Chapter 02
๐๐_*RAMIN K'ARYA*_ ๐๐
NA
IKILIMA ADAM
*( Kyauta daga Allah)*
Marubuciyar da ta nishandantar daku a littafanta kamar haka:
Kai ka jawa kanka
Kanwata
Rai daya ( Jan zaki)
Rudani
Makauniyar shari'a
And now
Ramin karya yan karin magana suka ce kurarre ne , mu je zuwa.
SHAFI NA BIYU
" Ina kika samu ciki?." Ya tambaya yana mai kusanto inda take . Ita kuwa soma ja da baya baya take , tana kokarin barin dakin a guje , kokan ta ankare ya cafkota tare da maida kofar dakin ya rufe , idanunta na kan yanda ya zare key din dakin daga kofar.
" Banda innalillah" babu abunda ke fita daga zuciyarta.
" Maimaita abunda kika fada "?". Ya fada yana shake da rigarta yanda kasan dukan kawo wuka ze mata .
Ita kuwa sosai ta tsorace tunda take dashi bata taba ganinsa cikin wannan yanayin ba . "
" Daman naga watan nan har ya gota banga al'adata ba , shine nayi tunanin ko ciki ne dani " ta furta cikin rawar murya.
" Na taba kusantar ki?" Ya tambaya cikin tsananin bacin rai .
Cikin hardewar harshe ta furta " Eh , a'a " .
Gira ya daga mata alamun me hakan yake nufi ? ".
" Don Allah ka cikani sai na maka bayani " ta fada cikin jin wuyar shakar da ya mata .
Yana saketa ta fara sauke numfashi sama_sama , kana idanunta na kansa .
" Prince kwanakin baya , ka shigo dakina, har kayi mu'amala dani ta karfi , tun lokacin ban kara ganin al'adata ba " ta fada murya na rawa .
Wani irin kallo masu wuyar fassara yake bin ta dashi , kalamata ba karamin yawo yake akansa ba , kana ya kalli hoton dake saman bangon dakinsa , tare da sake dawo da kallonsa akanta karo na biyu.
" In har kana tantama kalli hoton nan " ta juya masa fuskar wayarta domin kallon yanda yake kwance a jikinta . Zazzare idanu ya fara . Hankali tashe da rawar murya ya furta.
" Laila me kika min na tsinci kaina , cikin wannan yanayin ?" .
" Soma jujjuya idanunta ta soma .
" Kai ne zan ma wannan tambaya da zan ce fyade kamin " ta fada tare da nuna halin ko in kula.
Numfashi ya fesar yana mai jinjina kansa .
" Lailat wannan shine karo na farko da muka yi hira da ta wuce mintina goma ni dake , kin sani na sani babu tarayya tsakanina dake , Laila me ya sa kike neman , sai kin canza komi , karki fara cewa wannan cikin dake jikinki nawa , domin kuwa na san karya kike wallahi , Lailat Margayya ba haka take ba , an bata tarbiyya ta karba , ke kuwa kin watsar da naki , Laila kina son ki cuce ni , to bara ki ji abunda zan furta miki , ni Prince Adamsy bana son ki yau , bana son ki gobe , yayar ki nake so kuma mai rabawa ya raba ".
Sosai take juya kalamansa da baya sonta , kallonsa take yanda ya zauna bakin gado dirshan , idanunsa cike da kwallah , ganin zaman ya gagaresa ,tashi ya yi ya dauko hoton dake sama makale , jikin bango , shafa hoton matashiyar yarinya dake cikin hoton yake , wasu hawaye masu zafi suna sulalo masa a hankali. Kallonsa take tana cizar yatsa.
" Prince Adamsy , wannan fa antina ce , uwa daya uba daya , tunda ta rasu meye na wani kafe hoton ta , kana kallo Kuma.....". Ragowar kalamanta makalewa suka yi jin ya sanya hannu ya bige bakinta da karfi . Kana ya kama hannunta tare da sanya key ya bude kofar , hankadata waje ya yi tare da maida kofarsa ya rufe. Lailat kuwa daidai turowar da yamata sai kan Idanun Jakadiya.
Sosai Jakadiya ta zazzare idanu , cike da mamaki , haka ya sanya cikin hanzari ta karasa kusa da ita.
" Sannu Gimbiya " ta fada tana mai dan rike ta ".
" Aa babu komi" ta bata amsa, tana mai kauda fuskarta gefe , domin sam bata son taga yanda idanunta suka kada jajir .
Daga cikin dakin Prince kallon hoton yake yana surutai.
" Maryam , kin tafi kin barni , kin tafi kin barni da bakin cikin yar uwarki , maryam na miki alkawarin daga ke babu wata , maryam tun kina raye na sha gayamiki ki daina alakanta kanwarki dani ga shi kin mutu an bani ita , bana sonta maryam , don Allah ki rabani da ita " ya fada yana mai kara rumgume hoton tsam a jikinsa .
Lumshe idanunsa ya yi yana tuno lokacin da maryam take raye , kadan daga cikin firarsu.
" My chocolaty wallahi na fi son mutuwa ta fara daukata kafin kai, domin ba zan iya rayuwa ,babu kai a doron kasa ba " ta fada tana makale a kirjinsa cikin kayan barci.
" Shiiii" ya furta domin dakatarwa daga maganganunta.
" Haba Maryam taya kike wannan , ai nine dai zan rigaki mutuwa in sha Allah , domin rayuwata babu inganci , don daga ranar babu ni babu wata mace a duniya , bana son ki daina kawo mun zancen mutuwa pls My Wife".
Tashi tayi daga rumgume da suka yi da juna , tare da kallonsa , hannunsu tsarke cikin na juna .
" Aa Chocolaty , karka mun haka , yau inna riga ka, don Allah kayi aure , ko don a samu, wacce zata kula da ya'yan mu , kaga tsohon ciki ne dani Kuma...".
" Stop bana son ji".
" Am sorry my chocolaty" ta fada tana mai shafa fuskarsa cike da so da kauna.
Firgit ya dawo daga duniyar tunani , yana mai kiss din hoton, tare da mai da hoton mazauninsa.
______________
Lailat zaune bakin gadonta tana nazartan yanda Prince ya ci mutuncinta , Kara tashi tayi tsaye hannayenta goye a baya . Kana cike da takaici ta dauko wayarta mai kirar Samsung Galaxy S700 tayi Dial number tare da karawa a kunnenta.
" Nura yau prince ya ci mun mutuncina fa , kuma yana son ya musanta cikin dake jikina , kamar fa ya gane , be kusanceni ba , baka ganin ze tona mun asiri kuwa ?" ta fada tana mai saka yatsarta daya a bakinta.
" Aa wallahi ba ze taba ganewa ba , nafi ki sanin waye prince Adamsy ko babu komi Uban mu daya dashi , kuma cikin nan wallahi ko kur'ani ze rantse wallahi jininsa ne , kema kin san haka ".
" Na sani" ta bashi amsa a sanyaye.
" Babu abunda yake damuna kamar yanda yake yawan daukar hoton , anty Maryam ".
" Ki bar dan wahala ya yi ta soyayya da gawa in har dagaske yake , ai bari zeyi a binne su tare, don Allah share shi ". .
" Tom shi ke nan , na gode , anjima ina jiranka" "ta fada tare katse wayar.
_____________________
Masarautar *Lafiya* , Masarauta ce , wacce take zaune a cikin garin cotonou , babban Masarauta ce wanda duk kasashen Africa ๐ sun san da zamanta da kuma tasirinta.
Khalifa Adam , shine Sarki dake kan karagan Mulki , inda yake zaune da matansa uku , Fatima ita ce uwargidansa , wacce ta haifa masa ya'ya uku maza , mace daya.
Adamsy , Aliyu , Abdullahi , sai Sumayya.
Zainab ce matarsa ta biyu duk tsawon zaman shekarun da suka kwashe , Allah bai bata haihuwa ba .
Humaira ita ce Amaryarsa ta uku duk da a rana daya, ya auro su ita da Zainab din , sai dai ita bayan sati daya da bikin nasu ta tare.
Ya'yanta uku mata , namiji daya . Nura shine babban danta , sai Surayyah , Rayyah , khadija.
Sarkin Khalifa Adam , zaune yake da kannensa
maza biyu tare da matansu .
Ashiru da Falalu ,sune asalin kannensa da suka fito ciki daya , sai sauran da suke uba daya .
__________________
Kashe gari
Masarautar antashi da iska sakamakon hadarin da ya hade a sama , nan da nan , ko ina ya dau duhu.
Prince Adamsy , tashi ya yi daga kwancen da yake yana mai kai dubansa akan hoton Maryam , cikin dan saurinsa ya sauke kafafunsa kasa yana mai mika tare da harba idanunsa akan agogon dake makale bangon dakinsa mai adon zinare anyi shi kamar dawisu.
" Ya salam , wani irin barci nayi haka , har karfe goma na safe " ya fada yana sakin hamma . Rigar barcin dake jikin ya fara cirewa yana jefa su saman gadonsa , dan a hanzarce ya shige bandaki domin yin brush da wanka da bukatunsa .
Ahankali aka turo kofar, kasantuwa mai aikinsa karfe goma daidai da kwata take shigo masa coffee , hade da break , tayi knock baa bude, ko bata izinin shigowa ba , hakan ya sanyata , dan tsayuwa jira a bakin kofar.
__________________
" Umma kiyi hakuri fa , don wallahi jiya sai da na gayamata magana , akan me zata mareki a kyaleta dan kawai prince Adam mutumin kirki ne , kuma yana taimako sosai ba don haka ba ai da na cire mata hakora sai dai abunda za'a min sai dai a min" ya fada yana mai kara zamansa akan tabarma .
" Yanzu Ibrahim duk da na hanaka kenan sai da ka tafi , ashe ka fara bijire Umarnina Iro?" . Ta fada cike da damuwa.
" A'a kiyi hakuri ki yafe min , wallahi na kasa control din kaina ne " ya fada yana mai hada hannayensa alamun neman tuba yake.
" Shi ke nan , na ji amma pls karka sake yin abunda bana so , Allah ya maka Albarka " .
" Ameen ya furta yana kallon kanwarsa da ta fito daga dakin, dakyar take jan botikin awara zata fita suya a bakin kasuwa.
" Umma ina ga awaran jiya ya dan soma lalacewa " . In ji Matashiyar yarinyar wacce akallah shekarunta basu wuce sha tara 19 ba .
" Oh Jiddah , kin san awaran nan suka lalace ai mun Kade , kuma ki cire wannan nikaf din tunda ai mussahabi ne , kullum kiyi ta boye fuska , ke ba aure ba ".
Turo baki gaba tayi " nifa Umma kallo ne bana so , musamnan kasuwar nan , suyi ta damunka da surutu, Kuma ai awara na kai , ina ruwansu da ganin fuskata , sai fadi suke marasa gaskiya ke rufe fuska babu aure ".
Murmushi Iro yayi tare da tankwashe kafafunsa .
" Ke dai tunda Umma ta ce , ki cire , ki cire mana , kin san tana son taga surukinta ".ya fada ya san duk duniya bata son wannan kalmar.
" Kanka ake ji " ta fada tana mai cire nikaf din.
Waou , ya ilahi na furta ganin zunzurutun kyau mai cike tsaruwar ubangiji. Yarinya fara sol zubin matan Ethiopian ko shuwa , zanen hanci ba karamin sajewa yayi da dan karamin bakinta yayi ba , ita ba doguwa ba , baa sanya ta sahun masu kiba , hakan nan ita ba ramamma , ga hip da boob . Ma sha Allah duk wani namiji da ya fara sanya idanu akan ta ze furta.
" Na tafi sai na dawo, Umma ki min adua kai ma haka yaya Iro " .
" Allah ya bada sa'a " .suka bata amsa
" Ameen Ummata " ta fada tana yar dariya, Wanda ya kara fito da zallan kyawunta.
Cike da kunya ta fito wajen gidan , tare tsayuwa kan titi domin tare abun hawa.
" Jidda har kin fito" cewar kawarta mai suna Ummi.
" Eh kin ganni , ina son na je kada awaran nan ya lalace " .
" Yau ke ce kika fito babu nikaf, nayi mamaki jidda" .
" Humm kema kin san in ba Umma ba , babu wanda ze sanya na cire , Kuma ina bala'in jin kunyar shiga cikin kasuwar nan , ji nake kamar a tsirara nake " ta fada cike da rauninta.
" Kawai ki daure a haka zaki saba kin ji kawata , daman na zo ne , ko zan samu ko awaran ne , na kai gidan mu , wallahi yunwa kannena suke ji babu wanda ya karya " ta fada fuska cikin damuwa.
Cikin hanzari Jidder ta sanya hannu cikin robar awara ta fara zuba awara aleda sai da ta cika tam.
" Jidda yayi yawa fa ".
" Da abarshi ya lalace gwamma anci, kuma karki damu ai abun gidan mu naku ne. Cewar Jidda
" Na gode my Jidder , Kalli gefen ki cen Jidda , motar prince Adamsy nake hangowa."
" Prince Adamsy , a unguwar laka?". Cewar Jidda tana mai sauke idanu akan motocin dake karasowa a gaban su .
Dai dai gabansu suka faka , motocinsu , duk da sauke idanunta a kasa tayi , hakanan ta ji bari taga kalan kamanninsa , caraf idanunsa suka tsarke cikin na juna ".
Prince sauke gilashin motar ya yi , cikin zazzare idanu ya furta.
" Mary................
Mu je zuwa
Masu bukatar tallah haja ,kuna iya tuntuba ta .
***
Kyauta daga Allah