HAKURINMU

Chapter 17

by @117973140008139716403

HAKURINMU ๐Ÿ‘Œ๐Ÿป๐ŸŒผ

   Gidan Halifa

Haka de suka kwana, washe gari ya amina ta tashi da sassafe ta hau wankin bandaki, halifa yanata bacci, bacci yake me nauyi kaman betaba bacci ba.


Sannan ta kira mummy ta gaya mata komai, mummy tace zata turo me gadi ya karba kwalbar akaiwa malam.


Takira ya faty, tace zata gayawa Al-amin yazo yaduba shi, tinda jiya it was late kuma bayan aman dayai sun kwana lafiya.


Halifa ya kara tashi da zazzabi, ba shiri kuwa suka tafi asibiti bama su jira Al-amin din yakaraso ba.

kwanan su biyu a asibiti, se yaji sauqi na dan lokachi, sekuma zazzabi ya kara rufesa kuma aneasa meke damunsa a asibitin.


Yauwa! glad ka tashi, ya amina ta fada yayinda halifa ya farka.


How are you feeling? Ya amina ta tambaya.


Like hell. he answered but Alhamdulillah.


You will be better in sha Allah.


Ughm daxu abokanka na gun aiki sukazo dubaka kana bacci, sunce zasu dawo.


Allah sarki, sun kyauta, Allah bada lada.


Amin ya amina ta amsa.


Ughm mummy ta kirani tace  in zan samu zuwa dan Allah,   she wants to see me. I'll let you know whatever happened, nasan maganan wanan stuff dinne, sakinah na nan ta dan fita, tana waya ne, umma tanata kira kana bacci, damukai waya tace zata zo dayamma


Anjima ma abdullahi zezo, yau shi ze kwana abdulrahman yanada call.


(Abdullahi da abdulrahman ya'yan umma saadatu ne).


Toh halifa ya amsa. tareda kokarin tashi don yashiga bandaki yai alola.


Careful please ta fada yayinda ta taimaka masa ya miqe ta rakasa.


Ta taimaka masa ya qarasa kan dadduma ya tada sallah azaune.


Sekuma ta tafi domin zuba masa abincin da sakinah takawo, ga umma ma kuma takawo musu.


Bayan ya idar ta miqo masa abinci.

Zauna please ya Halifa yai patting gefen daddumar sa.

I want you to know that i really appreciate what you are doing.

Allah saka da alkhairi ah ya bada lada.

Amin.

Ahaka suka cigaba da hiransu yayinda yake cin abincin kadan kadan.


Seda Sakinah ta dawo dakin, sannan ya amina ta tafi.


Isarta kenan ko zaman kirki bataiba, Bayan sun gaisa, ya amina take tambayar mummy.


Mummy Allah sa lafiya?


Lafiya ba lafiya ba, mummy ta amsa.


Tofa.


Wannan abun dakika bani nakaiwa malam, a abinchi aka saka masa yaci.


Wannan harkan mallakan ne, yace dalilin dayasa har yanxu bashida lafiya,

sabida akwai wani asirin aqasa shiyasa, wannan anyi maganin sa anma akwai wani.


shi wannan bana mallaka bane? waennan text messages dinnan data turo miki batanata cewa zata hallaka ku gaba daya ba?


Toh wannan ya warwaru, ba abinda zatai miki.

Kince bama ya maganar ta ko?


Yo mummy yana takansa ma, yaushe ze wani yi takan wata yarinya.


Yanxu malam yace ki bi duk lungu da saqo na gidanki ki dudduba ko zaki ga something suspicious haka, in baki gani ba kigaya mini na gaya masa, yace ze tura yaransa wajen gidanku da  unguwar ku kap aduba ta.


Tohm mummy nagode sosai sosai.


Sannan yace inkuma kika gani, in kulle kullene da daure daure kokuma an sossoka abu, ki karanta suratul iklas, suratul nas da suratul falaq  ki chicchire ko ki warware, anma inkika ga abinda bazaki iya ba ki kawomin zan kai masa inkuma wanda zaki iya konawa ne, ki qona.


Ughh mummy koma menene nagani inaga kawai kawo miki zanyi ki kai masa koma meye acire.


Ade riqe addu'a, dan Allah, ariqe addini kuma, aji tsoron Allah, mummy ta dauko wani takarda again da dua ta miqa mata tace shi halifan yadingayi.


Toh mummy nagode sosai sosai.


Ta karba takardar tai sallama ta tafi.

Tana komawa asibiti ta tarar da ummah ta zo, shima kuma abdullahin yazo.


Suka gaisah tai mata yame jiki.


Ya amina tagaya musu komai yadda akai, sanan tacewa umma dan Allah ta bari yau su kwana agida ita da sakinah se su dudduba gidan.


Ummah ta yadda tace bakomai, tareda yi mata godiya sosai akan kokarin datakeyi akan danta.


Ya amina kunya kamar me, ta rasa ya zatayi, se kallon kasa take.


Bakomai wallahi ummah, nice da godiya, ai yiwa kaine.


Ummah de tachigaba da godiya harda cewa gobe zataje taga mamansu.


Ahaka de suka gama hirar su da zaman su har dare yai wurin karfe 9, suka taso suka taho, suka barsu su biyu, daga halifa se Abdullahi.


Ummah tace "she should not worry herself with breakfast, zata kai, su de they should focus on the task at hand.


Haka sukaje gidan, sakinah ta musu girki sukachi, suka dan dudduba sama sama, dayake agajiye suke sukache gobe sa karasa suka kwanta bacci.


Haka washe gari suka hau dube dube anma ina babu komai, babu abinda suka gani, har wajen gidan suka duba, me gadi ma ya taya su anma ina ba labari.


Ya amina da sakinah suka nemi gu suka zauna a court yard da ke bayan gidan, akwai plant ta gefen wurin inda tap din yake.


Suna ta tinanin inakuma zasu sake dubawa, watakila babu komai a gidan.


Ya Amina se taga kaman tana hango abu awurin bayan plant din.


Ganin haka se cewa tai sakinah look kasanchan kaman wani small flat bowl haka abayan pot din plant din.


Bashiri tajuya takalla gun aiko de sakinah ta fada tareda miqewa domin su karasa gun.


Ya amina tai bismillah hardasu ayatul kursiyyu sannan tasa hannu ta dauko,  hannunta se rawa yakeyi.

Kwarya ce yar karama an rufeta da wani kwaryan sannan anyi sealing bakin kwaryan, aikuwa ba shiri suka ziri mayafan su sukai mota se gidan su.


Kan su karasa ya amina tai mata waya tagaya mata, itakuma sakinah ta kira umma tagaya mata itama.


Awaje suka samu mummy tana jiransu, suna tsaya wa ta dane mota, se gidan malam.


Suka shiga aka gaisa, harda kawo musu ruwa, gidane normal gida kaman ko wane gida, ya amina tazata zataga irinsu bukkah da sauransu, shima zataganshi ta katon charbi da littattafai agefensa sannan yana zaune da babbar riga.


Well don't blame ya amina abinda take gani a movies kenan, setaga akasin haka, dan dattijo ne da aurensa ma da yaransa uku, aka kaisu dakin saukar baqi, akwai books anma anjera su a book shelf, normal sitting room ne, sanan manyan kaya ne ajikinsa anma ba babbar riga ba.


Ya shigo suka gaisa sannan mummy ta nuna masa, yai addu'a sannan ya bude, zuma ne fal aciki sewani tuggun jaraba da masifa baqi in a small circle an sossoka masa allura from all angles a tsakiyan zuman.


Ya amina tana gani ta tashi tai waje, sannan tacewa sakinah if its over call me please.


Hakanan taita zama awaje batasan ya akai ya akai ba, se gani tai sakinah ta sako kai taleqo tareda cemata zata iya shigowa.


Data shigo taga kwanon silver da alama konawa akai aciki, se kuma alluran agefe.

Bade tasan ya akai da zumar ba.


Sukaita hamdala suna godiya.


Mummy, ya amina da sakinah sunyi godiya sosai sannan suka wuce asibiti.


Ga mamakinta, tana zuwa ta gansa tarau tarwai, tsabar murna ma batasan sanda taje tai hugging dinsa ba,sannan kaman ta tina abu se tai sauri taja da baya, shi de se smiling yake.


Ummah taita musu godiya, uncle sulaiman ma yaxo, sukaita godiya.


Bayan sun tafi, halifa shima yai mata godiya, ya amina ta kallesa sannan tace, apology?


Yabude baki zebata hakuri kenan ta kastsesa....


Tabdi ai bazan karba words ba.


You are going to work for your forgiveness ingaya maka, just start getting ready, effective immediately muka bar asibitin nan.


Yako kwashe da dariya, dukya sirance yayi duhu.


Toh yazanyi ai dole nai biyayya, but first senayi sallah nagodewa Allah tukunna.


Aikam de yakamata ya amina ta fada.


Yana cikin sallah itakuma ta kira sumayya ta juye muta komai.


Tai mata addu'a tareda cewa Allah kara sauqi da kiyayewa, tace amin sannan ta katse wayan.


Ga mamakinta halifa tagani ya daga hannunsa alamar addu'a, harda kukansa, kawai tai smiling.



Gidan Ashraf


Sumayya kuwa hide and seek suketa playing da ashraf, ga wani abokinsa wai shi jazz dayaga sumayya rannan tadawo daga aiki, shima ya uzzara mata, hargun aikinta yake binta.


Ta fito da safe zuwa aiki, ta tarar dashi azaune kaman jiran fitowarta yake, ga mutane nan ashishirme akasa duk sunyi tattul sun make suna sharar bacci.


Ke yar iskar yarinyar nan, bata amsa sa ba tachigaba da tafiya, tazata baxe ganeta ba tinda a make yake.


Kee! badake nake bane kike daddagawa mutane kai, ya tashi ya miqe yana tafiya da kyar, itako se sauri takeyi takarasa gun motarta.


Ke da ke nake, wallahi da badan sama da qasa hademun suke ba, da sena chafko ki wallahi.


Keki bar dan iskan nan ki dawo guna, wallahi besan darajarki ba, kizo kiga aiki wallahi tallahi.


Kee! in baki amsa ni ba sena isheki ki wallahi, har sekin ansa ni.


Yana gama fadan haka ya fadi akasa, se bacci.

Tai Hamdala tashiga motarta tai gaba.