SARAUNIYAR KYAU (Book 1)

.

by @nkds

*SARAUNIYAR KYAU*


*BY NAINARH KD NKD'S.*



_____*


Rayuwa ta ci gaba da tafiya Yayin da ta gefe guda Abubakar ya kammala binkciken sa akan Ahalin Hajarah sai dai kuma wani Abin haushin shi ne.

Wai gaba ɗaya dangin sun koma ƙasar waje da zama kuma bai san wata ƙasa suka koma ba.


To koda ya sama Hajarah da zancen ba ƙaramin tashi hankalinta ya yi ba faɗa kawai take

"Shikenan ita kuma da sake haɗuwa da Ahalin ta sai dai a darrusalam inda rabo, a lokacin shima hankalin Abubakar ba ƙaramin tashi ya yi ba, jin abin da take faɗa haka ya dingi kwantar ma ta da hankali, harya samu ta dawo normal."


Rayuwa ta ci gaba da lulawa ta ko wani ɓangare abin dai sai godiyar Allah, domin kuwa ta ɓangaren Ahalin Alhaji Sameer Lamiɗo sosai suka dage suna bawa Hajarah taimakon da ya kamata.


Zaynerb Ɗiyar Hajarah nada shekaru biyu a duniya.

Wata Ranar Alhamis da Yamma wuraren ƙarfe Bakwai na dare, Hajarah ta santalo jaririyarta mace ƙatuwa mai kama da ubanta sak wannan karon, babu abin da ta rage daga jikin Abubakar komai nashi ta ɗauko abu ɗaya ne kawai na Hajarah wanda ta ɗauko wato Manya Manyan dara daran kyawawan idanu.


Daya ke wannan karon Hajiya Zuwairiya ce ta karɓa haihuwar shi yasa sai da ta kammala ba Hajarah da Jaririyarta duk Abin da ya kamata, tayiwa jaririya wanka ta shirya ta, sannan ta fito palo wurin su Abubakar da Rafi'at wacca ita ma cikin jikinta haihuwa yau ko gobe, sai Sakeenah da Jawaheer da kuma Yusra matar Yusuf da suka zo.


Fuska ɗauke da matsanancin farin ciki ga kuma jaririya ɗauke a hannunta ta ƙariso sannan ta miƙawa Abubakar Jaririyar. Bayan ya karɓeta Hajiya Zuwairiya ta ce


"Ga jaririya an sama Ɗiya mace Masha Allah, gata kyakyawar gaske duk da dai ba fara bace."


Ai da jin haka yasa gaba ɗaya mutanen palon suka ƙariso wurin suna kallon jaririyar da aka kira da baƙa bayan kuma gaba ɗaya Ahalin su ta babu baƙaƙe.😜


A je jaririyar dake sanye cikin kayan sanyi na jaririrai tana Baccin ta gunin burgewa, Abubakar ya yi a saman 3sieter aikuwa nan suka shiga kallon ta Abin gunin burgewa.


Sakeenah ta ce "Ni dai tunda nake a Rayuwata ban taɓa ganin Jaririya wacca kyanta da komai nata ya burgeni ba kamar wannan kyakyawar furanga haka, da take a gaba na, sai dai kuma wani abu ɗaya, naga kalar fatar ta shi ba fari ba, haka zalika ba baƙi ba, sai wani shaining da yake yi kamar tauraruwa cikin taurari."


Jawaheer ta amshe zancen da cewa "Ke dai bari ai jina nake kamar wannan Jaririya ta zama tawa, gata Tabarakallah Masha Allah ga kuma Kalar fatarta Wanda a turance ake kira da one in Dollars, domin kuwa kafin ki sama fata Kalar wannan to da aiki gaskiya fa."


Yusra wacca take mata wurin Yusuf ta ce "Ai Auntie Jawaheer baki kai ni ƙaunar wannan Ɗiyar ba domin kuwa jinta nake can, can a cikin ƙasan zuciyata, ga kuma fatar ta wanda iya shi mutum ya gani sai ya mance hanyar garin sa, gidan sa dama sunan sa gaba ɗaya."🔥


Dariya suka yi gaba ɗayan su, Rafi'at wacca ta ƙurawa jaririyar ido tun ɗazu ta ce

"Ummm hmm kun san menene kuwa?."


Gaba ɗayansu suka haɗa baki wajen faɗin

"A'a.'


Dariya tayi sannan tana faɗin


"Wannan Jaririyar ko, ita ake yiwa laƙani da kinfi nurul'in, Dan Allah please ku taimaka ku tayani kallon wannan haɗaɗɗiyar fatar nata wanda in banda shaining babu abin da take yi, ga manya manyan dara daran kyawawan fararen idanunta masu ɗauke da launin £ye ball's wasu masu shaining su ba blue color ba, kuma su ba green color ba, sannan kuma baza'a kirasu purple color ba, abin dai sai Wanda ya gani wallahi."


Gaba ɗaya mutanen dake palon in banda dariya babu abin da suke yi.


Hajiya Zuwairiya ta ce "Ai ina faɗa muku wannan jikar tawa, sai an dinga haɗa mata da Addu'o'i domin kuwa wannan kyan nata ko, Humm hmmm."


Gaba ɗaya mutanen palon babu wanda bai magantu ba, sannan kuma bai susuce da wannan kyau kyawu irin na na wannan Jaririya ba, tana da kyau sosai, she is so cute and so sweet so sexy and adorable, so and and so ka.!! abin ko humm Alƙalamin Nainarh Kd ya yi kaɗan wajen rubuta kyau da kyawu irin na wannan Jaririya.....ʝυʂƚ ιɱαɠιɳҽ...🥰


Abubakar da tun ɗazu ya yi shiru bai ce komai ba, amma idanun sa suna akan wannan kyakyawar furanya, ya sauke wata kyakyawar ajiyar zuciya na farin ciki sannan ya fara magana kamar haka..


"Kun san menene kuwa, jama'a?."


Dariya suka yi jin abin da yace kana suka haɗa baki wajen cewa "A'a a'a a'a...."


Yace 


"Wannan kyakyawar furanya Insha Allahu wata Rana za'a wayi gari ta zama SARAUNIYAR KYAU ta duniya Insha Allahu Burina ke nan a kanta.📷💃😎


<<<{Tofah masu karatu, kundai ji Burin Mister Mai Kyau, a kan wannan Ɗiya tasa da masoyiyar matarsa son sa Hajarah ta haifa masa, shin Burin zai cika, ko kuwa dai. Akwai Ƙalubale, kudai kawai ku biyo wannan Ƙayataccen labari mai suna *💋SARAUNIYAR KYAU 💋* domin jin irin abin da yake ciki, sannan da darasin da yake tafe dashi 💃💃}>>>


Gaba ɗaya mutanen dake palon suka ɗauki sowa na farin ciki Jawaheer faɗi take


"Ina bayanka Yaya ni ma dai Burina ke nan, akan wannan Ɗiyar tamu Ahaa muje zuwa *SARAUNIYAR KYAU*


Murmushin farin ciki Hajiya Zuwairiya tayi tana cewa

"To ai sai ku bar wannan Jaririya ta Huta, ga mahaifiyar ta can baku tambaya Lafiyar ta ba, kun tsaya a kan jaririyar ko?."


Dariya suka yi sannan Sakeenah ta miƙe tsaye da sauri tana cewa


"Ni Wallahi in banda Yanzu da kikayi maganar, ni harna manta da Hajarah mai jego, kyawun Jaririyar da ta haifa mana shiya saka hakan."


Tashi suka yi gaba ɗaya suka nufa bedroom ɗin da Hajarah take ciki 


Kwance suka same ta tana kwasar baccin gajiya.

Zazzauna wa suka yi suma suka ci gaba da fira sama sama suna ko ɗa kyau irin na wannan Jaririya.


Zuwa can wuraren goma na dare Hajarah ta farka aikuwa tayi kyakyawan gani gaba ɗaya mutanen gidan zazzaune suna fira ga Ɗiyarta da mijinta a gefanta murmushi kawai take yi na farin ciki.


Ganin ta farka yasa Abubakar ya yi murmushi da yake yana kusa da ita ne, a gefan gadon, cikin ƙasa da murya, yadda ita kaɗai zataji abin da zai faɗa Yace


"Nagode miki sosai da kika Haifa min wannan kyakyawar furanya, kyakkyawar Tauraruwa wacca hasken ta yake haske wuri, nagode miki sosai kin san kuwa wani suna zan saka ma ta?."


Fuskar ta ɗauke da matsanancin farin ciki na yabon da godiyar da mijinta yake ma ta ta girgiza masa kai alamar "A'a,"

Murmushi ya yi sannan ya matsa da Bakin sa dai dai sai tin kunenta ya raɗa ma ta a kunne.


Dariya tayi ba shiri wanda sautin dariyar da tayi Yasa gaba ɗaya mutanen Ɗakin juyowa suna kallon ta domin kuwa babu wanda ya lura da tashin ta.


"Ah ah kunga masoyan zahiri, wato ana jegon mah ana taɓa love ne ko?, Aikuwa Abin naku ya ƙayatar dani sosai, na ɗauki course daga Yau."


Cewar Jawaheer cikin dariya, "Wato ma saka mana ido kikayi ko?."


Hajarah ta tambaya tana jefa ma ta hararar wasa, Jawaheer ta ce "A'a nadai gani ne kawa Aha." 🤣


Habba ai nan kuma wata sabuwar fira ta ɓalle a tsakanin su, gaba ɗaya cike da nishaɗi yi suke yi kamar babu gobe, har wuraren ƙarfe goma sha biyu na dare.


Sannan ne kuma suka fara shirin komawa bedrooms ɗin su domin kwanciya bacci, gaba ɗaya suka fiffita bayan sunyi wa mai jego da jaririyarta sallama.

Suka bar Abubakar da Hajiya Zuwairiya a cikin bedroom ɗin.


Miƙewa Abubakar ya yi kamar mai neman wani abu. Da sauri ya fakaici idon Hajiya Zuwairiya ya haye saman bed ɗin.

Cikin sauri Hajarah ta kalle sa ganin abin da ya yi kana cikin ƙasa da murya ta ce 


"Menene haka kuma?, in ace kaima ɓangaren ka zaka wuce, sai kuma gobe ko?."


Dariya ya yi sannan shima cikin ƙasa da murya Yace


"Na fasa anan zan kwana, tare da mata ta da Ɗiyata domin kuwa wani kalar kewar su nakeji, tun kafin na tafi na barsu."


Shiru yayi kamar mai tunani, sai can ya kalle ta kamar yadda ita ma ta ƙura masa ido tana kallo, cikin sanyin murya yake faɗin


"Kin san menene kuwa?."


Bai jira ta amsa ba, ya ci gaba da cewa, 

"Jina nake kamar bani ba, ina jina gaba ɗaya jikina a sake, sannan kuma kamar wani abu mara daɗi zai faru, gaba ɗaya a sanyaye nake wallahi."


Ƙura masa ido Hajarah tayi tana kallo Sannan ta sauke ajiyar zuciya tana faɗin


"Duk wannan wasi-wasin aikin sheɗan ne kawai, ka karanto Addu'o'i komai zayyi Normalcy Insha Allah." ta ci gaba da cewa


"Ka tsaya da kyau ka saurari bugun zuciyar ka ka nutsu zaka fahimci aikin sheɗan ne kawai?."


Murmushi ya yi kana Yace


"Ina son ki sosai sosai fi ye da yadda kike sona fa."


Dariya ita kuma tayi sannan ta basa amsa da


"Ni kuma ina ƙaunar mijina abin alfaharina a kullum da ko yaushe ina ƙaunarka obaa, fi ye da ƙaunar da Lailah da Majnun suke ma juna Tabbas." Tayi maganar tana Rumgumo sa tightly.