LUBE (BODARA)

4

by @zinariya0102


    KANO


___________Dattijo ne zaune kan plastic chair gefensa kwagiri ne a jingine ya na duba littafin buguyatul Muslim, horn ɗin da ake ne ya ja hankalinsa, da hanzari Malam Dauda mai gadi ya buɗe, motar gidance ta shigo, fuskar Alhaji Usman ta cika da yalwa ganin jikarsa Insaaf ce aka ɗauko daga school.

Hango Alhajin tayi ita ma da fara'a a kan fuskarta ta,idi ya zagaya ya buɗe motar yana faɗin tawo zai saɓeta ta ce" ni da kaina zan sauka" hahhh to Uwar masu gida girmanki ne ai" ya faɗa cikin raha, saukowa tayi tana barin lunchbox da school bag ɗin ciki,da gudu ta faɗa jikin Alhajin ta na dariya" kai!kai!! Insaaf ai sai ki ƙarasamin ƙafar" ta ce" oyoyo nayi maka fa Alhaji, ya ƙafan ya yi sauƙi ko in faɗawa Abba a yanke wannan a sa maka na roba hahhhh" dungure mata kai ya yi yana faɗin" sai dai a saka miki ja'ira mai surutu kawai maza tashi ki shiga ciki ki huta" ta tashi tana faɗin" Alhaji ni nagaji da gidan nan yaushe Abbana zai dawo mu koma gidanmu?" ya ce"iyeh gidan nawa ne kika gaji da shi Insaaf,to ni bansan lokacin da Zayyad zai dawo ba, kawai ki yi ta yi musu addu'a ai kina yi ko?" kai ta ɗaga sannan ta ce" eh har kaima ina yi maka" Ya ce "yauwa ƴar albarka to Allah ya amsa mana" ta ce" amin".



Idi ya ɗauko school bag da lunch box ɗinta ya shige ciki, Hajiya da ke kishingiɗe a parlour kan center carpet tana jan carbinta kasancewar yamma ce biyar har da arba'in, "Assalamu alaikum, barka da yamma Hajiya" wa'alekumussalam yauwa Malam Idi kun dawo?" ya ce" eh ta tsaya wajen Alhaji" ta ce" to sannu da ƙoƙari" ya ce" yauwa na barki lafiya" ya ajiye kayan ya fita.

"Bilki Bilki" Na'am" Wata budurwa wacce bata fi eighteen years ba ta shigo parlour'n da sauri tana durƙusawa " salama alaikum gani Hajiya" Insaaf ta dawo je ki tawo da ita tana brander wajen Alhaji" to" ta amsa tana tashi ta fito.


Hango Insaaf ɗin tayi tana tawowa, "oyoyo ƴan makaranta an dawo" ce war Bilki, Insaaf ta yi mata shiru tana wucewa.

Bilki ta yi dariya ta ce" to yau kenan akwai daru da alama yau Hajiya ce zatayi aikin" ta bi bayanta. Uniform ɗin ta shiga cirewa tana bawa Hajiya labarin abinda ya faru a school.

Hajiya ta ce" Bilki ku je ciki ayi mata wanka" Insaaf ta ce"ni a'a ba ita ce zata yi min ba" Hajiya ta ce"Hajiya ta ce"aikuwa sai kin bi ta tayi miki" kuka zata sa, Hajiya ta tashi ta na faɗin "mu je inyi miki niɗin ce dai ba kyaso in huta" dariya tasa ta na faɗin" ai Abbana ne yake min wanka, kuma shi ya ke kaini school ma" Hajiya ta ce"oh wannan Abba yana shan kira" wanka tayi mata, ita ta shiryata sanin bata tare da yunwa dan Insaaf bata wasa da abinci da tuni ta buwayeta da yunwa nake ji.

Alhaji ne ya shigo domin yin alwala ya nufi masallaci, ina Fahad ya shiga ne?" ce war Alhaji, Hajiya ta ce" wani abokinsu ne ya rasu a Sumaila shine suka tafi gaisuwa" Alhaji ya ce" Allah ya ji ƙansa" ya wuce ta ce "amin".


A tare sukayi sallah da Insaaf wace wasa kawai take yi, waya ta ɗauko ta ce" kira min Mommy na" harararta Hajiya tayi tana  ci gaba da addu'a Insaaf ta ajiye wayar ta fita.

Fahad da Alhaji ta tarar zaune a parlour yana masa kwatancen abokinsu classmate ɗinsa wanda ya rasu. 

"Uncle Abbana" ta faɗa da alamar kaɗan take jira ta sa musu kuka.

"okay a kira miki Abbanki " kai ta ɗaga da sauri, wayarsa ya ciro yana kiran number Zayyad, Alhaji ya ce" yarinyar nan fa kwana biyun nan iyayenta take son gani" 

"hello Yaya, alhamdulillah, Insaaf ce ta ke son magana da kai" 

Zayyad da ke tsakar gida zafi ya ishe shi, Affan da ke ta kuka shima zafin dai ya dame shi, ko nono yaƙi karɓa, Humaira sai tsaki take tana ganin wannan zalunci ne kawai Zayyad ke musu.

"Bata mu ji mene ne?" ce war Zayyad, handsfree yasa wayar, Affan ya karb'i nonon tana ta yi masa fifita, "Abba ni nagaji dan Allah ku dawo in angama alluran" Zayyad ya ce" to Insaaf zamu dawo ya su Hajiya" ta ce"suna nan Alhaji ma ƙafansa ciwo take ka zo ka kai shi allura" Zayyad ya ce " Ayyah ƙafar ce ta motsa masa Allah ya ba shi lafiya" Fahad ya ce" ƙarya take yi fa Yaya wannan yarinyar sai ta kashe auren da babu soyayya" Humaira ta ce" Fahad ya gida ya su Hajiya" ya ce"lafiya ƙalau aunty Humaira ya garin" ta ce" gari ba daɗi" ya yi dariya yana bawa Insaaf wayar" Mommy ku dawo ni nagaji da gidan Hajiyan nan" Humaira da take jin kamar tayi tsuntsu ta je ga ƴarta ta ce" ayyah sorry dota ina nan tafe kinji, nima nagaji da wannan garin i miss you" sai suka bawa Zayyad ɗin tausayi ganin yanda suke kewar juna.

Sun jima suna hira da ƴarta sosai ta ji daɗin jin ta.Sai da suka gaisa da su Alhaji sannan suka yi sallama.




"Dear ni fa gaskiya jibi zan tafi ƴata tana kewata dan Allah ka barni na tafi" sai ta fashe da kuka, ajiye maficin ya yi ya zuba mata ido ganin da gaske fa take ya sa ya ce"to Allah ya kaimu jibin sai ku tafi Humaira" cike da farinciki ta ɗago ta ce" are you serious?"ya ce" yeah i'm serious" rungumeshi tayi ta gefenta tana haɗa su da Affan ɗin ta shiga godiya da nuna jin daɗinta.


Sai da ya yi sallar isha sannan ya fita shago, Humaira ta kira gidansu ta sanarwa da Ummanta jibi zata dawo.Haka ta shiga sanarwa da ƙawayenta tana nan tafe. Zayyad bai dawo ba sai sha biyu na dare dan garin ana zafi mutane suna ta kwanciyar waje,sanye take da nightgown milk wacce ita da babu the same.ta sakar musu net wanda yake saƙale da fankar solar ta ji shigowar shi.

Ruwa faro da leda ya ajiye bayan ya yi sallama, amsawa tayi tana faɗin" sai yanzu?" ya ce" kin kaimin ruwan?" ta ce" na kai tun ɗazu amma bari a sake wani dan wannan ya daɗe a toilet ɗin" ta fito ta buɗe bokitin fenti ta shiga bayin ta zubar da shi, ta sa masa wani ta shiga ɗaki ta ɗauko turarukansa na wanka ta zuba, ya ce" yanzu idan kin tafi waye zai dinga kula da ni?" banza tayi masa kamar bata ji ba, dan kar ma ya dawo da magana baya.

Wankan ya yi ya fito har ta juye kaza da hantar da ya shigo da su a babban trey ta ɗauko ruwan jin ruwan ma yayi bala'in zafi ya sa taji kamar ta kurma ihu, " oh my God freezer nawa ce a gidana,amma wannan ruwan zamu sha kai I can't leave in this village wallahi dole in koma gida" ta na ta mita a zuciyanta har ya kammala boxer kawai ya sa ya fito ya zauna, ta ce" yau ma sai da ka fita cikin gari ka samo wannan?" ya ce" a'a Alkasim na aika ya siyo min bazan iya zuwa ba saboda da mutane sun yi yawa a shago" ta taɓe baki ta shiga bashi a baki, cikin soyayya suke ciyar da junansu, kullum Zayyad da Humaira jinsu suke tamkar sabbin ma'aurata shekara biyar da aurensu.

Sai da suka kintsa suka kwanta bacci, Zayyad ya nuna buƙatarsa cikin ɗaga murya Humaira ta ce" ni kam meyasa ba ka son zaman lafiya ne Abban Insaaf ka yi wa Allah ka barni na huta" Zayyad ya ce" tafiya za ki yi ki,shiyasa zan yi na bankwana" abu tamkar yaƙi suka shiga kokawa, wannan ita ce babbar matsalar su a zamantakewar su na aure, Zayyad akwai buƙata while Humaira ba ta da wannan dan dole take biya masa buƙata, sai da ya nuna isa sannan ta haƙura ta sallama kai, almost two hours ya na abu ɗaya.

Ba ƙaramin ƙoƙari take wajen ɗaukan buƙatar Zayyad ba, babu yanda zatayi ne.

A daren suka yi wanka, ya hau nafilarsa, bayan ya gama ya janyo system ɗinsa ya shiga aiki, headquarters ɗinsu ya ke turawa saƙo, daga can ana ƙarɓa gami da tura information da suke bukata.


Humaira da take kallonsa, dogo ne irin Wanda ake cewa gent ɗin nan jikinsa madaidaici ba za a kira shi mai jiki ba kuma ba siriri ba ne, jikinsa a mummurɗe yake da alamar yana ɗaga ƙarfe, chest dinsa very large, sexy eyes ɗinsa tamkar na mace mai jin bacci, hancinsa dai-dai da fuskarsa hakama lips ɗinsa masu ɗaukar hankali, babu wata alama da zata nuna shiɗin Ɗansandan fari kaya ne, haskensa har wani jaja-jaja yake, haka hair ɗinsa baƙi ne sosai, wanda kullum luf-luf yake da alamar yawan saisaye, gashin bakinsa ya zagaye pink lips dinsa. "Ya akayi ne Madam?" Muryarsa ta dawo da ita daga duniyar tunaninsa da kallonsa ya kaita ajiyar zuciya ta sauke ta ce" Ina tsananin kaunarka habibina" smile ya yi yana faɗin "au da gaske" dariya suka yi ta ce" ka ajiye aikin nan ka kwanta ka huta kar wani ciwon ya kamaka" ya ce" zanyi amma sai na kammala da wannan aikin tukunna bana son na jima da yawa ban koma office ba" ta ce"okay good night" ta rufe idonta sai bacci.

Sai da ya yi sallar asuba sannan ya kwanta bacci mai nauyi ya ɗauke shi.




******


 Sa'idu, Lawan, Rabe da Ali ne zaune a ɗakin Baba Delu(mahaifiyarsu) tana zaune bakin gadonta tana karkaɗa ƙafa sanin indai ta gansu a haɗen nan to wani abun suka ƙulla.

"Ya akayi naganku a lokaci ɗaya ko maganar auren Alin ce?" Baba Sa'idu ya kuma gyara zama ya ce" a'a Baba ba wannan bace ba, daman hankalinmu ne wallahi ya ƙi kwanciya da zamanki a gidan nan ke kaɗai" Baba Delu ta ce" au,au ba na hanaku maganar komawata gidan nan ba, na faɗa muku nafi jin daɗin zama anan" Baba Rabe ya ce" dan Allah Baba ki dawo cikin gida daman ƙaddara ce tasa kika fita to kuma wacce ake dominta bata gidan to zaman me kuma kike anan ɗin, ki komo sassanki sai ki zuba hayar ba shikenan ba" ta ce" Rabe, Rabe ka fita idona in rufe watukun so kuke in koma can, a dinga faman faɗa da Lube dan nasan halin matanku sarai ba girma ne da su ba sai na jiki, su sa yara suna aibata min jika ana mayya ce ko?" a tare suka ce" a'a haba Baba Lube fa ƴarmu ce ko da mayya ce babu yanda zamuyi da ita ƴar Ali ce fa alkur'an Baba ko yatsa babu wanda zan bari ya ɗaga mata bare akai ga haka" Baba Sa'idu ya ƙarasa da sharhi, Baba Delu ta ce" ni dai nafison naga na aurar da yarinyar nan hankalina zai fi kwanciya" Baba Lawan ya ce" ai kamata ya yi Ali ya fara aure tukunna yanzu ace ƴa tayi aure Uba yana zaune ai hakan ba kamala, ki amince idan ya so sai a aurar da ita a can cikin gidan.


Baba Sa'idu ya ce" dan gudun gori ma sai a haɗata da Manu ɗan uwanta" Baba Delu ta ce "ni dai banason na koma gidan gandu a yanzu gaskiya saboda haka ku tashi ku ban guri" Ali mahaifin Lube ya ce" Baba ki koma can ɗin dan Allah"ta ce" zan koma amma sai ka yi aure kaga sai in bar maka nan kayi zamanka ko kuwa?"duk suka ce" hakane Baba" Ali ya ce" to ni meyasa ba zan zauna tare da ƴan'uwana ba, ko nayi sai dai asa hayar anan ɗin dan ni ba zama nake ba" Baba Delu ta ce" sai mu yi zaman mu da matar autana" duk ta inda suka ɓullo mata sai ta toshe dole suka haƙura har a aurar da Luben da take so.


"Ina Luben take ne?" ce war Lawan, Delu ta ce" ta na nan maƙota gidan Zayyanu wallahi mutanen kirki ne, suna yi mana hidima sosai" Allah sarki ankuwa gode musu sosai. Kowanne ya kawo abinda zai bata ya ajiye mata ta sa musu albarka suka tafi.

"uhm lallai yaran nan in haife ku da cikina ku zo wai ni za ku yi wa wayo, kar nake ganinku, insha Allahu sai na aurar da Lubabatu wa miji nagari, har da wani ga Manu nan ,ai ina sane na ƙi maganar duk da ɗan'uwanta ne amma Lube sai ta zaɓi Miji ta darje in Allah ya yarda.



Lube na filin kaci uwaka tasai faɗan da ba da ita ake ba." Alkur'an babu hegiyar da ta isa ta zagi babar ƙawata in barta ahee" ƙara kaurewa akayi Amina ma ta shiga suka yiwa Wattini duka, yarinyar da bata wuce sha uku ba duk sa'anni ne, da gudu Hamza ƙanin Wattini ya je gida ya faɗa, Inna Maimuna babar su Wattini sai ta tashi ta na faɗin" a ina yaran suke, me ya kaita faɗa da ƴar mayu mu je ka nuna min inda suke, yau sai na ci bantan uban Lube a garin nan...........