Chapter 4
HAKURINMU ๐๐ป๐ผ
Al-amin ya parka motarsa kirar BMW GOI X3,luxury compact SUV, a harabar gidansu, ya dade a motar kafin ya fito, ya meeno tana taga tana leqe, jin bell din kofa ya sa taje ta bude ta tarar da baba megadi, hajiya ina wuni? Lafiya baba ya aiki? Lafiya lau hajiya, anyi baqo, bantaba ganinsa ba shine nace bara na leqo nai magana.
Ok baba bakomai akwai wanchan falon ta baya anbude, kanuna masa dan Allah baba, nagode.
Angama hajiya.
Ta maida kofa ta rufe tai ciki da gudu tana tsokanar ya fati, he is here he is here.
Ke dallachan rabudani, go and tell mummy ba ni ba, ya meeno ta kumburo baki tareda cewa well whatever i wish sumayya is here, ta fita dan gayawa mummy, mummy tace taje sugaisa seta miqa masa snacks sannan tace ga fatiman nan zuwa, amina tace toh tatafi dan aiwatar da abinda aka sakata.
Al-amin yana zaune amina tashigo suka gaisa takawo snacks sannan tace yanzu ya faty zata karaso, bakomai ya ansaa, nagode. Azuciyarsa kuwa yanata saqe saqe yana warware warware.
Amina tai cikin daki tareda cewa ya faty waennan yaran ku za ai baturai, ke haske shi haske ai abin yamuku yawa.
Ke bazaki rabudani ba ko? Kibarni naji da abunda ke damuna mana?
Well you are nervous na miki uxuri.
In rakaki?
Nope don't worry am fine ya fati ta fada tareda miqewa domin taje tasameshi.
Assalamu alaikum ta fada tareda gaisheshi sanan ta nemi wuri a chan qasa ta zauna, daga nan bata kara cewa komai ba kuma ko dago kanta bata karayi ba.
Al-amin
Ina zaune ta shigo, ya Allah my heart, she looks soo beautiful masha Allah, and she smells so nice, gabadaya naji wani sanyi azuciyata, ina wuni ta fada, muryat nan tata me dadinji ta dakar mini hanci, na amsa ina binta da kallo, well she must think maye ne ni, wanan kallo haka Al-amin, na girgiza kaina domin kawarda tinanin nan.
Al-amin yai gyaran murya kafin yafara mata bayani.
Dafarko de suna na Dr. Al-amin auwal tafida a nan asibitin AKTH nake aiki.
There was one time, i was late to A&E call dina and i had a patient that was in a very critical condition, so danaxo se akacemin Dr fatima took care of it, i looked for you so i can thank you ,but danaganki i knew i just had to do right by you.
Yana fadan haka ya lura ta kara kallon kasa alamar kunya, anma yachigaba so naita bin diddigi ina neman information akanki har na hadu da kawunki ya bani izini.
So what about you? Ya tanbayeta.
Shiru bata ansa sa ba.
Well itsokay tinda ni na kawo kaina, ill take it you are shy.
I have two sister, humaira and zubaida, twins ne and i assure you basajin magana.
Jin haka yasa tadanyi murmushi, anma shikenan bata sake cewa koma ba.
Can i have your number or if u rather not talk can you just give me your phone so i can, bekarasa ba ta miqo masa wayar, ya rubuta yagama ya miqa mata.
Sunyi minti 20 ahaka ba wanda yakarai wa wani magana kamar daga sama yaji tace, bakaci komai ba, shikuma ganin dama tasamu dan yasamu yajata da surutu se cewa yai ai bakyaso naci shiyasa.
Banaso kaci?
Well bakizuba min ba, bakice gashi naci ba, taya za ai naci.
Aiko tini ta miqe ta karaso ta dauka plate ta sa samosa biyu, spring rolls biyu sannan ta dauka chicken lap guda daya tasaka ta dauka serviette ta ajiye agefe ta ajje agabansa akan stool sannan ta dauko lemo ta zuba a cup ta ajiye, ta koma inda ta taso ta zauna tareda cewa ance bakonka annabinka, ya gyada kai tareda cewa haka ne anma bakisamun chokali ba, aiko tini ta dago kai ta kallesa tareda cewa, they are called fingerfoods for a reason.
Ohhhh.
Be taba komai ba se ruwa kawai da ya sha. ya tashi ze tafi, yaimata sallama seda yakai bakin kofa ya lura bata tashi ba, se cewa yai bazaki rakani ba? Jinhaka bata ce komai ba ta taso tabi bayansa. Ta rakasa har bakin mota, tana tsaye ya shiga sannan ya tambaya when do i get to see you again?
Tai shiru har ya fidda rai zata ansa sannan tace next week same day same time. Alright bye, ill call you. Bye tace da yar muryar ta.
Ya fati na komawa ciki ta rufo kofa ta sulale agun tareda kallon abinchin daya bari be chi ba, azuciyarta tana fadin wanan bawan Allah ze iya gamawa da rayuwata, his voice is just... Soo deep and i can't get it off my head. Al-amin dogo ne anma ba sosai ba kuma yanada haske ga hanci baza ace masa siriri ba kuma baza ace masa yanada kiba ba, dan dede ne, gashi yasha manyan kaya da hula sun masa kyau, well sede surutu ba laifi akwai surutu, tana wanan tinanin ne wayarta kirar samnsung tai kara tana gani taga sabuwar lamba,wacce ta turo da saqo kamar haka *you look beautiful today, Masha Allah can't wait to get home and call you, please pick my call* tagama karantawa batai reply ba ta tashi ta bar gun.
Shigarta gida ya amina ta isheta da tambaya azuciyarta tace wai ma ahaka sumayya bata nan, yakenan da tana nan, ai sejitai wayarta na kara , *DAMMM* gabanta yafadi tana dubawa taga ashe sumayya ce.
Hello sumy kina ina ne?
Sorry na maqale a traffic, i know it's late but i promise nakusan karasowa gida, pls tell mummy in a very polite manner yadda bazatai min fada ba, please?
Ok to sekin dawo.
Bayan sunyi shirin bacci, amina da sumayya sukasata agaba wai seta fadamusu opinion dinta akansa, itakuma tace its too early for that. Ya amina kuwa se kara fire takeyi tana bawa sumayya labari, dan sumayya batagansa ba,
Ai summy you should have seen him.
huuuh dat dreamyy look in his eyes.
i tell you he loves her, and he is handsome.
This ya fatima is lucky wallahi, sumayya ko ta nutsu kaman me daukan karatu.
Anahaka wayan faty yai kara, taga unknown number tini ta miqe tabar dakin, sukuma suka bita da ido, amina kuwa se cewa tai tofa ankai stage din daza'a dauka waya ba a gabanmu ba, mude muna ganin ikon Allah, se rowarsa ake manna, anqi agaya mana komai akansa.
Sumayya tace kede bari, munzama abin tausayi taredayin fuskar tausayi.