ƘADDARA CE... 9
*ƘADDARA CE!*
*©SALMA AHMAD ISAH.*
*CANDY🦋*
_ArewaBooks @SalmaAhmad_
_Wattpad @Salma_Ahmad_Isah_
*09*
MUKTAR POV.
Kamar yanda suka yi alƙawarin komawa bincike layin BB hotel sun koma ɗin. Amma a wanan karon da shirinsu suka tafi, ta yanda ko da za'a kawo musu hari za su iya kare kansu. Amma kuma rasa makama ya sa shi da Ali yin cirko-cirko a cikin layin da Munira ta bi sanda motar nan ta biyota. Saboda tun da suka shigo ba su ga wani me tallah ko me abin siyarwa ba. Hatta da masu wucewa sai dai ka gansu jifa-jifa.
Shi ya sa ya faɗawa kansa cewar dole ne ma a sace mutum a wannan layin, saboda babu zirga-zirga a layin. Sai dai idan har Allah ya hukunta faruwar abu a lokaci, to ba makawa sai ya faru. Dan har sun riga sun cire rai da samun wani abu. Sai Allah ya jefo da dalilin tonuwar asirin da suka daɗe da son ya tonu. Saboda a sanda suke da niyyar juyawa su koma inda suka fito. Muktar ya yi arba da wata mabaraciya ta shigo layin. Hakan ya sa ya yi wa Ali magana kan ya tsaya.
Tsayawar suka yi. Kuma a kan idonsu matar ta tsaya a jikin wata bishiya. Ta shimfiɗa buhu, ta zauna a kai, sana ta aje wani kwano a gabanta ta fara barar da ta saba yi kullum a layin. Muktar bai san sanda murmushi ya suɓuce masa ba.
“Ali mu je”
Yace kawai. Sannan ya nufi wurin matar. Ali ya bi bayansa kamar kullum, zuwa jikin bishiyar da matar ke zaune a ƙarkashinta. Har ƙasa suka durƙusa suka gaisheta. Sannan Muktar ya fara tambayarta.
“Iya. Mu jami'an 'yan sanda ne. Kuma muna bincike a kan ɓatan wata matashiya. A cikin binciken mu mun yi karo da wani bayani da yace an ga sanda ita wadda aka sace ɗin ta shigo layin nan. Dan haka muke so mu tambayeki ko kin ga sanda ta shigo!”
Iya me bara ta jinjina kai. Sannan tace.
“To yaro, faɗa min rana da kuma lokacin da aka ga ta biyo ta nan ɗin. Idan zai iyu ma ku faɗa min har da kalar tufafin jikinta. Saboda idan har nan layin ta iyo to tabbas zan ganta. Dan ni nan da kuka ganni kullum nan nake zama ina bara, sai dai idan da magariba ko da sassafe ta shigo layin. To shi ne dai ba zan sani ba!”
“To Iya. Yanzu za'a iya kaiwa kimanin wata ɗaya da kwanaki da faruwar abin. Kuma ranar asabat ne da yamma. Sannan tana sanye da jallabiya kalar ruwan goro. Haka fara ce, me ɗan siririn jiki!”
Muktar na kaiwa aya Iya me Bara na buɗe bakinta.
“Ƙwarai kuwa yara. Na ga sanda ta wuce ta nan. Kuma ka ga can...”
Ta ɗan yi fasali tana nuna musu ƙofar wani gida, Muktar da Ali suka juya suka kalli gidan, sannan suka sake kallonta a tare, sanda ta ci gaba da faɗin.
“... A ƙofar gidan can wata baƙar mota ta tsaya. Wasu mutum biyu mace da na miji da baƙaƙen kaya suka fito daga ciki, sannan suka ɗauketa suka jefa cikin motar!... Ni kuma ganin hakan ya sa na tsorata, shi ya sa na yi gum da bakina ban taɓa faɗawa kowa ba”
“To iya shin kin iya ganin fuskokin waɗan da suka ɗauketa?”
Muktar ya tambaya da sauri. Iya me bara ta girgiza kanta.
“A'a. Ban gani ba. Amma ranar da aka saceta akwai wani matashi ɗan can gidan da shi ma ya ga sanda suka saceta, kuma har hoto me motsi ya ɗauke su a wayarsa. Da yace zai faɗawa 'yan sanda, amma sai mahaifinsa ya hana shi!”
Muktar da Ali suka dubi juna. Sannan suka jinjina kai a tare.
“Iya me nene sunan matashin?”
“Audil”
Iya ta amsa. Yanda ta kira sunan Audil ɗin instead of Abdul ya sa su yin dariya. Kafin Muktar ya ɗebo kuɗi ya bata. Har suka bar wurin tana saka musu albarka. A ƙofar gidan da ta nuna musu suka tsaya. Ali ya yi sallama. Sannan suka tsaya jiran fitowar masu gidan.
Da farko mahaifin Abdul ɗin ne ya fito. Sai da suka masa bayanin abin da ke tafe da su, sannan ya kira Abdul ɗin. Ya saka su a gaba yana son ganin abin da zai faru. Dan ko sama da ƙasa za su haɗe ba zai bari su tafi da ɗansa headquarter ba. Idan videon suke son kallo shi bai hana ya nuna musu ba. Za ma su iya turawa a nasu wayoyin, amma su tafi da ɗansa shi ne abin da ba zai lamunta ba.
“Abdul. Idan har ka san kana da videon nan a wayarka. Ka daure ka nuna mana. Saboda idan har ba ka nuna mana ba rayuwar sauran al'ummar gari tana cikin haɗari!”
Abdul da ya sunkuyar da kansa ya ɗago ya kali babansa. Wanda ya harɗe hannaye a ƙirji yana kallon kowa cikinsu. Sannan ya kalle su.
“Idan da akwai a wayarka ka nuna musu. Ni ban hana ba, amma fa daga nan babu inda za ka ƙara ɗaga ƙafarka. Ba zan bari ka tafi ko ina ba Wallahi!”
Faɗin baban Abdul. Kuma kalamansa suka sa Abdul ya sa hannu a aljihun wandon jikinsa. Ya ɗauko wayarsa ya cire password. Sannan ya nemo videon a inda ya ɓoye. Ya kunna, ya miƙawa Muktar.
Muktar ya karɓi wayar da dukkan zumuɗin duniya. A zatonsa zai ga abin da zai kawo ƙarshen matsalar ne. Bai sani ba cewa yanzu ne ma matsalar za ta soma. Saboda tonuwar asirin makashin ba ya nufin zuwan ƙarshen matsalar. Sai dai ma ya zama wani sabon mafarin tarin matsaloli.
Da farko da ya ga videon da fuskar macen dake cikinsu bai yarda ba. Sai da ya dawo da shi baya ya sake kalla, ya sake sakewa, wai dan ya tabbatar da abin da yake gani ko gaskiya ne. Duk da sau ɗaya ya taɓa ganin matar Faruk ya ganeta. Saboda kwanaki da yake ta neman layin Faruk ɗin ba ya samu ya sa ya tafi gidansa. Kuma a nan ya fara ganinta. Duk da ba wai ya tsaya ya ƙare mata kallo ba ne a wancan lokacin ya ganeta a nan.
Kuma idan zai iya tunawa, Faruk ya sanar da shi cewar Mariya matarsa ƙanwar Mu'azzam Gimba ce. Kuma ya san waye Alhaji Jibrin Gimba Gashuwa GG. Mutumin arziƙi me halin ƙwarai. Me dattaku da halin girmamawa ga naƙasansa ba ma ga wanda ke samansa ba. Lalle akwai magana!.
Yanzu me zai sa matar soja. Ƙanwar soja, 'yar babban mutum kamar GG ta aikata garkuwa da ɗan adam, da kuma kisan kai?. Gaba ɗaya ya kasa ganewa. Idonsa ya ɗaga ya kalli Abdul dake faɗin.
“Lokacin da suka tsayar da motarsu a ƙofar gidan nan na fito. Ganin suna shirin saceta ya sa na yi saurin komawa gida, na ɓuya a bayan ƙofa na naɗi wannan videon...”
Idonsa ya sake ɗaukewa daga kan Abdul ɗin. Sannan ya mayar da shi kan wayar ya na kallon bidiyon a karo na barkatai. Kansa ya jinjina yana miƙawa Ali wayar. Wai ko shi ma zai kalli videon dan ya tabbatar da fuskar wa cece a videon.
MARIYA POV.
Kamar yanda ta saba damawa Hilal custard haka yau ma shi ta dama masa. Sannan ta haɗa shi da shi. Wai ko ya yi shiru kunnuwanta su huta da kukan da yake mata tun safe. Tana saka masa baby bottle ɗin a baki ya yi sarin saka hannunsa ya dafe ya fara sha.
Ta juya idonta cike da gajiyawa da halin yaron. Ita ba dan tana so ta sadaukar da shi ga shaiɗan ba ma da ta kasheshi rana ɗaya kowa ma ya huta. Ba jimawa da fara shan custard ɗin nasa tafara jin ɗoyi. Hakan ke nuna mata cewar kashi ya yi.
Cike da jin haushi ta sa ɗan yatsanta ta dungure masa kai tana hararsa kamar ta samu abokin faɗanta. Ai ko ka zauna da shi daga nan har zuwa sanda ub*nka zai dawo ya wanke maka. Dan ni bani da wannan lokacin.
Ta faɗi a zuciyarta tana tashi daga kan kujerar da take zaune. Ta haye sama ta barshi zaune a falo yana shan custard ɗin. Juyawa ta yi ta saka sakata a ƙofar ɗakinta bayan ta shiga ciki. Ta juyo tana baza idonta a cikin ɗakin. Saboda jikinta ya bata cewar Lawan abokinta na ƙungiyar bayin shaiɗan na cikin ɗakin. Kuma shi ne dalilin da ya sa ta kulle ƙofar ɗakin.
“Gani a nan”
Ta juyo muryarsa a bayanta. Hakan ya sa ta juya. Tsaye ta ganshi a jikin ƙofar yana kallonta, fuskarsa ɗauke da murmushi. Ita ma murmushin ta yi tana nufarsa.
“Saƙo ne daga fadar shugaban bayin shaiɗan!”
Jin hakan ya sa fara'ar dake fuskarta ta ɗauke. Ta maida hankalinta duka kansa, domin jin saƙon da ya sa Wahash ya aiko shi gareta.
“A jiya Shugaban bayin Shaiɗan ya sa ɗaya daga cikin bayin shaiɗan ya je ya kashe wannan ɗan sandan. Amma kuma sai aka yi rashin sa'a ya sha. Kuma a yanzu haka yana da hujjar da take nuna cewa ke ce kika sace Munira, sanin cewa ke ce kika sace Munira na nufin ke ce wadda kika kasheta...”
Cike da razani Mariya ta zaro idonta. Ganin Lawan na murmushi ya sa tace.
“Amma Lawan me ya sa za ka na murmushi a cikin irin wannan yanayin?”
“Haba rezor. Ai abin bai kai mu tada hankalinmu ba. Kada ki manta da cewar shaiɗan na tare da mu. Da ƙarfin tsafin da ya bamu ni da ke za mu iya kawowa ƙarshen ɗan sandan nan”
Idonta ta juya tana jin kwanciyar hankali ta fara nufo inda take.
“Yaushe za mu je gare shi ke nan?”
“Da zafi-zafi a kan daki ƙarfe. Dan haka a daren yau zai baƙunci barzahu. Gobe da safe sai dai a samu labarin jana'izarsa!”
Mariya ta yi murmushi.
“Sai na jika zuwa an jima”
Lawan ya yi murmushi. Kuma ba tare da ya sake cewa komai ba ya ɓace daga ɗakin. Mariya ta zauna a bakin gadonta. Abin da ya shiga tsakaninta da Munira a wacan ranar na yawo a cikin tunaninta.
*Wata ɗaya da ya wuce...*
*BB Paradise Hotel, Abuja.*
A gaggauce Munira ta fito daga cikin motarta, wadda ta faka a parking lot, bayan da ta shigo harabar hotel ɗin. Kuma ba komai ya sa take saurin ba face saƙon gaggawa da tasamu daga wurin saurayinta Mubarak.
Da yake ya faɗa mata lambar ɗakin da yake ciki sai bata sha wahalar neman lambar ɗakin ba. Kai tsaye ta wuce zuwa ɗakin. A bakin ƙofar ɗakin da ya bata lambarsa ta tsaya. Sannan ta yi knocking. Ta ja baya tana jiran ya zo ya buɗe. Jim kaɗan aka buɗe ƙofar daga ciki, idonta ya sauƙa a kan Mubarak ɗin da ya buɗe ƙofar. Murmushi ya mata, sannan ya buɗe ƙofar gaba ɗaya tare da faɗin.
“Shigo mana My love”
Fuska ta ɗaure. Dan da ma sun samu matsala kwanan baya, yanzu kuka da ya kirata yace yana son ganinta sai ta yi zaton yana cikin wani hali ne.
“Me ya sa zan shigo ciki?”
“Ke dai ki shigo. Magana nake so mu yi”
Kamar ba za ta amince ba. Can kuma sai ta gyaɗa kanta. Sannan ta raɓa shi ta wuce. Mubarak ya kulle ƙofar ɗakin ya biyo bayanta. A tsakiyar ɗakin ta tsaya ta fuskance shi.
“Wace magana za mu yi?”
Ta tambaya fuskar nan a haɗe. Duk da dama can haka yanayin fuskarta yake, kasancewarta soja. Mubarak ya yi murmushi.
“Sai kace ina korarki? Ko ba komai ai kya zauna mu tattauna ko?”
Ta sake ɓata rai.
“Mubarak! Ba na son wasa da hankali. Kawai ka faɗi abin da yake bakinka... Ina da abin yi a barrack!”
Mubakar ya sunkuyar da kansa.
“Shike nan tun da kin dage My love. Da ma, ina so in baki haƙuri ne, na gane cewa ni ne me laifi, da fatan za ki yafe min!”
Ta kalle shi na sakkani. Kafin ta ɗauke kai tana harɗe hannayenta a ƙirji.
“Da ma ni ban ƙullaceka ba ai. Kawai dai na ji haushin abin da ka min ne!”
Mubarak ya yi murmushi ya na kamo hannayenta.
“To ki yi haƙuri. Ba zan sake ba”
Munira ta yi saurin janye hannunta da ya riƙe.
“Mubarak wai sau nawa zan ce maka ba na so ka na riƙe hannuna?. Ba na so ka na taɓani irin haka, duk wanna abin kamata ya yi mu bari sai bayan aure.”
Mubarak ya sake kamo hannunta.
“My love ya kamata ki fahimceni. Wai kwana nawa ya rage auren nan namu ne? Ki sani fa cewa baki da miji bayan ni.”
Ta sake janye hannunta.
“Mubarak kar ka sake taɓani. Ba na so”
Ta faɗa tana ja da baya. Ya nufota yana shirin rungumeta ta kauce. Sannan ta hankaɗa shi baya ta fice daga ɗakin da gudu. Kuma a sanda ta fita daga ɗakin, ƙaddarar da za ta kawo ƙarshen rayuwarta ta wanzu.
MARIYA POV.
Zaune suke a cikin motarsu da suka faka a harabar BB hotel ita da Lawan. Lawan ne zaune a driver seat. Yayin da ita kuma take zaune a ɗayar kujerar. Dukansu sanye da baƙaƙen kaya. Baƙar hand glove ta ɗauka ta saka a hannunta. Sannan ta ɗauki baƙar p-cap ta saka a kanta. Ta ɗora hular hoodie ɗin dake jikinta. Ta juyo ta kalli Lawan da yake rufe fuskarsa da glasses.
“Mu je Rezor”
Lawan ya faɗa yana buɗe ƙofar motar. A tare suka fita daga cikin motar. Suka nufi ƙofar shiga hotel ɗin ta ƙofar baya. Kai tsaye ɗakin da Vishal Kumar ya kama suka nufa. Saboda da ma shi ne target ɗinsu. Kuma Wahash ne ya aikosu domin su zo su kashe shi. Saboda ya saɓa dokar ƙungiyarsu. A dai-dai ƙofar ɗaki me lamba 24 suka tsaya. Mariya ce a kan gaba, Lawan kuma na tsaye a bayanta.
Ita ta ɗaga hannunta ta ƙwanƙwasa ƙofar. Suka tsaya suna jiran a buɗe. Suna jin alamun za'a buɗe ƙofar suka gyara takunsu. Vishal na buɗe ƙofar Mariya ta kai masa wani naushi a hanci. Hakan ya sa ya yi baya yana dafe hancinsa da ya fara zubar da jini.
Yayin da Mariya da Lawan suka shiga cikin ɗakin ba tare da sun rufe ƙofar ba, dan sun san cewa ba jimawa za su yi ba. Vishal na ganin fuskokinsu ya zaro ido. Sannan ya sauƙe hannunsa daga kan hancinsa. Ya yi kan Mariya zai daketa.
Amma yana zuwa daf da ita ta kama hannunsa da ya ɗaga zai dake ta shi, ta murɗe hannun har sai da Vishal ya yi ƙara. Sannan ta sa ƙafarta ta daki ƙafarsa. Kafin ta sa hannunta ta riƙo gashin ƙeyarsa, ta ɗaga ɗaga kansa sama yana kallonta.
A hankali ta kai hannunta da bata riƙe gashin kansa da shi ba, ta ɗaga harshenta kaɗan, ta ɗauko wata sabuwar reza da har ɗaukan ido take a cikin hasken ɗakin. Ta ɗaga sama, sannan ta yanka wuyan Vishal da ita.
A dai-dai lokacin Munira da ta fito daga ɗakin Mubarak da gudu ta dakata a ƙofar ɗakin. Ganin an yi kisan kai ya sa ta ƙwaka ihu. Ihun da ta ƙwala ya sa Mariya da Lawan juyowa suka kalli bakin ƙofar. Ganin fuskar Mariya ya sa tsoro da tashin hankalin Munira ninkuwa.
Hannunta na rawa ta nuna Mariya da shi. Sannan ta kalli gawar Vishal dake ƙasa. Ita ma Mariyan ta ganeta. Kuma ganetan da ta yi ya sa ta nufo bakin ƙofar ɗakin da gudu. Ita ma Munira sai ta ranta a na kare.
Ta fita daga hotel ɗin a kiɗime, ko motarta da ta zo da ita bata ɗauka ba. Ganin ta fita ya sa Lawan da Mariya bin bayanta a mota. Amma saboda ta iya gudu sosai ya sa ta musu nisa. Dan har wayarta ta ɗaga ta kira Faruk da ita. Sai dai kafin ta kai ga faɗa masa abin da ke bakinta tunaninta da komai nata ya tsaya cak. Har Mariya da Lawal suka ɗauketa bata cikin hayyacinta...
~~~
Munira ce yashe a tsakiyar wani ɗaki. Hannunta da ƙafarta duka a ɗaure. Sannan idonta a rufe. Idan ka kalleta ba ka ce tana numfashi ba...
Daga wajen ɗakin aka turo ƙofar ɗakin ciki, ƙaran buɗewar ƙofar ya sa ta motsa. A hankali kuma sai ta shiga buɗe idonta. Tun tana gani dishi-dishi har ganinta ya dawo dai-dai. Shiru ta yi tana kallon Mariya da ta shigo ɗakin.
Da ƙyar ta iya yinƙurawa ta miƙe zaune, duk da ƙafafuwanta da hannayenta a ɗaure suke. A dai-dai lokacin kuma Mariya ta durƙusa a gabanta tana murmushi. Yayin da ita kuma Munira take zubar da hawayen tausayin abokanta. Saboda ita bata ta kanta. Dan ta san ba lalle ta tsira a hannunsu ba.
“Mariya me ya sa?. Me ya sa kike cutar da Faruk da kuma MJ? Me ya sa?”
Ta tambaya hawaye na ƙara zubo mata. Amma ita Mariyan ba ta yi magana ba. Sai murmushi da take. Duk da haka Munira ba ta haƙura ba ta sake faɗin.
“Me zai sa ki kashe rai Mariya?. Mariya me zai sa ki zaɓi rayuwar da ba taki ba?...”
“Wa ye yace miki wannan rayuwar ba tawa ba ce?. Wannan rayuwata ce, rayuwa me daɗi a ƙarƙashin gata da tallafin shaiɗan!”
Mariya ta katseta tana faɗaɗa murmushinta. Munira ta yi shiru tana son gano inda zancen nata ya dosa.
“Mariya ke 'yar cult ce?”
Mariya ta lumshe idonta ta buɗe tana gyaɗa kai, hankalinta kwance.
“Ƙwarai kuwa Captain Munira Musa. Na bayar da ruhina ga shugaban mu shaiɗan. A yanzu ba ni da abin bauta sama da shaiɗan!...”
“Subhannallah! Subhannallah!. A'uzubillah! A'uzubillahi mina shaiɗanir-rajim!”
Wani duka da Mariya ta kaiwa bakinta ya sa ta faɗi gefe guda. Bakinta na zubar da jini. Mariya da fuskarta ta rikiɗa zuwa fushi ta sa hannu ta ta riƙo gaban rigar dake jikinta. Sannan ta janyota tana zare idonta a kanta.
“Idan kika kuskura kika sake buɗe bakinki kika faɗi wata ƙazamar kalma ɗaya a kan abin bautata shaiɗan sai na cinye namanki ɗanye!”
Bakin Munira na fitar da jini, idonta na zubar da ƙwalla ta girgiza kai.
“Ba ke ba ce Mariya!. Wallahi ba ke ba ce. Kowa ya na yabon kyan hali irin naki, kina da nutsuwa da kamala. Kina da sanin ya kamata da haƙuri, me ya sa yanzu kika sauya? Me ya sa? Innalillahi wa inna ialaihi raji'un!...”
Mariya ta saki gaban rigar tata. Sannan ta miƙe ta fice daga ɗakin a fusace. A wani ɗaki ta je ta samu Wahash.
“Shugaba! Wani kalar hukunci ya kamata mu mata?”
Mariya ta tambaya tana huci. Saboda an taɓa abin bautarta. Wahash ya dubeta.
(Wahalallu😒)
“Yanzu kun kashe Kunda (Vishal). Kuma za'a yi bincike a kai. Idan har aka kasheta ita ma zargi ne zai ƙara yawa. Dan haka dole mu jinkirta wurin kasheta!”
Mariya ta jinjina kai.
“Dole mutuwarta ta zama me tada hankali. Saboda ta taɓa abin bautarmu Wahash”
Wahash ya yi murmushi.
“Zamu ba ta irin mutuwar da hatta ahalinta ba lalle su ganeta ba”
Mariya ta jinjina kai. Kamar yanda suka tsara ba su kasheta a lokacin ba. Sun ajeta a masarautar shaiɗan na wasu satuka. Kuma a duk kwanan duniya da kalar azabar da ake ganawa Munira. Da haka har lokacin da za su sadaukar da jininta ga shiaɗan ya zo.
Sai da suka mata kisa irin na wulaƙanci. Kisan da duk wani me imani idan ya gani sai ya zubar da hawaye. Sun bata mutuwa irin wanda ko da fasiƙin mutum ne ba'a so ya yi. Haka suka cillar da abin da ya yi saura na gawarta a wata unguwa. Hankalinsu kwance...
*Present Day...*
MUKTAR POV.
Kamar kullum. Yau ma haka Ali ya sauƙe shi a unguwarsu. Sannan ya juya ya tafi da motar tasa. Saboda shi sam ba ya zama da motar a wurinsa. A ko da yaushe tana wurin Ali. Sai idan yana buƙatar zuwa wani wurin shi kaɗai zai sa Alin ya kawo masa ita.
Kamar jiya. Haka yau ma aka dalle shi da hasken fitilar mota, saɓanin jiya da ya kasance mashin. Cak ya tsaya da tafiyar da yake. Sannan a hankali ya juya bayansa ya kalli motar dake bayansa.
Duk da yanda aka haske shi da fitilar motar ya iya gane motar, har ma da mutum biyun dake cikin motar. Wannan motar ce da aka sace Munira a cikinta, sannan Mariya da crime partner ɗinta da ba su san sunansa ba ne zaune a ciki.
Kamar yanda yake tsaye haka ma motar tasu take tsaye a wuri ɗaya, duk da a kunne take. A hankali ya ja ƙafarsa ɗaya baya. Hakan ya bawa Lawan damar jan motar ma zuwa gaba kaɗan. Ganin haka ya sa Muktar ya sake jan ƙafarsa baya, Lawal ma ya ƙara jan motar gaba.
Muktar ya juya bayansa. Sannan ya ci gaba da tafiya a nutse, saboda ya ga abubuwan da suka ɗara wannan tayar da hankali. Ƙarewa har kan gadon baccinsa an zo an saka masa wuƙa a wuya an yi barazanar kasheshi. To ai su su Mariya ƙananun 'yan iska ne.
Kamar yadda yake tafiya a hankali, haka ma motar ta ci gaba da binsa a hankali. Can kuma sai ya fara tafiya da sauri, hakan ya sa Lawan ma ƙara gudun motar. Ganin haka ya sa Muktar ya fara gudu. Lawan ma ya taka motar da gudun bala'i.
Kuma ba'a je ko ina ba ya buge Muktar da motar. Ya faɗi ƙasa, hatta daƙaran da ya yi sun ji shi da Mariya. Kuma ya na buge shi sai ya tsayar da motar. Mariya ta dube shi.
“Ka taka shi ka bi ta kansa mana”
Ya kuwa taka motar, har sai da suka ji motar ta taka shi. Sannan suka ja motar da gudu suka bar unguwar, sun ɗauka cewa shikenan kuma, matsala ta mutu tare da mutuwar Muktar.
Sai da motasu ta bar unguwar, Sannan Muktar da ya kaucewa motar tasu ya tashi zaune da ƙyar. Dan a sanda suka bige shi bai kwanta a wurin ba. Ƙarfin hali ya yi ya murgina gefe. Su kuma suka taka dutse, har suna tunanin cewa shi suka taka.
Hannunsa da yake da tabbacin ya karye ya riƙe yana jin raɗaɗin azaba. Sannan ya yi ƙarfin halin ɗaukar wayarsa, ya kira Ali ya sanar masa da halin da yake ciki, sannan ya kira ƙaninsa Walid.
“Walid kana gida?”
Ya faɗi da ƙyar yana rsinte idonsa. Saboda yanda yake jin ko ina na jikinsa na ciwo, gaba ɗaya ma ya rasa takamemen ina ne yake masa ciwo. Daga ɗayan ɓangaren Walid yace.
“Eh Ya Mukhy. Ina nan, lafiya?”
“Ka fito ka zo kwanar gidan Alhaji Sadam. Ina wurin, na ɗan samu wani haɗari ne?”
Walid dake zaune a falo ya miƙe zumbur yana tambayarsa.
“Haɗari? Yaushe? A ina?”
“Stop asking just come and help me!”
“Okay”
Ya kashe wayar, sannan ya nufi ƙofar falo da gudu.
“Kai Walid! Ina za ka je?”
Mamansu da ta fito daga kitchen ta tambaya. Sai ya dakata, sannan ya juyo.
“Ya Mukhy ne ya kirani yace ya samu haɗari a kan kwanar gidan Alhaji Sadam. Shi ne zan je na duba”
“Haɗari?”
Mama ta tambaya a hargitse.
“Eh Mama. Bari in je na duba shi”
“To ka kula. Allah ya sa ba wani mummunan abin ne ya same shi ba.”
“Amin”
Ya amsa yana fita daga falon. Da yake shi ya fi kusa da Muktar ɗin sai ya riga Ali isa. Dan gidan Alhaji Sadam ɗin ɗan gaba kaɗan ne da nasu. Sai da Ali ya zo, tukkuna suka ɗauke shi zuwa asibiti.
-------------------
_Na lura da bana letter (M) ce ke zamani_
_Rabin 'yan wasanmu duka sunansu da ‘M’ ya fara_
_To gaba ɗaya babin yau ma a kan M ɗin ya ƙare. Ga Mariya fa Muktar._
_Sannan kun ji abin da ya faru tsakanin Munira da Mubarak_
_Kun kuma ji yanda aka yi Munira ta mutu_
_Mu je zuwa. Saboda yanzu muka fara sharar hanya😉_
_Share fi sabillilah❤️_
*Daga alƙalamin Salma Ahmad Isah✍️.*
*CANDY CE🦋.*
--------------------
_Kada a manta da biyan kuɗin littafi. Dan free page zai ƙare daga gobe in Allah ya kaimu. To subscribe pay ₦300 to._
5487270431
Salma Isah
Monie point.
And send the evidence of payment via.
***
#Candy
#SalmaAhmadIsah