Chapter 51-55
by @oumyasmeen
RASHIN SANI
By
Oum yasmeen
Chapter 51-55
Mussa'af shiru yayi yana lalibo mafita domin yasan Wallahi haɗuwar su da Giwa ba dadi
Wata uwar dariya Ihsan ta fara harda ruƙe cikin
A fusace ya biyo ta aikuwa ta zuba aguje ta bar shashin su baki ɗaya mom aysha mom aysha kinga yaya mussa'af ko
Wata mata nagani akalla zata kai shekara talatin taci ado da wani haɗaddan leshi pink colour anme adon flower blue saai ƙamshi take zubawa da sauri ta rumgume ihsan tace
"Haba mussa'af me yasa kullum kana girma kana ƙara shiga dawa mu da muke shirinyin yar gida ,
Saƙar baki yayi yana kallon ta
Cikin tora haushi tace
"Kaga yarinya kyakkyawa san kowa ƙin wanda ya rasa shine ka ta kurawa rayuwar ta to Ni de bazan bayar ba sai nasa mutum kuka babyn zo mu zauna ta kamo hannunta ta zaunar da ita a sofa ,
Shi kuwa mussa'af rasa bakin magana yayi ya ja ƙwafa yace
Mom aysha wa zai aure lukutar yar ki kiyi addu'a Allah yasa ta samo lukuti irinta amma ina ni ina jimgegiya amma bara in dawo daga kotun Shari'a ta Giwa zan zo mu zauna a samo muku mafita
Wani uban ihu ta saki tana buga ƙafafu tace
Mom aysha bakin ce adena ce min lukuta ba
Babyn kƴale shi we burin kunya yake yi
Hannu ya yarfa yace owo ku ta shafa Ni na tafi
Uncle sulaiman ne ya fito yace
"Habibty kamar Muryar mussa'af nake ji daman be koma makaranta ba ?"
Eh shine ya biyo min babyn Wallahi lamarin su har dariya yake bani yawa masu ganin hanjin juna shi girman kai ita tsoka na
Allah ya kyauta
"Ameen"
Uncle sulaiman ina huni
Lafiya qalau ihsan
Uncle ina my boy
Yana barci
A guje ta tashi zata ta doshi
Da sauri mom aysha ta sha gaban ta tace
Babyn bacci yaron ki yake ki bari inya tashi zan kawo miki shi
Zun ɓuro baki tayi tace
Zan faɗawa ya Giwa ya samo min jariri a asibitin shi tunda kullum hanani naki kike
Duban uncle tayi tana dariya tace
Ihsan kenan mala'ikan yara honey kaji abin da take cewa
Hmm so take a kama su ita da Giwa a Ina zai samo miki wani baby tab lalle da sauranki
Wannan kenan
Mussa'af mussa'af mussa'af Wallahi ka fita a idona wato har zaka iya daukan mota kuyi yar tsaire a makaranta har kuna koƙarin buge dalibai
Dan girman Allah yaya kai haƙuri daga yau na dena
Karma Ka dena Wallahi dedai nake dakai a gidan nan ta shi ka tafi sannan daga yau driver ne zai dinga kai ka yana dauko ka baza ka sake daukar mota ba
"To, na gode sosai Allah ya saka da alkhairi ,
Banza yayi mai ya dauki lapton ɗinsa ya fara duba saƙon da aka turomai
Washe gari
A sanyaye take komai shirya wa tayi tsab cikin Fararan kaya tas yau kuma hijabin tane pink colour haka ƙafar wando anmai ratsin pink wata hadaddiyar kimono baka tasa an mata adon duwatsu na golding glass dinta tasa ta dauki wayar ta tace
Lailai mu tafi 8:30 zai shigo tara yace inje
"Okay fanna kinyi kyau yau ina barimar ki ne ta faɗa tana danne dariyar da ta taso mata ?"
A fusace tace
" ban sani ba sai kin shaƙeni zan faɗa miki "
Ooo tawo matafiya
Harara ta hurga mata yawa idanunta zaso waɗu ƙasa ta fiya suke jikin nutsuwa
Wow tafida kalli wata hadaddiyar yarinya ita fa nake baka labari kaf makarantar nan ba wanda take kulawa sai wannan kanwar Giwa gaskiya ta haɗu
Boss aini kaga na kasa magana ji na shiga computer lab naji su munnir suna zancan ta anya wannan ba Balarabe ya ce ba kalli shigar ta fa
Tafida kenan ai daga gani ba tambaya sai de sufa basa auran bare
"Kai boss Wallahi ta tafi da imanina,
Ko ina ta huce kowa bin ta yake da kallo
Lecture suka shiga a layin farko ta zauna kafin malamin ya zo ta fara charting a wayar ta ji tayi an dena surutu da sauri ta ɗago wa zata gani zaro ido tayi ganin ya harɗe hannuwansa agirji ya zuba mata ido tuni ta shiga rudani lefi kan lefi cikin rawar murya tace
Sorry sir.....✍🏼