{12..}
💛 HAJAR 💛
Nurain ya mayar da ƙofa ya rufe, Mami ta riƙo hannunsa ta zaunar dashi a gefen bed kusa da gogaggiyar malum-malumsa da hula waɗanda yake shirin sakawa, da wani irin expressions yake kallonta, ta zaunar dashi sbd gudun kar ya faɗi idan yaji abinda zata faɗa duk da tasan shi mai tawakkali ne, a hankali tace "Uthman" tana shafa kansa, yace "na'am Mami na", tace "kasan duk wani abu da yake faruwa ko kuma zai faru nufi ne na Allah, kuma nasan cewa ka yadda da ƙaddara", ya lumshe idonsa yana jin yadda take shafa kansa kamar tana rarrashinsa, tinda yaji waɗannan kalaman yasan cewa something was odd, yace "Mami me kike so ki gayamin ne?", kusa dashi ta zauna kana ta fara magana a hankali tace "Ruqayyah yarinyar da zaka aura...", ta wassafa masa kaf abinda ya faru, wata irin aradu ce ta doka a zuciyarsa idonsa ya kaɗa yay jaa, ya kasa cewa komai sbd karayar zuci, ba ƙarya Ruqayyah broke his heart into million pieces, sama-sama yaji muryar Mami tana cewa "pray my Son, Addu'a itace maganin duk wata musiba, i know your in agony but plxx don't let it slaughter you", ya ɗago idanunsa da suke farare ƙal-ƙal amma a yanzu sun canja launi, ya buɗe baki kamar zaiyi magana sai kuma yayi shiru, ya miƙe da sauri ya zubar da links ɗin rigarsa da yake dunƙule a hannunsa, wayarsa da take kan mirror ya ɗauka, yayi dialing numbern Ruqayyah ya kara a kunne, bashi da shakku ko ɗigo akan maganar da Maminsa ta gaya masa, yana so ya tuhumi Ruqayyah ne ya tambayeta Why him?.., me yasa sai shi a duk faɗin mazan duniya zata yaudara?, me yasa ta zaɓi ta ragargaza masa zuciya?, wannan shine sakayyar da zata yiwa soyayyarsa agareta, All love dinda take nuna masa was it a pretence all those years, Mami tace "who are you calling?", ya sake dialing for the fifths times, Mami ta sake zaunar dashi a gefen gado tace "Uthman, plxx relax, ban sanka da haka ba", ya sauke ajiyar zuciya yace "Mami, I'm okay" sai ya dafe kansa, knocking door akay Noor ta shigo tace "Mami tin ɗazu Anty Zulaiha take jiranki", Mami tace "Ohk, muje", Noor ta kalli Nurain da ya dafe kansa sannan ta fita a ɗakin, Mami ta miƙe a hankali ta dubi Nurain sai kuma ta sunkuya ta kwashe links din da ya zubar ta ɗora akan mirror tabi bayan Noor, zuciyarsa tafasa take, akwai ciwo sosai ace wanda ka yarda dashi ya yaudareka, yaudarar ma me zafi irin wnn, wayarsa ce ta fara ringing, ko kallonta beyi ba at this time he don't want to talk to anybody, he don't want to see anybody, all what he want is an explanation from Ruqayyah, wayar ya fuzgo da niyyar dannata a jirgi wani kiran ya sake shigowa from Dr Marwan, ya haɗiyi wani abu yayi picking kana ya kara wayar a kunnensa, Dr Marwa yace "wai ina ka saka wayarka ne tin ɗazu nake kira baka picking, ka gama ne muzo mu ɗauke ka, everyone is there Ango kawai muke jira", Nurain yace "Marwan cancel everything", Marwa yace "Dr what do you mean?", da kyar Nurain yace "yeah, plxx cancel the reception, ka bawa kowa haƙuri" ya katse kiran, ya janyo curtain ɗin wayar zai sakata a jirgi message ya shigo, saida ya saka wayar a jirgi sannan ya dawo ya fara karanta message din da ya shigo from Ruqayyah.. ( 😭 Sorry dearest, i want you to know that i madly love and i will be back to be with you, plxx wait for me.), yana gama karantawa yaji soyayyar Ruqayyah tana juyewa zuwa ƙiyayya, yayi wurgi da wayar ta daki bango sannan ta faɗi ƙasa ta tawarwatse. wnn text din babu abinda yayi masa saima ƙara masa raɗaɗi a zuciya, shi Ruqayyah zata yayyankawa zuciya da wuƙa mai kaifi kuma ta dawo ta bayan fage tana barbaɗa mata gishiri, dama bata turo masa wnn text ɗin ba da maybe some percent na son da yake mata zai ragu koda 3 ne, amma yanzu zero, zeron ma behind decimal point, ƙarƙat an yiwa mai dami ɗaya sata soyayyar Ruqayyah ta faɗi a ƙasa warwas, babu abinda yake ji sai tsanarta. Ruqayyah ta rushe da kuka bayan ta gama tura text message din, ta rungume wayar a ƙirjinta tana kuka sosai, few mutanen da suke kusa da ita a waiting chairs suka dubeta, saida taci kukanta ta more ta ciro barimar kunnenta, ta buɗe wajen sim card ta zare sims dinta ta zubasu a jaka, wayar ma ta wurgata a jaka, a lokacin aka fara announcing jirginsu zai boarding, ta miƙe tabi queue akay checking dinta sannan ta shiga Flight, ta zauna a seat dake kusa da window ta jinginar da kanta ta lumshe ido, wata mata da take gefenta ce ta taɓota jin anata cewa kowa ya saka belt dinsa jirgi zai tashi amma bata motsa ba, Ruqayyah ta buɗe idonta da sukay jajur ta kalli matar, matar tayi mata murmushi tace "fasten your seat belt lady", Ruqayyah tace "thank you" da dasasshiyar muryarta, ta janyo belt ɗin ta ɗaura, Jirginsu ya sharara gudu akan runway kana ya ɗaga zuwa sararin samaniya.
★Da wani irin expression Anty Zulaiha ta kalli Mami jin abinda ta gama faɗa tace "innalillahi wa'inna ilayhirraji'un, yanzu yarinyar da Nurain zai aura ce ta gudu", Mami tayi ajiyar zuciya tace "wai neman me kike min ne tin ɗazu?", Anty Zulaiha tace "ai magana ma ta wuce, yanzu where is my Son", Mami tace "yana ɗakinsa, Allah yasa ma bai fita ba, he will be okay", Sakeena ta shigo tare da Noor, Noor ta kalli Mami tace "wai me yake damun yaya ne, kamar naga bashi da lfy lokacin da nazo kiranki?", Mami ta kalli Sakeena tace "ina abincin Abba da nace ki ajiye?", Sakeena tace "yana nan", Mami tace "toh ki kai masa yanzu", Sakeena tace "ai sun tafi wajen ɗaurin Aure", Mami tace "ai ba wani ɗaurin Aure da za ai an fasa" ta miƙe ta fita, Sakeena da Noor suka bi bayanta da kallo domin suna buƙatar concrete explanation ne akan maganarta, tana fita sai suka juya a tare suka kalli Anty Zulaiha da ta wayance da buɗe foil papern da aka rufe peppered chicken da ita, Na reception din Nurain ne wanda za a ƙara akan wanda akay order, Sakeena tace "Anty nifa bangane me Mami take nufi ba", Anty Zulaiha tace "Eh an fasa auren", Noor tace "but why?", Anty Zulaiha ta gaya musu komai. Sakeena taji zafi sosai, her only brother wanda take jinsa tamkar shaƙiƙinta, ita har mantawa take ba mahaifiyarsu ɗaya ba, indai Nurain zai kaiwa Ruqayyah wata kyauta kamar Ramadan basket da sallah gift ko kuma dai wani abin haka itace take shirya masa, ko jiya da ta ganshi da daddare a balcony yana waya da Ruqayyah saida ta tsokanesa, duk irin crush dinsa da ƴan mata suke amma ita ɗin dai yake so kuma bai haɗata da ko wace mace ba yana dating, shin her brother yayi deserving irin wnn yaudarar daga Ruqayyah. Biki dai ya mutu ƙurmus, ƴan biki da ɓaki kowa ya ɗaɗe gida ya koma sai ƴar cikinsa daga Anty Zulaiha sai Sakeena ne suka rage, Nurain all this while yana room ɗinsa bai sakko ba kuma Anty Zulaiha ta hana kowa yaje gunsa tace abarsa zuciyarsa ta huta, sai dare da misalin ƙarfe goma sannan Sakeena ta zuba abinci da drinks ta ɗora akan tray zata kai masa, Noor da Khausar ne kawai a main palour, Sakeena tazo zata wuce da abincin Noor tace "amm na yaya Nurain ne?", Sakeena tace "Eh", Noor ta miƙe tace "wait a minute" ta shiga kitchen, few minutes ta jona coffee maker ta haɗa wani yummy coffee ta tsiyaye a Mug, ta fito da Mug ɗin mai ɗauke da coffeen ta ɗora akan trayn hannun Sakeena tace "idan ma bai ci abincin ba I'm very sure zai sha coffeen ko yaya ne", Sakeena tabi stairs zuwa room ɗinsa, a hankali tayi knocking sai kuma ta kara bakinta jikin ƙofar tace "brother nice" ta murɗa handle ɗin ƙofar, half expected ta jita a ƙulle amma sai taji ta a buɗe, ɗakin dulum dunɗum duk an kashe light, ta wawaki bango ta danna switch ɗin fitilu, a take haske ya mamaye ɗakin, yana kwance akan gado yayi rigingine, farar T-shirt da brown trouser ne ajikinsa ya cire na ɗaurin Auren da basu gama daidaita ajikinsa ba, ga nan wayarsa a tarwatse ko sake bin takanta beyi ba, Sakeena ta kallesa kana ta ajiye trayn akan rest chair tace "brother ga abinci na kawo maka, plxx eat", ya ɗago ya kalleta yace "thank you", tace "ga coffee ma Noory ta haɗa maka", kalmar coffeen da ta ambata tasa yaji wata suya a zuciyarsa yace "sister off the lights", bata ce komai ba ta kashe fitilar sannan ta fita a ɗakin. Bayan kwanaki Biyu Momy da haj Safiyya da kuma Kulsum da Aysha suka zo gidansu Nurain, tamkar babu wani abu da ya faru Mami ta saukesu, bayan sun zazzauna ne saiga Garba nan ya fara shigo da akwatuna, Mami ta kalli akwatin na lefen Nurain ne, Momy ita dai duk kunya ta dameta, saida Garba ya gama shigo da akwatuna sannan Momy ta shigar da abinda ya kawosu, takanas suka zo bada haƙuri akan abinda ƴarsu tayi, Momy ta kalli akwatunan da suke tuli guda kuma shaƙure da kaya tace "ga kayan yaron nan, akwai waɗanda aka ɗinka Insha Allah suma za'a ciko su, dan Allah hajiya a bawa yaron nan haƙuri", Mami tayi murmushin yaƙe tace "ba komai ba sai an ciko ba, anga ita Ruqayyahn kuwa?", Momy tace "da kanta ta fita kuma dan kanta zata dawo, babu wani nemanta da zamu tsaya yi", Mami tace "Aa ai baza ai haka ba, hannunka baya taɓa ruɓewa ka gutsire ka yar, ya kamata a nemeta ai macace", Haj Safiyya ta ciro bunch of keys ta miƙawa Mami tace "mukullin gida ne da yake gurinmu, ai ba kaya ma muka zuba aciki ba ɗan albarkar yaron nan ya zuba komai a gidansa", Mami ta karɓi keys ɗin tana jin daɗi ɗanta ya samu shaida mai kyau, kuma ta godewa Allah da bashi bane ya kawo tangarɗa, basu wani jima ba suka yi sallama suka wuce.
★Da dare bayan Sallahr isha'i Hajar ta gyara fuskarta da oil control powder ta shafa colourless lipgloss a lips ɗinta, ta zauna a gefen gado tana jiran isowar Nura sbd yau ranar zuwansa ce, babu jimawa sai ga kiransa nan ya shigo wayarta ta ɗauka tace gata nan fitowa amma kuma tana zaune daram babu niyyar tashi, saida ta kwashi minti biyar sannan ta miƙe ta sake kallon kanta a mirror tana murza lips dinta ta saka hijab, darduma ta ɗauka guda biyu sannan ta fito tsakar gida, Umma da take bakin murhu ta kalla tace "Umma na fita soro", Umma tace "tom saikin dawo", Hajar ta nufi hanyar soro, tin kafin ta kai soron taji ƙamshin turarensa, ta isa da sallama ba tare da ta dubesa ba ta fara shimfiɗa dardumar, ya karɓi ɗayar yace "bari na taya ki" ya shimfiɗa ɗan nesa kaɗan da ta ta, ya zauna ya tanƙwashe ƙafarsa, itama ta zauna tana wasa da ƙasan hijab dinta suka gaisa, yace "kin taho da takardun naki kuwa?", tace "A'a zan shiga na ɗakko maka idan zaka wuce", ya ɗauki wayarsa da yake haska musu fitilarta, gallery ya shiga ya buɗo wani uncompleted building, ya haska mata screen ɗin wayar yace "kinga abinda ya wahalar miki dani", ta kalli hoton tace "har an zuba dakin?", yace "eh Allah ya bada iko" sai kuma yayi gaba ya buɗo wani hoton shi kuma na windows ne sliding da door irin na gida da ake ƙerasu da inganci, yace "kinga suma waɗan nan na gama da babinsu", ya sake buɗo wani hoton na kayan bathroom masu kyau har set biyu yace "kinga 2 bedroom toilets suma na gama dasu", Hajar sai murmushi take suna tsara yadda gidansu zai kasance tare da tanadi mai kyau na futuren su. da wata iriyar tafiya irinta mata ƴan duniya Sa'adatu ta shigo, har ta wucesu sai kuma ta dawo tana yamutsa fuska, Hajar da Nura ko ɗaga kansu su kalleta basuyi ba suka cigaba da kallonsu, Sa'adatu ta zuge handbag ɗinta ta ciro tsaleliyar wayarta da mabaruka ta siya mata, fitilar wayar mai haske ta kunna ta dallare su da ita tana jan dogon tsaki, Hajar ta ɗago kanta tana micincina ido sbd yadda hasken ya kashe mata ido, Sa'adatu ta hura kwai da chewing gum din bakinta sai kuma ta taunesa ya bada sautin ƙass, ta buga wani uban tsaki tace "ke ashe naki iskancin haka yake, wato ke ƴar iska shine kike kawo mana ƙattin banza har cikin gida ko?", Hajar ta ɗauke kanta sbd bata so ta tanka mata a wnn lokacin, Sa'adatu kuma already tayi noticing dinta dan haka ta sake ɗaura ɗammarar ci mata fuska a gaban Nura, ta sake dallare fuskokinsu tace "dalla malam tashi ka fitar mana daga gida, ka bari ta biyoka shago mana, amma bazaku yi mana sheɗanci a soron gida ba", Hajar was burning inside kuma she can't take it anymore, ta miƙe tamkar wacca aka tsikarawa allura tana huci..........✍️