SARAUNIYAR KYAU (Book 1)

.

by @nkds

*💋💋𝑆𝐴𝑅𝐴𝑈𝑁𝐼𝑌𝐴𝑅 𝐾𝑌𝐴𝑈💋💋*


*👑𝑇ℎ𝑒 𝐺𝑙𝑎𝑚 𝑄𝑢𝑒𝑒𝑛👑*




____*


Tun ana saura kwanaki takwas a ɗaura Auren, Abubakar ya dena zuwa gidansu Rafi'at domin kuwa bai ga amfanin zuwan nashi ba, ita ma dai Rafi'at ta wani ɓangaren jindaɗinta ne hakan, tunda dai wata magana zata dena shiga tsakanin shi da Haleesat Rashid Rayyan.


Rayuwa ta ci gaba lulawa kwanaki suna raguwa a kullum kwanan duniya lokaci daɗa ja yake yi domin shi baya jira sai dai a jira shi.


_____*


"An ɗaura Auren Abubakar Sadeeq Sameer Lamiɗo da zankaɗeɗiyar Amaryarsa Rafi'atu Rafiq Rayyan akan sadaki mafi daraja da cancanta lakadan ba Ajalan ba.'


Wannan maganar da wani maroƙi yake yi yana ƙarawa, ita ce ta dura a kunen Haleesat Rashid Rayyan tamkar Saukar Aradu.


Dafe kanta dake faman sara ma ta tamkar zai rabe gida biyu tayi da duka hannayenta babu abin da take furtawa a bakinta fa ce kalmar.


"Inna-lilahi-wa-inna-illahir-raji'un. Alhuma-la-sahla-illa_ma-ja'altahu-sahlan,wa-anta-taj'alu-l-hzana-idha-shi'ta-sahlan.


Ya Allah! Babu wani abu mai sauƙi sai abin da ka sanya shi ya zama mai sauƙi, kuma kai kana sanya tsanani idan ka so ya zama sauƙi.''


Haka kawai take iya furtawa a bakinta zubewa a ƙasa tayi tsakiyar Bedroom ɗin.

Wai meke shirin faruwa da ita ne?. wannan wata kalar makauniyar kaddara ce, ta rasa wanda zata so sai Saurayin Yayarta, a halin yanzu kuma miji a gareta...


"Kai! Kai!! Ya Allah! Allah na tuba, wannan wata kalar makauniyar soyayya ce?."😭


Ta furta a fili cikin matsanancin kuka, baiwar Allah gaba ɗaya tabi ta fita a hayyacin ta, komai abin mutum ya ganta cikin halin da take ciki sai ya tausaya mata.


Ta daɗe a wurin tana gurzar kuka kamar ranta zai fita. Kafin daga baya jin an fara knocking bedroom ɗin, yasa ta miƙe tsaye da kyar, ta shiga bathroom wanka tayi sannan ta fito zuwa lokacin kumburar da idanunta suka yi, sun ɗan ragu ba laifi.


Cikin kayanta na Anko ita ma ta shirya tsaf, sannan tayi kwalliya sama sama ba domin ya ƙara ma ta kyau ba sai dan ya rufe kumburin idanunta.


Ɓangaren da Amarya da ƙawaye da Ƴan uwa suke ta wuce kai tsaye.


Ita ma aka ci gaba da shagalin biki da ita, amma gaba ɗaya jikinta a sanyaye Yake.

{Allah sarki macen fah ke nan, komai tana iya shanyewa, tana iya sadaukar da farin cikin ta akan farin cikin wani mutum daban, zaka samu a koda yaushe fuskarta a washe take da fara'a, amma kuma can ƙasan zuciyarta ita kaɗai tasan abin da takeji. Mata na gari Allah ya ƙara ɗaukaka ku, sannan kuma Allah yasa kuci ribar haƙuri duniya da lahira Ameen}...🙏


Zuwa ƙarfe huɗu da rabi na marece, masu ɗaukar Amarya suka zo domin sai an fara kaita Jigawa State wurin dangin ango, sannan bayan kwana uku zuwa lokacin sun gama shagulgulan biki da na al-ada.

Sai a dawo da ita danƙareran gidan mijinta wanda Abubakar ya gina anan Abuja.


Tayi sallama da Ƴan uwa da Abokan arziki, sannan suka kaita wajen Dadynsu ya ma ta nasihar da ko wani uba na gari yake yiwa ɗiyarsa kafin a wuce da ita ɗakin miji.


Sannan aka fito da ita, suka shishshiga motoci aka nufa Jigawa State.

Amma har lokacin da aka fita da ita daga gate na gidansu ko gudan hawaye babu a idanunta.🌚


*JIGAWA_STATE_NIGERIA_*


Sun isa Jigawa State da Amarya Rafi'at wuraren ƙarfe takwas da rabi na dare, dangin Amarya sun sama tarba na mutun tawa da dajara a wurin dangin ango manyan mutane.


Haka ma sauran kwanaki uku da suka yi suna ganin yadda aka sha shagulgulan biki dana al-ada. Lafiya aka watse sannan kuma a rana ta huɗu aka juya da Amarya Abuja izuwa gidan mijinta abin alfarin ko wata matar kirki.


Sun isa Abuja City wuraren ƙarfe biyar na yammaci da yake ba fitowar wuri suka yi ba.


Da isarsu tanƙameman gidan Abubakar Mai Kyau, kai tsaye aka wuce da amarya ɗakinta bayan ansa tayi addu'a kafin shigarta cikin gidan, haka ma da zasu shiga ɗakin sai da tayi addu'a, kana ta saka kyawawan ƙafafunta na dama wa'danda suka sha jan lalle ta shiga cikin haɗaɗɗen Bedroom nata a gidan mijinta Abubakar Mai Kyau.


Zuwa ƙarfe tara na dare kowa da kowa an watse, an barta ita kaɗai domin kuwa ba ango ba labarinsa.

Ganin haka yasa bata wani damu ba a nata tunanin tunda dai an ɗaura aure tofa anyi mai wuyan, bathroom ta shiga tayi wanka haɗe da ɗauro alwala.


Sannan ta fito ta shimfiɗa darduma a wajen da aka tanadar domin yin sallah, sannan tayi magarib da isha'i waɗanda bata samu tayi ba tunɗazu.


Shiru shiru dai Amarya Rafi'at Rafiq Rayyan tana jiran ƙarisowar angonta Abubakar Mai Kyau har wajajen ƙarfe sha ɗaya na dare, amma shiru kakeji ba ango ba labarin sa kamar yaro yaci shirwa.


Harta fara gyan gyaɗi tajiyo ƙarar mota, alamun ƙarisowar angonta Abubakar Mai Kyau. Abin ƙaunar ta.


Cikin sauri ta miƙe ta ƙarisa wajen window, sannan ta ya ye labulayen sannan ta buɗe gilashin, tana leƙen farfajiyar gidan.


Hango shi tayi sanye cikin suit Ash and White color wa'danda ba ƙaramin Kyau, suka masa ba.


Karɓar Briefcase ɗin sa ya yi a wajen P-A. Ɗin sa sannan cikin sauri sauri ya shige ciki a dalilin Ruwan sama da ya tsinke kamar da bakin qwarya.


Da sauri ta saki labulen sannan ta mayar da gilashin ta rufe, kana ta dawo gaban madubi tana kallon kanta.


Murmushi tayi sannan ta cire hijjabin jikinta ta a je saman bed saboda ta fita ta tarbe shi.


Tana fita shi kuma a daidai lokacin yasa hannunsa ya buɗe ƙofar Bedroom ɗinsa da key, sannan ya shiga kana ya dawo da ita ya rufe.


Rafi'at tana masa magana amma ko kulata bayyiba, kuma tanada tabbacin ya ganta, tunani ta shiga yi shin taje ta masa knocking ne kuwa?.


Ko kuma ta kira shi a waya ya buɗe ma ta ƙofar?.


Ƙaramin tsaki taja sannan a fili ta ce "Idan ma na kirasa a waya, ko kuma naje na masa knock GIRMA YA FAƊI ke nan sha re shi tayi ita ma, ta wuce bedroom ɗin ta tabi lafiyar gado.


*WASHE GARI*


Amarya Rafi'at bata tashi da wuri ba, sai wuraren ƙarfe bakwai da rabi na safe.


Wanka tayi sannan tayi sallah a gaggauce ko kwalliya batayi tunanin yi ba, da saurin ta ta shirya cikin doguwar rigar atamfa, ta saka hula mai shigen kayan jikinta kana ta fito ƙasa ta sauka palo.


Kai tsaye kitchen ta wuce cikin sauri sauri ta kammala haɗa breakfast sannan ta jere a Dining Room kana ta koma Bedroom ɗin ta ta kuma yin wanka.

Bayan ta fito ta tsaya ta tsara kwalliya sannan ta shirya cikin shadda milk color mai adon stones coffee color kana ta ɗan ɗa sa ɗaurin ture kaga tsiya.


Tana fitowa daga Bedroom ɗin ta kai tsaye Bedroom ɗin mijinta Abubakar Mai Kyau, ta wuce ta kwankwasa ƙofar Bedroom ɗin dake garƙe.


Ta ɗan daɗe tana knocking sannan ta ciki taji ance ta shigo.


A hankali tasa hannunta wanda yasha jan lalle, ta tura ƙofar Bedroom ɗin a buɗe ta jita.


Kutsa kai ciki tayi tana mai masa sallama, sai da ta jira ya amsa sannan ta ƙarishe shiga ciki.


Tsaye ta hango shi can gaban madubi yana gyara zaman neck-tie ɗin Blue black suit dake jikinsa.


Da sauri ta ƙarisa wurin sa sannan ta karɓa tie ɗin, tana saka masa, sai da ta kammala gyara masa.


Ɗagowa tayi zata masa magana karaf suka haɗa ido, cike da kunya ta ce "Am so sorry Mister Mai Kyau dama kawai saboda naga ka kasa sakawa ne shiyasa, amma ina mai bada haƙuri."


Tayi maganar tana ɗan ɗagowa domin ganin Reacted ɗin sa.


Ga mamakin ta murmushi ya ma ta sannan cikin kamilalliyar Muryar sa yace da ita


''Thank You."


Ɗan murmushin samun nasara tayi, can ƙasan zuciyarta kuwa ta yanke zata biyo masa duk ta yadda ya buƙata, don taga alamar, yanasan mace mai kunya.


A fili kuwa kallon shi ta ɗanyi sannan cikin ƙasa ƙasa da murya ta ce 


"Good morning Mister Mai Kyau, da fatan ka tashi lafiya. Dama nazo ne na faɗa maka breakfast ya kammala, please idan babu damuwa zamu iya Karin kumallo tare?."


Ga tsananin maɗaukakin mamakinta gani tayi ya yi gaba yana faɗin.


"It's okay babu damuwa."


Ya yi maganar ne a yayin da ya nufa ƙofar bedroom zai buɗe.


Da sauri tabi bayan sa tana kuma murmushin samun nasara.


"Ashe dai wannan Bawan Allah ba shi da wani girman kai, kamar yadda nayi zato. Ashe dai HE IS VERY NORMALCY PERSON.."


gaba ɗaya wannan zancen a can cikin Ranta takeyi 🤓.


A tare suka sauko Downstairs suka ƙarisa Dining table.


Yanzu ma cikin sauri ta ƙarisa tayi serving ɗin sa, duk irin Abin da yake buƙata.

Sannan ita ma ta zauna suka yi karin kumallon a tare.


Bayan sun kammala ta riƙe masa Briefcase ta raka shi har Bakin motarsa dama kuma akwai scarf akanta.


Sallama suka yi sannan ya shiga mota driver yaja, ita kuma ta koma ciki, cike da farin ciki, saman bed ɗin ta ta faɗa tana sakin ihu a fili ta ce 


"Muje zuwa Malam Mai Kyau a tsakanin ni da kai a ga wanda zai sauke girma kai aha."


Haka ma da Rana ta tsara masa Lunch mai rai da motsi, ta zuba a food flask guda biyu sannan kuma ta haɗa lemun kayan marmari na musamman ta zuba a goruna duka ta jeresu a basket, ta haɗa da plate's da kuma cups ƙanana, sannan ta fito farfajiyar gidan ta sama driver ta bashi ya kaima Boss nashi office.


Da marece wuraren ƙarfe Bakwai da rabi ta kammala haɗa dinner, sannan gaba ɗaya ta jere a dining room, kana ta wuce bedroom nata.


Wanka ta fara yi sannan ta tsara kwalliya, kana ta shirya cikin shigar atamfa riga da skirt pencil wa'danda ba ƙaramin kyau shigar tayi ma ta ba.

Ta lura yafi son kalar shigar, to ita kuma ta ɗauki niyyar biyo masa duk ta inda ya buƙata.