Chapter 6-11
by @oumyasmeen
DESTINY LOVE
Oum yasmeen
Free book
Karku manta kuyi following ɗin channel ɗina
***
EPISODE 6-11
Amma ina garin kaucewa ya bugewata mota cikin sauri ya fito ya tsaya kusa da motar me motar ne ya fito nesa ba kusaba tareek ya girme sa zallar hutu da jin dadi suka zauna mai ganin irin kallo da yake wa tareek ya haɗiye wani miyau me ɗaci yace
"Dan Allah kuyi hakuri ban luraba na buge ka,
Cikin fusata yace
"Kai wanne irin mutum ne mahaifiyar mu na ciki kana ƙoƙarin bugemu ni wallahi ban zan damuba inni naji ciwo ammafa mahaifiyar mu da yan uwana wallahi da wani abu ya same mu da bazamu taɓa yardaba sai munyi Shari'a da kai,
Rumtsai idanuwansa yayi ganin ƙaramin yaro nagasa mai magana yace
"Nima ai ba'a son raina zan bugekuba tsautsayine tun da Ubangiji ya nufa sai anyi kuyi hakuri hurin da ya lotsai zan kai a gyara muku in hakan be muku ba ku fadamin kuɗinta in siya muku wata tunda na lura sabuwa ce ,
Kallon hadarin kaji ya shiga yiwa tareek tama raina musu hankali tab ya buɗe baki zai magana yaga mahaifiyar su na kokarin fitowa ya ja bakin sa yayi shiru
ganin irin ja'injar da akeyi da ɗanta ta fito sanye da lufaya wata buɗurwa na bayanta bata tsaya ta kalli wanda yayi musu wannan ta'annatin ba tace
"Aisar shigo mu tafi kyale shi ,
Four eyes sukai da tareek yace
"Dan Allah kuyi hakuri,
Bata tsaya bashi amsa ba ta shiga mota shima ganin ta shiga aisar ya shiga ya ja su shima shiga yayi ya fara tafiya a hankali saboda ciwonsa na gab da tashi buɗe baki yayi tari ya sarke shi da sauri ya jawo tissue paper ya goge bakinsa aikuwa sai ga jini guda guda parking yayi cikin wahala ya kifa kansa a sitiyarin matarsa wayar sa ya shiga lalubowa cikin Sa'a ya ganta cikin fitar hayyaci ya shiga contact ya lalubo wata number bakinsa na sarkewa yace
"Kazo kabuga ka daukeni ya sake wayar domin ciwon yayi tsamani cikin yardar Allah sai ga jamil nan ya kiɗema da yaga halin da abokin sa ke ciki kama shi yayi ya mai dashi baya ya kwantar kai tsaye asibitin da ake duba shi ya kai shi cikin gaggawa suka rufa akansa har numfashinsa ya dai daita
____________________
Ɗurƙusawa yayi cikin ladabi yace
"Sitti gani,
Gyara zama tayi yarda zai dau maganar da mahimmanci tace
"Ubaidullah daman maganar yaron nan ne an kyelesa ba aure ina so inhada shi da yar uwarsa ta rufa mai asiri safna ta aure shi da kyar na shawo kanta ta amince ,
Da sauri abbey ya ɗago kai cikin ladabi yace
"Sitti banƙi tataki ba amma da a kƴele shi lokacin da yayi niya yayi aure duba da irin tashi ƙaddarar dake ɗawainiya da shi a gaskiya bazan iya tursasa tareek ya aure ta ba sitti har yanzu tareek be yafemin ba har yau alaƙar mu bata dawo daidai ba duk da ko a fuska baya nunamin ninasan abin da yake nufi da hakan bazan so in ƙara lefi agunsa ba ,
Tsawa ta daka mai tace
"Wato ni zaka nunawa iya kacina akan dan shegen da ka haifa uwarsa ma ta guje shi mu mun ruƙesa ya ci ace ta juyo ta waiwaye sa tun yana zanin tsunma to in kaman ta bari intuna baka da kuɗin mahaifinka aka dinga suyimai madara ana bashi har ya girma wata ranma inta ƙare kafin asiyo nonan akuya ake bashi har ya girma sannan zaka nuna min iya kacina akan sa wallahi gaji na rantsai maka zan tsine maka in yau ba a ɗaura musu aure da safna ba ai yar ɗan uwan kace duk abin da zai yi yazo yayi ai ba tsoransa nake ji ba duk taurin kansa da kafiyarsa dole mu tanƙwara shi ai bashi ya haifi kansa ba mu muka haifesa muna kuma da iko akansa tana kai wa nan ta tashi ta bar gun
dafe kaisa yayi dake masa wani irin sarawa tashi yayi ya nufi shashinsa hajiya na'ima ya tarar ta zubawa tv ido duk da anyi mutuwa ta sa uban kida danma ba wanda zaijita bayan tareek be ƙara haihuwa ba shi yasa ya kwallafa rai akansa amma ina yayi mai nisa tunda tareek yasan waye shi ya dena yarda da kowa inciwonsa ma ya tashi ya dinga fashe fashe kenan duk abin da ya gani sai yayi hurgi da shi sanadin shock ɗin da kwakwalwar sa da tasamu na jin ko shi waye shikkenan kuma ciwonsa ya ta'azzara ga zuciyarsa duk a huje baya cin abincin da zai sa wa jininsa kauri yanzu haka injine ke temaka mata gurin aiki duk shekara yake zuwa a canza mai bedroom ɗinsa ya nufa akan luxury royal bed ta zauna ya zuba ta gumi ya shiga tunanin rayuwarsa ta baya
*Wai waye masu iya magana sun ci adon tafiya*
*1991*
Mudai asalin mu yan ƙasar marocco a wani ƙauye da ake kira da
*MARRAKESH*
kane kasuwanci ya kawo mahaifin mu kano kowa yasan fatar dabbobi da ita ake takalma jakunkuna yana siyanta ya kai marocco ya siyar da ita ga Company hada Leatherwork suyi amfani da ita Allah ya samai albarka a kasuwancin sa NADER BN UBAIDULLAH shine cikakken sunan mahaifin mu wataran bayan an gama loda mai kaya za akai shi Lagos a huce dashi ta jirgin ruwa zuwa marocco ma iya marocco yake kai kaya ba har sauran ƙasashen duniya Allah ya haɗashi da mahaifiyar mu yar garin Yola a wani gari da ake kira
*MAYO-BELWA*
duk da iyayensa bawani so suke ba ganin zai auro musu bare haka suka haƙura to da raban zuri'a a tsakani mu hudune a gun mahaifan mu UBAIDULLAH ABDULNUR ABDALLAH sai dan autan mu NASIR cikin kulawa da soyayyar juna muka tashi mumsami ilimin addini da na boko duk da akano muke amma duk wani abu da za ai a maroco sai munje kwasam ƙaddara ta gitta min bazan taɓa mantawa ba
*Ranar litinin shabiyar ga watan Oktoba ranar da yakasance baƙar rana a guna masomin ƙaddara ta da tareek toshen baƙin cikin da muke ciki nida ɗana har yau*
Fitowa ta kenan daga jami'ar Bayero University kamar ance ɗaga kanka naga wata kyakkyawar yarinya chocolate color bazata huce shekara goma sha takwas ba da alama abin hawa take jira daidai gunta na tsaya na zuge glass ɗina nace
"Assalamu alaiki,
Matsawa tayi zuciyar ta nawani irin zillo tsoro fal ranta cikin Sa'a kuwa taga napep ba tayi ta shiga ganin lokaci daya ta rikikice na saki murmushi binsu nake yi har unguwar rijiyar zaki aikuwa tana fitowa na buɗe mota nafito juyowar da zatayi tabawa me napep kuɗinsa ta ganni sauri ta ƙara amma sai da nasha gabanta bata tsaya ta saurareniba ta shiga gida in takaice muku labari ranar kwana nayi banyi bacci ba har sitti ta gane lokaci daya nayi zuru zuru kai kace mahaifina ne ya mutu kullum na taso daga makaranta sai naje gidan su amma bata saurarata alamu ta tsanani ƙarshe sai abokina yaban shawara in tambayi mahaifinta ko Allah zai sa ya bani nanfa ya ɓaɗamin ƙasa a ido yace
har abada bazai taɓa bawa bare yarsa ba ni sai a lokacin nasan ma kanurine jira yake falmata ta gama karatunta ya kaita Gamborin gala yayi mata aure yanzu tana shekarar karshe a secondary ranar na shiga rashin hankali nan fa sheɗan ya ƙitsamin inmata fyade insuka ga haka zasu bani mahaifina bashi da matsala zaine mamin auranta sitti ce me natsala ita zata ce bata yarda ba
haka washe gari na shirya na tsaya akan hanyar makarantar su na tareta Powder nashaƙa mata bata ƙara sanin inda kanta yake ba sai farkawa tayi taga ahalin da take tayi kuka tayi min Allah ya isa yafi cikin kwando nanfa nadama ta kamani amma ko saurarena batayi ba
Sosai na shiga nadama mara adadi tundaga ranar har iyau bana cikin kwanciyar hankali sai ko da ta koma gida ba abin da iyayeta suka fuskanta itama sai dai ta koma gefe tayi kuka batasan da wanne ido zata kalli mijin da ta aura ba ana haka tafara cuta nene wato mahaifinyar ta ta kaita asibiti nan fa likita ya binciko musu tashin hankali ranar taci duka tunda a asibitin
ko da aka tambaye ta waye ba ta boyewa mahaifanta ba nan fa aka nemo mahaifina ranar ya shiga baƙin cikin mara misali haka nima sitti kuwa ba ruwan ta domin ko a fuska bata nunan ba sai dai wani zubin ta yadamin da habaici haka na jure ina ganin cewa innata haihu za'a dauramin aure ashe da sauran rina a kaba wani irin kunci duk ta rame sai uban ciki ba kowanne abu take iya ci ba tana jin muryar mutane za su shigo da gudu take shiga daki wata iriyar tsana tayiwa cikin da ke jikin ta kamar shiyayi abun ba ma ita kadai ba har alanguburo wato mahaifinta ranar da ta haihu ranar ko tsayawa ta kalleshi batayi ba bama ta cikin hayyacinta saboda c.s akai mata ranar alanguburo yakira su alhaji nader su amshi yaron suje can da shi ɗan a duba shi saboda yana dauke da ciwon zuciya tana tashi Maiduguri zasu huce su da kano har abada daman gudun hijira ne ya kawo su ko da Ubaidullah yaji bayanin sa rikicewa yayi yana bashi hakuri
badawa idanuwansa tuka yayi yace
"Ko dan kaga ba dau wani mataki a kanka ba to wallahi kai da auran kaltum bulama gana har abada ,
Zumebewa yayi agun aka bashi gado shima bayan ta farka kallo daya tayi wa ɗan ta kauda idanuwanta hawaye na zuba waiyau ita yake da dan da bana sunnah ba yaron kamar shi daya da Ubaidullah sai wani abu da ba'a rana na kaltum da ya dauko kato da shi bakace yana da ciwon da aka fadaba to wayar gari mukai ba su ba labarin su ga dai yaron ana bashi temaƙon gaggawa duk mahaifina ne yake dawainiya da tareek domin sitti ta tsane shi har bata son ganinsa bayan ansallamo mu haka naci gaba da kula da Muhammad tareek na daina zuwa makaranta har ya fara girma tsanar da yan uwana sukai mai ba magana kuwa domin ko abu ya taɓa sai sun zage shi sunce shege sitti tana sane zata ɗauke madararsa wai gwara ya mutu da ta ajiye shege a zuri'ar ta haka na koma makaranta ina karatu ina rainonsa ban fuskanci matsalah ba sai ran da mahaifina ya mutu nan fa komai ya kara rukicewa Allah ya temaka ma na nasami aiki a NNPC na Abuja nanfa tsananta ta kara ƙarowa akan tareek
nima yawa anmin asiri nabi na fita harkarsa shiyasa bamu shaƙu da shi ba shi yayi wa kansa wahala har ya kai iyanzu ranar da yasan ko shi waye ranar aka cemin zuciyar sa ta huje haka na biya kuɗi da ƙƴar akai mai aiki aka samai inji shine ke control ɗin sa tissue ya yago ya goge fuskarsa tambas tareek abin tausayi ne duk da irin wannan matsala har kwanan gobe yana mutuntani sai dai ba wannan shaƙuwa ta ɗa da mahaifi banjin ko number yana da ita ban da ka cire uncle nasir da shi yayi mai ɗawainiyar karatunsa
Palestine.........✍️
*Perfectly pen's 🖊️ 🖋️*
*~_-_Perfectly Pen's_-_~*✊ 2024
*~_-_Perfectly Pen's_-_~*🤟
*Team One.*
*🌹 perfectly Pen's✍️✊*
*Our Ongoing Book's...✍️*
*1_ƘADDARA CE!.*
*BY: S Candy.*
*2_SHIRYAYYIYAR ƘADDARA.*
*paid 500*
*Season one Free. BY: Queen Kainaat.*
*3_RANAR BIYAN BUƘATA.*
*Free Book. BY: Nainarh KD Nkd's.*
*4_DESTINY LOVE.*
*FREE BOOK BY: Oum Yasmeen.*