Page 13
by @oumamani
ALƘALAMIN SO
DIJAHAM(OUM AMANI)
Page 13
Saura 2 pages In sha Allah free pages su kare😩 ku yi maza kuyi payment kar ayi tafiyar nan babu ku🤾♀️🤾♀️
In zaku yi payment zaku tura 500 ta wannan account din ***
Khadija Danasabe Adamu
OPay
Sai ku tura shaidar biya ta wannan numbern
***
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Kai na ne yake juya min a hankali a hankali ga yadda gaba na yake wani irin faduwa, lokaci daya kasala ta kama ni da wani mugun bacci da nake ji.
Bude ido na nayi don an kusa sallar magriba bana so na kwanta sai nayi sallah amma tuni bacci ya ci karfin ido na, dole ba yadda na iya haka na zame na kwanta ina ce wa Maryama ta taimaka ta gama mun list din da ban karasa ba.
MARYAM
Tun da taga Aisha ta shanye zobon da Mummy ta bata take ji kamar ta zuba ruwa a kasa ta sha sbd murna da farin ciki, amma haka ya shiga danne wa don kar Aishan ta zargi wani abu, sai da taga tayi nisa a baccin sannan ta dauki bottle din da Aishan ta yar ta fita da sauri zuwa part din su.
Bata tsaya ko ina ba sai a dakin Mummyn ta, tana shiga ta fasa Ihun da take rike wa ta nufi Mummyn a guje ta rungume ta.
Murmushi kawai Mummy tayi ta ce “to ya da alama komai ya tafi yadda ya kama ta Kenan koh?”
Dagowa tayi daga cikin Mummy ta ce “ban taho ba sai da ta fara bacci, ai tun da kika ce tana shan zobon za’a samu kan ta na dage sai da naga ya shanye sa tas”
Murmushi Mummy tayi ta ce “da kyau shiyasa nake kaunar ki ko a cikin yarana sbd ke din ba dai bin umarni na ba, ynxu ki je ki dauko kayan gyaran jikin nan dana hada ki dawo na fara miki, ai baza a bar amarya haka jiki ba gyara ba”
Ihun murna Maryam ta sake yi sannan ta saki Mummy din da sauri ta fita tana wata rawa, ita fa ji ta gama zama ma matar Ya Aliyu gaba daya.
Bayan fitar Maryam, waya Mummy ta fito da ita ta shiga kiran wata number.
Sai da ta katse sannan aka kira, cikin kashe murya tana juya ido ta ce “Hajjaju komai ya tafi yadda muka tsara..”
Shiru tayi alamar ana magana daga can bangaren kafin tayi dariya tana juya ido cike da bariki ta ce “nima dai nayi kewar taki ya kama ta mu hadi school mother, zan wa Daddyn magana cewa zani duba matar yaya(yayan ta) sai mu a hadu a inda muka saba hadu wa”
Shiru ta sake yi kafin ta mike tana cewa “bari ma kiga na tashi ynxu na fara shirya wa, ki kula min da kan ki sosai sai mun hadu”
Daga haka ta kashe wayar tana mai nufa toilet don yin wanka…..
AISHA
Ni dai zuwa ynxu na kasa gane kai na, wata iriyar kasala nake ji wacce da kyar take bari na nake yin sallah ma addu’a kuwa ynxu sati daya Kenan bana yi.
Gashi dai ina so nayi amma dana bude baki na sai naji yayi min nauyi dole nayi shiru kuma na kasa gaya wa kowa sai rame wa nake yi.
Kwance nake a dakin Hajja ina duba waya ta, so nake na kira Uncle amma na kasa sbd yadda gaba na yake ta faduwa, rintse ido na nayi wasu hawaye masu zafi suna zubo min, ban san me yake damu na ba kwata kwata duk lokacin da nayi tunanin kiran Uncle ko kuma shi ya kira ni sai na kasa dauka gaba na yayi ta faduwa haka kurin zan dinga Jin wani irin tsoro yana kama ni.
Hajja da ta dade a tsaye tana kallon ta, ta ce “ke kuwa takwara(ita ma sunan ta A’isha) me yake damun ki ne, tun da kika zo na fahimci cewa baki cikin nutsuwar ki ko auren ne bakya so, kar ki ji komai in har auren ne bai miki ba ki fada min zan shiga na fita naga an fasa”.
Goge hawaye na nayi ina turo baki na ce “ni wai Hajja nace miki bana son auren ne?”
Tsaki Hajja tayi tana neman waje ta zauna ta ce “kin ga takwara muyi magana ta fahimtar juna, Ali din bai miki bane ko? In ma tsoro kike ji kar ki ce bai miki ba suga kamar kin musu butulci tunda a gidan suka rike ki tsawon shekarun nan to kar ki damu, zan siyar da akuyoyina guda uku dake kauye a hada kudin a bawa shi Salisun duk meye a ciki, kudin akuya uku dai ai abin da yawa”
Zumburo baki gaba nayi na ce “ni ina son Uncle dina haka kurin sai ki dinga min fatan a fasa aure na kin San tsawon shekaru nawa Uncle ya dauka yana jiran zuwan ranar auren mu kuwa?”
Tsaki Hajja ta kuma ja da karfi ta ce “amma dai anyi asara yncu ni kike fada wa kina son shi Ali din, to sai me don kina son sa tun da kika zo na lura da ke kamar kina cikin damuwa baki da aiki sai zama a daki kiyi ta tunani, ko shi Ali din in ya kira ai ba dauka kike ba”
Hawaye naji suna neman zubo min amma sai na daure nayi murmushi mai Kama da yake na ce “ai sbd kin wajen shiyasa bana dauka amma in na shiga daki shi nake kira musha soyayyar mu”
Tabe baki Hajja tayi ta fita daga dakin tana mita.
Kuyi manage da wannan please rasuwa aka mana shiysa
DijahAM
***