SUMAYYA

Page 18

by @sanazdeeyah

*SUMAYYA*

_Wattpad@SaNaz_deeyah_

_Arewabooks@sanazdeeyah_

Youtube: ***

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*

_[tushen mu'amula tagari]_


```Page 18```


"Aunty kin dawo?" Amira ta faɗa tana ɗan sosa kai.

"Eh Amira"

"Ina wuni" Sadeeq ya faɗa yana ɗan zamewa daga kujerar da yake.

"Lafiya lau"

"Ashe kuma abinda ya faru kenan"

"To ya za ayi"

"Allah yasa mai ceto ne ita kuma Allah ya bata haƙurin rashi ya kuma bata lafiya"

"Amin mungode"

"Aunty baki gane shi ba?" Cewar Amira.

"Kamar dai ɗan uwan Kamal dan naga suna fuzgen kama"

"Eh ƙaninsa ne wanda aka yi bikinsu rana ɗaya"

"Oh Allah sarki, ya iyalin naka?"

"Lafiya lau"

"Madalla"

"Am nace ko akwai abinda kuke buƙata?"

"Eh to komai an kawo sai dai akwai wasu magunguna da allurai dole sai a lamco za a samu"

"To a bani sai naje na sayo.


Yana fita, ita kuma Aunty ta shiga toilet. Jidda kallon Amira tayi ta ce "Ka da ki kuskura ki faɗa masa komai a daren nan"

"Oh in bari sai da safe?"

"Bana buƙatar ki faɗa masa"

"Aunty dole ya sani fa, matarsa fa! Haba ai bana jin akwai aurensu ma, dan a musulunci jefeta kawai za ayi"

"To ina ruwanki, ki bari abi komai a sannu bana so a samu matsala ki bar komai har zuwa lokacin da za a sallameni"

"Taɓ shi lokacin da zai yi abinsa ya yi da sauƙi ne, da baki ga wannan abin ba da lafiya ƙalau za ki haihu kuma sai kice kar na ton..." Jin fitowar Aunty Aina'u daga toilet ya saka su yin shiru gabaɗaya. Kallonsu tayi tare da faɗin "Baku da gaskiya ko?"

"Ah haba Aunty wallahi da gaskiyarmu"

Murmushi tayi tare da faɗin "To naga ina shigowa kun yi shiru."

Amira ta ɗan sosa kai tare da faɗin "Cewa fa nayi Yaya Sadeeq ya fi Yaya Kamal kirki"

Kai Aina'u ta girgiza tare da faɗin "Ke kuma Jidda kina zaune tana zagin mijinki"

Murmushin yaƙe kawai Jidda tayi.


Ɓangaren Sadeeq kuwa yana driving kawai maganganun Laila suka dawo masa. "Anya zan yarda da abinda ta faɗa kuwa?" Ya furta a fili kamar yana tare da wani a motar.

"Idan da wanda zai fara shaidar Hamdiyya ni ne, gaskiya bai kamata na biyewa wata 'yar tasha ba, so take kawai ta ruguza aurena" Ajiyar zuciya ya sauke a ransa kuma ya ce _To amma inda wanda za ta ruguzawa aure ai Kamal ne, tunda shi ne ya yi soyayya da ita a ƙarshe kuma ya auri cousin sister ɗinta._ Haka dai ya gama saƙe-saƙensa baya da wata mafita da ta wuce ya sayi maganin sannan ya kai.


Ya jima sosai a asibiti sai kusan goma da rabi sannan kira ya shigo masa, ganin Mommy ce ya saka shi saurin ɗagawa "Mommy"

"Sadeeq ka koma gida?"

"A'a yanzu dai nake shirin tafiya" Ya yi maganar yana kallon agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa.

"To ka biyo ta nan ka tafi da Kamal"

"Mommy wai baya da lafiya sosai ne?"

"To gashi nan dai ni na rasa mene yake damunsa ma, Dr dai ya ce jininsa ne ya hau"

"Subhanallah, to Mommy zan biyo na ɗauke sa ɗin"

"To sai ka zo"

Yana kashe wayar ya kallesu tare da faɗin "Kamal baya da lafiya shiyasa ma bai samu ya dawo ba"

Dukkansu shiru suka yi, sai Amira ce daga baya ta ce "Allah ya sawwaƙe"

"Amin"

Miƙewa ya yi tare da faɗin "Ni zan koma,dan Allah idan akwai wani abu sai a kirani a waya."


              ***** *****


"Amma ai da ya kwana anan tunda matarsa ma tana asibiti bare ya ce saboda ita zai koma"

"To ni dai abinda na faɗa masa kenan ya ce shi dai ya fi so ya kwana a gidansa" Cewar Mommy.

"To shi kenan bari mu tafi saboda naga 11 har ta gota."

"Sai ku tafi da Nihal ta tayaku ayyuka"

"Wannan me ta iya ban da danne-dannen system"

"Kai Yaya" Ta furta tana turo baki.

Ya kalli Ayrah dake kwance kan carpet ya ce "Ayrah tashi ki ɗauko kayanki kala biyu mu tafi, tunda gobe ba school"

Kamar jira take ta miƙe da sauri.

"Dama fa so kake kawai kace Ayrah, ai na lura ka fi son Ayrah Yaya"

"Dukkanku ina ƙaunarku"

"Dagaske Yaya?"

"Sosai ma"

Murmushi kawai tayi cike da jindaɗi.


A parlour ya zauna kan kujera tare da lumshe ido. "Ya naga ka zauna anan?"

"Eh wallahi kawai nan ɗin ne naji ina buƙatar zama, gashi ina buƙatar tea"

"Okay" Sadeeq ya furta tare da kai dubansa ga Ayrah. "Ki sama masa ruwan zafi a kitchen" 

Ba haka yaso ba, domin ya yi tunanin zai ce bari ya kira Hamdiyya dan yana da buƙatar su yi magana. Yadda dai yaso hakan bata faru ba domin a ranar dai bai samu ya yi magana ko ganin Hamdiyya ba.


                ***** *****


"Ya kamata ki riƙa zuwa awo gaskiya, gudun kar a samu matsala"

"Doctor wai daske ina da ciki?" Kallonta yake da mamaki kafin ya ce "Oh da kin ɗauka ƙarya ne, to duk fitowar nan da ya yi kin yi tunanin tumbi ne ko me?" Shiru tayi bata ce "A baya na taɓa yin ɓari kuma likita ya tabbatar ba zan sake ɗaukar ciki ba, ko zan ɗauka to ba zai wani daɗe ba zan yi ɓari, kuma hakan ce ta faru dan na samu ciki kuma ya zube."

"Likita ai ba Allah bane, amma dai ni kaina da aka yi scanning nayi mamaki dan mahaifarki bata da wani ƙwari, dole sai kin kula sosai da lafiyarki gudun kar a samu matsala. Muddin kina son ki haifo abinda ke cikinki lafiya to dole ki riƙa zuwa awo dan a riƙa bincika lafiyarku"

Miƙewa kawai tayi bata ce komai ba.

Tana zuwa ƙofar asibitin ta tsaya tare da ɗauko ƙaramar keypad ɗinta da ta gaji da koɗewa ta kira Jamilu. Kira uku ta masa bai ɗaga ba sai ana huɗu shima da masifa ya ce "Mene?"

"Ina bakin asibitin na duba ban ganka ba"

"To ni bawanki ne da za ki ganni, na tafi neman kuɗi dan ba zan tsaya ki ɓatan lokaci ba"

"Amma kuma ka san bani da kuɗin napep da zan koma gida ko?"

"Idan kin ga dama ki taho a ƙafa tunda ke baki da burin daya wuce kashe kuɗi." 

Bata kai ga ƙara magana ba kawai taji ya yanke kiran, ajiyar zuciya ta sauke kawai.


Tsaya take kawai tana tunanin yadda za tayi tattaki daga asibitin Murtala har zuwa Mandawari. "Gaskiya da nisa" Shi ne abinda ta faɗa a fili kafin ta fara tafiya a ƙafa. Ta ci baƙar wahala daga nan zuwa ƙofar Nassarawa kafin ta samu guri ta tsaya dan ta huta sannan ta cigaba da tattaki.

"Sannu baiwar Allah" Jin an faɗi haka ya saka ta juya tana kallon mai magana. Sam bata gane shi ba amma tabbas fuskar tayi mata kama da wanda ta sani.

"Kamar abin hawa kike nema ko?"

"Eh" Ta furta a ƙagauce.

"Ayya ina za kije ne?"

"Zanje Mandawari ne"

"Okay idan ba za ki damu ba muje sai in rage miki hanya ga motana can tsallaken titi, na hango ki ne sai nace ai kamar na san fuskar nan"

"Amma ni kuma ban gane ka ba?"

"Eh ba lallai dama ki gane ni ba saboda sau ɗaya muka taɓa haɗuwa"

A yanayin da take kuwa tana buƙatar taimakon dan ta gaji da tafiyar ƙasa. 


Kafin ma ta ƙarasa gaban motar sai data tabbatar ta karanta ayatul kursiyyu. Suna shiga yaja motar sannan ya ce "Kun taɓa zuwa asibitin da nake aiki keda wata ƙawarki har kika manta zobe acan" Ji tayi gabanta ya faɗi, ta kai hannu ta ɗan sosa goshinta kafin ta ce "Allah sarki"

"Kin yi aure kenan?"

"Eh" Ta furta a sanyaye.

"Allah sarki, to Allah ya baku zaman lafiya, kiyi haƙuri a time ɗin hankalina ne ya tashi domin bana yin abinda kuka buƙata"

"Haba babu komai ai ya wuce"

"Sadeeq ya kai miki zobenki ki?"

"Eh" Ta faɗa tana murmushin yaƙe dan hirar ta gundireta. A daidai junction ta ce ya sauketa ya yi ta ƙwawar ya ƙarasa da ita har gida amma taƙi yarda.


Sai dai abinda ya bata matuƙar mamaki shi ne tana zuwa ta tarar da Jamilu zaune yana shan kayan marmari, kallon shi kawai tayi ta ɗauke kai sannan ta wuce bedroom, ranta ya ɓaci dan haka bata kulashi ba shi kuma dama haka yake so, dan haka bai tanka mata ba. Ji tayi ba zata iya daurewa ba ta fito ranta a ɓace ta kalleshi "Yanzu dama gida zaka dawo amma shi ne ba zaka iya jirana ba, bayan cikinka nake ɗauke dashi"

"Cikin mu dai, tunda mutum ɗaya dai baya iyayin ciki, kuma ciki ai ba sabon abu ne a gurinki ba"

"Me kake nufi da hakan?"

"Ban sani ba, kin ga Sumayya ni fa ba wani sonki nake ba dole aka min na aureki, kuma bari kiji ni ba bawanki bane da dole sai abinda kike so zan yi, sannan ba direbanki bane da za ki shanyani a asibiti"

"Amma dai ai ka san ba daɗi ne ya zaunar dani ba"

"Malama idan kayan nan kike son sha ki bari in na rage sai ki sha, baki tsaya kaina kina min hauka ba"

"Na fi ƙarfin cin guntu" Ta faɗa rai ɓace sannan ta koma ciki. Kan katifa ta zauna dan gadon ma ya sayar dashi, wasu hawaye masu zafi taji a kuncinta, bata ankara ba taji Jamilu na faɗin "Maimaita abinda kika ce"

Ɗago manya idanunta tayi tana kallonsa.

"Sumayya ke kanki ai guntu ce mene dan kin ci guntuna, ni fa har gobe ina ƙaunar Atika, da ace yau Atika za ta dawo ta ce tana sona da babu abinda zai hana na sake ki na aureta" 

Tunda ya fara maganar ta kafe shi da ido kuma har ya kai aya bata tanka masa ba. "Ki sani zaman Umma kike a gidan nan" Yana gama faɗa ya juya ya fita. Ji tayi zuciyarta kamar zata fashe, ta dafe gurin kawai ta saki kukanta a fili.


             ********


"Itace tsohuwar matar Kamal"

"What?"

"Yes itace, nima ban sani ba sai ranar da muka je yi mata ta'aziyyar mahaifanta" Ya sauke ajiyar zuciya sannan ya cigaba da faɗin "Tun daga wannan ranar na fara ƙoƙarin cireta a rai saɓanin a baya da naji kamar wani abu mai kama da so"

"Au wai dama itace, kenan cikin dai dagaske shege ne!"

"Ba shege bane Nasir"

"Kamarya kenan?"

"Ban san ta ina zan fara ba, amma zan warware maka komai"

"Yaushe kenan, ai yanzu ne lokacin daya kamata na san komai"

"A ina Sumayya take aure? Ina buƙatar ganinta"

"Wallahi ban sani ba, amma dai a mandawari take aure sai dai bata yarda na sauketa a gida ba, amma da gani tana cikin damuwa sosai"

"Ya salam, wallahi abubuwa ne suka rikice shiyasa ma na manta da wancan batun amma zan je har gidansu ayi min kwatance gidanta."

"Ka faɗa min mene yake faruwa?"

"Nasir mu yi magana later, yanzu ka ga Kamal ba lafiya, matarsa ta haihu ɗan ya rasu, Hamdiyya na kasa gane kanta wallahi ni kaina ba a nutse nake ba"

"Ayya ai ban sani ba, Allah yasa mai ceto ne"

"Amin"

"Tana wane asibiti?"

"Tana wani Best private hospital anan nassarawa kan titin da zai kaika filin sukuwa"

"Na gane hospital ɗin insha Allah zanyi ƙoƙarin zuwa na dubata"

"Okay ya yi"

"To bari na barka"

"Ok sai mun yi magana"

"Alright."


        ****** ******


Yana gama shiryawa ya juyo ya kalleta "Amma da kin daure kin shirya munje kin dubota, yau kwana biyu tana asibiti bai kamata ace baki je ba"

"Baby kaje kawai idan zakuje da yamma na biku, amma yanzu wallahi bana jindaɗi"

"Ni na rasa damuwar nan ta mecece kuma kin ƙi ki sanar dani"

"Zan sanar da kai, ai ka san bana ɓoye maka komai, amma yanzu kana busy kar na ɗora maka wata pressure"

"Duk wani abu da zanyi ai kina gabansa sweetheart please ki faɗa min"

"Akan Babynmu ne" Bata san lokacin da ta shimfiɗo wannan ƙaryar ba itama.


Murmushi ya yi tare da rungomota jikinsa "Karki damu Babe insha Allah Babynmu zai zo duniya lafiya, ke dai ki kula da kanki kinji, na san kina ɗaga hankali ne saboda kin ga matar Kamal ta samu matsala, to ke ba zaki samu ba, kowa da tashi ƙaddarar"

"Shi kenan Baby na gamsu da abinda ka faɗa, ka tashi ka tafi kar a makara wurin kai musu breakfast na san Ayrah na jiranka a parlour" Ta ƙarasa tana masa peck a goshi.

Ita ta rakashi har bakin mota, suka tafi shi da Ayrah, sai da ta tabbatar sun fita sannan ta koma cikin gidan, sai data ɗan tsorata ganin Kamal tsaye a parlour, ta ɗan juya ta kalli ƙofa sannan ta kalleshi. "Yaya ina cikin tashin hankali, duk ranar da Sadeeq ya gano abinda ke faruwa wallahi na shiga uku" 

"Ki kwantar da hankalinki ni na san wacece Jidda na san ba zata taɓa tona min asiri ba"

"Amma karka manta ƙanwarta ma ta ganmu"

"Tunda har ya kai yanzu basu faɗa ba to ba zasu faɗa ba, ai sun san gabaɗayansu nine gatansu idan suka tona asirina wa zai cigaba da ɗawainiya dasu"

"Kana ganin ƙanwar ma ba zata tona ba?"

"Haka ne"

Ajiyar zuciya kawai ta sauke tare da zama kan kujerar.


 "Jiki ya yi sauƙi da alama" Murmushi tayi sannan ta ce "Eh alhamdulillah"

"To Allah ya ƙara afuwa"

"Amin ya rabbi"

Kallon Ayrah ya yi sannan ya ce "Mu wuce ko?"

"Okay" Miƙewa tayi shima ya kalli Jidda.

"Fatan ba wani abu da kuke ɓuƙata?"

"Eh babu, amma ina tunanin yau in an sallamemu gida kawai za mu wuce"

"Meyasa? Ai naga kin samu sauƙi"

"Eh da buƙatar inje gidan" Ta faɗa cikin dakiya."To shi kenan zan sanar da Kamal ɗin"

Bata sake magana ba har suka fita. Suna rufe ƙofa Amira ta kunno kai.


"Yaya Sadeeq ina kwana?"

"Lafiya lau Amira ya mai jiki"

"Da sauƙi"

"Allah ya ƙara lafiya"

"Amin"

"Yawwa ranar naga kina ƙoƙarin faɗa min magana kuma sai kika fasa"

"Aunty ce ke ta kwaɓata"

"To ai yanzu bata nan sai ki faɗa min ko"

"Ya kamata ka sani kam tunda abin ya shafe ka, amma kuma ina tsoron na faɗa gaskiya"

"Amira ki cire tsoro feel free"

"To shi kenan, amma gaskiya ina buƙatar privacy"

"Okay." Ya kalli Ayrah ya ce "Ko za ki ɗan koma gefe?"

Ɗan hararar Amira tayi sannan ta matsa can nesa dasu, suma suka koma gefe.


Yanda Ayrah ke hangosu ta tabbatar maganar da ake faɗawa Sadeeq tana da matuƙar tashin hankali dan tana ganin reaction ɗin sa har da inda taga ya yi saurin runtse ido. Tana ganin ya nufota kawai ta kauda kai. "Ayrah" Yanda ya faɗa ya saka ta kalleshi da sauri, ta ga idanunsa har sun canja kala.

"Kin iya driving"

"Yaya lafiya?"

"Ki kaini gurin Goggo" Ya furta da alamun yana so ya yi kuka.

"Yaya mene ta faɗa ma?"

Kawai gani tayi ya riƙe kai yana baya da baya. "Yaya lafiy...!" Bata ƙarasa ba kawai ta ga ya zube ƙasa wanwar.


_SaNaz_deeyah_🌸