SARAUNIYAR KYAU (Book 1)

.

by @nkds

*💋 SARAUNIYAR KYAU💋*




_____*


Rayuwa ta ci gaba da tafiya yau da daɗi gobe a kasin haka, to dama haka duniyar take, ba koda yaushe ake cikin jin daɗi ba.


Auren Abubakar Sadeeq Sameer Lamiɗo da Rafi'at Rafiq Rayyan nada wata biyu Rafi'at ta koma bakin aikin ta, zuwa lokacin sunje Jigawa State sun duba su Dr_Raheemah dasu Hajiya Harirah, Hajiya Zuwairiya daga nan suka wuce wurin Zuwaira, Jawaheer, Jummai, duka anan Jigawa State ɗin, daga nan kuma Adamawa State suka yi wurin Sakeenah nan ma suka sha murnar ganin juna, basu yi ƙasa a gwiwa ba, suka wuce Mai Duguri wajen Yusuf da matar sa Yusra, daga Mai Duguri kuwa Lagos suka antaya wajen Sameen da matar sa Sadiya.


Bayan sun kammala ziyarce ziyarce suka dawo Abuja City, waɗanda kuma basa a ƙasar sai dai ta waya suka gaisa, zuwa lokacin Yunus dake a ƙasar France ya zama ambassador na ƙasar.


Auren su nada watanni uku Rafi'at ta fara laulayin ciki, aikuwa koda aka gwada a kaga ciki ɗan wata biyu da satikai nanfa sabuwa, domin kuwa gaba ɗaya kulawar Abubakar akan Rafi'at ada da yake baifi kashi Ashirin cikin ɗari ba, albarkacin cikin dake jikinta kulawar da yake bata sai ta ninku ta koma kashi sittin cikin ɗari.


Rayuwa ta ci gaba da tafiya cike da nasara a ta kowani ɓangare, amma banda ɓangaren Haleesat Rashid Rayyan, domin kuwa Rayuwa tayi ma ta zafi musamman ma da ta fahimci Rafi'at suna zaune lafiya da mijinta Abubakar Mai Kyau, ta taya Rafi'at murna sosai domin kuwa ba Burin ta raba su ba, amma kuma ta yanke ba ita ba aure har duniya ta naɗe, domin kuwa zuciyarta ɗaya ce kuma ta riga da ta mallakawa wanda yafi cancanta a gareta, sai dai kuma tasan koda zata mutu ta dawo Abubakar Mai Kyau ya yi ma ta nisa, saboda yana Auren ƴar uwanta Rafi'at, tana ƙaunar ƴar uwanta, ba zata so suyi zaman kishi ba, a dalilin haka ta sadaukarwa da Rafi'at Rafiq Rayyan duka soyayyar da take yiwa Abubakar Sadeeq Sameer Lamiɗo har qarshen duniya kuwa ta haƙura dashi.😰


    


 


__*BAYAN WATANNI HUƊU*


Cikin Rafi'at Rafiq Rayyan ma ta ga Alhaji Abubakar Sadeeq Sameer Lamiɗo nada watanni bakwai kenan.


**

Ɓiit! Ɓiit...!!!


Haka sautin yake tashi gaba ɗaya yankin a yayin da jerin motocin suke buga horn a ƙofar ƙerarren gidan.


Da sauri gate man ya ƙarisa bakin gate sannan ya wangale gaba ɗaya, sannu a hankali motocin suka shiga gidan, sannan a jere suke tafiya har suka ƙarisa wajen da aka tanadar domin ajiyar motoci, shikuma gate man ya mayar da gate ya rufe.


A hankali ya zuro ƙafarsa waje daga cikin Motar kana ita ma ɗayar ta biyo baya, daga ƙarshe kuma gaba ɗayansa ya fito daga motar, kamar yadda yasa ba sanye cikin Business suit black and White color.


Tafiya ya fara sannu a hankali a yayin da da escort service nasa suke take mishi baya, wasu kuma suka tsaya suna ciro trolleys a boot na Mota.


A dai-dai bakin ƙofar palo escort ɗin suka dakata, shikuma ya shige ciki yayin da waɗanda suka ɗauko jakunku nan na tsaraba suka biyo bayan shi a palo suka jere wuri ɗaya sannan suka fice abun su.


Staircases ya hau yana qwalawa matar sa kira, amma yaji shiru shi dai yasan yana dawowa zai sameta a Palo tana jiransa amma yau tsit kakeji, babu ita babu alamar ta.


Qara ɗa ga muryar sa ya yi yana kiran sunan da ya raɗa ma ta 


"Matar Mai Kyau.!"


"Matar Mai Kyau.!!"


Still shiru dai, da sauri ya tura ƙofar bedroom nata ya shiga tun daga kan mattress bathroom wardrobe babu inda bai duba ba, amma ba Rafi'at ba labarin ta, da sauri ya kuma fitowa wannan karon bedroom nasa ya nufa yana tunanin ko tana can ne bacci ya ɗauketa shi yasa bata fito ba.


Sai dai abin mamaki bedroom ɗin nasa ma, ba inda bai duba ba, still dai babu Rafi'at.


Zuwa lokacin fa hankalinsa ya fara tashi danma shi ɗin Namiji ne.


Fitowa ya kumayi ya shiga duba gaba ɗaya gidan, amma ba Rafi'at ko alamar ta


Zuwa lokacin ya fara gajiya da nemanta domin kuwa shi ba Engine bane.


Dawowa palon ƙasa ya yi ya zauna ya zuba uban tagumi yana kallon tilin kayan wasan yara da ya bada ordered ɗin su aka kawo.

Can gefan zuciyar sa kuwa tunani yake wai shin yaushe ya fara son Rafi'at Rafiq Rayyan ne da zai damu haka da rashin ta?.

Ko dai ya manta ita ɗin Likita ce wata ƙila ma tana can anyi ma ta kiran emergency shi yasa ta fita ba tare da ta faɗa masa ba.

Wani ɓangare na zuciyarsa kuma cewa yake


"To dama kasan da haka shine zaka dama kanka kodai ka fara son matar mai kyau ne?."


Da sauri ya ba kanshi amsa da faɗi a fili "A'a ba sonta nake ba, unborn ɗina dake a cikinta nake so, ba ita ba, zuciya ta ɗaya ce, kuma na riga na mallakawa wacce ta cancanta da samunta..."


Shiru ya yi daga hakan. Ya daɗe zaune a palon yana tunane tunane a cewarsa ba Rafi'at yake jira ba.


A kalla yakai mintuna talatin da biyar a wurin yana jira, can ɗa go kansa da zayyi suka yi ido huɗu da ita, a Yayin da take ƙoƙarin wuce shi, da alama bata lura dashi ba.


Da sauri ya miƙe ya ƙarisa wurin ta yana kiran sunan ta


"Rafi'at.! Rafi'at..!! Lafiyarki kuwa daga ina kike haka?."


Tambayar yake hankali a ɗan tashe, ganin kamar ba'a cikin hayyacinta take ba yasa ya ɗauketa gaba ɗaya bai damu da cikin dake jikinta ba, ya wuce sama da ita.


A ranar Rafi'at gaba ɗaya jikinta kamar a sanyaye yake, saboda haka Abubakar bai takura ta da tambayar inda taje ba, saboda yasan yana yin aikinta daɗi da ƙari kuma ita ɗin mace ce mai ɗauke da juna biyu.

Wata ƙila a can Asibitin da take aiki ne taga abin da ya firgita ta saboda haka ya yanke shawarar ba zata ƙara zuwa wajen aiki ba har sai ta haihu.


Koda ya sameta da maganar bata wani damu ba saima cewa da tayi "Allah yasa hakan shine mafi alkhairi."


Zuwa daren Ranar kuma ta ware kamar ba ita bace jiki sanyaye da rana.


__*GAB@ KWANAKI BIYU*

      {_TWO DAYS LATER_}


Suna zaune a palo Rafi'at kwance saman 3sieter Yayin da Abubakar yake zaune gefanta yana karanto mata wani £nglish story.

THE MOST BEAUTIFUL HEART.


Gaba ɗayan su labarin yana ƙayatar dasu yadda ya kamata.


Wayar Rafi'at dake gefe ne ta farayin ƙara alamar shigowar kira.

Da sauri takai hannu ta ɗauka, sannan ta tashi zaune da taimakon mijinta, kara wayar tayi a kunne bayan tayi picking.


Shiru tayi tana sauraron abin da ake faɗa ma ta ta ɗayan ɓangaren.


Ko ƙaramin motsi ta gaza yi da alama ta fita daga hayyacinta, ganin kamar bata hayyacinta yasa Abubakar tambayar ta Abin da ke faruwa.

Kallon sa tayi kamar wata zautacciya batasan lokacin da ta saki Wayar hannunta ba, aikuwa ta faɗi a ƙasan tiles ba ta tarwatse.


Da sauri Abubakar ya janyo ta jikinsa yana rarrashi, ganin yanda hawaye yake zuba daga idanunta tamkar an buɗe famfo.


Sai da ya tabbatar ta sama nutsuwa sannan ya sake ta yana tambayar abin da yake faruwa.

Cikin shashsheƙar kuka Rafi'at take faɗin


"Haleesat Rashid Rayyan." 


"Haleesat....


Haleesat ce wai wai ita ce..."


Sai kuma tayi shiru tana kuma fitar da siraran hawaye.


A mugun tsorace Abubakar yake kallonta sannan cikin tsananin matsanancin tashin hankali da murya wacca bata fitowa sosai saboda rarrabewar da takeyi wajen furta maganar yake faɗin


"Haleesat Rashid Rayyan. Kuma to Menene abin da ya sameta, ki faɗamin mana kinji Rafi'at Please..."


Ya yi maganar yana jijigata tamkar ta faɗa mishi Haleesat ɗin rasuwa tayi.


Cikin tsananin kuka Rafi'at ta ci gaba da cewa 


"Haleesat ce wai aka sace ta tun kwanaki huɗu da suka wuce shine, Sailuba ta kirani tana faɗamin...."


Bata ƙarishe maganar ba ta kuma fashewa da matsiyacin kuka kamar zautacciya.


Shi kuwa Abubakar za'a iya cewa suman zaune ya yi jin abin da Rafi'at take faɗa Tamkar shock na wutan lantarki haka maganar tazo mishi a ba za ta sannan kuma ta dake shi yadda ya dace.


Sun ɗauki tsawon lokaci a haka ba wanda ya iya qwaqwqwaran motsi cikin su.


Sai can Abubakar da yake Namijin gaske ne, ya kalla Rafi'at bayan ya dawo hayyacinsa daga duniyar tunanin da ya lula yana faɗin


"Ki kwantar da hankalinki in Allah ya yarda za'a ganta nanda bada ɓata lokaci ba, kinji. bata bashi amsa ba, sai ma faɗawa jikinsa da tayi tana kuma fashewa da kuka.


Da yake a lokacin wuraren ƙarfe shida na yamma ne.


Yasa sai da aka kira sallar isha'i sannan suka shirya suka wuce gidan su Rafi'at.


Can ma dai banda kuka babu abin da Rafi'at take yi gaba ɗaya Ahalin Alhaji Rafiq Rayyan sun taru anata faman addu'o'i ana fatan bayyanar Haleesat Rashid Rayyan cikin gaggawa daga hannun wa'innan kidnappers da ake tunanin sune suka sace ta.


Sai can cikin dare wuraren ƙarfe sha ɗaya sannan Abubakar ya ɗauki Rafi'at suka koma gidan su, gaba ɗaya jikin ko wannensu a mugun sanyaye.