Chapter 01
馃崅馃崅_*RAMIN K'ARYA*_ 馃崅馃崅
NA
IKILIMA ADAM
*( Kyauta daga Allah)*
Marubuciyar da ta nishandantar daku a littafanta kamar haka:
Kai ka jawa kanka
Kanwata
Rai daya ( Jan zaki)
Rudani
Makauniyar shari'a
And now
Ramin karya yan karin magana suka ce kurarre ne , mu je zuwa.
Domin Karin bayani ***
Da sunan Allah mai Rahma mai jin kai .
Yanda na fara Littafin nan lafiya , Allah ka nuna min na gama shi lafiya cikin amincinsa.
Allah kasa sakon dake cikin littafin nan ya isa inda ake so.
Ina yiwa Al'ummar Muslim barka da sallah , Allah ya maimaita muna.
Tafiya jirgin ruwan yake , kana kallon mutanen cikin sa kasan kowanne baya cikin nutsuwarsa , domin gabakidaya hankalin su ya karkata kan kallon yanda jirgin ruwan ya rage gudu.
Sannu a hankali dattijon dake zaune kan dan kujera , ya dau salati yana taba hannayensa , hakan ya zaburar da farar datttijuwar data lulluba da yara mata biyu a jikinta zabura daga barcin dake shirin daukarta.
" Baffa lafiya kuwa ?" tayi tambaya tana mai sauke idanunta akan yanda ruwa ke dan sassarfo jirgin ruwan .gefe daya kuma bayan drever take kallo.
" I...n..a.... fa....lafiya" . Ya bata amsa hankali a tashe , bakin sa dauke da salati.
Cikin rudewa da tsananin tsoro da tunanin makoma ta furta.
" Baffa kalli ruwan yana shigo mana cikin jirgin !! " tayi magana tana mai jin wani irin gudawa na azaba ya taho mata gadan_gadan.
" Wayyo !! Wayyo !! Baffa daman mutuwa zamu yi kenan , mun gudu bamu tsira ba" cewar dattijuwan a sa'in da ta dago yarinyar dake kwance kan cinyarta , wacce akalla bata fi shekara hudu zuwa biyar ba , mika masa dayar yarinyar tayi a zafafe
hannunta yana rawa .
" Ina ganin komi wallahi" ya bata amsa cikin dari dari.
" Drever lafiya kuwa , kana ganin ruwa na shiga a jirgin nan , kuma wallahi gud'a nake ji na tashi daga cikinsa " cewar Baffa yana mai kara kankame yarinyar a jikinsa.
" Eh nima haka gud'a nake ji !! wallahi ruwa ke tsarfafowa duk iya dabarar da zanyi na kasa wallahi" . Kalamansa ba karamin tada hankalin Baffa da dattijuwar ya yi ba.
Shi kansa drever fita daga wurin tukin ya yi Yana mai daukar botiki Yana dibar ruwa daga cikin ruwan , duk a banza domin ruwan kara yawa yake . Duk abunda yake idanunsu na kansa , dattijuwar cikin rauninta da sarewa da lamarin, ta furta.
" Baffa na san ka iya ruwa , ka amshi yarinyar nan ka hada da na hannunka komi na su yana cikin jakarta , don Allah ka fitar dasu daga barazanar mutuwa " ta furta tana mai damka masa yarinyar.
Shi kuwa idanunsa sun cika tam da hawaye .
" Haba Emma in sha Allah ba zamu mutu ba , Kuma kema Babu abunda ze sameki " katse zancen nasa yayi ganin drever ya yi tsalle ya fada cikin ruwa domin fidda kansa. Kallon juna sukai suna taba hannu , ga wani mugun iska da ya kusa kifar da jirgin ..
Baffa na goye da yarinyar da zani , dayar ya rike hannunasa , kokan kace me , ya rike hannun Emma , domin shiga ruwan , duk da a zuciyarsa ya san ba lallai ne su tsira ba. Karar ruwan ya tabbatar sun fada kusan a tare .
Tirkashi !!
Bayan shekaru goma sha biyar 15ans
Garin cotonou ranar juma'a da misalin karfe daya na Rana , lokacin da musulman ke hada hadan zuwa massalacin juma'a . Motoci guda uku ne a jere wanda suke tambarin *Prince Adamsy*, kirar prado 2020 , parking space motocin suka faka wanda nan ne suke fakawa duk sati , babu wanda ke gigicin ajiye motarsa anan.
Daga cikin motocin karatun al'kurani mai girma ke tashi.
Ganin angama parking ne yasanya , Matashin dake zaune kujerar baya , dago idanunsa yana kallon fadawar dake nuna masa inda zebi ya taka . Be daina tasbihi ba , haka nan cikin aji da kasaita da kamala ya sauke, koda fitarsa nan da nan talakawa almajirai suka soma masa kirari , shi kam , in har ba an idar da sallah ko magana baya yi da kowa . Wata dattijuwar Almajira karo na farko da ta fara sanya idanu akansa .
" Allah mai halitta , shi wannnan yaron , Allah ya hada masa komi , kyau , kudi , nagarta da kamala" ta fada a zuciyarta cike da jin dadin yau taga Bin Adam.
A hanzarce tagawarsa suke take masa baya , domin kana kallonsu kasan gidan sarauta ne.
Matashiyar yarinya wacce zata kai shekaru ashirin da haihuwa ne , ta fito ita da wasu kananan yara mace da namiji , kallon jama'ar wurin take cike da takaicin barinta da prince yayi ba tare da yaga fitowarta ba .
Wannnan dattijuwar kuwa , jin an ce ga matarsa nan , hakan ne yasa cikin hanzari ta karaso domin mika sakon gaisuwa dan Mijin nata yana hidima almajiran dake taruwa anan massalacin , cikinsu har da ita.
" Madam ina wuni barka da juma'a ". cewar dattijuwar tana yar dariya irin tasu ta manya.
Wani irin kallon mai wuyar fassara , ta aika mata tare da bin da kallo tun daga sama har kasa, tana mai jin kyankyaminta.
" Dallah gafara cen ! Haba ku wai bakwa ganin mutum sai kun zo inda yake " cewar matashiyar cikin fada .
" Allah ya baki hakuri daman gaisuwa na zo ". ta fada tana mai dariyar yake .
Murguna baki tayi cike da takaici , tayi gaba yaran suna bin ta a baya cikin saurinsu.
Jin antaba bayanta yasa ta waigo a zafafa ganin waye , wanda har ya iya taba jikinta , ga tsananin mamakinta wannan dattijuwar ce . Cikin tashin hankali ta ce " Ke mayyah ce ?" .wannan kalaman ba karamin janyo hankalin mutane ya yi ba akan su.
Saukar marin da ta dauke ta dashi ,ba karamin jan yo hankalin mutane ya yi ba akan su , ji kake tass .
Nan take idanun dattijuwar yaci ka da kwallah , murya na rawa ta ce " Daman gyalen ki ne ya fadi , shine na biyo ki in baki" tana fadar hakan , ta mikaka yaran gyalen , kana dakyar , ta daga kafafunta domin barin wurin , duba ga yanda idanun kowa a kansu.
Ita kuwa kallon gyalen take tana yamutsa fuska, tana jin kyankyamin Kara yafa wannan gyalen. kallon banza ta aikawa masu kallonta suna tabe baki. Tana shiga ana tada sallah.
Koda aka idar da sallah , ta riga kowa fitowa yanda kasan saman wuta take zaune .
An dau kamar minti talatin kana , Prince ya fito da magoya bayansa , fuskarsa dauke da Annuri yake bi daya bayan daya Yana gaisawa da dattijai hatta Limamin sai da suka gaisa, cike da mutuntawa .
Suna karasowa domin shiga mota , kallo daya ya mata yanda take hawayen takaicin , wannan jiran da ya sanyata gashi babu drever da tayi tafiyarta. Karamin tsuki ya ja wanda sakon ya isa kunnen wacce aka yi domin ita . Cike da mamaki take juya tsakin da ya mata bainin jama'a.
Yana kokarin sanya kafafunsa cikin mota , ya ji muryan wani Matashin Yaro.
" Amma ke wallahi kin ci darajan mai daraja , kin ci darajan kamalar Mijinki da yau wallahi sai na rama marin da kikai wa gwagwona wallahi sakarya kawai" ya fada yana huci kamar wani zakanya.
Cikin tsanain mamaki da tarin damuwa Prince ke kallon yaron .
" Bawan Allah , dawa kake ne ?" ya tambaya yana kallon yanda take wa yaron kallon banza .
" Da azzalumar matarka nake mana ,wacce ta dauke Uwata da mari dan...." Rike ragowar kalamansa ya yi jin prince na fadin .
"Laila ashe har rashin mutuncinki ya wuce inda nake tunani " ya fada ne ,yayin da idanunsa suka kada jajir. Hade hannayensa duka biyun yayi alamun ban hakuri ga yaron. " Don Allah , don Alfarman Manzon Allah ( S A W) ka yi hakuri , mu je ka rakamu wajenta mu bata hankuri".
" A'a ba sai mun je ba , dan sai da ta hanani maida martani, na ki jin zancen ta " yana fadin haka ya juya cikin hanzari ya bar wajen .
Prince kallon jama'ar dake Kai kawo dake kallon duk yanda akayi lamarin a gabansu. Yana tambayarsu yanda lamarin ya faru . Cikakken bayani wani daga cikinsu ya masa Wanda ya bashi shaidar a gabansa aka yi marin. Kallon sama yayi kana ya sauke idanunsa akanta cikin tafasar zuciya , dawo da kallonsa akan jama'ar wurin ya yi cikin sanyin murya mai dadin sauraro yake nuna musu rashin jin dadin haka , ya kume nemi a bashi adress din gidan matar, domin musamnan ze taka zuwa gobe domin bata hakuri . Koda suka kama hanya sosai yake jinjina karfin halin Laila har abun nata ya kai tayi shi a gaban massalaci.
Ita kuwa Bangaren Lailat gabanta ne yake tsananta bugawa da karfin tsiya , shirun da prince ya mata ta san akwai wata a kasa .
Kusan a jere motocinsu suka kuno kai a gaban gate din Masarautar Lafiya.
Horn din motar farko ya sanya , Mai gadi hanzarta soma budewa inda ma'aikatan tsaron dake wajen suka fara bada domin motocin su shiga daga ciki.
" Barka da zuwa , Dan Sarki , jikan Sarki " kadan daga cikin furucin mai gadi kenan , ya yin da yake daga hannu cike da girmamawa .
Prince ta cikin glass yake kallonsa , sam be kulasa ba , kasantuwa ransa a bace yake .
Mai gadi cikin zallan mamaki yake fadin
" Anya prince lafiya kuwa , mutumin da duk juma'a annurinsa yana fin na kullum, kuma lafiya lau ya fita " yana maganar zuci tare da maida get din gidan ya rufe .
Prince Adamsy cikin hanzarinsa ya fice daga cikin motar bayan , parking din motocin.
Gabadaya magoya bayansa , sun san akwai matsala babba ma kuwa , kowannensu , yana rike da baki sunata jinjina yanda abubuwa zasu kasance a cikin gidan. Fadawa kuwa matsawa suka ringa yi dan sun san akwai matslaa in suka tare masa gaba. Ita kuwa Lailah cikin saurinta tabi bayan Prince har tana tuntube , yaran kuwa sai bin ta suke a baya.
Wow na furta ganin cikin daular gidan Sarautan zamani Wanda yake ciki da kayatattun kayan zamani Dana gargajiya , tsarin Masarautar ya bambamta dana sauran masarautu dana sani.
Prince zaune bakin gadonsa , babu abunda yake juyawa cikin kwakwalwar kansa , sai kalaman yaron nan a babban massalacin juma'a. Jin karar bude kofa ne , ya sanya idanunsa akan kofar, ga mamakinsa Lailat ce . Caraf ya tashi tsaye kamar an tsinkaye shi da Allura bakinsa na rawa ya ce .
" Me kike nema a dakina"?. Ya fada cikin tsananin karuwan bacin rai. Cikin nuna rashin damuwa da abunda ta aikata ta furta .
" Naga dakin Mijina na shigo , daman kuma na shigo dan in fada maka ina dauke da cikinka na wata biyu ko uku.
" Innalillah wa'innalilah raj'un" shine kalmomin dake futa daga bakinsa. Cikin rikicewa da karin mummunar tashin hankali ya furta.
" Laila ciki?".
" Kwarai kuwa ciki ne dani" ta fada cike da gadara.
" Ina kika samu ciki Laila?".
Toh masu karatu yanzu mu ka tsoma hannu cikin miya.
Shin me kuke tunanin ze faru a gaba?
Wasa farin girki
Taku har kullum kyauta daga Allah