karfe 4 na isa company din don na dan tsaya a makaranta sbd Exam din da zamu fara so muna revision.
Duk na gaji daga fara aikin nan bana samun lokacin kai na balle na je ziyawa gurin Inna, ban tsaya gaishe gaishe ba kamar yadda na saba gurin Baba kawai naje na gaishe sa na wuce floor dinmu.
Ban ga Yasir ba wata kila ko ya je wani gurin haka yasa na bude office din MD kawai na shiga.
Baya ciki amma sai kamshin sa da yake tashi kamar Yana zaune a ciki, murmushi nai ina jinjina son kamshi irin na wannan bawan Allah.
Gyara office din na shiga yi cike da nutsuwa, sai da na gama na kunna burner sannan na shiga dakin sa don gyarawa.
Na gama wanke toilet din ina cikin gyara masa gado Wanda kullum sai na gyara duk da bana ganin alamun ana kwanciya akai naji an bude office din an shigo.
Da sauri na karasa gyara gadon na zo lekawa nai ta jikin kofar Jin magana kasa kasa yana tashi, ban ga fuskar ko waye ba sbd ya juya min baya amma tabbas naga ya bude wata drawer dake office din da key yana yi yana juya don kar wani ya shigo.
Ban ga mai yake ba amma naga ya koma gurin computer din MD yasa wani abu kamar flash, bai 2 minutes ba ya cire yana gyara bakar rigar dake jikin sa mai hula.
Soke flash din yai a aljihun wandon sa ya juya zai fita, ban ga fuskar sa ba amma na lura da yadda yake sauri kafar sa ta hagu tana dan dingisawa wanda bana raba dayan biyu ko a dalilin saurin da yake ne kafar take dingishi ko kuma ciwo yaji a kafar.
Sai da Naga ya fita sannan nima na fito gabana yana faduwa sosai, a Palourn na zauna ina dafe kirjina.
Ni dai duk da karancin shekaruna amma nasan ko waye wannan tabbas wani mugun abu yake bin Ya Ustaz dashi, shiru nai ina buga tagumi don ban san mai zan yi ba duk jikina a sanyeye.
Ina zaune Yasir ya shigo hannun sa rike da file, kallon sa nai amma ban iya magana ba don jikina a sanyaye yake sosai.
Kallona yai ganin yadda nai shiru yasa shi Zama a gefen kujerar da nake yace "lafia kanwata ko baki jin dadi?".
Kallon sa nai a hankali na girgiza kai ba tare da nayi magana ba.
Duk sai ya bi ya rude yana tambaya ta ko wani abu ne yake damuna, ni dai shiru na masa kawai na rufe idona.
Shigowa yai yana tafiya cike da nutsuwar data zame masa jiki, kallon su yai yaga yadda Yasir yake ta tambayar ta ko wani abu ne yake damun ta.
Har zai wuce sai yaga rashin dacewar haka, ko ba komai a karkashin sa take aiki.
Gurin su ya nufa sai da ya tsaya a kanta sannan yace "lafia?".
Da sauri na dago ina kallon sa wani irin madarar tausayin sa tana kwaranya a zuciya ta.
Mike wa nai ina dan matsawa baya nace "Ina wuni Ya Ustaz".
Girgiza kai kawai yai yace "lafia, wani abun ne?".
Yasir da shima ya mike din yace "MD nima haka na ganta tun da na shigo".
Turo baki gaba nai a shagwabe nace "sbd kawai na saba surutu shiyasa don nayi shiru yau ake ganin kamar ban da lafia, gaskia ya kamata na daina surutu daga yau".
Tabe baki Elhajj yai yace "u're not serious".
Murguda bakina nai ina juyar da kai na gefe.
Da sauri ya bar gurin ganin murmushi na neman subuce masa, shi dai wannan Yarinyar tana basa mamaki sosai.
Yasir ma murmushi yai yace "amma kin bani tsoro gaskia, na dauka ko baki da lafia ne fah".
Dariya nai nace "haka kake Sona dama wai".
Fuskar sa dauke da Murmushi yace "ba dole naso kanwata ba, har Umma na fada mata cewa nayi kanwa a gurin aiki".
Dariya nai na bisa gurin table dinsa ina tambayar sa yaushe zai Kira min Umman mu gaisa.
Anan na zaune yana aiki ina kallon sa, daga fara zuwa na har na soma sanin wasu abubuwan a Kan computer da yadda ake sarrafa ta, don tunda na nuna wa Yasir sha'awa ta akan iya amfani da ita yake koya min kuma Alhamdulillah na fara fahimta.
Lokacin da aka tashi a kasa na samu Baba yana jirana, bayan machine dinsa na hau ina daga wa Yasir hannu muka wuce.
********
Alh Husain ya kalli Hajia Batula cikin jinjina kai yace "ina sauraran Hajia".
Gyara zama hajia Batula tai tace "na fadawa malamin duk abinda muke so, ba dai kudi keke so Yaya ya baka ba, sannan kuma in so samu ne ma duka dukiyar Ka ta Zama tasa".
Murmushi Alh Hussain yai yace "tabbas kuwa Hajia, ai ni kinga ko dukiyar sa bata Zama tawa ba ban damu ba, ni dai kawai ya bani kudin nan".
Murmushi itama tai tace "toh an gama, ya bani kwalli yace Ka saka a idon Ka, in zaka je gurin sa sannan Ka tabbatar cewa kun hada ido sannan Ka tambaye sa kudin, toh da a take a gun zai baka kuma baxai ce ka mayar masa ba".
Wata dariya Alh Hussain yai yace "Hajia Batula sarauniyar Mata, ynxu ma ai sai naje kawai koh ya kika ce?".
Da sauri tace "A'a ba ynxu ba dai koh, Ka bari sai zuwa gobe da daddare sai kaje kaga lokacin sawu sun dauke".
Daga kai yai yana Dan bata rai yace "gaskia amma ban ji dadi amma nifa a yau naso naji saukar kudin nan".
Dariya tai tana riko hannun sa tace "kwantar da hankalin ka shalelen Batula, kamar mun samu kudin nan mun gama.."
Nan suka shantake suna fadin yadda zasu samu kudaden nan Kota yaya ne....
*BOOK DINNAN NA KUDI NE AKAN FARASHI MAI SAUKI 300 KA/KI SIYA KI KARANTA CIKIN SALAMA, DUK WANDA YAKE SON SIYA YA TUNTUBI WANNAN NUMBERN*
***
Comments Nd share plz
Mrs A.M🥰