Chapter 21
HAKURINMU ๐๐ป๐ผ
Ahaka sumayya tai girkinnan, hannunta se rawa yake.
Bayan takai dining table, ashraf yasakata zubo musu duk tarin yawansu, seda yasaka ta zubo musu kowanne a plate takai musu, sannan bayan sun gama duk da hannunta na ciwo seda ta wanke kwanukan tas.
Ahaka magrib yayi, bata samu ta dauko jakanta ta tafi ba.
Da daddare suka ware kida, ita kuma hannunta daya qone ya dinga azabar ciwo ga uban kumburi duk yaja ruwa.
Haka de tana ta gyangyadi tana jira suyi bacci itakuma ta gudu.
Se chan tsakar dare kaman ance "tashi" sumayya ta farka kowa yai bacci, ta samu ta miqe da kyar, riqe da hannunta ta duba sitting room, tanayi tana tsatsallake su anma bataga jakarta ba, haka tai dakin ashraf nan taganshi a rigingine akwance, ga yanmata da kuma kwalbobin giya kashi kashi, aiko se ta hango jakarta a side drawer an ijje kusa da cigarette holder. sumayya tana takawa ahankali, tai sadaf, sadaf ta karasa, sejitai ashraf da yanmatan da ke kwance na juyi.
Sumayya ta dan tsaya harda holding breath dinta, seda taji babu wani motsi again, sannan ta karasa, ta dauka jakar ahaannkkaalli, tana dauka da sauri da sauri ta sauko tayo hanyar waje, da sauri ta bude jakarta ta dauko key din gidan ta bude kofar waje tana sauri taje ta tashi megadi ya bude mata kofa.
Megadi ya fito setai gaba ta barsa, chan kuma setaji shiru, jin shirun yayi yawa yasa ta juya, juyawar dazatai se gani tai an mako mata abu ta goshinta aka kuma kara mata akanta, tini ta fadi sumamiyya.
Ashraf ya jefar da katon katakon dake hannuna sa, yana tangal tangal yace gobe ma kya kara.
Nabeel yana tafe a expensive BMW dinsa black, ya saka T-shirt sky blue da ash sweatpants, kana ganinsa hankalinsa akwance yake, kaman fitar sauri yayi zeje yai abu ya dawo, yana wannan yanayinne wayarsa tai qara.
Nabeel yadanyi tsaki da wannan tsukakken bakinnasa, ga hanci, da dreamy golden eyes dinsa, da fulani beard, sede nabeel is abit dark in complexion.
Ya daga cikakkiyar girarsa sama sannan ya ansa wayar tareda sawa a speaker.
Morning sir, kakeji an fada ta wayar,
Morning, nabeel ya amsa, is there any problem? Nabeel ya tambaya.
Yes captain, wanda yakirashi ya amsa.
Captain your presence is needed immediately a nan lagos, latest by tomorrow.
Thank you. Nabeel ya fada tareda katse call din, alokachin kuma ya sha kwanar gidan ashraf.
Nabeel haka yaita horn, ba'a bude masa gate din gidan ba, yai tsaki tareda cewa nida abu zan ajje nai gaba abina, kawai ya dauka envelop dake kan passenger seat yafita daga motan, yaita bubbugawa ba'a bude ba.
Nabeel ya gaji ya tura kofa, yaga ta budu, aiko ya kutsa kansa, ga mamakinsa, seyaga megadi adaure, an daure hannunsa, shima bakin adaure yake.
Megadi naganinsa ya hau murna, da alama yachi kuka ya gode Allah, nabeel da sauri yai gunsa tareda cewa "Subahanallahi" ya kunce hannun ya cire daurin bakin.
Megadi se cewa yai, ita zaka taimakawa, ita zaka taimakawa.
Ita wa? Nabeel ya tambaya,
Gata chan.
Nabeel yana juyawa yaga sumayya ayashe akasa achan nesa dasu.
Baqin ciki ya tirniqe nabeel, wai me abokinsa yake nema yazama ne?
Da sauri yayo kanta, duk jini agun ga kanta da goshinta afashe, da alama she is not conscious.
Nabeel ya dauketa yai sauri yai waje ya sata a mota sega me gadi shima ya fito.
Ina zaka? Nabeel ya tambaya
Nima binka zanyi.
To dauko jakarta mu tafi, naganta a gefenta.
Megadi ya dauko suka shige mota sukai gaba.
Nabeel gudu yake anma ina, gani yake kaman tafiyar agwagwa suke, se buga tsaki yake yana dukan steering duk inda ya hadu da traffic.
Tin kan nabeel yakarasa ya kira abokinsa, wanda likita ne, yacemasa gashinan zuwa, emergency ne.
Miqo min wayarta, nabeel ya fada, megadi ya binchika jakar, ya miqo waya.
Nabeel ya karba domin kiran yan uwanta.
ya danna wayar bata kama ba alamun ba charge, kawai yai wurgi da ita, shi gaba daya ji yake duniyarsa ajuye take.
Waima ya akai haka ya faru? Nabeel ya tambayi kansa anma seyaji megadi ya amsashi.
Wallahi taxo guduwa ne, se oga ya kamata ya maka mata katako akai ta suma, nikuma dazan bude mata kofa ta gudu, ya daure ni.
Mtswwww nabeel ya kara tsaki. Dafuq is wrong with this dude.
To danazo kofar abude nasameta.
Ai masu fita da sassafe ne suka bude ta.
Allah ya kyauta.
Nabeel ya fada.
Ahaka suka karasa asibitin, shikuma ya rasa ta yanda ze contacting yanuwanta, sabida larshe ma bawa megadi wayar yai yakai gyara sabuda taqi takama ko bayan yasa charge.
Yana nan har yamma, sannan abokinsa yaxo ya samesa azaune ya hada kai da gwiwa.
Nabeel ya kira sunasa tareda dafasa, firgigit nabeel ya miqe.
Kash ashema kaine, muktar ka tsorata ni.
Matsoraci kawai, toh she is stable for now but gaskiya se anyi CT scan.
Dan tayi sustaining injury akanta sabida trauma din datai suffering from.
But anyi brain MRI daxu wanda kabata consent, anga fluid accumulation (which could be blood), kuma anyi surgery anyi draining, yanxu semu jira wani dan lokachi se akara CT scan ko brain MRI din agani ko an samu dacewa, but gaskiya nabeel bazan iya ce maka ga lokachi ko ranar dazata tashi ba.
Tashiga coma.
Nabeel yai salati tareda furzar da iska.
Na tambayeka! DR. muktar ya fada,
Meye alaqar ka da ita?
Nabeel ya kallesa sannan yace wallahi matar ashraf ce.
Dr. Muktar ya zaro idanuwa,
Kai mutumina, meya hadaka da matarsa.
Dogon labari ne, yanxu zani gida please take good care of her, momma nata kirana a waya.
Chan gida su ya amina da ya faty wacce ta dawo ranar, hankalinsu ba karamin tashi yai ba, basu san yadda zasu samu ashraf ba, su umaima da maimuna anata kiransh anma sunqi su dau waya, ga itakuma sumayya wayarta akashe.
Anje airport kuma ba'aganta ba.
Bashiri suki sai ticket din jirgi, da niyar dira a abuja gobe da sassafe.