HAJAR

{13..}

by @feenerhfeeche


Sa'adatu ta dallare Hajar da ta miƙe da fitilar wayarta, Hajar tayi mata wani irin kallo sai kuma ta wuce cikin gida ta shiga ɗaki, umma tana ganin yanayinta saita bita ɗakin, wardrobe ta buɗe inda take ajiye muhimman takardunta tana dube-dube, umma ta kalleta tace "lafiyarki kuwa hajara?, Nuran ya tafi ne?", Hajar ta cigaba da ɗaɗɗaga takardu hawaye ya cika mata ido tace "umma wnn wane irin masifa da bala'i ne?, Maama da ƴaƴanta wllh annobane, ni kam nagaji da haƙuri dasu, na rantse da girman Allah daga yau duk wacca ta sake shiga harkata saina raunata ta, anƙi ayi haƙurin dasu, idan zaman lfy toh za'a zauna lfy ɗin, idan kuma zaman tashin hankali toh za'a tashi hankalin fiye da kima.....", umma ta katseta tace "toh maza ki ɗauki harama tinda ke kika haifi kanki, yanzu me ya faru?, naga dai zaune kike a soro da Nura", Hajar ta ɗauki envelop ɗin credentials ɗinta ta zauna a gefen gado ta share hawayen da ya zubo mata tace "Sa'adatu ce", umma tace "me Sa'adatun tayi?", Hajar ta gaya mata abinda tayi musu a soro, Umma tace "shknn, dafatan dai biki tanka mata ba?", Hajar ta girgiza kai tace "bance mata komai ba kawai tasowa nayi na dawo gida, wllh nasan idan na zauna za'a iya haifar ɗa mara ido", umma ta zabga mata harara tace "wato har wani cewa kike za'a haifi ɗa mara ido ko?, Hajara ki ringa sanyaya zuciyarki, ki dena ɗaukar komai da zafi, yanzu waɗan nan takardun su kuma me sukay miki da kika birkito su?", Hajar tace "shine yace na kai masa", Umma tace "A'a naga ai kin basa takardun naki kwanaki?", Hajar tace "Eh, ai na secondary na basa, yanzu kuma primary certificate da testimonial zan basa", umma tace "toh, tashi ki kai masa saiki dawo gida gobe kwa ƙarasa". Hajar ta miƙe ta fita da envelope a hannunta, kasa kallonsa tayi tace "ga takardun", ya miƙe ya amsa sai kuma ya nannaɗe dardumar da ya tashi daga kai ya naɗe ta Hajar ɗinma, ita dai kawai wasa take da fingers ɗinta tace "dama ka barshi zanyi ai", yace "na hutar dake", ya miƙa mata darduman tare da wayarta da ta ajiye a wajen yace "toh seda safe", ta karɓa kanta a ƙasa tace "seda safe", ya tsaya yana kallonta yace "toh shiga gida", ta juya a hankali ta shiga gida shi kuma yayi tafiyarsa, Hajar ta tsaya daga bakin rariya ta kunna wayarta tana murmushin mugunta tace "idan kinci bulus shegiya nake", ta shiga contact ta lalubo numbern Naseer tayi dialing, bata daɗe da fara ringing ba ya ɗaga, ta sauke ajiyar zuciya tace "Yaya ina wuni", daga ɗayan ɓangaren Naseer yace "lafiya lou Hajar", tace "yaya daman Sa'adatu ce tazo, gata can sai rashin kunya takewa Maama sbd tace karta sake barin gida..", Naseer ya katse kiran ba tare da ya ce komai ba, Hajar ta kalli screen ɗin wayar tayi murmushi, tasan yanzu haka gida zai taho, daman tasan yana neman Sa'adatu tinda duk zuwan da yake takan ji yana tambayar Nabila ko Maama ina take wani sa'in. ta wuce tsakar gida ta tsaya tana kallon ɗakin Maama da ake jiyo muryoyinsu daga ciki suna hira da shewa, muryar Sa'adatu tafi ta kowa tashi, Hajar ta yamutsa fuska tace "zaki ɗanɗana ne jaka" tayi wucewarta ɗaki. Nabilah ta juya tsaleliyar wayar hannunta tace "yanzu Sa'adatu wnn wayar ta mazajen kuɗi itace a hannunki", Sa'adatu tace "rass ma kuwa ya son ranki, masoyiya Mabruk ce ta siya min", Maama ta karɓi wayar daga hannun Nabilah tace "gaskiya yaran nan suna sonki da arziƙi, nawa ma kika ce kuɗin ta?", Sa'adatu tayi kwai da chewing gum ɗin bakinta tace "dubu ɗari biyar", Maama tace "caɓɗijam", Maimuna da take kan gado ta sakko tace "yawwa Sa'adatu kince zaki faɗamin sunan man da kika koma shafawa wanda yasa kika koma fara gaba ɗayanki", Sa'adatu ta harareta tace "wane irin mai, yarinya wasa ma kike, ni na dena shafa mai sbd ɓata lokaci ne, allura ake min", Maimuna tace "Allura..??", Sa'adatu tace "rass, har fatar kaina da mazaunai na sun koma farare yanzu", Maimuna tace "chab gaskiya bazan iya allura ba", Sa'adatu tace "yo shknn kiyi ta shafa mai yana miki glass a fuska, yanzu ma kalli fuskarki kamar an watsa fitsari duk tayi wani jirwaye, ga wani map of Africa a kumatunki", Maimuna tace "naji, a haka Alhaj ɗina yake so", Sa'adatu ta warce wayarta da take hannun Maama ta duba lokaci, ta ɗauki handbag ɗinta ta ciro maƙudan kuɗi ta lalo dubu ashirin ta miƙawa Maama tace "toh da haka da haka baƙo zaiyi halinsa", Maama ta soke kuɗin a kirjinta tace "Au ƴar nan tafiya zaki yi baza ki kwana ba", Sa'adatu ta miƙe tsaye tana kakkaɓe jikinta sai kace wacca ta zauna a sahara tace "la la la bazan kwana ba wllh, kuɗin cizo da sauro suyi min illah", Nabilah tace "Sa'adatu naga kin mayar da kuɗin jaka, ni kuma fa ba ki ɗusheni ba", Sa'adatu ta yamutsa fuska tace "ai kece kinƙi ki waye, yanzu Maimu ba gashi nan ba kullum da ƴan canjinta a ƙugu, miƙomin jakar", Nabilah gaba take da Sa'adatu amma haka ta ɗauki jaka ta miƙa mata da hannu biyu, dubu biyar Sa'adatu ta lalo ta mannawa Nabilah a ƙirji tace "gashi dai mai kai a tukunya", Nabilah ta dafe kuɗin ta linkesu ta cusa a bra. Sa'adatu tace "toh na tafi Maama", Maama tace "karki daɗe baki zo ba kinji", Sa'adatu tace "toh zan duba na gani" ta fito tsakar gida ta saka takalmi ta fita. A soro sukay kaciɓus da Naseer wanda ya shigo a fusace, zuciyarta ta buga da ƙarfi ta juya zata koma ciki, wani gigitaccen marii ya sauke mata a fuska, tayi taga-taga tamkar zata waɗi ta bugu da bango, tsaleliyar wayarta saura ƙiris ta faɗi daga hannunta, tana dawowa hayyacinta ta ruga cikin gida ya biyota da sauri, takalmin da yake ƙafarta mai tsini ya gurɗeta aikam tayi mummunar faduwa a ƙasa daɓas, wayar hannunta kamar wacca aka fuzge haka tayi tsalle ta daki bango, Sa'adatu ta ɗora hannu a ka ta kurma ihu tace "wayyo wayata", Baba ya fito daga ɗakinsa da sauri yace "Nasiru zane min ita, zaneta nace", Maama ta fito jin abinda yake faruwa tana hura hanci tace "wllh karka kuskura ka taɓa ta", Baba zuciyarsa na masa zafi yace "Rabi idan kika sake magana anan wajen na rantse da girman Allah saina tsinke jemammiyar igiyar aurenki guda ɗaya da ta rage", Maama ta dafe ƙirji ta zaro ido amma ta kasa cewa komai, Saki kuma da girmanta da gemunta ace za'a saketa, dama igiyoyin auren saura ɗaya ce ta rage, Baba yace "Nasiru ka zane min ita", Sa'adatu ta wawaki ƙasa zata miƙe ta afka ɗakin Maama amma ina tini Naseer ya fuzgota. wani mabirki mai kauri na icce wanda ake kaɗa miyar yauƙi dashi ya ɗauka, Naseer ya ringa rankwala mata shi a jiki, saida ya kakkafe mata tsoka tass, ƴan yatsenta kam kamar zasu zube sbd yafi rankwala mata anan, Maama dai kawai kumbura take tana sacewa ita kaɗai, saida Sa'adatu ta faɗawa ƴan garinsu sannan Baba yace "ya isa haka, kullemin ita a can" yayi nuni da kitchen wanda basa amfani dashi sai tara shirgi, gaba ɗaya kitchen ɗin ya mutu, Naseer ya figi Sa'adatu ya dannata aciki ya banko mushiyar ƙofar langa-langar, Baba ya numfasa yace "ka gaji ko kuma da sauran ƙarfinka?", Naseer baice komai ba, Baba ya ɗaga murya da kanaji kasan a ɓace ransa yake yace "Maimuna!!, Maimuna!!", wani irin juyawa ƴan hanjin Maimuna da take laɓe jikin labule sukay, daga ita har Nabila sai suka fara neman gurin ɓuya, Baba yace "Shiga ka zanemin ita itama", wayyo daman Naseer duk kansu yanada cikinsu, ai Maimuna a ɗaki akay mata nata walmukalafatun, itama tasha mabirki daidai gwargwado, Baba yace itama a haɗata da Sa'adatu a rufe, Nabilah ma ta amshi rabonta saidai bai kai nasu ba, ita akai aka rarrankwala mata mabirkin sannan ta amshi maruka biyu zafafa, zuciyar Maama ta soyu iya soyuwa, tanaji tana gani aka zane mata ƴaƴa, Baba ya bawa Naseer padlock yace ya kulle kitchen ɗin anan zasu kwana. Hajar da take jikin window tana hangen duk abinda yake wakana tayi murmushi zuciyarta fess, ai ita dukan da akay wa Sa'adatu da kuma yadda wayarta ta daki bango shi yafi mata daɗi, wayar da aka wulaƙanta ta da ita a soro gashi nan ta fashe. washe gari da safe Hajar ta fito tsakar gida da kayanta da zata wanke, ta deɓi ruwa a bucket ta zazzaga omo ta sunkuya ta fara wankinta tana humming song, a fakaici ta kalli ƙofar langa-langar kitchen da take a garƙame da kwaɗo, har yanzu Sa'adatu da Maimuna suna ciki sunyi bugun sunyi kukan har sun gaji, muryar Maimuna taji tana kuka tana cewa "dan girman Allah Baba kayi haƙuri wllh bazan sake ba, wayyo Maamana, na shiga uku na lalace, wllh kunama ta harbeni dan Allah a buɗe mu, Sa'adatu ta yanke da ƙarfen langa-langa", Hajar ta kyalkyale da dariya tana wankinta, Maama ta fito daga ɗakinta zuciyarta busu-busu ta shiga ɗakin Baba, Baba ya gama shiryawa tass zai fita aiki, Maama tace "mal fita za kay?, yaran nan fa har yanzu ba a buɗesu ba", Baba ya gyara wuyan rigarsa yace "sai aka yi yaya da ba a buɗesu ba?", tace "daman naga ko sallar asuba basu yi ba gashi rana ta fito", yace "Au daman kina damuwa idan basuyi sallah ba?", ta fara ƙinƙina tace "dan girman Allah mal kayi haƙuri, a yi musu afuwa", Baba ya gyaɗa kai yace "za a yi musu, amma in tambayeki mana?", tace "toh mal", yace "waye uban Sa'adatu da Maimuna?", ta saki baki sai kuma tace "kaine mana mal", yace "ni mijinki ne ko A'a?", tace "kai mijina ne mana", yace "idan kina so igiyar aurenki ta cigaba da rayuwa to ki gyara tarbiyyar ƴaƴanki, idan kina son ƴaƴanki to ki gyara tarbiyyarsu, kar Sa'adatu ta sake barin gidan nan, Maimuna karta sake fita da daddare, Nabilah ta fito da miji na aurar da ita", Maama ta gyaɗa kai tamkar tsohuwar ƙadangaruwa tace "tom", ya ciro muƙulli daga aljihunsa ya bata yace "ki buɗesu idan na dawo ina son ganinsu", Maama ta karɓi muƙullin tana harararsa ƙasa-ƙasa tace "toh" ta fita a ɗakin, ruɓaɓɓen kichen ɗin ta buɗe Sa'adatu da Maimuna suka fito wujiga-wujiga, zafi ya dakasa ga kuma jikinsu da yayi tsami.


★Nurain ya fita masallaci sallar la'asar, bayan ya dawo ya tsaya suna gaisawa da Garba da yake bawa flowers ruwa, Nurain yace "wace motar ka wanke min?", Garba yace "farar na wanke maka", Nurain yace "Ohk, ka amso min takalmana daga wajen polish", Garba ya dukar da kai yace "toh alhaji ƙarami", Nurain ya wuce ciki, har zai zauna a balcony sai ya fasa dai ya shiga main palour ya zauna a kujera, remote ya ɗauka ya canza channel, bayan few minutes ya miƙe ya shiga kitchen ya buɗe fridge ya ɗauki Apple guda uku ya ɗora akan plate ya dawo palour ya zauna yana ci, Noor ta shigo palourn tace "Yaya Mami is calling", yace "Ohk", ya miƙe ya ɗauki plate ɗin Apple ɗinsa ya shiga part ɗin Mami, Mami ta ringa kallonsa har ya zauna a kujerar kusa da ita, ya ɗan rame kaɗan amma kuma fuskarsa babu wata damuwa, Mami tace "where is your phone?", ya shafa kansa yace "Ta fashe ne", tace "Ohk, toh dan ta fashe shine ba za ai amfani da ita ba, saika zauna haka ba waya", yace "zan siyo wata ne", tace "good do that fast", yace "yeah" tace "when are you resuming work?", yace "next week, daman na ɗauki leave na two weeks", ta gyaɗa kai tace "Son, why not go towards Khausar", yace "Khausar?", tace "yess Khausar"..........✍️