SUMAYYA

Page 13

by @sanazdeeyah

*SUMAYYA*

 _Wattpad@SaNaz_deeyah_

_Arewabooks@sanazdeeyah_

Youtube: ***


```Page 13```


Tana ƙarasawa gaban Sumayya ta wanka mata marin da har sai data kusa kifawa sannan ta ɗago, hannu biyu ta saka ta dafe kuncin nata, idanunta tuni sun fitar da ruwa saboda tsananin azabar marin da taji. "Waye sa'anki? Ko baki ji ana miki magana kin yiwa mutane shiru"

"Sumayya ce" Ta furta muryarta na rawa kamar za tayi kuka.

"Oh kece shegiyar da aka aurowa Babe?"

Kallon Laila kawai take kafin ta ɗauke kai jikinta a sanyaye.

"Be on your kneels" Ta faɗa cikin tsawa, kallonta kawai Sumayya take dan sam bata gane me take nufi ba, dan bata iya haɗa sentence duk ƙanƙantarsa words ƙanana kawai ta sani a turanci.

"Ba dake nake magana ba?" Shiru tayi kawai tana kallonta har lokacin hannunta na kan kuncinta. Juyawa tayi ta kalli Kamal dake tsaye baice komai ba. "Da alama fa jahila aka auro maka" Murmushi tayi lokaci ɗaya kuma ta haɗe rai. "Durƙusa ƙasa" Ta furta da tsawa, da sauri Sumayya ta kai gwiwoyinta ƙasa, sai kuma ta fashe da kuka. "Kuka ai yanzu kika fara muddin kina cikin gidan nan" Sai lokacin Kamal ya ƙaraso gabansu hannunsa naɗe a ƙirjinsa, yaƙi daina murmushi sam "Babe!" Ya furta yana murmushi da ita kanta Laila ta kasa gane ma'anar hakan.


"Mene na ɗaga hankalinki a kan macen da babu abinda za ta nuna miki?"

"Na sani ko wata rana kyawunta ya ruɗeka" 

"Idan kyau ne ai ni naga mata sama da dubu wanda suka fita kyau amma ni sam basu gabana, ki mu shiga kawai ki tayani na watsa ruwa dan babu lokacin ɓatawa akan wannan sakaran yarinyar, ki barni da ita da ƙafafunta za ta bar gidan nan"

"Are you sure?"

"Am very sure"

"It's alright" Ta faɗa tare da wucewa tamkar dama ta san gidan ko kuma gidanta ne.


Anan Sumayya ta cigaba da rera kukanta, har tayi mai isarta ta gama basu fito ba, tana nan zaune ta kafa uban tagumi ta ga fitowarsu, kallon mamaki kawai take musu dan sun ɗauki tsawon awa uku da rabi a ciki, kenan irin wannan namijin aka aura mata, mashayi kuma fasiƙi, ta ina zata iya dashi bayan tsoron shi take ji sosai, ko da bata tsoron shi ita ta san bata isa taja da masu kuɗi ba.

Dining suka ƙarasa suka ci abincin da aka kawo na breakfast, sannan suka bar gidan ba tare da wani a cikinsu ya sake yi mata magana ba, tanajin tashin motarsa da buɗe gate da rufewarsa.


Ranar haka ta yini da tunani da kuma zulumin sabuwar rayuwar da ta shigo da tunani akan makomarta. "Ya rabbi wane zunubi na aikata ka haɗani da irin wannan mijin? Allah na tuba Allah ka yafe min" Ta furta tana hawaye.


_Bayan Wata Uku_


Tuni Sumayya ta fara sabawa da rayuwar gidan Kamal da kuma zaman kaɗaici, yanzu baya kunyar ya zauna a parlour ya yi shaye-shayensa ya bugu anan ya yi bacci ko ya yi mata amai a carpet yana iƙirarin kuɗin ubansa. Wani lokacin ma baya kwana a gida haka take kwanan zaune saboda tsoro, sai dai in gari ya yi haske ta samu ta yi bacci kafin yazo, haka take kwana tana sallah da rana kuwa ta yini tana kallo dan bata da waya ko 'yar keypad a hannunta, dan ma kullum cikin haske take, sai wata maƙociyarta da suka saba da ita ta nuna mata yadda ake kunna cooker gas da kuma wasu 'yan abubuwan amfani da bata sani ba, ta nuna mata har yanda ake amfani da kayan kallo hakan ta saka kullum tana gaban plazma tana kallon Zee word, anan ne ma ta ɗan iya wasu words na turanci amma sam ba za ta iya haɗa sentence ba.


Kamal kuwa gabaɗaya ta fitar da rai da shiryuwarsa dan bala'in tsoronsa take, da taji motsin shigowarsa take shiga ɗaki, sai dai dole ta fito saboda ya mayar da ita tamkar wata ƙasƙantacciyar baiwarsa, har ta koyi yanda ake haɗa flavor na shisha kullum haka zai saka ta haɗa masa tana kallonsa yake ɗaga kwalabe ko pills yana watsawa a bakinsa, da taga ya bugu kuwa take yin ɗakinta ta saka key tasha kukanta.


Har wannan lokacin babu wata mu'amala ta aure da ta shiga tsakaninsu, bai taɓa shiga ɗakinta ba, haka itama bata taɓa yunƙurin shiga nasa ba, dan gargaɗi ya mata sannan ya zaɓa mata ɗaki ɗaya, wanda nan aka saka mata suturunta da akwatunan lefenta, sauran ɗakunan ta kan shiga ta share tayi mopping amma ɗakinsa kuwa kullum a kulle kuma zare key yake sam bata san dalili ba.


Yau tana zaune a farfajiyar gidan tana shan iskar waje, dan ta kan fito ta zauna, saboda tunda aka kawota gidan bata taɓa saka ƙafa ta fita ba, hakan ya saka jikinta ya yi kyau duk da tana cikin damuwa, babu wanda take gani daga nata ahalin har na Kamal, tun ranar da aka kawota har zuwa yanzu bata taɓa ganin wani nashi yazo ba, sai dai maƙociyarta Ramlat ta kan leƙo jefi-jefi, ko maigadi har zuwa wannan lokacin babu a gidan duk kuwa da girma irin na gidan. Jin ana bugun gate ya saka ta kai dubanta, kafin ta miƙe a sanyaye, ta san baya wuce Ramlat ko yaranta da sukan shigo idan ta aiko su, sai dai tana buɗe gate taga Maryam da Atika, cikin farin ciki ta rungumesu tare da fashewa da kuka. "To mene abin kuka, na ɗauka ai farin ciki za kiyi da kika ganmu" Bata ce komai ba har suka shiga gidan, Atika kuwa sai santin gidan take, a parlour na biyu wanda kusan rabin rayuwarta anan take yi, anan suka zauna. "Yanzu sai yau zaku zo?"

"Adda wallahi kullum ina son zuwa Iya ce take cewa ba yanzu ba"

"Dama wallahi na san iya ce zata hana ki zuwa."


Ruwa da lemo ta kawo musu sannan ta zauna. Atika na murmushi ta buɗe murfin lemo bata ma tsiyaya a cup ba ta fara sha. "Adda ban taɓa shan lemon kwali ba sai a gidanki, gaskiya kin ji daɗi, ni da Baffa zai barni ai nan zan dawo da zama"

"Sannu sarkin son banza" Maryam ta faɗa tana dariya.

"Aunty Maryam gaskiya ce fa, ki ga gidan Adda kamar aljannar duniya"

"Kefa surutunki ya fiya yawa"

"To ni nayi shiru, ƙara min ƙaran talabijin inyi kallo Adda wallahi ban taɓa ganin irin talabijin ɗin nan ba"


Ajiyar zuciya kawai ta sauke, Maryam ta kalleta ta ce "Da gani baki tare da yunwa amma hakan bai hana ramarki ta fito ba, mene ke damunki?"

"Maryam kenan ai gidan ne kawai amma wallahi ji na nake kamar a gidan waƙafi"


Caraf Atika ta ce "Adda wallahi a'a duk wannan jindaɗin da daular" Tana rufe baki Kamal ya shigo ɗakin, ko ƙaran motar ma bataji ba sai shigowarsa. Wani yawun tsoro ta haɗiya da ƙyar.

"Su waye wannan?" Ya tambaya yana ƙarasowa cikin parlour.


"Ina wuni" Suka haɗa baki wurin gaidashi.


Kallon Sumayya ya yi wadda gabaɗaya ta tsure, ta sauke kanta ƙasa. 

"Tambayarki nake wannan ƙauyawan daga ina?"

"A..Atika...Atika ce...dad...da Maryam" Tayi maganar cikin sarƙewar murya, Maryam da Atika kuwa sakin baki kawai suka yi saboda mamaki.


"Malama ba sunansu na tambaya ba so nake na san daga ina kuma su waye?"

"Daga garinmu suka zo 'yan uwana ne, dama...dama...dama tunda aka yi bikin basu zo ba sai yanzu"

"To ni ina ruwana da wannan?" Ya mayar da kallonsa garesu.

"Dalla ku tashi ku tafi duk kun cika ɗaki da wari"

"Wari?" Atika ta faɗa.

"Ku tashi ko na kwaso muku karnuka su rakaku" Jin haka ya saka suka miƙe da sauri.

"Bana son ganin ko wane ɗan ƙauye a gidana, haba gida sai ɗoyi yake, dalla ku tashi ku wuce"Ya furta yana toshe hanci.


Dukkansu jikinsu a sanyaye suka miƙe. "Mtsww" Yaja dogon tsaki. Haka tana ji tana gani suka tafi, sai daya rakasu har gate ya kulle sannan ya shigo, har lokacin tana nan tsaye a parlour.

"Kee!" Ya daka mata tsawar da sai da ta ruɗe sannan ya cigaba da faɗin "Idan wani ɗan iska ya ƙara zo min gida da sunan wurinki wallahi sai na karairaya ki, ke kanki kin zamar min liability haka nan nake zaune dake ba wai dan ina so ba, dalla dubeki wata kucaka ƙazama, jaka kawai. Ki ƙara bari su zo nan sai na lahira ya fiki jin daɗi" Zama ya yi ita dai tana nan bata zauna ba.

"Ki zo ki haɗa min shisha"

Shiru tayi bata ce komai ba.

"Ko baki ji na ne?" Ya daka mata uwar tsawa, da sauri ta bar gurin taje ta ɗauko shisha pot ta haɗa masa ya bata kayan mayen ta zuba tana ji tana gani, tana gama haɗa masa kuwa ta koma ɗakinta, a gado ta kwanta kawai ta fashe da kuka, sai da tayi mai isarta sannan ta haƙura ta share hawayenta a nan bacci ya ɗauketa ba tare da ta sani ba.


_A Month Later_


Faɗa Daddy yake tayi ta inda yake hawa bata nan yake sauka ba, Sumayya dai na zaune kan kujera ta jingina bayanta. Ya sake kallonta sannan ya kalli Mommy "Kamar ma bata cikin kwanciyar hankali wallahi"

Ɗan taɓe baki Mommy tayi kafin ta ce "To ina zaka ga mara lafiya a cikin kwanciyar hankali"


Da kanshi ya ɗauki waya ya kira Dr sannan ya kira Kamal ya ce duk abinda ya ke yi ya dawo gida. Aikam Kamal ya riga Dr zuwa tuni Daddy ya rufe shi da faɗa "Kai baka da hankali yarinya tana fama da ciwo amma ka saka ƙafa ka bar gida ba tare da ka kira Dr ko kuma ka kaita asibiti ba?"

"Daddy ni bata faɗa min bata da lafiya ba"

"To sai ta faɗa, kai ba kaine namiji ba, baka da hankalin da zaka iya gane matarka na da lafiya ko a'a, a zuwanmu ma tayi amai ya kai sau huɗu wannan wane irin rashin hankali ne?"

Shiru Kamal ya yi, ita kuwa ta sauke kai ƙasa har tsoro take yanda taga Daddy na masa faɗa, ta san tsab zai iya hucewa kanta.


Suna nan zaune Dr ya duba ta, sai daya mata 'yan tambayoyin abinda take ji sannan ya bata tsinken kwaji guda uku ya ce taje ta duba, tana dubawa ta kawo ya ga duk abu ɗaya ne, murmushi ya yi sannan ya ce "Wannan ciwon ma ashe laulayi ne, congratulations Kamal"

"Congrats as in how?" Jin haka ya saka Daddy cewa "Kamar ya kenan? Aka ce matarka tana da ciki"


Tuni Sumayya taji zuffa ta karyo mata, jikinta taji gabaɗaya ya ɗauki rawa, musamman lokacin da taji Kamal yana tabbatarwa da Daddy cewar shi bai taɓa kusantar ta ba.


"Daddy wallahi ba cikina bane, tunda ka aura min ita, ko ɗakinta ban taɓa shiga ba, kuma ko yatsarta ban taɓa riƙewa ba"

"Kamal ka san abinda kake faɗa kuwa?"

"Wallahi na sani Daddy ai gata nan a gabanta ake maganar idan sharri nake mata ta musa mana"

Daddy kallon Sumayya ya yi tare da faɗin "Ki faɗa min gaskiyar maganar nan"

"Daddy wallahi ban taɓa sanin wani ɗa namiji ba"


"To ɗan aljani ne? Kin san dai ciki baya yin kansa ko?" Kamal ya faɗa a fusace. Jikinta har ɓari yake saboda tsanani tsoro da furgici.


Daddy ya numfasa sannan ya ce "Ku tsaya wannan magana ba ta ɗaga hankali bace, ya kamata ayi komai a nutse." Shiru ba wanda ya iya cewa komai, ya kalli Dr ya ce "Doctor mun gode Allah ya saka da alkhairi"

"Amin." Shi ma a sanyaye ya faɗa tare da miƙewa ya haɗa kayanshi ya tafi sannan Daddy ya dawo da kallonsa ga Sumayya dake faman kuka. "Sumayya, mene gaskiyar abinda ya faru? Kina nufin babu wani abu daya taɓa shiga tsakaninku na auratayya ko kuwa ƙarya yake"

Kai kawai ta gyaɗa tana kuka.

"Babu abinda ya taɓa yi miki ko cikin maye"

Kai ta sake gyaɗawa cikin kuka.


"Na ga kamar so kake ka liƙawa Kamal abinda ba nashi ba, zai mata ƙarya ne? Ko kana son ka nuna cewa kafi yarda da bare akan ɗan cikinka?" Bai kulata ba, dan dama tun lokacin da za ayi auren ba so take ba, shiyasa ma yanzu ta samu damar yin tijara.

Kallon Kamal ya yi ya ce "Ka tashi kuje asibiti dan tabbatar da abinda yake faruwa."

Kamal tashi ya yi a fusace yana faɗin "Dama tana fita ba tare da ta nemi iznina ba yanzu haka ma yawon banza take zuwa"

"Ba surutu nace kayi ba, cewa nayi ka tashi kuje wani asibitin"

"Daddy ni ta sameni a mota kawai" Yana faɗa ya wuce fuuu.


Sumayya jiki a sanyaye ta shiga bedroom ta wanke fuskarta sannan ta ɗauki gyalenta duk da hawaye bai bar zuba ba, ita sam ta kasa yarda cewa ciki ne da ita, a cikin ranta kuwa addua take tayi Allah yasa ba gaskiya bane.


Suna cikin mota ban da bala'i da zagi babu abinda yake mata, karo na farko da ta shiga motarsa, sai dai abin bai zo mata a yadda tayi tunani ba. Suna zuwa kuwa basu sha wahala ba aka mata test kasancewar asibitin kuɗi ne. yana zaune ita kuma daga can gefe a tsaye, tana ta addua Allah yasa ba ciki ne da ita.

Wayarshi data fara ringing ya ɗaga "Babe yane?"

Daga ɗayan ɓangaren Laila ta ce "Na jika shiru fa?"

"Wallahi kuwa kin ga wata karuwa na kawo a duba dan a tabbatar cikin shegen tayi"

"Kamarya?"

"Wannan baƙauyiyar mana, ai in faɗa miki an kile har ta san maza, shi kuma Daddy yaƙi gaskatawa shi ne ya ce azo asibiti dan a tabbatar"

Sumayya na ji yana zaginta da aibata ta a waya har ya gama.


A sanyaye ta shiga office ɗin Dr lokacin daya kira domin faɗa musu sakamako. Kamal hankalinsa a kwance ita kuwa cikin furgici da tashin hankali take.

"Congratulations matarka na da ciki har na tsawon wata uku da sati biyu"

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Ta furta cikin kuka tare da miƙewa tsaye, tunda suka fito bata yi magana ba sai yanzu da taja dogon salati, da sauri kawai ta fida daga office ɗin.

"Dr mun gode" Kamal ya faɗa tare da karɓar takardar ya fita, tana tsaye a bakin ƙofa, yana fita kuwa ya ɗauketa da mari. Hannu ta saka a kuncinta cikin jin azaba da raɗaɗin abinda ya mata.wani namiji dake tsaye yana waya ya ƙaraso da sauri.

"Haba bawon Allah bai kamata ba, 'ya mace ai darajane da ita"

"Masu darajar dai na da ita amma banda wannan fasiƙar, malam ka barni kawai baka san me tayi ba"

"Ko ma mene tayi bai kamata a cikin irin wannan guri ba"

"Kai idan matarka tayi cikin shege how would you feel? Malam ka rabu dani kawai"

"It's alright amma a ganina ko kisa tayi bai kamata ka mareta in public ba"

"Sannu wanda ya san ya kamata mtsww" Ya kalli Sumayya ya ce "Dalla wuce muje" Da sauri ta wuce jikinta na kyarma.


Daddy na gama karantawa ya ajje tare da cewa "Positive ne" Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce "Zuwa da safe ka kaita govt hospital mu gani, idan sakamakon ya zama uku to sai mu san hukuncin da zamu yanke"

Shiru ba wanda ya iya cewa komai, har Daddy ya basu umarnin su tafi gida.


Kuka sosai tasha dan a bakin layin ya parker ya ajiyeta shi kuma ya yi tafiyarsa, ranar kwana tayi batayi bacci ba, kuma bai dawo gidan ba sai asuba taji shigowar motarsa. Gabanta bai daina faɗuwa ba, tana ji ya shigo amma bai shigo ɗakinta ba dama batayi tunanin haka ba, sai dai ba a ko yi mintuna talatin ba taji ya turo ƙofar, da sauri ta sauke kanta ƙasa "Ki shirya 6am zamu fita asibiti" Bata iya bashi amsa ba kawai ya juya ya yi gaba abinsa. 


A asibitin da suka je 'yan night suka tarar ya basu kuɗi sosai dan su yi masu aiki dan da cewa sukayi sai 'yan morning duty sun zo, ana dubata kuwa result ɗin bai fi 30mnts ba ya fito kuma possitive, tana ɗauke da ciki na wata uku da sati biyu.


_*SaNaz SaNaz_deeyah🌸✌️*_