SARAUNIYAR KYAU (Book 1)

.

by @nkds

💋SARAUNIYAR KYAU💋


💄The Fashion Show💄




Tun kafin ta ƙarisa shiga palon take jiyo muryar su Lailah da alama gardama sukeyi ko makamancin haka.


Shiga tayi ciki a palo ta samesu su duka Afeefah, Lailah,da Haleesat saikuma wasu ƴan mata su biyu da alama ɗaya daga cikin su da ita akeyin gardaman, guri ta samu saman one siter ta zauna ba wanda ya lura da shigowar sai Afeefah hannu. Afeefah ta ɗaga mata daga inda take zaune a dinning Room tana cin abinci, alamar gaisuwa ita ma Zaynerb ɗin ta mayar ma da Afeefah martanin murmushi tana gyara zamanta a kujerar da take tana sauraron firansu Lailah tanason gano inda firar tasu ta dosa.

Abin dariya wai gardama suke akan film Yayinda Lailah take faɗin film ɗin, "TILL THE END OF MOON" yafi kyau ita kuma ɗayar matashiyar budurwar da aka kira da Ameenah take faɗin, ina ae film ɗin "THE LEGEND OF ZU yafi kyau👌


Ikon Allah Zaynerb ta furta ganin gardaman nasu yaƙi ƙarewa "wai akan menene ake wannan gardaman Zaynerb ta Tambaya kamar bata fahimci komai ba.


Da sauri ɗayar budurwar wacca bata saka musu baki a firan nasu ba ta ce "kema dai Sister Zaynerb ƙya tambaya wannan abu haka kamar wasu Yara wai akan film sukeyi fa" Ta faɗa tana taɓe baki alamar dai abin bai dameta ba.


Ohooo akan film ake wannan tada jijiyon Neck haka ashe, Zaynerb ta maimaita kamar irin tun farko bata fahimci abin ba.

"E` wai Haka matashiyar budurwar ta kuma bata amsa still Baki a kyaɓe dama gashinan kamar na hmm umm a gurin😇


"Yawwa Aunty Zaynerb raba garma dan Allah wanne yafi" cewar Ameenah cike zaƙuwa. "E to inaga dai "THE LEGEND OF ZU," Yafi kyau saboda ana zuba Love ciki koba haka ba?", Zaynerb ta faɗa tana yiwa Lailah dariya ganin yadda ta ɓata fuska ba'a yabi film ɗin da take supporting ba.


"Ato dama ni na sani wama zai haɗa, Ae kai dama daga ji kasan wanda yafi" Cewar Ameenah cike da farin ciki wai ita anyabi film ɗin da take supporting.

A fusace Lailah ta ce "ae shima dai "TILL THE END OF MOON," ɗin ana zuba soyayyar,"

"Eh dan soyayya anayi amma kuma ana magic ciki, Dan Haka ni nafi supporting "THE LEGEND OF ZU!, Ameenah ta faɗa lokacin da take ɗaukar handbag ɗinta tana gyara tsayuwa.


"Ah badai tafiya zakuyi ba dan Allah," cewar Lailah, eh tafiya zamuyi Ameenah ta bata amsa, ita ma ɗayar budurwar da suke tare da Ameena ɗin miƙewa tayi tana faɗin "To sai wataran kuma Ƙyawawan Ahalin Mister mai ƙyau. 

miƙewa Lailah tayi dan ta musu rakiya zuwa gurin motar su, sallama sukama su Zaynerb sannan suka fita Lailah na take musu baya suna ɗan taɓa fira suka fita.


Dawo da hankalinta Zaynerb tayi kan Haleesat dake kwance saman three siter da littafin koyon ITALIAN COOK a hannunta tana karantawa dayake Haleesat akwai sun karance karance especially na koyon girki amma badai ka ganta a kitchen ba, ɗan gyaran murya Zaynerb tayi tana gyara zama, Hakan da tayi ne yasa Haleesat kallon ta dan kuwa tasan indai Zaynerb tayi gyaran murya to gulma zatayi, Ganin Haleesat ta maido da hankalinta kanta ne yasa Zaynerb ɗin yin murmushi sannan ta ce "duk kin buɗe jiki gida ya cika da baƙi ke jiki ba suturan kirki ba" ɗan kallon jikin ta Haleesat tayi taga ta inda ta buɗe jikin, Sanye take cikin Riga t-shirt dark green sai wando jeans pencil dogo baki ta ɗaure gefen Rigar da wani bakin gyalle ta gefa Wajen waist ɗinta, sai hula dark green akanta an rubuta benz ajiki saita fito Like a indian actress Krithi_shetty.


"To menene a jikin nawa da yake a buɗe?", Haleesat tambaya dan kuwa ita iya dubawan ta bata ga wani aibun shigar jikinta ba, Lailah ce da shigowar ta yanzu kenan ta ca fe canzen da faɗin "a'a kidai duba ki gani ke baki ji alamar ana kallon ki ba tun ɗazu?", "Kallona kuma kamar YaYah kallo na ban fahimta ba" Haleesat ta Tambaya cikin ɗaurewar Kai da shiga confused.


"Eh ina nufin bakiji a jikin ki ana kallon ki ba" Lailah ta faɗa tana zama a two sieter ta ci gaba da faɗin "wannan ƙawar Ameenah ɗin tunda suka shigo idonta yana kanki ke bakiji alama ba?,"

Ɓata fuska Haleesat tayi dan kuwa sai yanzu ta gano abinda su Lailah keson ganar da ita cike da takaicin ƙare mata kallon da aka ce ƙawar Ameenah tayi ta ce "ni ina zan sani naje na saki baki ina karatu ashe ita tananan tana bina dana mujiya,"


Zaynerb tana cire hijjab ɗin dake jikin ta take faɗin "ae shiyasa ma dana shigo ko cire hijjab ɗin jikina banyiba yanzu duniya ta lalace mata ma bin mata suke Allah Yasa mu da ce kawai da ameen su duka suka amsa.


Afeefah da ƙarisowar ta gurin kenan hanunta ɗauke da ɗan tray ciki snacks da drinks ne. 

Ajewa tayi a saman Glass center table ɗin dake a palon sannan ta ɗiba snacks ɗin a plate ta zauna a two sieter kusada Lailah tana faɗin "Jama'a ga Valentine's cooking fah idan akwai mai buƙata tunda dukanku ba mai boyfriend balle ayi mishi."


 Afeefah ta tayi maganar tana kai kallonta ga Zaynerb dan taji mai zata ce, suma dai su Haleesat ɗin kallonta suke dan jin abinda zata faɗa.

Ga mamakin su sai sukaji ta ce, "Eh akwai wanda muka haɗu dashi a social media munyi dashi gobe zaizo mu haɗu karku damu ba zan mishi yadda nake ma sauran ba," Zaynerb tayi maganar tana miƙewa ta zuba lemon abarba da kwakwa ɗin da Afeefah ta haɗa cikin mug sannan ta zauna tana shan juice ɗin.


Haleesat da maganar Zaynerb na saurayi ya bata mamaki ta buɗi baki ta ce "Saurayi kuma Zaynerb kodai wasa kike?,"


Zaynerb da dama can da biyu tayi maganar tai murmushi kana ta ce "a'a da gaske ne gobe ma zaizo idan Allah ya kaimu zaku ganshi."

"Allah ya kaimu cewar Lailah da ta ɗauki remote control tana canza tasha zuwa korean drama [NO TURNING BACK ROMANCE].


A haka suka ci gaba da fira sama sama wanda yawanci Zaynerb ce mai janyosu da firan Yayinda da take ƙarewa Haleesat kallo tana nazarin ta da karantarta har can wajen shida na marece Momy Rafi'at ta dawo daga HOSPITAL dayake likitace babba ma dan kuwa har hospital gareta na Ƙashin kanta. {Mrs Mai ƙyau Pediatric Hospital}.


WANNAN KENAN


**


🅰🆁🅾🆄🅽🅳 9:20🅿🅼


Da dare Afeefah fitowar ta daga wanka kenan ta tsaya gaban dress mirror tana busar da doguwar sumar kanta da hand Drier saida ta busar da shi sannan ta nufi cloth set shiri tayi tsaf cikin kayan bacci riga fara mai taushi sai wando shima fari dogo kana ta ɗauki ribbons ta tufke gashin ta daya zubo mata har gadon baya, hula ta sa fara dayake ita ba ma'a bociyar sa kallabi bane, Saman doguwar softened stool ta zauna sannan ta ɗauki wayarta tana karanta Wani £nglish Novel.


Lailah ce ta shigo bedroom ɗin tana jan tsaki saman doguwar softened stool ta hangota a kwance ga waya a hannunta sai faman murmushi take ƙarisawa tayi ta zauna kusada ita.


Afeefah tana riƙe da waya tana zuba murmushi taji an wabce wayar, a firgice ta dubi Lailah dake sakin huci, malama bani wayata Lailah bata kulata ba ta koma ta zauna saman softened stool ɗin gefe tana dafe kanta.


Ganin haka yasa Afeefah tashi zaune tana kallon Lailah "what's wrong with you?", Afeefah ta tambaya Lailah lokacin da takai hannu goshinta da wuyanta tana so taji ko batajin daɗi ne Lailah bata kulata ba still.


Ganin haka yasa Afeefah ɗin dawowa kusa da ita ta zauna a ƙasa tana kallon ta a hankali ta kira sunan ta "Lailah!"


Kamar ba za ta kulata ba sai kuma a hankali Lailah ta ɗago tana kallon Afeefah amma har lokacin bata ce komai ba, cikin muryar kwantar da hankali Afeefah ta ce "Lailah pleased faɗamin meke damunki please Lailah tawa, Ajiyar zuciya Lailah ta sauke kana a hankali ganin yadda Afeefah duk tabi ta shiga damuwa da halin da take ciki.

Ckin murya mai sanyi kamar ba Lailah da Afeefah ta sani ba ta ce.

"ina cikin damuwa....

"Damuwa kuma?", Afeefah ta tambaya da sauri, girgiza kai Lailah tayi sannan ta ci gaba da cewa "ina cikin damuwa sosai, wallahi sister na rasa ya zanyi...

Shiru Afeefah tayi tana kallon ta ganin haka yasa Lailah ci gaba da faɗin "ina cikin damuwa guda biyu na farko akan family na kinga YaYa Maleek har yanzu ba'a san duniyar da yake ba gashi Daddy yaƙi sawa a nemo shi tunda ya bar gida har takai ta kawo ko maganar shi Daddy bayaso ayi mishi ga matsalar xixi ya kunno kai ta nace saita dawo gida gashi nayi nayi ta faɗamin abinda ke damunta taƙi ga shi ɗazu ɗazunnan munyi waya da Aunty Nailah faɗamin take wai zata dawo gida cuz sunyi rigima da mijinta, kuka fa ta kirani tanayi, A lokacin saina koma kamar ni ce YaYar ita kuma ƙanwar da kyar nasamu ta haƙura amma ta ce saita dawo gida gashi kinsan halin Daddy ba barinta zayyi ba tunda ga yadda tun farko yanayin auren nata ya kasance dama Daddy ba wani son auren yayi ba kin sani, ita kuma Aunty Nainarh munyi waya ita ma dai ba daɗi abin, wai dangin miji sun saka ta a gaba da maganar rashin haihuwa gashi ita kuma Momy ce matsalar Dan tun farko bata amince da Auren Aunty Nainarh ba, Toh kinji dai...

Lailah ta ƙarishe maganar tana mai jan dogon numfashi.

Tunda ta fara maganar Afeefah bata dakatar da ita ba saida taji tayi shiru.


Ajiyar zuciya Afeefah ta sauke tana kallon Lailah kallon mamaki dan kuwa gani take kamar wannan Lailah dake zaune a gabanta ba Lailah da ta sani bane, Lailah dai mace mai son kanta wacca bata damu da damuwar kowa ba sai nata kuma ba ruwanta da sha'anin kowa sai nata, Lailah da ake mata Kallon Haughty lady, Amma yau gata a gabanta tana faɗa mata damuwar wasu,Lallai.


Da wani ne ya faɗa mata wai cewa koda nan gaba ne Lailah zata damu da damuwar wani, ba zata yadda ba amma yau gashi taji kuma ta gani Lailah ce a gabanta tana koro mata damuwar wasu, Yaran Momy Rafi'at shida ne Abdulmaleek ne Babba, Sai masu bi mishi Nainarh nd Nailah twins ne, Sai kuma Haleesat wacca rana ɗaya aka haifesu da Zaynerb, Haleesat da safe ita kuma Zaynerb da Yamma aka haifeta sai kuma Lailah mai bima Haleesat, Sai Zinaru Auta sakamakon taci sunan kakar su ne mahaifiyar Momy Rafi'at Yasa ake ce mata xixi Yaran Momy Rafi'at Ba wasu shekaru masu Yawane a tsakanin su ba Haleesat da Lailah shekara biyu ne a tsakanin su, suma sauran Yaran duk shekara biyu biyu ne a tsakanin su kuma ko wanne halin sa ya banbanta, especially ma Lailah da halinta yafi banbanta dana sauran Yayyinta ana cewa halin Momy Rafi'at tayo a wasu lokutan.


Ganin kamar Afeefah ta shiga duniyar tunani ne yasa Lailah ɗan tafa hannu a fuskar Afeefah ɗin, "Hey my friend menene kina jina ma kuwa?," Lailah ta faɗa tana kallon yadda Afeefah ta zuba mata ido tana kallon ta.

Firgigit Afeefah ta dawo hayyacin ta daga duniyar tunanin da ta faɗa ajiyar zuciya ta kuma saukewa a karo na biyu tana kallon Lailah sannan ta ce "indai akan wannan ne kika shiga damuwa ki kwantar da hankalin ki, Domin zanyi ma Daddy maganar da na tabbatar da zai fahimce ni akan su Aunty Nainarh harma da YaYa maleek ɗin insha Allah zai fahimta kuma zaisa a nemo YaYa maleek ɗin a duk inda ya shiga, Kinga saiki saki ranki ko saiki faɗamin damuwar naki na biyu muji ko zan iya yi miki solving ɗinta," Afeefah ta ƙarishe maganar tana murmushi.


Ita ma Lailah ɗan murmushin tayi tana kallon Afeefah ƙaunar ƴar uwan na ta na ƙara shiganta, "A'a shi wannan ba wani matsala bane sosai kawai dai Uncle Al'ameen ne ya takura min da maganar soyayya kuma ni kinsan tsarina ba soyayya a tafiya ta, Dariya Afeefah tayi "kina bani mamaki Lailah wani lokacin saiki ce wai ba soyayya a tsarin ki to haka zaki dogara ba aure ina tausayin ki duk ranar da soyayya ta shige ki ba zata miki shigan sauƙi ba Allah, Kuma da kike maganar Uncle Al'ameen ae naga ya daɗe yana ƙaunar ki kawai ki bada kai musha biki sister, Afeefah ta ƙarishe maganar tana dariyar shaqiyanci ganin yadda Lailah ta haɗe rai.


"Ke sis feefah bana son wulaƙanci fah, kisani ae idan ma maganar gaskiya za'a bi kece zaki fito da miji musha bikin tunda naga kullum sai an miki layi wajen zuwa fira," Tamke fuska Afeefah tayi ta ce "amma dai kinsan aure lokacin ne ko zan fito da miji soon amma sai buri na cika dan kuwa ae amfanin soyayya aure," Murmushi Lailah tayi dan kuwa tasan babban burin Afeefah shine zama SARAUNIYAR KYAU👰👸


"Sha re wannan topic ɗin kinji ga wani Special Dress fa na samo amma naga alamar nuna tsiraici zayyi yawa ciki amma duba ki gani", Afeefah ce mai maganar tana nunawa Lailah Dress ɗin da ta yi searching a wayarta, Karɓa Lailah tayi tana faɗin "Okay sis let me it, Sannan ma ana bedroom ɗin zan kwana".

Baki da damuwa madam Lailah Mai ƙyau, Cewar Afeefah cikin murmushi.

Murmushi Lailah tayi ita ma haka suka ci gaba da fira har can Afeefah ta ce bacci take ji sannan ta kwanta, Saida Afeefah ta ɗan daɗe da kwanciya da alama ma bacci yayi gaba da ita, sannan ita ma Lailah ta kwanta tana ɗan murmushi a zuciyar ta furta ina ƙaunarki ƴar uwata duk da cewa ba ciki ɗaya muka fito ba amma muɗin JINI ƊAYA NE tunda dai mahaifin mu ɗaya, addu'a tayi ta shafe jikinta sannan ita ma sarkin ɓarayi yayi gaba da ita


🅷🅰🅻🅴🅴🆂🅰🆃♥︎🅼🅰🅸♥︎🅺🆈🅰🆄


Misalin ƙarfe goma sha ɗaya da rabi na dare ta shirya tsaf cikin wasu ƴan iskan kaya doguwar riga maroon color mai hannu ɗaya anyima rigar tsagu tun daga cinya zuwa ƙasa, sannan ta ɗauki takalmi heel mai tsini shima maroon color tasa ta ɗaure igiyoyin jiki, Ga gashin kannan nata ya sha gyara in Braid style, Ɗaukar dogon hijab har ƙasa fari tayi tasa da niƙab sannan ta ɗauki jakarta ta fito, A hankali take sanɗa saɗab saɗab saida ta tabbatar da ba kowa a palon sannan cikin sauri ta nufi kitchen ta buɗe ta ƙofar kitchen ta fita sannan tabi ta garden ko tsoron dare bata yi tabi ta ƙofar dake garden ɗin wacca aka mata ado da wasu flowers masu shaining a qawace ta fita.


A hankali Momy Rafi'at wacca akan idanunta Haleesat tayi duka abinda tayi tun daga kan fitowarta daga bedroom ɗinta bin da tayi ta ƙofar kitchen fitarta ta garden, duka abinda ya faru ta gani daga tsayen da take, Zuge curtain ɗin window ɗin tayi sannan ta koma ta zauna a saman Royal bed ɗinta na alfarma, Wayarta ta ɗauko ta kira lambar Haleesat amma a kashe, Murmushi tayi tana gyara zaman ta saman Royal bed ɗin, Still tana kuma sakin murmushi mai ɗauke da ma'anoni kala kala.

Kwanciya tayi abinta kamar ba uwan da taga ɗiyarta ta fita ba cikin dare baccinta tayi hankalinta kwance..............{ Ikon Allah sai kallo 🏃🏃}


🆉🅰🆈🅽🅴🆁🅱♥︎🅼🅰🅸♥︎🅺🆈🅰🆄


Tana so tasha whiskey ko kwalba ɗaya ne amma kuma tana tuna alƙawarin da tayi ma Afeefah na bazata ƙara shan wani abu daya danganci maye ba, Wanda wannan dalilin ne yasa ta tashi ta ɗauro alwala a Bathroom, nafila tayi raka'a huɗu sannan tayi sallama Al qur'ani mai girma ta ɗauko tayi tilawa sannan Batareda ta cire hijjab ɗin dake jikin ta ba.

Ta tsaya gaban window tana shaƙar fresh air, Kamar da wasa ta hango mutum yana sanɗa ya nufi hanyar garden.

Tuni ta fahimci ko wacece Haleesat ce domin kuwa two months da suka gabata ta fahimci Haleesat tana satar hanya tana fita da dare, Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta koma ta zauna saman bed tana mai yima Haleesat addu'ar shiryuwa a ƙasan ranta don banda wannan ba abinda zata iya mata.


Ita kuwa Haleesat tana fita ta nufi wata Jar mota ƙirar BMW dake a pake acan gefe, shiga tayi cikin motar ƴan mata ne aciki su uku biyu a gaban mota, Ɗaya a baya duk da Haleesat suka zama su huɗu.


Cire dogon hijab ɗin dake jikin ta tayi tare da Niƙab ɗin tana faɗin, "Oh God zufa huh", Budurwar dake kusa da ita tayi dariya tana faɗin "Baby leesat yau fa kin ɓata mana lokaci wannan tsayawa ɓadda kaman da kikayi".

"Ke dai rabu dani kawai, Kinji ki Zuree babe yanzu ma da ƙyar na fito, Samu nayi ba kowa a palo ma shiyasa kuka ganni, Cewar Haleesat lokacin aka tayar da motar suka bar gurin suna taɓa fira da budurwar da ta kira da Zuree babe da kuma sauran ƴan matan biyu dake gaban motar Feenah da kuma ɗayar budurwar Jenny.


𝔻𝔸𝔾𝔸 𝔸𝕃Ƙ𝕃𝔸𝕄𝕀ℕ✍️ 𝕋ℍ𝔼♥︎ℕ𝔸𝕀ℕ𝔸ℝℍ♥︎𝕂𝔻📲


Isarsu Night club ɗin suka fito a tare, Haleesat ce a tsakiya hannunta riƙe da hannun Zuree sai kuma Feenah ita ma hannunta riƙe da hannun Jenny shiga ciki sukayi, wa'iya zubilla ƴan mata ne kawai ciki kamar yaran arna ba wata suturar kirki bane a jikin su, abin dai ba ƙyan gani ga samari nan iri iri kuma abin da zai kuma ba mutum ta kaishi da mamaki shine zallah gurin Yaran Hausawa ne birjiq😭


Shigarsu wajen keda wuya, nanfa kiɗa ya canza manyan Yaran sun iso nan wajen ya ɗauki sowa da tafi faɗi, Suke ga manyan Yaran masu ji da lokaci sun iso ae dole a basu guri, don masu guri sun ƙariso, haka suke ta faɗi Cikin Yanayi irinna su.


Kujeru masu arnen kyau suka zauna akai Haleesat tare Zuree a kujera mai mazaunin mutum biyu sai Feenah tare da Jenny a ɗayar kujerar ita ma mai mazaunin mutum biyu sai fasa musu kai ake da yabo su kuma suna ƙarajin ba kamar ya su lokacin sune bawai bane😎


Wani ƙayatacen Tray na glass mai ɗauke da whiskey kala kala ma'aikacin gurin ya kawo ya aje saman glass table ɗin dake a gaban su sannan ya koma ya kawo wani tray ɗin kuma daban mai ɗauke da glass cups na zinare ya aje, Sannan cikin nutsuwa yake zuba musu whiskey ɗin acikin cups ɗin Haleesat ya fara miƙa ma dan kuwa ita ce jigon abun mahaifin ta yafi mahaifin su Zuree kuɗi nesa ba kusa ba shiyasa suke girmama ta ba kaɗan kaɗan ba shiyasa ta zama kamar ita ce shugaban su sai abin da ta faɗa ake bi.


Wani irin tsawa Haleesat ta bugawa ma'aikacin wanda yasa saida ya kusa zubar da whiskey ɗin dake hannun shi tsaban firgita da tsoro.

"Bala'i amma Kai wani kalan bagi dajen mutum ne ka taɓa ganin nasha whiskey a gurin nan, Ko shashancine da rashin kulawa yasa zaka bani whiskey saboda ka mayar dani nonsense wacca batasan abinda take yi ba.

Cike da masifa da kuma gadara Haleesat take maganar tana girgiza ƙafa, Game da sakin huci dan ƙiris ya rage ta kai mishi mari...

Gabaɗaya hankulan wasu daga cikin maza da mata na gurinne ya dawo kansu domin ganin abinda ke faruwa.


Shi ko ma'aikacin mai suna Vinood sai faman bata hakuri yakeyi duk yabi ya haɗa uban zufa jikin shi sai faman rawa yakeyi tsoron shi ɗaya shine karya ya rasa aikin shi a gurin.


Ganin Haka yasa Feenah wacca duk cikin su tafisu sanyin hali kuma bata cika san hayaniya ba, Alama tayiwa ma'aikacin daya tafi ya bar gurin, da sauri kuwa ya bar gurin har yana tuntuɓe.


Kamo hannun Haleesat Feenah tayi tana faɗin "please baby leesat ki kwantar da hankalin ki yanzu zai kawo miki abin da kike buƙata kinji?", Feenah ta faɗa hakan ne saboda tasan Haleesat bata shan whiskey ko kuma Wani Abu daya danganci kayan maye...Tafi ganewa ta busha shisha ko wani abun, Amma bata shan kayan ruwa ma'ana abin da ya danganci maye. 

Ajiyar heart Haleesat ta sauke sannan ta ce "ba damuwa kawai dai ya ɓata min raine amma ba komai "forget about the pass".

Murmushi Feenah tayi "shiyasa nake son ki ta waje na akwai ki sauƙin hali", Feenah ta faɗa tana komawa ta zauna.

Feenah ƴace ga Alhaji Sulemanu canji, shahararren ɗan canji ne a garin Abuja da kewaye, Yana da kuɗi obaa highly dan kuwa bayan harkar canji da yakeyi ɗan kasuwa ne shi na bugawa a jarida, Feenah itace ƴar shi ta biyar mahaifiyar ta ta rasu tun tana da shekaru sha biyu a duniya a gurin kishiyar uwanta take.


Yayinda Zuree take ƴa ga malam Adamu jama'are mahaifin ta shahararren malami ne a garin Abuja asalin shi ɗan garin jama'a re ne na jahar Bauchi, Kasuwanci ne da kuma malimta ya dawo dashi garin abuja har ya gina family ɗinshi anan yaran shi tara, Zuwairiya wato Zuree ita ce ta fita zakka a yaran malam Adamu dan kuwa ƴar malam ce wacca taƙi halin malam.


Sai kuma Jennifer lopez, wato Jenny mahaifin ta cikake kuma shahararren mai dukiya ne a garin Abuja sannan kuma pastor ne wanda akeji dashi Jenny ta kasance, Ƴar shi ɗaya tilo tsoka ɗaya a miya shiyasa take abin da taga dama saboda a sangar ce iyayen ta suka raine ta bata san wani abu waishi wahala ba a rayuwa dukansu ajin su ɗaya a University sannan kuma course ɗaya suke karanta wato Microbiology.


Dogon tsaki Zuree taja tana faɗin, "Wallahi Baby Leesat kina Bani mamaki da takaici bansan ranar da zaki waye ba wallahi ke ba shan wannan kayan ruwa ba, Bakya taɓa harkar nan ke gabaɗayanki sai aslow wallahi", Tayi maganar cike da takaici.


Haleesat bata kulata ba da dan kuwa idan da sabo yaci ace ta saba da wannan tsoki burushun na Zuree.

Saima cewa da tayi, "Okay guys kuzo mu motsa Jiki mana,"

Gabaɗaya su ukun tashi sukayi gabaɗayan su suka hau kan dandamali nanfa akayi changing ɗin wakar speakers ɗin CLUB ɗin zuwa wani korean song na zamani, habba nanfa suka fara dancing kamar ba gobe cike da kwarewa suke rawan su abinsu ba ruwansu.


Tsaye take can ɗaga wani ɗan korido na club ɗin, Yayinda take ƙarewa club ɗin kallo dama society ɗin dake ciki.


Pin-up dress ne a jikin ta, Riga black color sai belt golden color da ta kama ƙugunta ta ɗaureshi, Rigar iya gwiwar ta tsaya sannan kuma ta kama ta ɗam, ga wani tsinannen takalmi hill a ƙafafunta kanta kuwa yasha kitson attach mai masifar tsada, Hannunta na hagu kuwa zanen tattoo ne brown color.

Doguwa ce sosai dan kuwa a shekaru ba za ta haura ashirin da uku zuwa da huɗu ba, Idonta yana sanye cikin wani arnen glass no respect launin eye balls ɗinta kuwa abin burgewa ne ga mai kallon tsakiyarsu launin Blue color suke.


Hannyenta rings na diamond masu masifar kyau da tsada ne, Ga wata arniyar chain na diamond a neck ɗinta siririya mai kyau da kuma tsada, Ear ɗinta kuwa ba`a magana wasu kalan earings ne a kunnenta na diamond amma kuma Yanayin shape ɗinsu cross ne, Fuskar ta kuwa tasha light make-up launin hair ɗin ta kuwa brown color ne dogo, ta fito sak Like a indian actress RAKUL PREET SINGH fara ce tas fatar ta har wani shaining takeyi saboda haske gashi kuma ya haɗe da jindaɗi Yanayinta tafi kala da mara sa son Hayaniya obaa highly.


Hannu tasa a pocket ɗin rigarta ta ciro wayar ta ƙirar iPhone 14promax daga inda take a tsaye take ɗaukar Haleesat a hoto, Tayi sunkai kala biyar sannan ta turawa wata number wanda akayi saving da MR. AMIGO sannan ta kira lambar cikin sa'a kuwa ringing ɗaya aka ɗauka magana ta fara cikin Harshen

farasanci, "Hello Mr. Amigo ga wasu pics nan na turo maka nan da gobe nakeso a samomin taƙaitaccen tarihin Yarinyar cikin pics ɗin in Tomorrow please."

On the other hand mutumin shima cikin Harshen farasanci ya ce "shikenan madam amma nace!,"

Bata tsaya jin abinda zai kuma cewa ba ta katse wayar ta mayar cikin gown pocket ɗin ta sannan ta fito daga cikin club ɗin gabaɗaya motar ta ƙirar bugatti ta shiga taja motar da gudu ta bar gurin.


A takaice dai su Haleesat basu suka bar club ɗinnan ba sai wuraren ƙarfe biyu da rabi na dare kamar yadda suka saba sauke ta sukayi a gurin da suka ɗauke ta ɗazu har zata fita a motar ta tsaya jin abinda Jenny take faɗa.

"Wai guys baku kula da wata red ɗin mota da take binmu ba tun ɗazu na lura da'ita fah, Tunda muka fito daga club Take binmu."


Ɗan juyawa sukayi a tare suna kallon inda Jenny ke nuna musu motar a daidai lokacin kuma motar dake binsu ƙirar Benz tayi ribas tabar gurin da speed, Tsaki Haleesat taja irin she don't care ɗinan "koma waye ne matsalar shine fa ba wai namu ba" Ta faɗa hakan yayin da take barin gurin bata tsaya jin abunda suke faɗa ba da sauri ta buɗe ƴar ƙaramar ƙofar da take bi ta gurin ta wuce.

Kai idan baka lura ba bama zakace da hanya a gurin ba balle har a sama ƙofar wucewa saboda gurin akwai wasu flowers da suka rufe ƙofar sai suka zama kamar kwalliya.


Cikin sanɗa take taku harta shigo palon gidan sannan in rushing ta wuce bedroom ɗinta.

Zaynerb da har gyangyaɗi ya fara ɗaukar ta, Baiwar Allah ajiyar zuciya ta sauke ganin Haleesat ta dawo cikin ƙoshin lafiya, Miƙewa tayi ta shige bathroom tanajin zuciyar ta ba daɗi, It's Necessary gareta ta sama Haleesat akan wannan satar hanyar da take tana zuwa Night Club, Ba tare da sanin ƴan gida ba.

Bayan wasu mintuna ta fito ɗaure da brown towel a chest ɗinta ko lotion bata tsaya shafawa ba cikin sauri sauri ta shiga cloth set ta shirya cikin sleeping dress riga na saka maroon color doguwa, Saman bed ta hau tayi addu'ar bacci sannan ta lumshe kyawawan idanun ta bayan wani lokaci bacci yayi awon gaba da ita.


Haleesat kuwa tana shiga bedroom ɗinta kai tsaye bathroom ta shige bayan ta cire dogon hijab ɗin dake jikin ta da niƙab da ta qwaqwama.

After some minutes ta fito jikinta sanye cikin bathrobe gaban dress mirror ta tsaya tana ƙara goge sumarta, da ɗan ƙaramin towel ɗin dake hannunta zama tayi akan stool na madubi tana shafa lotion Bayan ta gama busar da gashin kannata saida ta kammala shafa lotion ɗin, Sannan ta miƙe ta shiga cloth set ta shirya cikin pyjamas mai taushi milk color, System ɗinta ta ɗauka ta koma saman mattress ta zauna tana sarrafa system ɗin ta ɗauki lokaci tana amfani da system ɗin sannan ta mayar da system ɗin ma'ajiyar ta, Kana ta koma saman bed ɗin ta kwanta, Pillows ta rungumo a chest ɗinta tana sauke ajiyar zuciya ba batun addu'ar bacci a haka har sarkin masu iya sata yayi gaba da ita.


Can cikin baccinta mai daɗi taji ana tashin ta ana jijjigata ana kiran sunanta.

A hankali take buɗe lumtsatstsun idonta mai cike da bacci, Biji biji ta fara ganin mutum a gabanta kafin idanun ta suka buɗe duka.

 Afeefah ce tsaye a gabanta tana sakin murmushi, riga ce short a jikin ta iya ka gwiwar ta sai dogon wando ga apron blue color da ta ɗaura a saman rigar jikinta, Kanta kuwa hular apron ɗinne shima blue color da alama kitchen zata shiga.


"Aunty Zaynerb" "Aunty Zaynerb!! ki tashi mana tun ɗazu naketa faman tashin ki, kitchen zamu shiga kinsan yaufa Aunty sa'adah bata ta tafi garinsu," Afeefah ce ke maganar tana tashin Zaynerb.


A Hankali ta sauko daga saman mattress ɗin miƙa tayi tana karanto addu'ar tashi daga bacci clock ɗin dake manne a wall na ɗakin takalla ƙarfe bakwai na safe da sauri ta diro daga saman gadon tana faɗin "Yah Allah yaushe lokaci ya tafi haka ban tashi nayi sallah ba," Bathroom ta shiga da sauri bayan wani lokaci ta fito ɗaure da towel fari a ƙirjinta dubawa inda tabar Afeefah tayi, Bata da alama ta fita ne, Cikin sauri ta zura doguwar riga, A jikin ta sannan ta saka hijab ta tayar da sallan asuba bayan ta iddar cire hijjab ɗin tayi sannan ta fito kitchen ta Shiga.


A can ta samesu da Lailah suna kici kicin haɗa breakfast.

"Yauwa Aunty Zaynerb please ɗan kira Haleesat tazo muyi mu kammala haɗa breakfast ɗinnan tare", Cewar Afeefah ba tare da kalla Zaynerb ɗin ba.


Fita Zaynerb ɗin tayi ɗakin Haleesat ta shiga bata ciki dubawa bathroom tayi nanma bata, Fitowa tayi zata koma kitchen ɗin a palo sukayi karo da Haleesat Jogging suit ne a jikin ta da alama daga morning Exercise take.

"Good Haleesat ki shirya Yau dai kitchen za'a shiga dan haka ki shiga ki shirya muna kitchen muna Jiranki, Kinsan dai Yau Aunty sa'adah bata nan kuma su Ummi da Elina Basunan".

Zaynerb ta ƙarishe maganar tana bin ta gefan Haleesat zata wuce, Da sauri Haleesat ta sha gabanta a ɗan hasale ta fara magana "waime? ni Haleesat ni ce zan shiga kitchen ɗin huh to akan wani dalili?".

Murmushi Zaynerb tayi sannan ta ce "akan dalilin da yasa kike cin abinci mana" tayi maganar tana kuma bi ta gefan Haleesat zata wuce, "Yauwa kuma kiyi sauri fa, dan kinsan umarnin shalelen Daddy ne ba'a sanya ko jin kiri, Idan kuma akayi tofa rai yana ɓaci kinsan da wannan.

Tana gama faɗin haka tayi gaba abinta.

Tabar Haleesat da cizon yatsa tsaki taja tana bin Zaynerb ɗin da kallon banza dama can basa ga maciji da Zaynerb ɗin cuz indai zasu zauna guri guda tofa saisun raba hali.

Ɗakinta ta shige dayake ɗakunan nasu a jere suke ɗakin Afeefah ne a farko sai na Lailah sai kuma na Zaynerb dake ɗayan Wall side ɗin sannan sai na Haleesat a ƙarshe.