RASHIN SANI Complete

Chapter 81-86

by @oumyasmeen

RASHIN SANI



       By 


Oum yasmeen 


_________



Chapter 81-86





Ya gana fitowa tayi ta bar ta bayan ta ce mata tayi wanka 


A ɓangaran Mani kuwa ba kowa domin ita ba wanda ta gayyata yar uwar ta ma wacce suki uba ɗaya sai jiya ta ji zancan shine ta zo sosai yan zu Inna falmata take Jin kunyar haɗa ido da ita bayan kowa ya san me ta aika ta komai na bikin da ya kura ake yi ita kuwa mami idone nata yau zata raka ni'matullah filin jirgin saboda yau zata koma Turkiyya tun safe ta fita sai yan zu ta dawo hannun ta nuƙi nuƙi da kaya numfashi ta sauke ta dubi ni'matullah tace 


''yi sauri ki haɗo kayan ki nan da anjima in Kai ki kinsan yau Abbie baxai Sami damar kai ki ba ,,


Zubawa mahaifiyar ta ido tayi tace 


"To, Bara inje gun ya fanna in mata sallama ,,


Banza tayi mata ta ɗauki wayar ta tana charting sallamar ya kura ce yasa ta ɗago ta amsa cikin saƙin fuskan


Gu ta samu ta zauna tace 


"Anty kaltum yanzu za mu tafi Kano ko akwai kayan da kika siyawa fanna mu tafi da shi duk da a gaskiya abbien fanna yayi ƙo ƙari domin Company da ya siyi kayan har sun je gidan mu suke jira kin san order yayi mata a Turkiyya da yake suna da reshe a nan har kayan kitchen a can yayi mata ?"


Gir giza kai tayi tace 


"Babu ,,


Da sauri ni'matullah ya ɗauko wani kwali a kayan da suka siyo tace 


Anty ya kura ga wannan gift ɗi nane ki bata 


Murmushin tayi tace 


"Mun gode Allah ya ƙara haɗa kan ku ,,


Cikin jin dadi tace 


"Ameen ,,


Ɗauka tayi ta fita ganin ta fita yasa mami ta shi ta shiga ɗakin ta ta kwanta ta ƙwantar da nana 


Tuni koma ya shirya a ɓangaran mami ya kura ce kawe su anty ya gana da anty naja sai yayar ammy anty bilkisu ita kuma anty Hafsah da Hajara sai gobe za su zo saboda kawo fanna tuni suka hau jirgi cikin ikon Allah suka isa Kano ƙarfe 3:00 kai tsaye Giwa estate suka nufa kowa yaba ƙyan gidan ya ke Musamman shashin Giwa haka sukai jera mata kayan ta 


A ɓangaran hajiyan daura tuni ta naɗa anty Amina da Sa'adatu su kai musu abinci cikin dauki na samun dama suka ta shi inda aneesa da Ameera suka roƙe musu kayan abinci saƙar baki sukai da hanci ganin irin uban dukiyar da aka saka mata yawa yar gwamna wani baƙin ciki ne ya kara to kare zuciyar anty Sa'adatu ciki ciki suka gaishe da su 


Cikin fara'a da sanin ya kamata suka amsa tare da yi musu sannu da zuwa 


Bayan sun gama suka shiga shashin jadda domin kai gara tuni gun ya ɗi ke da jama'a ganin irin yar masu hannu da shuni Giwa ya aura domin ko ganin irin dukiyar da suka zuba ga kayan abinci da na sawa da suka kawo ban da su alkaki ,da dubulam ,nakiya ,daƙuwa, ga gireba , har da cin cin, ga cake 

 

Bayan tafiyar su hajiyan daura ta dubi Hajiya da mom aysha tace 


"Kun ga dai irin abin alkhairi da sukai mana to dole ne muma in ƙara muku kuɗi ku ƙara jidowa yarinyar kaya ku duba ku gani ko laife ba a kai musu ba ji irin ba jin tar da sukai sun nuna mana su sun san mutumci dukiya bata gaban su ,,


Hajiya tayi ƙasa da kai tace


"Duk abin da kike shine dai dai ,,


Hakama mom aysha tace 


To washe gari tun da safe order kayan laife ta zo akwatin goma sha biyu cike da kaya tuni numfashin ruky yake neman ɗauke wa da tuni fa ita za'a kawo wa wannan kayan ashe da sauran kallo jadda ma ya yi mai laife a kwati goma sha biyu itama baƙil da kaya kai ka ce sabon shago za'a buɗe 


    Maiduguri jahar Borno


Cikin wani haɗaddan leshi blue Black mai yarfin flower pink colour Riga da zani tasa fusƙar ta ba ƙwalliya amma tayi kyau tayi fayau gyaran da akai mata fatar ta har wani ƙyilli take yawa kwai ga sarƙar gold a huyan ta wanda ammy ta siya mata lufaya tasa pink colour da adon flower blue Black sai zuba ƙamshi take ga wani irin kunshi da akai mata yayi kyau sosai kukan tane ya ƙaro ganin anzo daukan ta sosai take kuka su anty Hafsah ne suka kai ta gun Abbie yayi mata faɗa sai gun mamy ita kuwa cewa tayi tana yi mata fatan alkhairi 


Ta shi sukai suka nufi fita da ita a guje ta rumgume ammy tana kuka itama ammy kuka take sosai da ƙƴar a ka raba su ta shiga mota suka nufi airport suka shiga jirgi sai Kano ta dabo tumbin kiwa motoci aka kawo musu kanta a ƙasa ta na ta kuka har zazzaɓi ya fara kamata kai tsaye shashin jadda aka nufa da ita yayi da su lailah ruky aneesa Ameera husna basma su anty Sa'adatu suna zaune suna jiran su cikin tarbiya da mutuntawa suka amshe su anty Hafsah ce ta ce 


"Hajiya ga amanar fanna mun baku a yanzu kune iyayen ta duk abin da tayi ba dai dai ba ku mata faɗa ,,


Cikin farin ciki hajiyan daura ta ce 


''mun amshe ta sannan mu kuma ta roƙe mu a matsayin iyaye


 kuka Hajiyan daura ta saki tace


Ashe zan ga auran Giwa kai Allah na gode maka 


Sosai lailah take so taga fusƙar ta 


Ruky ce ta ce


Anty Bara in buɗe fusƙar ki mu ganki..✍🏼