.
by @nkds
*SARAUNIYAR KYAU*
Ganin dai abin nasu bana ƙarewa bane. Yasa Hajiya Zuwairiya da tun hawar Abubakar saman bed ɗin, take ankare dashi, miƙewa tsaye tana faɗin
"Toh idan an gama rashin kunyar a gaba na, sai a tashi a tafi inda aka fito, domin zan kulle ɗakin."
Da sauri suka juyo suna kallon ta su biyun, aikuwa ta galla musu harara duka.
Ƙasa da kai Hajarah tayi cike da kunya, shikuwa Abubakar ko'a jikin sa ya sauko daga saman gadon idanun sa akan Hajarah harya fi ce daga bedroom ɗin, yana yiwa Hajiya Zuwairiya dariyar ƙeta.
Ajiyar zuciya Hajiya Zuwairiya ta sauke sannan ta kalla Hajarah tana qalla ma ta harara sai dai bata ce komai ba, taje ta kulle ɗakin, ta dawo ta koma can gefe saman wata doguwar stool mai faɗi ta kwanta, domin kuwa wani kalar bacci mara misaltuwa take ji kamar Ƴar maye, Aikuwa ko mintuna biyar batayi da kwanciya ba, bacci ya yi gaba da ita.
Ajiyar zuciyar ita ma dai Hajarah ta sauke sannan ta sauko daga saman mattress ɗin, ta shiga bathroom, ta ɗauki tsawon mintuna goma a ciki.
Jiyo kukan Jaririyarta da tayi ne, yada da sauri ta kammala abin da take yi sannan ta fito, ta ƙarisa saman gadon jariran ta ɗauka Ɗiyar ta ta tana ma ta wasa, daya ke Jaririyar taƙi karɓan Breast ɗin ta, tun ɗazu kuma ba'asan dalili ba, shi yasa ma batayi tunanin bata ba.
Sai da ta tabbatar da jaririyar ta ta tayi bacci, sannan ta kwantar da ita, kana ita ma ta koma ta kwanta saman bed, bayan tayi duka abin da take yi a al'adarta kafin ta kwanta, bata daɗe da kwanciyar ba, ita ma wani bacci mai ƙarfi Ya yi gaba da ita.
*WASH£-GARI*
Wuraren ƙarfe Bakwai na safiya, Sakeenah ta fito daga bedroom ɗin da ta sauka, jikin ta sanye cikin dogon hijjab blue color har ƙasa.
Hamma kawai take yi domin kuwa baccin bai isheta ba ta tashi, amma duk da haka sai da ta makara.
Tasha mamaki sosai ganin Palon ba kowa, bata kawo komai a Ranta ba, ta wuce kai tsaye tabi ta wani korido Wanda zai sadata ɓangaren Hajarah.
Knocking ƙofar bedroom ɗin tayi, amma shiru ba'a zo an buɗe ba.
Ƙara yi tayi nan ma shiru, ganin haka yasa ta ɗan tura ƙofar da hannunta, aikuwa sai ƙofar ta buɗe.
Sallama ɗauke a Bakinta ta shiga bedroom ɗin, amma sai taji ba'a amsa ma ta ba.
Ƙarisa shiga tayi aikuwa tayi kyakyawan gani can saman doguwar stool mai faɗi ta hango Hajiya Zuwairiya tana ta faman sauke snored bacci ya yi daɗi.
Dariya Sakeenah tayi tana faɗin "Ashe dai bani kaɗai na makara ba, tunda dai ga mai jego da Hajiya suna faman sauke numfashi bacci ya yi daɗi da alama."
Qarisa wa gadon da Hajarah take a kwance tayi, sannan ta kai hannu ta fara ɗan bubbuga gadon. Tana dai yi irin idan mutum yana so ya tashi wani daga bacci.
Amma ga mamakin ta sai taji shiru Hajarah bata farka ba, ɗan waro ido tayi waje, sai kuma a fili take faɗin
"Haba Sakeenah sai kace ba mace ba, don't be shy mana haba."
Tayi maganar tana kuma ƙoƙarin tashin Hajarah daga bacci.
Sai dai kuma har lokacin ko motsi Hajarah ba tayi ba zuwa, taƙin fa Sakeenah ta fara tsorata domin ko dama can akwai ta da mugun tsoro.
Hannu na rawa takai sai tin hancin Hajarah domin taji ko tana numfashi, sai dai kuma wani ƙarin tashin hankalin shi ne ko numfashi bata ji alamar tanayi ba, izuwa lokacin zufa kawai take haɗawa, ga jikinta dake faman rawa kamar mazari.
Fa sauri ta kai kunnen ta saitin hancin Hajarah, ko dai zata ji wani alamar amma kuma har lokacin shiru.
A mugun tsora ce ta fara ja da baya, sai kuma da gudun gaske tabar wurin, ta ƙarisa wurin da Hajiya Zuwairiya da take a kwance, ta fara bugunta cikin matsanancin kuka da tashin hankali take tashin ta, ganin ko motsi taƙi yi ne yasa ta ƙarisa wurin wani ɗan madaidaicin fridge a ɗakin ta buɗe, sannan ta ciro ruwa mai sanyi a ciki, kana ta dawo ta buɗe gorar ruwan ta watsawa Hajiya Zuwairiya a fuska.
A firgice Hajiya Zuwairiya ta tashi daga zaune tana karanto duk Addu'ar dake zuwa bakinta, sai da ta ɗan dawo nutsuwar ta sannan ta lura da Sakeenah dake faman rizgar kuka tamkar ranta zai fita.
"Ke, lafiyarki kuwa, Menene ya faru kike wannan kuka kamar anyi miki mutuwa?."
Hajiya Zuwairiya ta tambaye ta hankalin ta a ɗan tashe.
Sakeenah bata tsaya amsawa Hajiya tambayar da take ma ta ba, ta kamo hannunta ta ƙarisa da ita bakin gadon da Hajarah take kwance, sannan cikin kuka da wahalar fitar numfashi taƙe faɗin
"Hajiya Dan Allah ki duba Hajarah taƙi tashi fa, tun ɗazu, tsoro nakeji kar mu rasa ta."
Da jin haka yasa Hajiya Zuwairiya ta ƙarisa wuprin Hajarah ɗin nan ta shiga duba ta cikin sauri.
A hankali a hankali ta fara ja da baya babu abin da take karantawa a bakinta sai kalmar "Inna lil lahi."
Har ƙarshe saboda tsananin tashin hankali ta ma kasa magana, a matsayinta na cikakkiyar likita ta fahimci komai saboda haka kasa magana tayi.
Ganin Hajiya ta kasa magana ne, yasa Sakeenah ta fita da gudu daga bedroom ɗin saboda tsananin tashin hankali bata ma san inda take jefa ƙafafunta ba, a dai dai tsakiyar palon ta hango Abubakar da Jawaheer da kuma Rafi'at da Yusra suna magana.
Da gudun bala'i ta ƙarisa wurin tana kuka na fitar hankali, gaba ɗaya suka yo kanta suna tambayar ta ko lafiya, tama kasa magana, sai faman nuna musu bedroom na Hajarah take yi Yayin da wasu siraran Hawayen suke biyo idanunta suka wanke ma ta fuska.
Lura da inda take nuna musu ne, yasa gaba ɗaya suka nufa bedroom ɗin cikin tashin hankali ita ma ta mara musu baya.
Can gefe suka hango Hajiya Zuwairiya tana zaune kamar bata cikin hayyacinta saboda zaman Ƴan borin da tayi, Yayin da idanunta suke akan gadon da Hajarah take kwance saman shi.
Da sauri Abubakar ya ƙarisa wurin gadon ya fara kiran sunan Hajarah, amma ina rai Ya yi halinsa, gata dai Tamkar zata amsa masa, amma ina.
"Ta mutu, ta tafi shikenan ta tafi ta barmu, da Yaranta da jaririyar ta, ta tafi gidan ta na gaskiya, ba tare da ta cika Burinta na haɗuwa da Ahalin ta ba, shikenan kuma ta faru ta ƙare, Hajarah ta tafi ta Barmu a duniya, shikenan fa munyi Rashin mace ta gari, ga kirki, ga Haƙuri, Yah Allah bazan iya jurewa ba."
Duk wannan maganganun Hajiya Zuwairiya ce take yin su a Yayin da har lokacin idanunta suke akan gadon da Hajarah take kwance saman shi.
Tamkar Saukar Aradu haka zantukan Hajiya Zuwairiya suke shiga kunnen Abubakar Wanda ya tsaya cak da ƙoƙarin Tashin Hajarah da yake yi.
Zai iya cewa tunda Yake a duniya bai taɓa shiga matsanancin Tashin Hankali ba, irin na Ranar har Ranar kuwa da Haleesat Rashid Rayyan ta Rasu, komawa Ya yi Tamkar Statue a wurin gaba ɗaya zuciyar sa da gangar jikin sa sun tafi Hutun Rabin lokaci.
Yayin da gaba ɗaya mutanen palon suka ɗauki kalmar "Inna-lilahi-wa-inna-illahir-raji'un."
Suke faɗa cikin tashin hankali, amma banda Sakeenah wacca tuni ta sume a wurin.😭
A taƙaice dai faɗin irin tashin hankalin da wannan Ahali na Alhaji Sameer Lamiɗo suka tsinci kansu a ciki Tofah Tabbas Baki ko Alƙalami Ya yi kaɗan. 😓😥
Koda mutanen Jigawa dana Kano da sauran Ahali suka zo da Farin cikin na ganin mai jego da jaririyarta, suka sama wannan mummunar Labari na rasuwar Hajarah ga kyakyawar Jaririyarta da ta Bari.
Gaza jurewa da yawa daga cikin su suka yi domin sai da suka yi kuka.
Haka Rayuwar ta ci gaba da tafiya gaba ɗaya ɓangarorin babu daɗi sam, musamman ma ɓangaren Abubakar domin kuwa Rasuwar Hajarah ba ƙaramin taɓa Ya yi ba sosai sosai.
A Ranar da Hajarah ta cika sati biyu da Rasuwa Yusra matar Yusuf ta ɗauki Jaririyar Hajarah wacca taci suna 'AFEEFAH' /Tagari/
Ta koma Mai Duguri da ita da umarnin Abubakar domin kuwa da yardansa sannan kuma da amincewar sa Yusra ta ɗauki jaririyar domin ta ci gaba da kulawa da ita har zuwa wani lokaci, Wanda kuma wannan shawarar da ya Yanke, ba ƙaramin daɗi yayiwa gaba ɗaya Ahali ba.
Yayin da ita kuma Zaynerb ta koma Jigawa State hannun su Dr_Raheemah da zama.
Wanda Hakan ba ƙaramin haushi yaba Rafi'at ba, domin kuwa a cewarta ita Yafi kamata da ya bawa riƙon Zaynerb da kuma Jaririyar domin kuwa ta kusa haihuwa sai ta haɗa da Wanda zata haifa ta kula dasu duka, shiru kawai dai tayi ta shanye duka ɓacin Ranta.
Don karta kuma saka mijinta cikin wani hali bayan Wanda yake ciki.
Tofah haka suka ci gaba da gudanar da Rayuwar.
Tsakanin Rafi'at da Abubakar kuma zaman nasu dai abin babu yabo balle kuma wani abu wai shi Fallasa.
- *-
-
Hajarah nada wata Biyu da rasuwa, ranar wata Alhamis ita ma Rafi'at ta haifo Ɗiya mace, sai lokacin kuma Abubakar ya ɗan fara dawowa Nutsuwar sa.
Ranar suna Jaririya taci suna Lailah, zuwa lokacin Jaririyar da Hajarah ta Bari wacca Yusra take Riƙo duk da cewa madara take sha tayi ƙiba gata da kuma yi, ga wani kyau na musamman da ta ƙara.
Aikuwa a Ranar da Yusra taje da ita Abuja a hannun mahaifinta ta wuni yana bata wani kulawa na daban, duk cewa a duk ƙarshen wata Yana tafiya can Mai Dugurin domin ganin ta sannan ya wuce Jigawa State ma domin ganin Zaynerb.