SUMAYYA

Page 17

by @sanazdeeyah

*SUMAYYA*

_Watpad@SaNaz_deeyah_

_Arewabooks@sanazdeeyah_

Youtube: ***

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*

_[tushen mu'amula tagari]_


```Page 17```


              ***** *****


"Babu kowa amma kuma sun bar tv a kunne?" Cewar Amira wadda ta kasance ƙanwa ga Jidda.

"Anya kuwa? Gaskiya sai dai idan bacci yake dan nace masa ba zan dawo ba sai dare, in kuma acan zan kwana zan kirashi, sannan ai dama shi ne ya kamata ya je ya ɗauko ni Amma ta dage sai mun dawo wai Yaya Mahmud ya kawo mu, ni wallahi sam ban so ba."

"Saboda tsohon saurayinki ne?"

"Ki kiyaye ni Amira"

"Ah to ai gaskiya ne, koma dai mene ne ɗan uwanki ne ba yanda za kiyi, ni yanzu gani nan da girmana saboda kawai ban yi aure ba an giggiɓoni wai na tayaki zama"

"Shiyasa kike ta ƙunci?"

"Eh mana, dama ace gidanki ne ke kaɗai da daɗi amma fa da facalarki"

"Kowa fa da side ɗinsa, wannan falon ne kawai muke tare amma ai akwai falo na, kin ga mu wuce in duba ko bacci Habibi yake da yammar nan"

"Ka ga masu Habibi" Amira ta faɗa ƙasa-ƙasa.


Tana ajje mayafi ta ce "Amira bari na duba ɗakin Kamal ko yana nan, dan bana jin ya fita naga motocinsa duka a parking space"

"To ni kam bari nayi wanka, ai ba zai shigo nan ba ko?"

"Eh, amma da kin bari anyi magrib baki tsoron zazzaɓi?"

"Kai Aunty" Amira ta furta tana zama ita kuma Jidda ta fita.


Tana murmushi ta murɗa handle ɗin ɗakin Kamal, kai tsaye kuma ta shiga, a kan gado ta gansu turmi da taɓarya, dukkansu babu komai a jikinsu sai rabin blanket daya rufesu. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Ta furta da ƙarfi tare da ƙwalla wani mahaukacin ƙara, sai a lokacin suka dawo hayyacinsu, tuni ya sauka daga kan Hamdiyya ya fara laluben rigarsa. Amira kuwa jin ƙaran Jidda ya saka ta fito da sauri tayo ɗakin. Tana shigowa a lokacin Kamal yana ƙoƙarin zura rigarsa, ita kuma Hamdiyya gabaɗaya a ruɗe take sai ƙara ƙokarin ɓoye fuskarta take da blanket ɗin. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Amira ta furta cikin tashin hankali. Kallon Jidda tayi wadda har lokacin ta kasa sauke hannunta ƙasa, kuma taƙi yin ƙwaƙwƙwaran motsi.

"Yaya Kamal dama ka..." Bata ƙarasa faɗa ba, taji Jidda na faɗin "Na shiga uku." Juyawa tayi sai dai batayi ko taku ɗaya ba ta zube. Da sauri Amira tayi kanta tana salati, shima sai a lokacin ya samun ƙarfin ƙarasowa inda take.

"Habibty!" Ya furta yana jijjigata, kallon wulaƙanci kawai Amira ke watsa masa, ganin jini ya fara zuba ne ya saka ta haƙura ya ɗauki 'yar uwarta zuwa asibiti. Hamdiyya kuwa sai da har taji tashin motarsu sannan ta fashe da kuka "Shi kenan asirina ya tonu" Ta furta tana zura rigarta, under wear kawai ta saka ta ɗauki skirt ɗin a hannu ta fita. Jikinta a sanyaye a kuma tsorace take haka tayi wanka ta koma kan gado tayi lamo.


             ****** *****


Yana shiga ya fara kalle-kalle dan ba mutane da yawa, amma dai bai ga alamun wanda ta kirashi ba a mutanen dake zaune duk da bai san wacece ba. Wayarsa ya fiddo a aljihu yana ƙoƙarin kira ya ji ance "Gani ta nan" Da sauri ya juya jin magana a bayansa.

"Laila!" Ya furta da mamaki. Murmushi tayi tare da faɗin "Na san dama za kayi mamakin ganina ko?"

"Ni na fara tantama meyasa nazo nan saboda ban ga wani abu da kika sani a game da Hamdiyya ba, kawai dai da alamun kin kasa manta abinda Kamal ya miki"

"Sadeeq mu samu guri mu zauna dan maganar ba ta tsaye bace, ban kuma yi maka dole akan ka yarda da abinda zan faɗa ba, amma dai ina so dan Allah ka saurareni"

Shiru ya yi na ɗan lokaci kafin ya gyaɗa kai "Okay let's have a seat" Ya faɗa yana wuce wa.

Suna zama waiter ya ƙaraso gabansu "Me kuke buƙata?"

"Ruwa ya isa" Ya kalleta "Kina buƙatar wani abu?"

"Ka kawo min milkshake da ruwa" 

"Okay" Yana wuce ya kalleta "Ina saurarenki"

Murmushi tayi sannan ta ce "Kafin in faɗa maka ina son sanin inda Sumayya take"

"Sumayya kuma?"

"Eh ita, tsohuwar matar Kamal"

"Amma meyasa kike son ganinta? Kuma amfanin me hakan zai miki?"

Shiru tayi saboda lokacin an kawo musu abinda suka buƙata, ta janyo jaka ya yi saurin dakatar da ita sannan ya zaro 20k ya bashi.

"Bara na kawo canji"

"No just leave it"

"Thank you sir" Ya furta tare da barin gurin.

"Ina jinki Laila" Sadeeq ya faɗa yana kallonta.


Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi tare da faɗin "Ina son na nemi yafiyar Sumayya kafin na mutu, domin na san komai akan cikin jikinta amma na kasa faɗa mata gaskiya duk da nima ban sani ba har sai da aurensu ya mutu kuma lokacin muna abroad tare da Kamal anan yake faɗa min gaskiyar abinda ya faru."

"Kina nufin kin san wanda ya yiwa Sumayya ciki?" Sadeeq ya faɗa da mamaki.

"Ba wani bane face Kamal, cikin Sumayya ba shege bane"

"What!? Wai mene yake damunki ne Laila? Duk abinda kikayi da dinner bai isheki ba sai kin sake biyo shi da wani sharrin" Ya miƙe tsaye "Ba zan iya tsayawa cigaba da jin wannan ƙarairayin naki ba"

"Za ka tafka babban kuskure Sadeeq, domin har voice recording zan kunna maka dan ka tabbatar"

Zama ya yi yana dariyar takaici ƙafin ya ce "Kunna ina jinki"

"Hmmm" Kawai ta ce sannan ta buɗe waya ta kunna tare da ajiye wayar akan table ɗin. Muryar Kamal ne yana bawa Laila labarin yadda ya yiwa Sumayya ita kuma tana ta dariya.

"Kashe kawai" Ya furta yana lumshe ido. 

"Nadama ce nayi amma ba wai ina son yi masa sharri bane, komai zai fito daga bakina gaskiya ne a yanzu"

Buɗe idonsa ya yi har sun ɗan fara canja launi ya kalleta "Kina nufin yana sane ya riƙa dawowa da rana yana saka mata abin maye a ruwan shanta?"

"Ƙwarai da gaske, kuma duk a inda tasha ta zube tana bacci anan zai yi amfani da ita sannan ya mayar mata da kayanta jikinta yanda suke, ya ce min ya yi haka ne saboda rama abinda tayi masa, dan kwaɗayi bata sanshi ba ta aure shi sai bayan ma da aka kawota sannan suka ga juna, wallahi da kanshi ya tabbatar min da cikinsa ne amma kuma baya ƙaunarsa dan bai shirya haihuwa da talaka ba?"

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Ya furta a sanyaye.


Shiru ya biyo baya kafin ya kalleta "Matata kuma fa?"

"Baka faɗa min inda zan ga Sumayya ba?"

"Ni ban san inda take ba, saboda bani da wata alaqa da ita, amma dai zan binciko miki, ki faɗa min me kika sani game da Hamdiyya"

"To ai baka da nutsuwar da zan faɗa maka"

"A nutse nake Laila ki faɗa min"

"Ni gaskiya ban ga hakan ba"

"Ki faɗa min nace" Ya yi maganar cikin tsawa wanda sai da ta tsorata sosai.

"Ki faɗa min" Ya ƙara faɗa a sanyaye.

"Zan faɗa" Ta furta tare da ɗan kauda kai gefe. "Ni ba zan faɗa maka komai ba, amma matarka tun kafin ka aureta dama idanunta a buɗe suke, sannan kuma a yanzu da tayi auren ma bata shiryu ba, domin tana cin amanar aurenta ka binciketa"

Ƙura mata ido ya yi har sai da taji ta tsargu, ta miƙe tare da faɗin "Ni zan tafi" Bai tanka mata ba har ta ɗauki jakarta ta bar gurin. Ya daɗe anan zaune yana saƙawa yana kuncewa saboda idan da wanda za ta yi wa sharri ai Jidda ce ba Hamdiyya ba, domin Jidda ce ta mata ƙwacen saurayi, shiyasa ya kasa gane inda gaskiyar take.


Kusan awa ɗaya ya ɗauka a gurin har sai daya ga duhu ya fara sannan ya miƙe ya ɗauki key da wayoyinsa ya yi mota.


               **********


Harara kawai take watsawa Kamal yana ta yawo a ƙofar labour room "Tswww" Tayi dogon tsaki tare da gyara tsayuwarta, a kuma dai-dai lokacin Amma mahaifiyarsu ta ƙaraso tare da ƙanwarta Aina'u, da sauri Amira ta rungume Amma tare da fashewa da kuka. "Bar kukan Amira daina" Hannu ta saka tana share hawaye kafin ta ce "Amma kusan awa ɗaya fa amma har yanzu ba wani labari"

"To wai mene ya janyo naƙudar yanzu bayan akwai sauran lokaci ma" Cewar Aunty Aina'u. Amira ta kalli Kamal suka haɗa ido kafin ta mayar da kallonta ga Auntyn "Faɗuwa tayi"

"Faɗuwa kuma, garin ya?"

Amma ce tayi saurin cewa "Ya isa yanzu ba lokacin tambayoyi bane, Allah dai ya raba lafiya"


Har cikin ran Kamal ya ji daɗin haka, dan haka ya samu ƙarfin gwiwar gaishe su. "Sannu da ƙoƙari Kamal Allah ya yi albarka"

"Amin" Ya faɗa yana murmushin yaƙe ita kuwa Amira tana aika masa harara.

Suna nan tsaye Dr ya fito yana share zuffa da hanky. Gabaɗaya suka fara jera masa tambayoyi akan Jidda.

"Mun samu mun shawo kan matsalar, sai dai kuma ina mai baku haƙuri abinda ke cikin nata yazo babu rai, saboda bata cikin hayyacinta kuma naƙuda ta taho gadan-gadan ba zata iya wani yunƙuri na fito da jaririn ba, da mun yi tunanin yi mata CS to kuma sai muka fahimci yaron ma ya rasu a cikin nata, da kyar dai muka samu muka ciroshi da ƙarfe."

"Allah sarki Jidda baiwar Allah duk yadda taso ɗanta yazo duniya, duk wahalar da tasha ashe ba zai zo da rai ba, Allah yasa mai ceto ne, Allah ya mayar musu da mafi alkhairi" Cewar Aina'u.

Amira ta ƙara haɗa ido da Kamal a ranta kuwa ta furta _Ai gara daya mutu, dan da an haifo mugun iri._

"Dr zamu iya ganinta?" Sai lokacin ya yi magana.

"Eh amma sai an gama shiryata za a fito da ita zuwa ɗakin hutu."

"Okay"


Suna nan aka fito da ita idanunta a rufe da alamu bacci take ko kuma sun mata allurar bacci, amenity suka biya aka kaita, ya ɗan daɗe a nan amma bata farka ba, shi tsoro yake kar ya tafi Amira ta tona asirinsa, amma ganin ana kiran isha'i ya saka dole ya nufi gida dan ya yi wanka ya kuma ɗebo masu kayan da zasu buƙata, saboda ko magrib bai yi ba dan har lokacin baya da tsarki.


              ***** *****


Yana shiga bedroom ɗin ta ɗago a furgice, da mamaki ya kalleta dan bai ga abin tsoro ba, tunda sai da ya yi sallama sannan ya shiga.

"Lafiya?" Ya faɗa yana tambayarta, duk da ya yi ƙoƙarin danne damuwarsa amma sai da ta gane kamar da ɓacin rai a tattare dashi.

"Ni kaɗai ce a gidan shiyasa"

"Jidda bata dawo ba?"

"E..eh..eh basu dawo ba" Kallonta ya yi yadda ya ga tana ta in ina kamar bata da gaskiya. Sauke kai tayi ƙasa yadda ta ga yana kallonta gabanta ba ƙaramin faɗuwa ya yi ba, kaya kawai ya cire ya shiga toilet ita kuma ta dafe kai. Yana fitowa ya shirya ya zura jallabiya sannan ya kalleta "Abinci fa?"

"Wallahi ban samu nayi ba gabaɗaya ba a nutse nake ba"

"Wai mene ke faruwa, kamar ba dai-dai kike ba?"

"Bab..babu fa, nayi bacci ne sai nayi mafarki" Bai dai gamsu da abinda ta faɗa ba kawai ya share ya wuce.


Indomie ya dafa da ƙwai sannan ya tafasa ruwan zafi da kayan ƙamshi ya fito parlour yana ci. Wayarsa data fara ringing ya kalla. "Nihal lafiya kuwa? Allah yasa ba Ayrah ce ta sake yin wani abu" Ya furta yana ɗaga wayar tare da karata a kunne.

"Yaya Mommy ce ta ce a sanar da kai Aunty Jidda na asibiti ta haihu ɗan babu rai"

"What?" Ya furta yana miƙewa tsaye.

"Amma kuma Kamal bai faɗa min ba, wane asibiti ne?"

"Best Clinic inda dai muke da file"

"Okay gamu nan zuwa insha Allah, ina Kamal ɗin?"

"Gashi nan kamar baya da lafiya ma"

"Subhanallah, bari na fara zuwa gida sai naje asibiti" Jin haka ya saka Mommy karɓar wayar

"Sadeeq kaje asibitin dai ka bar Kamal nan dan kar kuma a buƙaci wani abun"

"To shi kenan Mommy, wane ɗaki take?"

"Tana amenity 7"

"Okay"

"Nima dana ga ya warware zanzo insha Allah ko zuwa da safe"

"Allah ya kaimu"

"Amin ya rabbi."

Yana katsewa ya ji haushin Kamal ɗin ma ya turƙesa, yaci zarafin Sumayya cikin da yake ɗan halak amma ya sheganta shi kawai dan ya muzanta ta.


Miƙewa ya yi kawai ya shiga bedroom, yadda ya bar Hamdiyya haka ya sameta "Ki shirya zamu je asibiti, Jidda ta haihu ɗan ba rai"

A kiɗime ta ɗago tana kallonsa, ta kuma kasa cewa komai.

"Ko ba ki ji abinda na faɗa ba?"

"Bana jindaɗi ba zan iya zuwa ba" Sai kuma ta fashe da matsanancin kuka kamar an aiko mata da saƙon mutuwa. Kallonta kawai yake da mamaki kafin ya ce "Wai mene ke damunki Hamdiyya?"

"Ba inda zan iya zuwa Sadeeq kawai kaje" Ta furta tana juya baya tana shashsheƙa.


                 ***** ****


Zama ya yi a kujerar da Amira ta bashi babu kowa daga Amira sai Jidda da take ta faman kuka har lokacin.

"Ya jikin nata?"

"Da sauƙi" Amira ta faɗa tana kallon Jidda. Shima kallon Jiddan ya yi tare da faɗin "Kiyi haƙuri haka Allah ya ƙaddara Allah yasa mai ceto ne"

"Amin amma ita kukanta ba wannan dalilin bane" Cewar Amira.

"Amira karki sake kice komai"

"Dole na faɗa masa gaskiya Aunty domin dake dashi ne aka cuta"

"Mene ke faruwa Amira?" Ya faɗa yana kallon Amira. Har ta buɗe baki za tayi magana aka turo ƙofar.


*Assalamu alaikum, ina sanar da masoyawa wannan labarin cewa na mayar dashi na kuɗi a bisa wasu dalilai, ga masu buƙata zasu iya yin payment tun yanzu a saka su a group, ina so ya zama na san inda nake posting. Amma zan ƙarasa muku book1 sai book2 da book3 zasu zama paid, nagode da bibiyar labarina, ina so ku nuna min ƙauna ta hanyar sayen littafina.*