SARAUNIYAR KYAU (Book 1)

.

by @nkds

*💋💋𝑆𝐴𝑅𝐴𝑈𝑁𝐼𝑌𝐴𝑅 𝐾𝑌𝐴𝑈💋💋*


*👑The Queen Of Beauty 👑*


/𝐓𝐡𝐢𝐬 𝐏𝐚𝐠𝐞 𝐈𝐬 𝐃𝐞𝐝𝐢𝐜𝐚𝐭𝐞𝐝 𝐓𝐨 𝐙𝐢𝐞𝐞𝐲 𝐌𝐮𝐜𝐡 𝐋𝐨𝐯𝐞🥰/


💄The Fashion Show💄




"Zaqwaqwurar mu ta uku, kuma ta ƙarshe a wannan gasar na SARAUNIYAR KYAU matakin Jaha, ba kowa bace fa ce ABHI GAIL ELIAS, so that, muna gayyatar miss Abhi Gail, izuwa saman floor, domin ta karɓa gift nata na mussaman kuwa."


Da takun ƙasaita take tafiyar kyakyawar budurwa har ƙarisa gurin Sandra, sannan ta tsaya fuskar ta cike da annuri.

Haɗaɗɗen Diamond ring da chain ɗin shi suna shaining da ƙalli, Sandra ta miƙa ma ta tana mai tayata murna, cike da murna Abhi Gail ta karɓa gift ɗin sannan sukayi pictures kala biyu da Sandra kana ta koma ta tsaya kusada su Afeefah da Sameeha. (💋ZAQWAQWURAN MU💋)


Mrs William ta ci gaba da faɗin "munataya ku murna sosai kyawawan ƴan matan da suka sama nasara a wannan gasar, hakama sauran da basu sama nasara ba, muna tayasu jaje, sannan ku sakama ranku shekara mai zagayo daku za'yi."


Nan ta ɗan basu baki da tausasan kalamai. Dan kuwa babu daɗi mutum ya shiga gasa ko waca kala ce, ace bayyi nasara ba.


Tana kammalawa ta koma ta zauna, sannan ɗayar Baturiyar ita ma ta miƙe tayi taƙaitattun maganganu.


Sannan ita ma baƙar fatar cikon ta huɗun su, ta miƙe ta ɗanyi ƙarin bayani daga ƙarshe ta rufe da faɗin "muna yiwa kowa da kowa duka waɗanda suka halarci wannan special gasar muna godiya sannan kuma muna fatan kowa zai koma gidajensu lafiya kamar yadda kukazo lafiya."


Tana gama faɗin haka ta koma ta zauna daga haka taron gasar SARAUNIYAR KYAU matakin jaha ta shekarar yazo ƙarshe, daganan mutane suka fara tashi ana watse wa, daga ɓangaren ƴan matan gasa kuwa, suma komawa sukayi ta gurin da suka shigo sannan jajayen labulayen gurin suka koma da kansu su haɗe.


💗Ahalin Mai Kyau💗


Tsaye suke gaba ɗaya a gurin da sukayi parking tsadaddun motocin su, daga harabar Hall ɗin na taron, suna jiran ƙarisowar Daddyn da kuma Sarauniyar wato Afeefah 😍


Lailah ta ce "a gaskiya wannan gasar ta ƙayatar dani sosai, da ace ina da account na Tik Tok ko kuma Facebook da Instragram dana ɗaura ɗaukar, saboda abin ya tafi yadda nakeso, especially ma da Afeefah tayi NASARA a gasar ga Kalar dressing ɗin da tayi ya tafi da mutane highly."


Zaynerb ta amshe da cewa "aha ƴar uwa, ai Lailah ina faɗamiki abin yayi yadda ya kamata Allah ya kaimu Gasar na matakin ƙasa, akwai ɗaukar SHOW kuwa, huh wayaga Afeefah Mai Kyau As Sarauniyar Kyau ta ƙasa huh The Glam Queen."


"Ina da tambaya, wai shin a'ina ne, za'ayi na ƙasa ɗinne, naji wannan Baturiyar ta ce 'nanda one month' amma bata faɗa ko'a ina za'ayi ba."


Deejarh tana dariya tayi musu tambayar, Lailah ta bata amsa da, "inaga a Lagos za'ayi, nanda wata ɗayar kamar yadda kikaji ta faɗa, muna fatan shima na matakin ƙasa ɗin ƴar uwanmu Afeefan mu ta lashe gasa."


Wani ihun murna Zaynerb ta saki da ƙarfi, a lokacin da ta duba wayarta taga abin da ke faruwa ciki faɗa take "muje zuwa Guys, aha ai yanzu aka fara gasar akwai na matakin Ƙasa yana nan tafe, ku saka ranku a inuwa." Ta ƙarishe faɗar hakan tana tsalle abin ta Like a Little Kid.😎


Har rige rigen ƙarisawa gurin ta sukeyi domin ganin abin da ke cikin wayar nata da ya sakata ihun murna a cikin mutane haka.


Tsakanin Haleesat, Lailah Deejarh.

Haleesat ce ta rigasu ƙarisawa don haka, wani cafka takaima wayar dake a hannun Zaynerb ɗin, saiga wayar a hannunta da sauri tayi unlocked na wayar tana dubawa, lokacin Lailah da Deejarh suma sun ƙariso gurin Lailah cikin haki abin ka da ba'a saba ba 😅


Cikin Tik Tok Account na Zaynerb ɗin, ta tsinci wayar, da sauri ta shiga duba videos na Show ɗin da Zaynerb ta ɗaura a Tik Tok Account ɗin nata, videos ne kala kala kusan kala goma. Na farko daga ciki ta shiga ta fara dubawa, cikin ƴan mintunan da Zaynerb ta saka Videos ɗin, har ta sama Likers kusan mutune fiye da dubu ɗari, ga ruwan Comments kala kala kusan na mutane dubu goma, Kai bama iyaka ƴan Najeriya ba kowa yaba wannan gasar SARAUNIYAR KYAU na garin Abuja yake kowa da abin da yake faɗa akai.💃💃


Kakkaurar ajiyar zuciya Haleesat ta sauke ta ce "A gaskiya wannan Fashion Show, Championship ya karɓu a gurin mutane sosai, duba fa, ki kalla yadda mutane maza da mata suke zuba ruwan like da comments kala kala a wannan videon."

Tayi maganar tana ƙarisawa gurin Momy Rafi'at ta miƙa ma ta wayar Zaynerb ɗin.

Da sauri Momyn ta karɓa wayar kamar mai jira ai nan take tahau washe baki tana yabawa.


Ita dai Zaynerb tana daga gefe tana kallon ikon Allah sannan kuma idan angama a bata wayarta.😂


"Kema Auntie Haleesat ina ce kin saka a Instagram Account ɗin ki ko?, ki duba mana domin muga halin da ake ciki."


Lailah ce tayi maganar cike da zaƙuwa game da farin ciki. Da sauri Haleesat ta saka hannunta a cikin handbag ɗinta ta ciro wayarta da ya ke babu Password kai tsaye Instagram ɗin ta ta shiga bayanta kunna Data.


Zaro ido tayi waje ganin uban likes da comments da take samu suna shigowa babu qaqqautawa. Dalilin ganin yadda Haleesat ta kasa magana ne gaba ɗaya, yasa Lailah ta karɓa wayar tana dubawa. Murmushi tayi ganin ashe anan Instagram manyan qwarin suke likes ne da comments kawai ake zubowa ta wayar Haleesat kamar kamar me.

Shiga tayi cikin wani Video akalla likes ɗin da Video ɗin ya samu sunkai one million a iya tunanin ta fa.😎


Ɗagowa tayi cike da farin ciki zatayi magana ta hango Afeefah da Daddyn suna tahowa Afeefah sanye cikin kayan Gasar amma yanzu ta saka mayafi fari tayi rolling kanta dashi sai dai ta cire Fancy Glass ɗin fuskar ta.


Da sauri Lailah ta ƙarisa suka rumgumo juna da Afeefah cike da farin ciki, bayan sun gama Deejarh da ta ƙariso ita ma tayi hug ɗin Afeefah tana faɗin  "Balarabiyar Indiata ina ta ya ki murna sosai sosai, sannan ina cikin farin ciki mara adadi fa"


Murmushi Afeefah tayi sannan ta ce "Ina godiya sosai nima Deejarh tawa Allah ya bar ƙauna mara adadi tsakanin mu."


Mister Mai Kyau ya ce cike da zolaya "Yanzu dai a barmin Shalele taje ta shiga mota driver yaja mu tafi gida, sannan ayi taya murnar a gida can ina ga zaifi. Dariya sukayi sannan babu musu suka ɗun guma cikin motocin su cike da farin ciki sai gida.


KANO


HUMAIRA


Humaira zaune suke a ƙaton wajen gunadanar da gasar SARAUNIYAR KYAU matakin jahar Kano, wanda ya sama hallatar manyan mutane maza da mata da ƙananan yara hadda ma Larabawa da Turawa da kowa da mutane, gurin ya haɗu sosai sosai. Especially ma saman floor ɗin gaba ɗaya launin komai na gurin sky blue and White color ne, jama'a ƴan kallo gaba ɗaya an nutsu ana jira a fara gunadar da Gasa. Daga gefe gasu Photographers nan birjik, ga ƴan gidan T.V nan, ƴan jarida ne da sauransu ana sai ta camerori ana jira lokaci ya cika da.


Daga ɗayan gefan kuwa Alƙalan Gasar ne kamar yadda aka saba mutane huɗu Baƙaƙen fata biyu, sai Baturiya ɗaya sai kuma wata Kyakyawar Balarabiya suna zaune saman wasu haɗaɗɗun kujeru irinna zaman manyan mata masu jida kansu, ga wasu uban littafai da papers a gaban kowannensu, mutane an cika gurin ba masa tsinke gurin yayi tsit ana jira lokaci ya cika a fara kafta Gasa.


MISALIN ƘARF£ GOMA SHA ƊAYA DAI DAI...


Humaira suna zaune a first chairs na gurin ita da Ni'ima dake a gefanta na hagu sai kuma Auntie Mrs Komai Naka, daga gefan dama, sai su Auntie Nafeesa da su Na'ima.


Gaba ɗayansu sun bada hankulansu suna jira suga kyakyawar da zata fara fitowa. ah domin kuwa taron na kyawawa ne.


TOHM


Ta wani dogon korido wata haɗaɗɗiya kuma kyakyawar budurwa ta fito tana takun gayu, tana sanye cikin shigarta na Gasar tayi kyau harta gaji da yin kyau ɗin, duk taku ɗaya da zatayi sai ta tsaya masu ɗaukar hoto sunyi ma ta sannan...


Da sauri Humaira ta ciro tsadaddiyar wayarta a jakarta, ta fara ɗaukar Video ana gudanar da Gasar, ita kuma tana ɗaukar duk wacca tazo sai ta ma ta Video idan ta koma kafin wata tazo sai tayi saving ɗin Videon a wayarta, idan wata ta fito ita ma ta ma ta nata ɗaukar daban.


TOFAH


Gasa ta fara ɗaukar ɗumi fa, a domin kuwa ƴan matan Gasar biyar har sun fito saura biyar kenan.


Gaba ɗaya gurin ya kuma yin shiru ana jira budurwa ta shida ta fito. domin ganin nata salon kyawun😘


WOW


Daga ganin irin shigar Princely Dresses ɗin da take ciki sai ka rantse ƴar sarkin ETHIOPIA ce, saboda tsananin kyau irin kyawun da tayi.

Tayi irin kyan nan na bugawa a kowani irin takarda da kuma bayyanawa game da nunawa a gidan talabijin na duk duniya.

Irin kyawun nan wanda samari suke poster su dinga liqawa a unguwa unguwa fa, tayi kyau as Diamond.


So Casual and Perfect take cikin wata arniyar Gown sky Blue irinna ƴa ƴan sarauta. Har ƙasa rigar ta sauka ma ta.

Pastel twist hair ɗinta lulluɓe da wata kalar mayafi sky Blue mai adon stones, fuskarta tasha make-up abin sai wanda ya gani, hannayenta cikin wasu handgloves sky Blue irinna Princely Princess, hannunta na dama riƙe da wata ƴar siririyar sanda mai launin sky Blue and purple color, shima dai irinna na yaran sarauta, kai idan nace zan tsaya lissafo kalar kyan da tayi sai a kwana ba'a kai ko rabi ba, saboda haka just kuyi imagine kawai guys 🥳


Kyawawan ƙafafunta kuwa cikin wani haɗaɗɗen Crystal Princess Heels mai shaining, launin shi white and blue color, ga kyawawan idanunta masu launin Ash color cikin wani arnen glass no respect mai launin sky Blue.


Tafiya take a dogon koridon Hall na Gasar har ta ƙariso tsakiyar floor ɗin. So Casual and Perfect Jiddarh ta gama haɗuwa tako ina abin dai hmm hummm sai mai iya imagine, gata kyawun ta Natural ne babu ƙarin na kanti ko kaɗan fa.


Fuskar ta cike da fara'a take kuma taku mai cike da salo na musamman, tunda Jiddarh ta fito gurin ya ɗauki ihun murna anga kyau kamar a wanke hannu sannan a taɓa.


Daga ɗayan ɓangaren kuwa gaba ɗaya Photographer's sun tattare hankulansu guri ɗaya suna ɗaukar hoton Jiddarh domin takai a ɗauketa hoton, harta wuce matsayin tuni.

Sai da tayi mintuna biyar dai dai sannan ta koma ciki, wata ta fito haka abin ya dingi tafiya har akazo kan ta goma kuma ta ƙarshe wacca daga ita shikenan Bye Bye Gasa😊


Ita ma dai ta haɗu babu ƙarya sam z tsarin, sai da ta goma tayi five minutes kamar sauran ta koma, bayan mintuna goma ansamu dai gurin yayi tsit sannan...


Miƙewa ɗaya daga cikin Alƙalan Gasar tayi tana magana cikin harshen Turanci magana take akan yadda su duka suka nuna farin cikin su akan hallatar Gasar da mutane sukayi sannan suka bada gudun mawa wajen ganin Gasar ya tafi yadda ya kamata, kana ta gangaro da maganar nata akan ƴan matan Gasa, ta ɗanyi bayani a taikace sannan ta bada dama duka ƴan matan Gasar su goma suka hallara a tsakiyar gurin Gasar.


Madam Miracle ta ci gaba da cewa "A halin yanzu zamu ji kuma mugani sannan musan wacca ta sama nasarar lashe wannan Gasar ma'ana dai tazo ta ɗaya."


Tayi maganar tana duba wata white paper doguwa dake a hannunta na dama tayi murmushi sannan!.


Ta ci gaba da faɗin "Ya kamata mu taya Malama Jiddarth Komai Naka, murnar lashe wannan Gasar na SARAUNIYAR KYAU matakin jaha...Dan haka cikin girmamawa muna gayyatar Malama Jiddarth izuwa saman floor domin ta karɓa gift ɗinta na musamman da ta cancanci samu."


Ta ƙarishe maganar a yayinda take kallon kyakyawar Diamond Lady ɗin da sunanta yake a matsayin Jiddarth har cikin zuciyarta ta yaba da kyawu da komai na Jiddarh, don ita Jiddarh ake kira one in Dollars bama

 million ba eheee . 🤗😁


🎀J££DD@RH🎀


Fuskarta kawai idan mutum ya kalla zai fahimci tana cikin farin ciki ba ɗan ƙarami ba, farin ciki irin wanda mutum baimasan taya zai bayyana shi ba.

Tafiya take cikin nutsuwa a yayinda zata ƙarisa ta karɓa gift a matsayinta na wacca ta lashe Gasar SARAUNIYAR KYAU matakin jaha. A garin Kano Najeriya.


Sannu a hankali take tafiyar yayinda duk taku ɗaya da zatayi sai kaji ƙarar Crystal Princess heels ɗin dake a kyawawan ƙafafunta.


Ɗoss, Ɗoɗɗos, Ɗas, Ɗas.


Haka sautin yake bayarwa, gaba ɗaya gurin yayi tsit hankulan mutanen gurin gaba ɗaya yana akanta.


Qarisawa tayi saman floor ɗin sannan taja ta tsaya a gaban Madam Miracle, murmushi Madam Miracle tayi sannan ta ɗauko wani haɗaɗɗen box Blue color an nanɗeshi da wasu kyawawan igiyoyi Yellow color and other's ta miƙa ma ta tana faɗi cikin ƙasa da murya.


"Malama Jiddarth ina tayaki murnar lashe wannan Gasar ina fatan zamu haɗu a gasar SARAUNIYAR KYAU matakin ƙasa?."


Washe fuska Jiddarh tayi sannan ta ce.


 "In Allah ya yarda."


Ta faɗa hakan a lokacin da Madam Miracle ta miƙa ma ta box ɗin, harta juya zata koma, Madam Miracle ta ce


"Baki ji ba,"


 

Juyowa Jiddarh tayi tana kallon ta, murmushi Madam Miracle ta kumayi sannan ta miƙawa Jiddarh wani haɗaɗɗen Diamond Ring ta ce "Wannan dagani ne, na baki kyauta saboda kyanki kawai." 😃


Ihun mutane da sowa gurin ya kuma ɗauka kamar kamar mene.

Dariya kawai Jiddarh takeyi a lokacin da Madam Miracle ta kammala zura ma ta Diamond ring a yatsarta na Ƙarshen hannun damar ta, godiya tayiwa Madam sannan ta juya tana nunawa mutane gift ɗinta da kuma tsadadden Diamond ring ɗin bayan komai ya lafa ta koma ta tsaya a gurin ta.


Haka aka ci gaba da kiran sunayen ƴan matan Gasa har aka zo kan ta uku, aka bata kyautarta sannan ta dawo kusa dasu Jiddarh da budurwar da tayi ta biyu ta tsaya.


Madam Miracle ta ci gaba da jawabi cike da qwarewa da sanin takan abin, ana cikin haka ana shirin tufe taron kenan wata kyakyawar matashiyar budurwa daga cikin sauran ƴan matan Gasan bakwai ta zube a gurin a sume.


Da sauri wata kyakyawar budurwa daga cikin ƴan kallo ta hau saman gurin tana kiran sunan budurwar da ta suma da alama budurwar Ƴar uwanta ce, duk yadda akaso wannan budurwa ta farka daga suman da tayi abu ya cutura, haka aka kwasheta ranga ranga zuwa asibiti.

Daga haka kuma taron dai ya tashi jikin kowa yayi sanyi laqwas.


Da gudu Jiddarh ta ƙarisa wajen su Humaira da suke tsaye curko curko a harabar Hall ɗin taron, bata damu da tarin mutanen dake kallonta da ɗaukar Video da kuma hotunan ta ba.


Rungumo Humaira da Auntie tayi a tare tana dariya.

"Oh Allah wai ke Jiddarh bakya girma ne?, ai wannan sai ki karyani fa." Cewar Auntie tana dariya.


Dariya Jiddarh takeyi ta ce "Auntie na ina farin ciki da murna yau, kawai dan ma abin da ya faru yanzu ya ɗan sanyaya min jiki ne, don da alama yarinyar ta gaza jure rashin nasara ne shiyasa harta suma ko?."


Humaira ta ce "E, gaskiya abin akwai taɓa zuciya wata ƙila tayiwa Gasar dogon buri ne, sai kuma Allah yasa ba ita zata sama Nasara ba, sai ita kuma ta saka jure hakan ta sume."


"Koma miye matsalar ta can taje taji dashi ba damuwar ku bane, kuji da abin da yake a gaban ku yarana."


Cewar Auntie tana ya mutsa fuska. Da tsananin mamaki su biyun suke kallon ta jin abin da ta ce Jiddarh mamaki ya hanata magana, sai Humaira ce tayi ƙarfin halin cewa.


"Auntie wai mane naji kina faɗane?, mutum ce fa ita, kuma mace dole zataji babu daɗi kinsan zuciyoyin mu ma ta akwai rauni."


Ɗan dafe goshi Auntie tayi tana cizan harshenta ganin tayi sakin layi a gabansu.😳


"Auntie dake fa nakeyi, kin min shiru?." Humaira ta faɗa a hasale tana fitar da numfar fashin ɓacin rai.


Gane yanayin da Humaira ta shiga ne yasa Auntie saurin kamo hannunta tana faɗin.

"Am so sorry my Dear, it's all my fault, na yadda bai kamata nayi wannan maganar ba. Amma ki yafeni kuskuren baki ne."


Da ƙarfi Humaira ta qwace hannunta daga cikin na Auntie, ta buɗe mota a fusace ta shiga ciki.

Ajiyar zuciya kawai Auntie take saukewa cike da tsaban tsoro, kamo hannunta Jiddarh tayi idanunta sun cicciko tab da qwalla ta ce "Dan Allah Auntie karki saka wannan abun a ranki, saboda ke mahaifiyarta ce kinsan dai ba halinta bane raini, bata cikin hayyacinta ne shiyasa.


Ɗan murmushi Auntie tayi sannan ta ce "Ba komai Jiddarh na sani gaskiyarta ne duka laifina ne, da banyi wannan maganar ba, da ranta bai ɓaci ba, har waɗannan mutanen su leƙo kuma a fusace."


Magana Auntie takeyi tana leƙen motar da Jumaira take ciki.


Hakan da tayi da kuma maganar da tayi duka ba ƙaramin dariya taso ta ba Jiddarh ba. Amma ta danne ta ce "Auntie wai ina su Sister Ni'ima ne suzo mutafi gida, lokaci yana ƙurewa fa, naji da wannan ɗaukar Video da hotunan da ake min."


Murmushi Auntie tayi ta ce "Su Ni'ima akwai gurin da zasu biya, ki shiga mota kawai mu tafi gida zamu haɗu dasu acan.


"To" Jiddarh ta ce sannan ta nufa motar da Humaira take ciki. Da sauri Auntie ta ce "A'a Jiddarh inaga kizo wannan motar da nake mu tafi tare naga kamar mutanen basu koma ba."


Qumshe dariya Jiddarh tayi tana rufe baki ta ce "A'a Auntie barni na shiga wannan kawai, ai sun sanni Abokai nane, babh abin da zasumin fa domin mun saba."


Tayi maganar tana buɗe motar zata shiga, Auntie ta ce


"Ni dai ba ruwa na, Jiddarh tunda kince wannan motar zaki shiga su waɗannan mutanen ba ruwan su da wata Abota ko ƴan uwan taka uban mutum zasuci da gayya." 😝


Dariya Jiddarh tayi sannan ta shige motar ta zauna gefan Humaira dake waya abin ta. Daga ɓangaren hannun hagu ta zauna sannan driver yaja suka fita daga gate ɗin gurin motocin nasu guda huɗu rass, sannan suka ɗauki hanyar gida ɗoɗar.


A hanya Jiddarh ta ɗan kalla Humaira sai kuma da sauri ta kauda kanta tana karanto duk addu'ar da tazo bakinta, ƙara kallon Humaira tayi a zuciyarta ta ce "Wata ƙila sun koma."


Ɗan taɓo kafaɗun Humaira tayi cike da tsoro, wani irin juyowa Humaira tayi gaba ɗayanta tana kallon Jiddarh da idanunta waɗanda suka canza kala izuwa dark maroon.


Wani irin fitsarin tsoro ne yazo ma Jiddarh amma ta maƙale shi tana zare ido, so take tayi ihu koda driver zaiji ya tsayar da Motar kota samu ta tsere, amma ta kasa daga ta buɗe baki sai taji kamar an mayar dashi da ƙarfi an rufe. Ba abin da takeyi sai zufa ƙoƙari take tayi hawaye koda zasuji tausayinta. amma mandaƙas idanunta suke ko ɗan qwalla babu.


Matsawa jikin murfin mota take yayinda Humaira take biyota kamar wata 😘.


Wata dabara ce ya faɗo ma ta da sauri ta lalubo wayarta, a cikin jakarta dake a hannunta, cikin rawar hannu ta lalubo lambar Humaira ta danna kira.


Kai tsaye kiran ya shigo wayar Humaira dake saman cinyarta sautin zazzaƙar muryar Ahmad Sulaiman yana karanto suratul Ma'ida ya karaɗe motar.


Firgigit Humaira ta dawo hayyacinta, wata wawiyar ajiyar zuciya Jiddarh ta sauke sannan tayi rejected kiran, kallon Humaira tayi tana murmushin yaƙe ta ce "Uhm sannu Humaira kin farka daga baccin kenan.?"


Ya mutsa fuska Humaira tayi tana faɗin "Wai ya akayi ma na ganni a mota ba'a tsaye muke ba munajiran ƙarisowar Ni'ima.?"


Da sauri cikin sarƙewar murya Jieddarh ta ce "E, e mana kwarai, ai a tsaye muke sai kikace muzo mu tafi gida bacci kikeji, wannan ne abin da ya faru fa."


Qura ma ta ido Humaira tayi tana kallonta sannan ta ce "Ya naga kina inda inda kodai ƙishi kikeji ne.?"


Da sauri Jiddarh ta fara tari kamar da gaske tana faɗin "Ruwa, a bani ruwa please, dai dai lokacin da driver ya shiga da motar gidan.


Fitowa tayi daga motar tana riƙe baki kamar mai jin ƙishin da gaske da sauri Auntie ta ƙariso gurin tana tambayar ba'asi.


Cike da damuwa Humaira ta ce "Wai ƙishi takeji shiyasa take tari fa."


Kallon Jiddarh Auntie tayi zatayi magana Jiddarh ta kashe ma ta ido ɗaya, tuni Auntie ta ramfo abin da take nufi. Dan haka kallon Humaira tayi ta ce "mu shiga ciki ko."


Da gudu Jiddarh ta taye sama bayan sun shiga palon saboda sauri in twin's take taka staircases ɗin hannunta na rawa tasa key ta buɗe Bedroom ɗin ta.


Da ido Auntie da Humaira suka bita da kallo Sannan Auntie ta dawo da kallonta kan Humaira cike da tuhuma ta ce "Menene ya faru a mota naga kamar bata cikin nutsuwar ta.?"


Fuskarta da alamar Rashin jindaɗi Humaira ta ce "Nima dai bansan abin da ya faru ba, farkawa kawai nayi na tsinci kaina a cikin mota driver yana tuƙi ga Jiddarh a gefena, shi ne na tambaye ta abin da ya faru tahau inda inda, bayan na tambaye ta ko qishi takeji sai ta hau tari ba ƙaƙƙautawa."

Humaira tayi maganar tana zama a two sieter.


"To Allah ya kyauta gaba."


Cewar Auntie a lokacin da tayi picking call ɗin da ya shigo wayarta, sannan tayi hanyar kitchen tana magana.

Da ido Humaira ta bita sai kuma ta taɓe baki tana gyara kwanciyar a saman kujerar da take akai.


Jiddarh kuwa tana shiga haɗaɗɗen palon ta wanda ya gaji da haɗuwa, jifa tayi da handbag ɗinta saman kujera sannan ta ɗauki ruwan roba a fridge tasha, kana ta dawo ta zauna akan kujera tana kici kicin rage kayan jikinta.


 

Sai da ta kammala cire doguwar gown ɗin jikinta sannan ta miƙe ta shige Bedroom a saman bed ta aje gown ɗin sannan ta shiga bathroom.

Sai da ta kwashe mintuna Ashirin tana wanka kana ta fito ɗaure da towel White color a chest ɗinta.


Gaban Dress Mirror ta tsaya tana kallon kanta tayi murmushi afili ta ce "Saini Jiddarth ɗiyar Ahalin Komai Naga, yau na cinye Gasar SARAUNIYAR KYAU matakin jaha saura na ƙasa, ina fatan kamar yadda na lashe wannan shima na lashe shi." 😎


Sai tayi shiru da sauri ta ɗauki red jam baki ta buɗe, sannan ta zizara a saman jajayen laɓɓanta kana ta mayar da jam bakin saman Dress Mirror.


Kallon kanta ta kuma a madubi washe baki tayi a fili ta kuma cewa "Amazing Masha Allah sai ni Jiddarh kuma fa wallahi ina da kyau sosai. Ya Allah wannan baiwar ta ka Jiddarh tana godiya da wannan hallitar da aka ma ta bada wayonta ko dabara ba."

Kwance Ribbons ɗin da ta ɗaure dogon gashin kanta tayi aikuwa gashin ya zubo ta gabanta da bayanta duk yabi ya rufe ma ta fuska.


Gefe ta matsa da gashin da ya rufe ma ta fuska, kallon kanta ta kumayi a madubi ta ce "Wash sai ni Jiddarh SARAUNIYAR KYAU a garin kano, wannan kyau haka aiko Larabawa da Turawa saina cinyesu a Gasa bansani ba."


Dariya tayi sannan ta ɗauki kwalli ta kuma zizarawa a dara daran kyawawan idanunta, bayan ta gama haka ta ci gaba da yaba kanta da kanta har sai da gaji dan kanta sannan ta hakura dan kanta.