HAKURINMU

Chapter 24

by @117973140008139716403

HAKURINMU ๐Ÿ‘Œ๐Ÿป๐ŸŒผ

  lokachi ba wuya, duk an hallara agidan uncle farouq, harda nabeel, su ya faty, mummy, su umaimah da uncle sulaiman da halifa duk sunxo.


Uncle sulaiman, yai gyaran murya, tareda farawa da addu'a, sannan yace duk mun san abinda yakawo mu nan, yarinya ce ba'a ganta ba, kuma mijinta ba'a san inda yake ba, anma kafin nan, "kai farouq baka kyauta ba" uncle farouq najin haka yai sauri ya dago kai.


Eh! Uncle sulaiman ya fada, nace baka kyautawa!

Baka kyautawa yanuwanka ba, baka kyautawa yaranka ba, kuma kaima kanka baka kyautawa kanka ba.


Kuma waenan yaranka ne, anma agabansu zanmaka fada, yadda inda me taking footstep dinka ma, ita ko shi yasan ba hanya bane me bullewa.


Kai kawai kai kudi, ka yada kowa, kana ganin irin tarbiyar da kaiwa yaranka, jibesu, uncle sulaiman ya fada, tareda nuna su umaima da maimuna da suke zaune, ka tura yara waje, ba waiwaye, bakasan halin da suke ciki ba, kawai ka tura musu kudi suyi busha sha da shi, baka bibiyar me sukeyi, ko me sukayi, duk ba ko daya.

Babu ruwanka.


Haka de wallahi ba wayewa bane.

Kuma Allah seya tambayeka.

Yanxu ina karamin danka?

Uncle farouq wanda kunya duk ta isheshi qasa kawai yake kalla, idonsa yayi ja, yama kasa dagowa.

Shiko uncle sulaiman yachigaba da maganan sa, nace ina salim? (Qanin su umaima).

Kai kawai ka tura sa makaranta, ko waiwayansa bakayi, baka san halin da yake ciki ba, baka san halinda ya fada ba, kaide kawai ka turawa yaro kudi shikenan kar adameka.

Ance ka kara aure kace ah ah, sannan ka kasa kula da yara.

To wallahi ka gyara, sannan shi ashraf din ka turasa wata kasar yai karatu, sannan ka dauka parenting din gaba daya ka danqawa abokinsa, shi abokin ai shima yana bukatar akula dashi ko?


Gashinan shi lafiyar sa kalau dayake iyayensa sun tsaya masa, kaikuma da kake gudun yaran gashinan ai.


Sukuma yara sun zama baturai baza ai musu fada ba ko? 

Ya dauko yar mutane, kuma yar uwarsa anma ba ruwansa da harkokinta, matarsa ce, kuma tanada haqi akansa, am sure ko daya be sauke ba, ganin yadda akai bikin.


Haka de uncle sulaiman yaita fada, sanan daga baya yaiwa nabeel godiya akan taimakon sumayya dayayi.


Uncle farouq yai gyran murya sannan yace, naji duk abinda ka fada yaya, kuma in sha Allah zan gyra, dan Allah karkai fushi dani kai hakuri.

Ah ah ba wani fushi, ni de kawai na gaya maka gaskiya ne.

Nabeel, uncle farouq ya kira sunan sa,

Na'am! Ya amsa.

Nasan ashraf da siye siyen gidaje yache wai hideout dinsa, dan Allah in akwai waenda zaka iya tinawa, ko kake tina nin yana nan ka fada se aje aduba.

Nabeel ya danyi jim kadan, sannan yace, eh za'a samu dan zan iya tina wasu guda uku.

Zaka iya kaimu? Uncle sulaiman ya tambaya.

Eh zan iya, nabeel ya amsa.

Toh halifa muje.

Aiko se gani yai kowa ya miqe.

Ah ah fa, uncle sulaiman ya dakatar da su, ku bari mazan mana suje su.

Mummy zatai magana ya dada katse ta, hajiya kiyi hakuri ki bari muje iyakar mu ahaka, zamu dawo miki da yar ki in sha Allah.

Toh Allah kiyaye hanya.

Amin duka suka amsa.


Uncle farouq, uncle sulaiman, halifa da nabeel, haka suka shiga motar nabeel duk suka tafi, sukaje gida na farko, bayanan, se wasu mata suka tarar sunata sharholiyarsu, duk abige suke.

Haka sukaje gida na biyu, nan kam ma babu kowa agidan.

Uncle farouq ya qullu sosai, kawai ya dauka waya ya kira ashraf, nan ma wannan mutumin nan shi ya kara dauka.

Jin haka uncle farouq kawai ya kashe wayar yai tsaki tareda cewa nabeel, muje dayan gidan.

Haka sukaje gida na uku har magariba ta gabato, nan kam da alamar mutane, anma wani mutum ya hana su shiga, harda bindiga ahannun sa.

Uncle farouq ganin haka ya fita daga motar, yace masa ashraf yake nema.

Auu baban oga ne kai?

Ba matsala ai girmanka ne, bara akirashi a waya, dan oga baya nan.

Kai bojje kira mana oga awaya kace UBANSA ne yaxo neman sa.


Bayan yan mintuna aka kawowa uncle farouq waya, yana dora wa adodon kunnensa seji yai "popsieee" ya daki dodon kunnensa alamar abige yake ashraf din.

Kana ina ashraf?

Ba ko ina popsie,

Meyene ake nema na?

Matarka ake nema ba kai ba, kasan inda take?

Oh popsie kenan, nasan inda take mana, ni da matata za'a wani nuna mini anfisonta, tama qi ta tashi itama yar chin kwakwa kawai, wallahi zan binneta ahuta.


Yanxu tana ina?


Tana guna, ni naje na daukota ai.


Toh kana jina? Ka dawo da yar mutane, na baka yanxu zuwa gobe karfe goma, in bahaka ba wallahi zan baka mamaki, am cutting your supply gaba daya, nasa kuma ai blocking card dinka.

Uncle farouq yana gama fadan haka ya kashe ya ajje wayan ya shige mota, suka bar gun.

Uncle sulaiman yace abin ya zama na gida tinda an tabbatar da tana gun ashraf duk yan sandan nan a sallamesu.

Haka ko akayi.

Tinda uncle farouq ya fada musu yadda akai, gabadaya babu wanda yai bacci daren ranar, daga masu sallah, se masu jan charbi, se su umaima da suka tsure, daddy zeyi blocking card dinsu, ba siyayya da tafiye tafiye kenan. 

Su halifa da nabeel suka tafi asibiti zaman jira a office din Dr. Mukky.


Ya faty!

Ya faty!!

Ya faty!!!

Ya amina se kiran, ya faty take daketa faman bacci akan dadduma.

What is it? Ya faty ta tambaya.

Ya halifa just called.

Haba ya faty ta fada tareda miqewa.

Me yace?

An dawo da ita,

Tana ICU.

ALHAMDULILLAH, ya faty ta fada tareda yin sujjada, domin nuna godiya ga Allah.

Da sauri suka yi inda mummy take don sugaya mata, daga nan su wuce asibiti.


Authors note


Here is another chapter, Enjoy.

And kurubutamin tinaninku gameda littafin.