SUMAYYA

Page 25

by @sanazdeeyah

*SUMAYYA*

_Wattpad@SaNaz_deeyah_

_Arewabooks@sanazdedyah_

Youtube: ***

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*

_[tushen mu'amula tagari]_



*Free*

_Page 25_


Juyowa tayi ta kalleshi "Sadeeq!" Ta furta sai kuma ta ƙaraso da sauri ta tsaya gabanshi tare da kafe shi da manyan idanunta. "Dan Allah Hafsat kiyi min jagora gurin Mommy na sanar mata"

Ji tayi gabanta ya yi mummunan faɗuwa, ta sauke kanta ƙasa tare da sauke ajiyar zuciya. "Sadeeq har yanzu fa Mommy haushi na take ji gani take kamar ni ce dalilin fara shaye-shayenka, yanzu ya kake so nayi, ni na shiga uku" Ta faɗa tana saka hannunta akan fuska.

"Okay shi kenan zanje ni kaɗai" Janye hannu tayi ta kalleshi "Za mu je tare kawai, amma ka bari sai daga baya ba yanzu ba"

"Amma wata biyu zuwa uku ba"

"Duk da haka kawai ka bari sai daga baya dan Allah sai a sanar musu ka ga yanzu ba a lafa da wannan case ɗin ba"

"Kenan sai daga baya kar su sani yanzu?"

"To mai afkuwa ta afku, ta faru ta ƙare, kawai sai dai a kiyaye gaba. Amma dan Allah ka bar maganar nan for now"

"To shi kenan na amince" Tausayi yake bata sosai, ta ɗanyi murmushi "Za mu fita yau da yamma?"

"Anya zan iya?"

"Za ka iya, mu ɗan fita mu samu refreshment ko"

Kallonta kawai ya yi, ta ɗanyi murmushi "Ni sai yanzu ma nake ƙara jin yunwa mu je mu yi breakfast"

"Bana jin cin komai"

Har ɗe hsnnayenta tayi a ƙirji ta turo baki "Shi kenan ni kam zan tashi na tattara na koma gida tunda Sadeeq baya son abinda nake so"

"Ba haka bane"

"To ya ya ne? Ni dai please mu tafi na saka a yi mana warming"

"Okay" Ya furta sannan ta ce "Yawwa ko kai fa" Murmusxhi tayi ta wuce, shi kuma ya mara mata baya.


Ita tayi serving ɗinsa Goggo na ta tsokanarshi sam yaƙi ya yi ko murmushi talkless of dariya, Hafsat dai murmushi tayi dan ta san Goggo dole sai tayi tsokana ko da zai ji haushi.


           ******* ******


Da ƙarfin tsiya aka fimciketa, ta riƙe wannan matar dake gefenta, tana karkarwa tana kuka, a haka aka mata ɗaukar jarirai aka fitar da ita daga ɗakin nan. Kallon gurin take tana zare manyan idanunta da suka zama tamkar garwashi saboda taci kuka ta ƙoshi.

Ji tayi kawai suna wasu maganganun da ta kasa gane me suke faɗa gabaɗaya tsoki burutsu ne, addu'a kawai take duk wacce tazo mata baki, a wannan lokacin har addu'ar shiga banɗaki da ta saka kaya sai da tayi, suna aurutansu ita kuma tana ambatar suna Allah. Wata babbar tukunya taga an dire gabanta, sai kuma wani abu mai kama da jallo a ciki. "Ku banƙareta a yanka ita zamu bawa dodo" Shi ne kaɗai furucin da aka yi da yaren da tafi iyawa, a take a gurin ta saki fitsarin dole. Ji tayi an banƙareta, ta runtse ido kawai ta fara karanto kalmar shahada, taji an ɗora wuƙa amma kuma daga nan bata sake sanin inda kanta yake ba.


A hankali ta fara buɗe idonta tana ƙara kallon ɗaki da yake da duhu, a farko ma ta ɗauka a kabari take sai dai jin ana tari a gefenta ya saka tayi zunbur ta miƙe. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Ta furta cikin tsananin tashin hankali.

"Kema kin samu kanki, basu yanka ki ba?"

"Dama kin san in sun ɗaureni yankani za suyi?"

"Eh yankawa suke yi zuwa nan mutane kusan 7 aka kashe, nima har an mun aski za a yankani ta ce a'a akwai matsala to tunda aka kawo ni nan har yanzu ba a ɗaukeni ba"

"Ya kamata mu samu hanyar guduwa daga nan"

"Ta ya ya?"

"Dole mu nemawa kanmu mafita"

"No way out 'yar uwa"

"Kin gs ni ba turanci na iya ba amma kin san mene?"

"Kai ta girgiza alamar a'a"

"Na ji suna faɗar yau akwai meeting na musamman da dare, to mu a lokacin zamu samu mu gudu"

"Ta ina?"

"Meeting ɗin na kowa da kowa ne?"

"To ai mu kuma a rufe muke"

"Kin ga" Ta ɗaga key guda ɗaya.

Zaro ido waccan tayi ta ce "A ina kika samo?"

"A ƙugu ta ɗaure ni kuma na samu na ɓallo ɗaya dama damar nan kawai nake jira, zan kintaci lokacin meeting ɗinsu na tsire in kuma ba za ki tafi ba to ni kam wallahi gara na mutu a gurin kuɓutar da kaina..." 


_Few Hours Later_


Gudu sosai suke a cikin dajin, sai dai basu yi nisa sosai ba Atika ta tsaya cak. Ɗayar matar mai suna Jamila ta riƙota tare da faɗin "Ya kamata mu samu ko titi ne mu ƙarasa...." Gani tayi idon Atika ya fara kakkafewa "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Ta furta da tashin hankali."Baiwar Allah ki tashi dan Allah mu ƙarasa titi" Ai tuni Atika ta zube a ƙasa ta fara jijjiga kumfa na fita daga bakinta. Jamila ta daɗe sosai tana tashin Atika sai dai ina bata ma san inda hankalinta yake ba, dan haka a ƙarshe haƙura ƙawai tayi ta barta anan ta tafi ba dan taso hakan ba.


 _Bayan Shekaru Huɗu_


Tana zaune a gefen katifa, ta ƙurawa guri ɗaya ido, har Jamilu ya yi sallama ya shigo bata san inda hankalinta yake ba, har sai daya zauna kusa da ita sannan tayi saurin dubansa. "Ya dai? Naga kin ƙurawa guri ɗaya ido kuma da alama a damuwa kike"

"Dole na damu fa, saboda har yanzu babu Atika ba labarinta, mijinta ma bai damu ba tunda gashi nan ya yi aure abinsa matarsa har ta haihu fa, shekara huɗu kenan, tunda ga Hanifa har ta shiga pre nursery."

"Insha Allah za a ganta, muna ta addu'a Allah ya bayyanata."

"Amin" Ta faɗa tare da saka hannu ta share hawaye.

"Dan Allah ki daina damuwar nan Sumayya za a ga Atika insha Allahu"

"shekaru huɗu har da watanni fa, ko Atika mutuwa tayi gara ace naga gawarta da irin wannan ɓatan dabon"

Zai yi magana wayarsa ta fara ringing, ya kalla sannan ya miƙe da sauri "Ina zuwa."


Sai daya fita har ƙofar gida sannan ya ɗaga kiran. "Ina wuni Yallaɓai"

"Tun yanzu Yallaɓai na ɗauka zaka ɗan jira ayi ko wata biyar haka ko shekara ma"

"Eh na fahimta, to shi kenan amma dan Allah ku ɗan bani ko kwana biyu ne."

"To shikenan ya na iya, Allah ya kawo ku lafiya" Yana gamawa ya sauke ajiyar zuciya. "Ana wata ga wata" Ya furta a sanyaye.


_Bayan Kwana Biyu_


Hugging ɗinta tayi sannan tayi mata peck a kumatu. "Ki kula sosai ban da wasa kinji Hanifa ta" Kai yarinyar ta gyaɗa sannan Sumayya ta miƙe tare da saka mata 'yar ƙaramar jakarta, ta ɗauki lunch box ɗinta sannan ta kama hannunta suka fita parlor.


Madaidaicin parlour ne da aka ƙawata shi da maimaidashi kujeru masu ɗan kyau. Jamilu dai da ya yi aure ko kujeru babu a ɗakinsa, amma gab da Sumayya zata haihu suka komai gidan daya saya, wanda madaidaici ne dai-dai na masu ƙaramin ƙarfi sai dai kuma yasha kayan ɗaki, Sumayya dai hankalunta ya kawanta ganin Jamilu a yanzu ya buɗe shagon provision ta tabbatar ba a sama yake samun kuɗin ba, yana da abin yi, yaje shago wata rana ya ƙarɓi napep ya tuƙa haka yake yi.


Yana kwance da remote a hannunsa yana kallon Hijra tv a ƙaramar plazma ɗinsu dake manne da bango.

"Yayana naga baka shirya ba, ga Babynka har ta gama shiri mun ma so mu makara" Miƙewa zaune ya yi sannan ya ware hannayensa ya ce "Baby taho" Da sauri ta ƙarasa gabansa ya rungumeta, Sumayya tayi murmushi tana zama a kujerar kusa dashi, tana ta kallon yadda Jamilu ke wasa da Hanifa.

"Kana ji da Babyn nan taka"

"Ba dole ba, ai ita ɗin alheri ce a gareni, amma kuma duk jin da nake da ita sai naga kamar ma kin fin?i"

"Ina ƙaunarta sosai, saboda ganinta yana sa inajin a raina na fara gina sabuwar rayuwa, ka ga dai Atika har yanzu shiru, sannan ka ga Hanifa theater aka yi aka fitar da ita, sannan Dr ya ce dole sai na riƙa ɗibar kamar shekaru biyar kafin na sake haihuwa koma na haƙura saboda mahaifata bata da ƙwari a dalilin abinda na aikatawa kaina a baya" Sai kuma tayi shiru, hawaye ya cika kurmin idanunta "Yaya ka tashi karta makara.

"Yau ba zata je school ba"

"Meyasa?"

"Akwai baƙo da zamuyi anjima kuma ina so ya ganta ƙila ma ya canja mata school"

"Gateway ai makaranta ce mai kyau, Hanifa bata buƙatar canjin school a yanzu, dududu a pre nursery fa take"

"Sumayya abokina ne kuma ya daɗe bamu haɗu ba, bai san nayi aure ba, bai kuma san Hanifa ba ya tafi Lagos to sai yanzu ya dawo kuma zan so ya ganta dan shima ya buƙaci haka"

"Amma da wuri zai zo haka da za a katse mata makaranta"

"Idan ba da wuri bane zan ce kar taje, ke fa kin iya musu Malama ki cire mata kayanta ki canja sannan ki haɗa mata kaya masu kyau a akwati zan kaita gurin Umma"

Bai jira me zata faɗa ba ya wuce, da ido kawai take bin gurin.


_Ta ya ba zon Hanifa ba, bayan auren ma na jeka na yi ka ne, a shekaru biyar da aurenmu ban taɓa samun farin ciki na sati guda daga Jamilu ba, dama ina haihuwa komai ya ƙara lalacewa sa'a ta ɗaya yana matuƙar ƙaunar Hanifa._


Ji tayi an saka hannu ana goge mata hawaye, ta ɗago kai ta kalli Hanifa, sannan itama ta saka hannu tana goge hawayen da bata san lokacin da suka zubo ba.


"Mameey ki daina kuka, Abba ne ya taɓaki ko?"


Murmushi tayi sannan ta janyo Hanifa ta rungume "Ba Abba bane, abu ne ya faɗa min ido" Kawai tayi maganar dan ta lura Hanifa ta fara yin wayo ga yawan tambaya.


*05:30pm*


"Yanzu a wannan gidan 'yata ta rayu?" Ya faɗa yana kallon ƙofar gidan.

Murmushi Jamilu ya yi kafin ya ce "Gidan ne kawai ƙarami amma Hanifa 'yar gata ce"

"Wace Hanifa?"

"Bilkisu" Jamilu ya faɗa yana murmushi.


Ajiyar zuciya ya sauke tare da faɗin ban san a gidan nan kuke rayuwa ba ai da an canja muku ko dan Bilkisu."

"Yallaɓai bismilla mu shiga.


A madaidaicin tsakar gidan suka yi sallama, Sumayya ta amsa musu tana daga can uwar ɗaki har suka shiga parlor bata fito ba.


"Ka zauna bari a kawo maka ruwa ko"

"No karka damu a ƙoshe nake dan kai tsaye daga gida nake kawai ina buƙatarta ne"

"To shikenan bari na fito maka da ita."

Yana shiga ya kalli Sumayya "Kin haɗa kayan na ta?"

"Eh komai na haɗa"

"To Hanifa taso muje ko"

"Amma sai yaushe za ta dawo? Kuma naji kamar kayi baƙo ba gidan Umma za a kaita ba?"

"Ina ruwanki da baƙona"

"Allah ya huci zuciyarka" Ta furta tana sauke ajiyar zuciya.


Hannun Hanifa yaja, ita kuma Hanifa da ɗayan hannun take yiwa Sumayya bye-bye.


"Masha Allah gaskiya ka iya reno, na ɗauka zan dawo naga 'yata a rame, amma ga dukkan alamu kuɗaɗen da nake turowa kana yin abinda ya dace dasu, gata har ta girma naso ace tun ranar da aka haifeta na karɓi kayata saboda ta saba dani sosai."

Jin wannan maganar ya saka Sumayya miƙewa da sauri, dan ta kasa gane maganganun da baƙon ke yi. Da sauri ta fita parlour, lokacin yana ƙokarin ɗaukar Hanifa ita kuma taƙi yarda ta bar hannun Jamilu.


Cak ta tsaya, ta buɗe manyan idanunta tana kallonshi. _Dama ya san Jamilu?_ Shi ne tambayar da ta fara wullawa zuciyarta.

"Sumayya!" Ta tsinkayeshi ya kama sunanta.

"Ka santa ne?" Cewar Jamilu.

Kai kawai ya gyaɗa, ita kuma Sumayya har lokacin da mamaki a fuskarta.

"Kenan Sumayya ce ta raini cikina ta haifa min Bilkisu"

"Ban gane ba, me kake nufi?" Sumayya ta faɗa da mamaki.

Kallon Jamilu ya yi sannan ya ce "Alamu yana nuna kamar bata san komai ba, bayan ka faɗa min cewa ta yarda a lokacin da za a mata transplaPnting?"


Kai Jamilu ya sosa kafin ya ce "Yallaɓai ta sani amma dai muje waje mu yi magana"


"Babu inda zaku je, Jamilu kayi min bayani ka saka ni a duhu?" Sumayya ta faɗa tana fitowa tsakiyar parlour.

"Sumayya ki koma ɗaki kafin ranki ya yi mummunan ɓaci"

"Ba zan koma ba, sai na ji dalilin daya sa kake danganta 'yata da wannan mutumin da sam na tsani jin sunan ahalinsu ma a rayuwata"

"Ke dakata!" Sadeeq ya faurta cikin tsawa. Sannan ya cigaba da faɗin "Wannan yarinyar" Ya janyo Hanifa.

"To jinina ce, 'yata ce, kuma da na san ke zaki raini cikinta ki haifota ba zan yarda ba, saboda sam ban yarda da tarbiyyarki ba"

Ya juya ya kalli Jamilu ya ce "Da alama baka faɗawa matarka cewa Bilkisu 'yata ce, ita kawai an mata transplanting an mata dashen ƙwammu a cikinta ta haifa mana, kuma biyanku mu kayi naira miliyan 10 sannan bayan ta haihu na ƙara maka naira miliyan 5 ko ba haka aka yi ba? Ko baka sanar mata cewa ba jininku bace?" 

Jamilu shiru ya yi kamar ruwa ya shanye, sam baiso aka fallasa yanzu ba, yaso Hanifa ta tafi ba tare da Sumayya taga wanda ya ɗauke ta ba, ya san zai iya handling komai dan Sumayya na matuƙar tsoronsa.


"Bana ƙasar ban dawo ba sai yanzu amma da tuni na ɗauki 'ya ta, yanzu kuma na dawo na kuma karɓi kayata, dama biya nayi ba kyauta aka riƙemin ba"


"Ƙarya kake, wallahi babu inda Hanifa za taje, in raini ciki, in haifa amma dan ka raina min hankali kace 'yarka ce, wallahi baka isa ba" Ta furta tana ƙoƙarin janye Hanifa, Jamilu ya yi saurin ɗagata sama "Sumayya ranki zai ɓaci"

"Wallahi Jamilu a wannan gaɓar ba zan maka biyayya ba, ba zan yarda ka rabani da 'yata ba"

Ganin ta fara kuka ya saka Hanifa ta fara kuka itama.

"Yallaɓai muje kawai" Jamilu ya faɗa yana fita a lokacin ma Hanifa ta miƙowa Sumayya hannu tana kuka. Kallonta Sadeeq ya yi sannan ya fita. Ta bi bayansu a haukace, har sai da 'yan unguwa suka taru, da ƙarfin tsiya ya mayar da ita cikin gida a lokacin kuwa tuni Sadeeq yaja motarshi tare da Hanifa wadda ko kayan nata bai ɗauka ba.


"Ki dawo cikin nutsuwarki" Ya furta da tsawa. Kallonsa take ko alamar tsoro da furgici babu ba kamar a baya in ya mata tsawa take tsorata ba.

"Hanifa ba 'yarki bace, rainon ciki kawai kikayi kuma a lokacin duk abinda kike so na baki"

"Rainon ciki!?" Ta maimaita tana kallonsa da idanunta da sukayi jajir kuma basu daina zubda hawaye ba.

"Eh Hanifa ba 'yarmu bace" 

"Me hakan ke nufi?"

"Mtsww ban sani ba" Ya furta tare da wucewa, sai gani ya yi kawai ta zube a gurin, jini kawai ya gani kan sumuntin da yadda ta faɗi tuni kan nata ya fashe. "Sumayya" Ya faɗa yana kallonta, sai dai ko motsi bai ga tanayi ba.


SaNaz_deeyah🌸