MUMMUNAR DABI'A

Chapter 2 Book1

by @asmabaffa1

https://www.arewabooks.com/chapter?id=6683ec1256566fe605af16a3


🪸MUMMUNAR DABI'A🪸


         6-10


Official


By

AsmaBaffa



Sadaukarwa ne ga 'Yata Tasnim



Pagae naki ne

Ummu Khinal



GARGADI GA MASU AUDIO BAN YARDA A SACI LITTAFINA A JUYA ZUWA AUDIO BA.



*ZINARIYAR MACE⚡*

*Wai shin 'yar'uwa menene matsalarki? zubewar nono, ko kuma rashin kwankwason juyawa a falo maigida ya shiririce ya manta da tibi da matan tictok, menene matsalarki ne? rashin ni'ima ko kuma mugun sanyin da ya yi miki katutu, shin rashin taushin fata ne ko kuma kuraje da tabbani, ko bala'in ramar da ta addabeki kuma babu rashin ci ba rashin sha a gidan auranki, gwaigwayewar gashi ce matsalarki ko kuma kaushi da faso na tafin kafa da bushewar fata, kina bukatar fatarki ta yi glowing kalarki ta fita kuraje su mutu, ko kuma kina bukatar azababbun turaruka da humra tare da turarukan wuta. Na san dai kuna da yawa matan da tumbi ya yi musu karan tsaye ina nufin ya katse muku hanzarin yi wa maigida gwalli da muskuce-muskuce a falo😃 Nesa fa ta zo kusa AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE sun tanadar muku da nau'in magungunan da suke magance kowace irin matsala da izinin Allah. Babban burinmu shine sha'ani na aure ya inganta a samu daidaito. Muna da.*

Na gyaran nono.

Na sanyi.

Dilka tare da hadin sabulu.

Duk Wani nau'in maganin mata.

Humra turarukan wuta perfumes, original miski tahra  3in1, ciccibi budurwar kaza. Had'addun supplement irin wad'anda ba su da matsala. Maganin Sliming wato narka tumbi. Abubuwan da muke sayarwa suna da yawa, kuma babu asarar dukiya. Muna garin kano kuma muna tura kayanmu kowane gari fad'in Najeria da Nijar har ma da kasashemn ketare. Kai tsaye a tuntu'bemu ta lambobin wayarmu domin karin bayani.

*****

*****





     Su Sohail suna karasawa har asokoro wani mahaukacin gidane na alfarma gida ne na musamman wanda komai nasa ba karamin dukiya aka narkar ba wajen gina gidan ba,komai akwai na more rayuwa,Adnan suka gani yana hutawa zaune a wasu kujeru na hutawa masu kyau ya dora kafa daya kan daya yana latsa waya sannan yana kora ruwan lemo me inganci da kara lafiya a jikin dan Adam, kallon su yayi wani haushi ya kama Adnan sun fisu kyau da cikar zati da komai ma,baki ya tabe tare da mikewa,akwatunan su suka dakko tare da kallonsa "how far bro" suka furta.


  A hasale yace kunga respect your self ni ba sa'anku bane kar ku sake kirana da wani bro,who is your brother? Dalla ku wuce muje ya ja wani tsaki tare da wucewa ciki suka bi bayansa suna murmushi ko a jikinsu,hirarsu ma suka fara yi,a fusace ya sake juyowa yace kai kun cika min kunne,shuru suka yi kawai suka haura sama ya nuna musu dakinsu hadadden gaske me dauke da makeken bed da toilet komai a kwai ciki,suna ajiye Jakar su bai bari sun huta ba yace ku fito na nuna muku gidan sannan na zana muku aikin ku,suka biyo shi kamar 'yan aiki.


   Sai da ya nuna musu ko ina na gidan sannan suka koma palo,Sohail yace wash na gaji,Ibrahim ne ya shigo yana magana yace ai ba hutu ne ya kawo ku ba,kai bari kuji aikinku a gidan nan 

 Gyara gidan nan ku share ko ina ku goge,sannan kuyi mana wanki da guga, kuyi girki,ku wanke mana motoci kullum,bude gate da kullewa,komai da kuka sani na gyara gida da kula da shi kune zaku yi shi kunji,su Sahil suka ce sun ji,su kansu ganin basu san komai ba sun hakura da rayuwar, tunda ana kiransu da mahaukata gani suke basu da amfani a duniya,gani suke ba abinda zasu iya tabukawa a duniya,shi yasa suka hakura kawai tunda sunga kowa baya daukan su a mutane,kuma suma abinda suke yi da abinda suke ganin suna yi sai yasa suke ganin lallai ba daidai suke da kowa ba,suka riki aikinsu hannu bibiyu,sun zama 'yan aiki ta karfi, sun fara musu bauta ba ji ba gani har sun kai matakin samari na gaske ya isa ace sun kammala degree din su amma sun kare a bautar yan uwan su, sun kwashe shekaru biyu suna bauta musu.


  Su Sohail sun girma sosai dan sunfi ma su adnan girman jiki da tsayi,kai in ba fada maka aka yi ba baka isa ka gane wane Sahil wane Sohail ba sai wanda ya mugun saninsu zai iya tantancewa shima ba ko yaushe ba,kansu daya,tsayinsu daya cif,kibarsu da jikinsu komai irinsu daya kai daya babu banbanci,sun ajiye saje da gemu madaidaici,gasu jajir da su,ga tsayi gasu su ba ramammu ba sannan baza ace suna da kiba ba,idanuwansu masu kyau farare tas,gasu da yalwar gashin gira da sumar kansu me kyau da baki sai sheki suke yi kawai,kana ganinsu kasan ba wahala a tare da su,sai dai suna bautuwa sosai, ko waye ya kalle su bazai so ya dauke idonsa a kansu ba,gasu da kwarjini da cikar zati,gasu da tsafta ta gaske ga daukan wanka tunda ana basu sutura da cima me kyau,komai iri daya suke yinsa,kawai banbancinsu Sahil yana da wushirya yar kadan shi kuwa Sohail baida ita banda wannan basu da banbancin da za a gane waye Sahil waye Sohail,halayyar su ma tazo kusan daya,Sohail yafi fara'a,Sahil baida wata fara'a sai dai in suna tare da Sohail kawai zaka ga yana dariya, 'yan mata kuwa basa tunanin ma sun kai mutanen da har zasu iya son mace bare su aure ta wannan yasa ma su ba ruwansu da mata basa harkar su.


  Ci gaban labari


  Ibrahim ne ya shiga kwalawa Sahil kira "Sahil" "Sahil" kamar zai fasa gidan,Sahil ya fito da gudu a gigice,dake su ba wahala sun gigice sun rude,sanye yake cikin gajeren wando da riga armless maroon,Ibrahim yana wani gadara ya sha wata azababbiyar shadda fara yana shining yace baka da hankali,jakin ina ne kai kalli takalmin da koge min,brown nace ka goge? Na fada maka meeting zanje black nace ka goge min amma ka goge min brown useless,karbi ka goge wannan,kuma idan 15mnt tayi baka goge ba wlh sai ka gane kurenka stupid,Jikin Sahil yana rawa ya karba yace kana nufin a goge wannan? a'a goshin uwarka zaka goge min,Sahil yace uwata ai bata nan ina zan ganta na goge maka goshinta? Dan Allah ka taimake ni ina zanga Mummy na goge maka goshinta? Kuma kasan Mama ta rasu,dama Mama tana raye wlh sai naje Kano na goge maka goshin nata,cike da mamaki Ibrahim ya tsaya sololo yana kallon Sahil,yau ya tabbatar Sahil basu da hankali,tsaki yaja yace "Sahil" yace na'am ka goge min takalmi zan fita, a goge dai ko kace? Sahil ya sake tambaya,Ibrahim ya hasala sosai ya sake dakawa Sahil tsawa ya juya ya tafi gogewa.


  Adnan kuwa cikin shirinsa ya fito zai fita ya samu motarsa da yace zai hau da alama ba a wanke ta ba,Sohail ya dinga kwalawa kira,Sohail ya fito, yana zuwa Adnan ya fara bala'i kai dan uwarka wacce motar nace ka wanke? yace bakar na wanke,haka nace? ae cewa kayi na wanke maka fara kawai ni kuma na wanke bakar tafi kyau, Adnan ya zaro ido yace are you mad? Ni in saka abu ka canja min zabi,ba komai ai zaka aikata ai kafi kowa hauka da ciwon aka haife ka dalla bani key ya fisge key dinsa ya wuce ya shiga motarsa ya tafi,Sohail ya juya ya wuce kitchen ya duba ba abubuwa da yawa wanda yana bukata yayi amfani da su wajen girkin da zasu yi, yana shirin fita ya siyo kawai Ibrahim ya dawo ya kulle kitchen din yace tunda baku da hankali sai kunyi kwana bakwai baku ci abinci a gidan nan ba,sai dai ku siya da kudinku useless ya juya ya tafi,Sahil ya kalli Sohail suka yi shuru basu ce kala ba.


  Yau haka suka yini basu ci komai ba a gidan gashi su Ibrahim a waje zasu ci hadadde abinsu,su kuwa basu ma da kudin ko sisi sabo da kawai komai sai dai su gani an siya musu har sutura ba a basu kudin su siya an maida su kamar yara,idan ma sunce a basu kudi baya wuce 1k, Sahil dazu kace zaka je shopping ina kudin? Sohail yace ai kasan kayan abincin dama idan munje su suke transfer da kansu sai dai kawai mu karbo a shagon,Sahil yace na tuna kuma gashi har yamma tayi likis wlh yunwa nake ji, fita zamu yi ko zamu samu wani abu,Sahil yace nifa na gaji da wannan rayuwar bro gidan nan zan bari na gudu kawai,Idan ka tafi ina zaka je? Wa kake da shi? Sohail ya tambaya,Kazo mu gudu kawai,Sohail yace ba inda zanje ni,ina zani bamu da hankali ance waye zai zauna damu a haka,Sahil yace to zan tafi na barka ni domin gwara naje na bautawa wasu wlh,Sohail yace a dawo lafiya ma dinga waya.


  Tafiya suke yi kawai a titi har sai da suka bar layinsu suka bar unguwar ma baki daya,sai da suka shiga wata unguwar suka samu wani shago karami da shi kamar container ce ma har sun wuce Sohail yace muje kaga wata a ciki kamar zamu samu wani abu,dawowa suka yi da baya wata budurwa ce kyakyawa ajin karshe ta saka face mask tana zaune a ciki,tana danna waya,ganinta da suffar musulmi suka furta salamu alaykum cewar Sohail,Sahil kuwa ya hade rai yana gefe a tsaye.


 Amsawa tayi sannan tace me za a baka? Sohail bai kulata ba, wani botikin gyada fari me murfi dake gabanta ya fara yin kida da hannu biyu yana kida da bokitin,ta tsaya tana kallon ikon Allah!


 Dariya yayi ya tsaya yace to ya aka yi? Ya ake ciki? mene da ke na ci? 


tace ga gyada,akwai biscuits,bread,cake etc gasu nan dai,Sohail ya kalleta suka hada ido"

dariya tayi yanda yake leke leke a wajen yana kalle kalle yana sosa gashinsa,"

yace bamu da kudi ne magana ta Allah bamu ci komai ba,ki taimaka ki bamu bashi in na samu zan kawo miki.

budurwar ta kare musu kallo tace guys kamar ku ace baku ci komai ba?

ke karki kara ce mana gayu mu ba gayu bane cewar Sahil yana hade hade rai, Sohail yace bama gane komai ki bamu please


 Budurwar ta lula tunanin oganta idan ta bada bashi,haka tayi shahada tace me zan baku a ciki? Sahil yace Cake da lemo da gyada,Sohail yace da bread dinma da wani abubuwan har da biscuits duk zamu ci,Mikewa tayi,amma Sohail har ya bude botikin ya kwaso gyadar da yawan gaske ko irgawa baiyi ba,tace hey dan tsaya mana please.


  Leda ta dakko ta dakko bread ya sa hannu zai fisge ta doke masa hannu ya janye hannunsa da sauri ya harare ta, ta zuba musu cake manya biyu,ta zuba musu gyada guda hudu ta dari biyar biyar ta saka musu bread kato slize bread,sai lemo biyu,Sahil yace a kara da yogurt ta saka musu biyu ,sai da ta hada duk abinda suka ce sannan tace da Sohail miko min wayarka"

wayar ya mika mata ta dakko littafi tayi rubutu tace sa hannu a nan,ya karbi biro ya sa hannu tace kuje idan kun kawo kudi sai na baka wayarka.


  Ran Sahil ya baci sarkin zuciya yace bata kayanta,Sohail yace kyaleta lets go,suka juya suka tafi abinsu, har sunyi nisa Sahil ya dawo yace da budurwar marar mutunci tare da sa yatsa ya dungure mata kai, ya juya ya tafi abinsa,dariya budurwar tayi kawai tana cewa ikon Allah.


  Kayan da suka karba a hannunta sai da suka yi kwana biyu bata ga keyar su ba shi suke ci,sai da ya kare Sohail yace bari naje na karbo mana bashi,Sahil yana gida Sohail ya tafi shi daya,budurwar yau tazo kenan da abincinta a flask cikin wata leda Viva,taga Sohail tace kaine yau? yace ae bashi na dawo ki bani na bar miki wayar tawa ki dinga bani abinci,kallonsa tayi tace wai kai ya sunanka ma? Yace Sohail,tace ina dayan? Yayi mamaki data gane su,yace ta ya kika gane mu? dayan ai yana da wushirya sannan bai son wasa baya fara'a,yace lallai kina da kwakwalwa,amma ta daya kike zuwa a ajinku? dariya tayi,ya sunanki ke? No barshi na sani sunanki Maheera,

A ina ka san sunana? ta furta tana kallonsa,yace bani alawa to na sha,robar alawar ta bude ta bashi daya kyauta,ledar Viva ta mika masa tace dauki kaje gobe ka kawo min flask dina,me zan baka bashi? Sai da yayi tunani sosai sannan yace Yogurt,ya sake lulawa tunani yace cakes,yawwa ehmmm na tuna da lemo,sai da ta gama zubawa yace da biscuits,cike da gajiyawa ta zuba ta bashi ya tafi.


  Yana tafiya ta zauna tana mamakin anya kalau suke kuwa? Abinda suke yi sam baiyi kama da na mutane normal ba a shekarun su,sunansa ta nanata "Sohail da Sahil" uhm nice name ta jawo wayarta tana dannawa.

  

  Sohail yana komawa abincin da Maheera ta basu a flask suka bude tuwon shinkafa ne miyar egusi da nama yanka hudu a ciki,gashi tuwon da yawa zai ishe su ma,fara ci suka yi da sauri da sauri yanda suka saba cin abinci basa amfani da spoon yawanci,Sohail yace babar su ta iya girki,da alama makarantar koyon girki tayi,Sahil yace ei ga dadin tsiya ba.


 Adnan suna mamaki yanda suka kulle kitchen amma suke ganin su Sahil kalau da su,takaici ya sa suka bude kitchen din ma,Sahil a zaune ya iske Adnan da Ibrahim a dining suna duba files na aikin su,yana inda inda yana magana da kyar yace Adnan...za...zan...tafi...unguwa..Ibrahim yaci magani yana masa wani irin kallo cikin hargagi yace ina zaka je? Sahil yace kawai duniya zan shiga zan nemi kudi nima....kafin ya rufe baki sun kece da wata mahaukaciyar dariya suna ta faman sheka dariya,ya tsaya yana kallon su har suka gama dariyar,Adnan ya kalle shi sama da kasa yace so a haka zaka nemi kudi? Dama kana da kwakwalwa? Ina kaga kwakwalwar neman kudi?...suka sake kecewa da dariya,dama zaka iya tunani haka? Cewar Ibrahim,dariya suka sake saki suna tafa hannu,Sahil gaba daya sai yaji gwiwoyinsa sunyi sanyi,sai yaji ya sare gaba daya,ya tsaya kamar gunki,idanuwansa suka cika taf da kwalla yanda suka sashi gaba suna ta dariya.


  Adnan ne ya dakatar da Ibrahim ganin zai fara masifa,yace wait Ibrahim,kai Sahil kudin mota za a baka? Sahil da kyar ya iya magana yace ae,Adnan yace wow Sahil you get heart wooo,nan take ya zaro 20k yace gashi ya isheka kayi manage har ka samu dai ka samu aikin yi,idan wahala tasa ka gaji zaka iya dawowa Abuja ga gida baka da damuwa.


  Ibrahim yace yanzu duniya zaka shiga kenan Sahil? Sai kuwa suka sake barkewa da dariya,Adnan yace dan Allah jeka dariya zata kashe ni,Sahil ya juya jiki ba karfi ya tafi.


  Dakin su ya wuce direct yana shiga ciki ya fada saman bed yana kuka wiwi,Sohail ne ya shigo ya same shi a haka,Shima bai ji dalili ba ya kwanta a gefensa ya fashe da kuka har yafi Sahil dinma kuka,Sahil a hankali ya dago da kansa yana kallon Sohail,Sohail yana kuka yace kar mu daina muci gaba dan uwana,Sahil ya daga kai sama alamar suci gaba din,suka ci gaba da kukan su,sai da aka dade suna abu daya sannan Sahil ya furta kai na gaji ya goge hawayensa ya jawo akwatinsa ya hada komai nasa,Sohail yace yanzu tafiya zaka yi? Yace mene amfanin zama ni tafiya zanyi na shiga duniya,gwara naje koma mene zai same ni ya same ni,to muje na rakaka.


  Tare suka fito da Sohail suka shiga mota har tasha Sahil yace Lagos zan tafi naje nayi ta kwana a kasan gada a haka idan abubuwa suka warware sai na maka waya ka taho kaima kaji ko,Sohail yace to ba damuwa,har tasha suka je amma Sahil baida kudin hawa mota me kyau dole ya shiga trailer wacce ake zuba yan cirani a ciki ruwa da iska ya kare a kansu a hanya cikin kudi kadan.

  Kudi ya biya aka rubuta sunansa da komai,yazo hawa trailer ya kasa,Sohail ya tsuguna a kasa Sahil ya hau dokin wuyansa ya mike sannan Sahil ya kama motar ya hau ya fada ciki,yana fadawa ya fada kan wata yar budurwa,yarinyar kuka take yi ta ture shi gefe tace malam mene haka,sorry ya furta ya dago ya kalleta,gabansa ne fadi ya ganta kyakyawar gaske yar fulani da ita,Jakarsa ya dauka tare da gyara zamansa a gefen yarinyar ga kafadarsa ga tata,gashi motar wani kan wani ake hawa ba wani Space dole a haka ake zuwa.


  Sohail ne daga kasa a tasha ya kwalawa Sahil kira,Sahil ya mike tsaye ya daga masa hannu suna dariya,yace karka manta in kaje ka kirani, inshaallah bro,ka kula da kanka,Sahil ya daga masa kai,mutane suna ta hawa motar kamar kasa,Sahil mamaki ya kamashi,gaba daya ba space a motar,wani akan wani haka ake a ciki,ko shanu baza a saka haka ba,jikinsu har yayi futu futu da kura,ga wasu gaba daya wari suke yi,ya rasa inda zai saka kansa a motar.

  

   Wari ya isheshi,budurwar dake gefensa ya kalla ta toshe hancinta itama an matse ta da kyar take shakar numfashi a haka motar bayan ta dame da mutane babu kalar yaren da babu a ciki ta tashi ta hau kwalta suka fara tafiya.


 Budurwar ce ta kwala ihu wani ya danno kanta tace wayyo zai kashe ni...zan mutu.....tana jan numfashi da kyar, Sahil ne ya dagata tana daga zaune ya dawo da ita saman cinyarsa,tace kai malam dan iska sauke ni,haka kawai ka dorani bisa cinyarka,suka fara kokawa da Sahil yace dole ki zauna ai nan yafi Safe,kina safe waje za'a kashe ki a nan wlh a banza,kina yar yarinya har kin san iskanci ne dalla rufe mana baki ko na kwada miki mari,budurwar ta zaro ido,wanda suke kusa da su sai dariya da ihu,wani dattijon banza yace wallahi kun dace kuma sai ace ma kanwarka ce kuna kama,Sahil yace na fita kyau ai,Budurwar tace Allah karya ne inji wa ka fini kyau?


  Jifa taji anyi da ita a motar,wanda ta fada kan mutane sai da taji rauni,sabo da bata san Sahil ba shi a tabin nasa zafi ne da shi,mutane suka sake hankadota,kuka ta saki taji wuya,da kyar ta samu ta dawo wajen zamanta,Sahil shi kanshi motar ta ishe shi ya rasa inda zai sa kansa,ya gaji da tsaiwa ya gaji da zama.


  Tausayi ya bawa budurwar tana satar kallonsa duk ya gigice kamar kansa da motsi,ana haka ruwa ya tsuge da iska me karfi,jakarsa tayi sauri ta jawo ta saka masa a cikin katuwar ledar da ta taho da ita yanda ruwa bazai taba ta ba,Suna tafiya ruwa na zane su a hanyar lagos,sai da suka kwashe lokaci me tsawo ruwan ya tsaya,mura da zazzabi suka kama Sahil,sai rawar sanyi yake,budurwar ta kalle shi tace ka canja ko rigar jikinka ce,bata jira amsarsa ba ta zuge ta zaro riga me kauri ta bashi,ya karba da kyar ya cire rigar jikinsa matan dake motar suka zubawa surarsa Ido suna kallon cikar sura da zallar kyau na halittar Allah,rigar ya canja,ta karbi wacce ya cire ta ajiye a gefe,dake ita da ledoji tazo manya ana ruwa ta saka abinta,ruwa bai jikata ba sam.


  Gyangyadi ya fara bai sani ba ya dora kansa a saman kafadar budurwar ,da sauri ta juyo ta kalle shi zata yi magana ya dagata sai taga bacci yake sai kawai ta hakura ta kyale shi,kowa ya zaci tare suke ma mata da miji ne,basu san kowa tafiyarsa daban ba,wata mace dattijuwa tace gaskiya kinyi dacen miji 'yar nan gashi kamar yaro shagwababbe da shi ba ruwanki,dariya ta kusa kwacewar budurwar sai dai ta fuske tace uhm kawai, suna tafiya duhu yayi ba sallah ba salati ga uban duhu suna tafiya a daji,Sahil baccinsa yake kawai shi,zamewa yayi a hankali cikin bacci ya dawo da kansa kirjin Budurwar,tana jinsa gashi ko bra babu a jikinta, fuskarsa ya dinga turawa cikin kirjinta kamar zai sha nonon uwarsa,duka ta dirka masa a bayansa ya farka a hankali ya bude idonsa,sai lokacin ya tuna fa a mota yake.


  Muryarta yaji me dadin saurare tace ka tasar min a jikina, tashi yayi a hankali yace ruwa....dariya ya bata tace lallai ma wannan wai sai kace yaro mutum da gemu kato da shi amma ni ina karama yake min haka, sai ka bari ai aje inda za a tsaya sai ka siya ka sha,wai kamar ba namiji ba kai,shuru ya mata yana zaune a gefenta ya sake komawa baccinsa.



  Motar su ce ta lalace a dajin kowa tsoron hanyar yake,ana ta salati masu addua suna yi amma Sahil shi baccinsa yake ma,sun dade a wajen kafin ta tashi suci gaba da tafiya,sai cikin dare suka samu aka tsaya a garin yarabawa tasha suka firfito kowa ya tafi neman abinda zai ci da masu sallah,budurwar ce kadai ta kasa fitowa kafarta daya waje daya a ciki,Sahil yayi dariya sannan yasa hannu ya dakkota kamar ya dauki tsinke ya direta a kasa.


  Kunya ta kamata ta diririce, Masallaci ya nema yaje yayi sallolinsa itama haka sannan yana fitowa ya siyi Apples,ya siyi ayaba,ya siyo naman kaza,sai ya siyo yogurt da lemo ga ruwa da wuri ya dawo cikin motar sabo da kar a fara turereniya,Ita kuwa budurwa bata da ko sisi na siyen komai kawai motar ta koma sabo da itama bata so a dinga ture ture da ita wajen shiga,shi kadai ta samu a ciki ya hau saman jakarsa ya zauna.


   Kallonta yayi yace ya baki siyo komai ba? murmushi tayi tare da zama tace banda kudi ni,yace tab rayuwa sai da cin abinci,ki dinga cin abin kanki,shi yasa bakya ci gaba kullum jiya i yau gaki nan tsiya tsiya sai son kudin tsiya, kici a jikinki baza kici ba sai shegen asusunki a boye,Ido budurwar ta zaro duk abinda ya fada gaskiya ne,bata kashe kudi,indai abu ne wai tasa kudi ta siya sabo da ta ci to baza ta siya ba kuwa sai dai ta tara kudin a asusunta.


 Abinda ya siyo ya mika mata gaba daya yace gashi ki cinye,baki ta bude tace kai fa? Yace kici kawai in kin rage ni na ci,tace no ai baza ayi haka ba to muci tare, a hasale yace kici dalla ko na kwashe na zubar,mamaki ya kamata,ita wannan wanne iri ne,haka ta fara ci duk abinda take sai da taci da yawa tace na koshi alhalin bata koshi ba.

 Yace baki koshi ba kici karya kike,"hmm" kawai tace taci gaba da cin abinta sannan tace ya sunanka wai? Yace "Sahil",tace ni kuwa...katseta yayi yace sunanki Islaha,baki ta bude tace a ranta ko ba mutum bane wai,amsa taji ya bata yace mutum ne mana.


  Tsoro taji yace ki daina tsoro mutum ne,ido ta zaro ta kasa cewa komai,yace zan iya fada miki asalinki gaba daya da tarihinki tsaf, tace to fada min naji.

 

  Asalinki ku ba hausawa bane wani yare ne ku can yankin Taraba State wanda kamar fulani kuke da shanunku da komai amma ku ba fulani bane kuma,iyayenki yan Taraba ne,Babanki mahaifi sunansa Sule mamanki sunanta Halisa ana kiranta Nany,kuma ke kadai suka haifa sannan sun rasu, a hannun kanwar Mamanki kika taso a taraba,karshe itama mijinta ya rasu ta fara tuwo tuwo,daga nan ita da yaranta data haifa mata su uku namiji daya gaba daya da yaran nata karuwanci suke yi.


  Cikin yaranta babbar yarta Shema'u ta zama me kudi sabo da karuwanci,ita kanta kanwar mamanki da sauran yaranta sun zama masu kudi sun koma lagos da zama a nan suke rayuwa ba ruwan su da sa ido na hausawa da dangi,kece anyi anyi a fara koya miki kema ki fara kinki yarda,shine ta maida ki yar aikinta wanda yar aiki ma ta fiki daraja a wajen su,azaba suke gana miki,yanzu ma aikenki tayi kauyen ku kika kai sako shine zaki koma,sannan shekarunki ashirin da biyar 25, sannan abinda yasa suke so kema ki fara sabo da kina da kyau matuka gaki da diri me kyau komai naki yayi,duk wani namiji zai so ace ya mallake ki.

  Kina son white color,kina son sakwara da miyar egusi,kina son wankan shadda,sannan period 4days kike yi....kuma....Islaha taji tonon sililin yayi yawa komai ya fada ba karya a ciki,ta dakatar da shi tace naji to,yace sannan kin gama secondary kin shiga NCE sai suka daina biya miki dole kika hakura da karatu.


  Mukus tayi duk abinda ya fada ba karya ciki,abincin ta mika masa tace na koshi,lokacin ya karba ya fara cin abinsa,ido Islaha ta tsura masa tana kallonsa kamar mayya,na miki kyau ne? ta tsinci muryarsa ya furta ba tare da ya kalle ta ba,da sauri ta dauke kanta ta fara wasa da yatsunta tana yarfe hannu,dariya yayi ba shiri tare da kamo hannunta yace mu gani ciwo yake,a hankali cike da kunya ta zame hannunta,tambaya ya jefo mata ke baki da kayan wasa ne muyi wasa? Cike da mamaki tace wanne irin wasa? A gidan ku ba a siya miki doll Baby su Teddy,murmushi tayi tace da girman nawa? baki ya turo,jajayen lips dinsa suka birge ta,kanta ta sadda kasa sabo da kunya,sun dade a haka kafin mutanen motar su dawo suka ci gaba da tafiya abin su.


  Sai washe gari da safe suka isa lagos,Islaha bayan sun sauka,ta tambayi Sahil ina zaka kai? yace gari mana ya juya dauke da jakarsa yayi tafiyarsa ko waigowa bai sake yi ba,baki ta tabe tayi tafiyarta itama.


  Gidansu ta nufa a taxi tana zuwa Kanwar Mamanta da suke kira da Aunty ta ga ta shigo da safe,ranta a bace tace uban me kika tsaya yi Islaha baki dawo da wuri ba,aikin gidan nan uban wa zai miki? Islaha cikin tsoro tace kiyi hakuri kin san motar da kika ce na shiga bata da sauri ga tsaye tsaye shi yasa,ke dalla rufe mana baki cewar Khairat yar Aunty ta cikinta,a kalla zata kai 30yrs,kanwarta Khalisat ce tace wannan fa sam bata da saiti,Islaha tayi shuru dai ita,Aunty tace ai kuwa ga aiki nan ya taru sai ki fara,a gajiye Islaha take amma haka ta fara aikin gidan.


  Gidane me kyau cikin estate duk gidajen layin iri daya ne,gidan yana da kyau a me rufin asiri dai a lagos duk da unguwar ta masu karamin karfi ce amma tayi kyau,Islaha sai da ta gyara gidan tsaf ta gama komai tazo ta dora girkin dare,Khairat tace wankin namu fa sai yaushe? Zanyi gobe inshaallah,da sauran rana a gari madam ki wanke mana kaya,Khalisat ce ta kawo mata kaya ta jibge,Islaha haka tana girki tana wankin sai da ta gama tas,Allah yasa ma kayan ba dirty,sai da ta gama komai sannan ta samu tayi wanka ta canja kaya cikin riga da wandonta yan gwanjo amma sun mata kyau sosai abinka da me kyau,abincin ta ebo taci ta koshi,tana palo Yaseer ya shigo babban dan gidan Aunty,Aunty tace Yaseer bana son wannan yarinya r da kace zaka aura Rukayya take ko,Yaseer ya kalli Mahaifiyar su ya furta amma kin san an sa rana fa!

 

 Aunty tace ai baza ka aure ta ba gaskiya na tambayi malamai na sunce sam ba Alkhairi a auren ku sannan indai ka aureta sunce kai da arziki sai dai kaga ana yi,nasan tun tana karama kuke soyayya hasalima ta samu mazajen aure amma ta makale sai kai ta dinga jiranka tun bamu da kudi gashi muna da rufin asiri amma baza ka aure ta ba,malamai sunce babu alkhairi.


  Islaha tana jinsu tace amma ai ba wanda ya isa ya hana wani arziki a duniya,Allah shike bayarwa shike hanawa,Aunty rankwashi ta zubawa Islaha tace wlh idan ina magana kina sa min baki sai naci ubanki, shuru Islaha tayi tana jinsu har Yaseer dinma katon jahili ya yarda da abinda uwarsa ta furta,yace to Aunty ai kuwa sai dai kije wajen Malamai a cirewa Rukayya so na a ranta,idan ba haka ba ta ya zan iya cewa na fasa? karka damu wannan me sauki ne za a sa taji bata sonka da kanta tace ta fasa,ya furta to shike nan tunda ba alkhairi me zanyi da ita yanda nake so nayi kudi ido rufe.


  Sahil machine ya hau yace kasuwar 'yan tumatir zaka kaini,me machine kuwa ya kaishi babbar kasuwar tumatir dake Lagos,hausawa da yare ne damkam ana ta hada hada,Sahil ya tsaya rataye da jakarsa yana kallon abinda akeyi,gashi su baza su iya aikin karfi ba,wani ne a ciki ya kalli Sahil ya ganshi ya dade a tsaye,ya zaci wani shahararren me kudi ne yazo daga kasar waje zai siyi tumatir,da sauri ya karaso gabansa yace


 Good day sir, Hausa Sahil yayi yace sannu da aiki,ashe kana jin hausa ai na zaci daga Tunisia ka sauka,Sahil yace no,okay kaya zaka siya ne? Mota nawa kake so? 

 Sahil ya kalle shi yace aiki nazo nema ni dan gidan malam shehu ne,mutumin ya kalli Sahil sama da kasa yace aiki? Irin wanda muke yi na karfi na sauke tumatir daga mota? 

Sahil ya amsa da ae mana shi,ai gidanmu ma sabo da bani da kudi idan aka ga hadari ya taso har danyar daddawa ake kaimin dakina na kwana sabo da kasan life no balance at all,yanzu idan baka da shi a gidanku sai uwarka ta mutu baka sani ba.


 Wanda suke magana me suna Aminu dariya ya dinga yi yace gaye kamarka sabo da talauci sai a kai daddawa dakinka na kwana? 

Sahil yace sai dai in hadari bai taso ba amma yana tasowa za a kawota a faranti.

Mutumin yace au baka da ko sisi a haka?kalli fa kayan jikinka sai me kudi ke sa irinsu"

 Sahil ya furta ae nema dai zanyi,dariya mutumin yayi sosai yace kalli kalarka fa zaka iya kuwa? Zan iya mana,mutumin yace sunana Aminu to kaifa? Sahil nake,yace indai aikin wahala ne baya wahala zaka samu,ka sauke duk kwando daya 50 Naira.


  Sahil yace zanyi haka,Sahil suna da karfi wanda bana mutane ba ma amma na aikin banza da anzo wanda mutum zai amfani kansa da shi sai lalaci yazo ya lullube su karfin bazai zo ba sam,haka ya ajiye jakarsa ya ratsa ta cikin kwandunan tumatir,Aminu yace waccen motar zamu je,suna karasawa Sahil ya shige cikin katuwar trailer a dole ya fito neman kudi,kwandon tumatir ya duka zai daga amma yayi yayi amma ya kasa,matasa dake wajen suka dinga ihu da dariya.


 Sahil zuciya ya sake yi ya yunkura zai dauka amma yin duniya ya kasa yana matsawa kansa ma sai ya fada saman sauran kwandunan,mutane wannan ya ja hankalinsu aka taru ana kallonsa yana ta faman nishi da haki,mutane suna ta tunanin hutu ne ya masa yawa kawai duba da kalar jikinsa ana gani an san ajebo ne,masifa suka fara masa ya sakko musu daga mota,haka ya sakko kawai jikinsa a sanyaye.


  Wajen masu abinci ya nufa sabo da tun a mota bai ci komai ba,ya samu ya siyi jullof din shinkafa da yankan namansa biyu ya zauna yaci ya sha pure water sannan ya mike ya mike ya koma cikin kasuwar.

  

 Aminu ya kira ya tambaye shi dan Allah a ina kuke kwana? Aminu yayi dariya tare da nuna masa wasu dakuna na langa langa yace kaga wannan dakunan a haka duk shekara kasan nawa muke hadawa muna biya? Sahil ya tambaya nawa? Yace dubu dari biyu kalli dai dakine kamar container,a haka ma munfi mu ashirin a ciki wani kusan a kan wani yake kwana,sannan ka jira kaga wasu a inda suke kwana.


  Sahil yayi mamaki ya koma gefe ya zauna,ga hadari ya hado sosai,yana zaune aka fara yayyafi sai yaga duk wasu suna saka rigar ruwa ga dare yayi wasu a cikin kurar ruwa da suke turawa ta eban kaya a ciki yaga sun saka kwali sun kwanta,wasu yan achaba a saman machinan su suka hau da rigar ruwa suka kwanta ruwa na dukan su,abin babu kyan gani yanda wasu a hausawan mu da gatansu da komai amma suke tafiya suna zubarwa da arewa mutunci,baza ka taba ganin yare a haka a wulakance a arewa ba da sunan neman kudi amma yan arewa duk inda kaskanci yake suna can,kana magana ace neman kudi ne,neman kudi sai mutum ya jefa rayuwarsa a hadari bayana a arewa ma wani yana da jarin da yafi zamansa a can.

 

  Sahil dare yayi yana wata yar runfa a tsaye ya fake ga mutane sunyi yawa,wasu yan shaye shaye ne suka zo da gudu suka hankado Sahil cikin ruwan suka tsaya a rumfar babu inda Sahil zai fake gashi dare yayi ga ruwa ana tsinkawa kamar da bakin kwarya,waige waige ya fara cikin ruwan amma ba inda zai shiga,gani yayi babu amfanin tsaiwarsa kawai yabi ta cikin ruwan yana tafiya wanda bai san inda ya dosa ba,ruwa na dukansa yana ji wayarsa tana ringing yasan Sohail ne ke kiransa yaji ya sauka lafiya ba damar daga waya.


  Yana ta tafiya cikin ruwan har ya bar layin ya shiga wani layin me kyau wanda bai san a ina yake ba,dai dai wani katafaren hotel yazo zai dan fake a jikin katangarsu, cikin tsararen hotel din ya kalla ya samu ya rakube ya fake a jikin wajen ya tsuguna! a haka yayi baccinsa har rana ta fito bai sani ba,karar mota ce tasa ya bude idonsa,kafafunsa har kumbura suka yi sosai,da kyar ya iya mikewa tsaye ya sake kallon cikin hotel din kenan


  Ido ya zaro yana kallon Islaha wacce suka zauna a mota budurwa tsaleliya cikin damammun kaya, bum short ne a jikinta da guntuwar riga gaba daya ta kudundune jikinta sai kakkare jikinta take yi tana jin kunya wanda da kyar take tafiya da alama bata saba ba,ga duwawu kaya guda komai ya ji,a gigice ta fito ta fice da sauri bata iya kallon kowa ta tare taxi ta fada ciki suka tafi,Sahil yana tsaye yana mamaki


 Ya furta wonder shall never end,so duk mata haka suke wannan wato mummunar dabiarta ce ashe amma a haka kamar ta kirki,tsaki ya ja yana mamaki yace ahhh amma na dorata a cinyata harda wani ita ba haka take ba,shi yasa ni fa dama can jinina bai hadu da mata ba,indai akace mata ne to ba ruwana da su,Allah yasa nidai bana jin sha'awa,mata suje da abin su gwara da Allah yayi ni haka Dagger din bata aiki thank God ya juya zai tafi kenan sai Khalisat yar uwar Islaha ta fito cikin tsaleliyar motarta fara kal" 


  Sahil ta kalla ta furta wow kaga wani handsome,harshenta ta zaro ta lashi labbanta tace wannan idan na mallake shi aurensa ma zanyi,zan iya cinye wannan danye wow,da gani dan me kudi ne ba karya,anya ma kuwa yasan hausa,Sahil kuwa waya yake da Sohail bai ma san me take yi ba sai ji yayi an masa horn,bai ko juyo ba sai da ya gama wayarsa ya juya zai tafi Khalisat ta sauke glass kasa tana murmushi,ba karya ta zuba kyau doguwar rigar silk material ce a jikinta kusan tsirara tsirara haka take komai ana gani,Tunaninta zata birge Sahil sai taga ko a jikinsa kamar namiji ya kalla.


  Murmushin da tasan yana kara mata kyau tayi cikin yanga da salon lankwasa murya ta furta zan iya dropping naka? Sahil da sauri ya furta no,please ta sake cewa tana wani shagwaba, gashi yana ta tunanin ko aljanun nasa zasu fada masa wace ita amma shuru,haka Islaha ya kasa gane gaskiya wanda a aikin banza kawai sai dai suji an fada musu abu amma wannan karon shuru ba labari.


   Motar ya bude a fusace ya shiga baya yace muje,tace gaba zaka dawo sai kace ka shiga taxi

  Yace haka nake so idan baza ki iya ba sauke ni,shuru tayi ta ja motar ta hau titi tana tambaya ina zan saukeka? Kafin ta rufe baki yace kasan gada,baki ta bude tace wacce gadar? Ya furta inda mutane suke kwana, Khalisat tayi mamaki sannan 


 Tace wai baka da gidan zama? Ya furta ae neman kudi nazo cirani,Wani dadi taji itakam tayi tsuntuwa,tace no ai baka samu aikin ba ko? Yace yeah, Alright muje gidanmu zan baka daki ka zauna har na wani lokacin da Allah zai sa ka samu wajen zama? Ko godiya Sahil baiyi ba ya furta Okay da fatan dai ba karuwanci zanyi ba? Domin kudin karuwanci da za a biyani bazai dauke ni ba,yana wani fisfisga shi kadai yana muzurai,dariya khalisat tayi kawai itama kyakyawa ce mashaallah komai na birge maza tana da shi.


  Gidansu me kyau ta nufa da Sahil ba wani shayi ko dar dar, suna zuwa tayi parking ya fito ya kalli gidan yace gidan ba laifi,Khalisat tana murmushin jin dadi,ciki suka shiga tare.


FREE PAGE


400 NE


0175487861

Asmau Garba Muhammad

Gtbank 


'Yan Niger

+22790795939





AsmaBaffa

***