BABI NA ƊAYA
by @billysfari
GS 1.
Tunda ta nufo cikin parlorn gabaki ɗaya hancinsa ya shaƙo masa lafiyayyun ƙamshin turarukanta masu matukar daɗi, gabaki ɗaya sai yaji tamkar bai shafa nashi turarukan ba saboda yadda nata ya yi bala'in yin tasiri a gabaki ɗaya wajan. Zaune Alhaji Sha'aban Sada yake akan 2seater hannunsa riƙe da wayarsa yana dannawa wanda shigowarta yasa shi ɗago kansa yana kare mata kallo mai cike da soyayya. Kyakkyawar mace ƴar gayu da kuma ƙwalisa da kallo ɗaya zaka yimata kasan don abun duniya ya tattara gareta, Murmushi suka sakarwa juna a lokacin da ta gama ƙarasowa inda yake yana ɗan matsawa can gefe alamar tazo kusa dashi ta zauna. Wani kallo tayi masa wanda yasa shi sakin ƙawataccen murmushi tare da maida kansa yana kallon side table ɗin da ya janyo zuwa gabansa wanda yake cike da tarin dukiya akai da alama amfani zai yi dasu. Zama Hajja Maimoon tayi tare da rungume shi tana kwantar da kanta saman kafaɗarsa cikin kulawa, hannunsa ta kamo cike da hikima da soyayya tana matsa su cikin nata. Sumbatar hannun tayi kafin ta ɗan ɗago kai ta kalleshi tana yatsina fuska kamar shagwaɓa take faɗin.
"Ya Habiby shine ka gudo nan ko?" Murmushi Alhaji Sha'aban Sada ya yi yana dawo da kallonsa gareta, ta lumshe ido zuciyarta cike da tunanin mai zai yi da uban kuɗin nan haka dake gabansa? Matse hannunsu da ya yi ne yasa ta dawowa cikin hayyacinta. Cike da sanin yakamata domin Alhaji Sha'aban mutum ne da yasan kansa yasan kuma mutunci da karama na iyalinsa yake faɗin.
"Nan na taho ina jiran Irfaan ya ƙaraso." Murmushi ta saki tana sake kallan uban kuɗin dake gabansu, bataki a bar mata su ba gabaki ɗaya dan tsab zata iya ɓatar dasu a yau ɗin nan ba tare da ta jinkirta ba, tana mamakin yadda mijin nata yake da uban arziki amma kuma baya sakar mata su tayi yadda takeso. Sai dai duk abinda take buƙata yana batashi, takan tuna maganar ƙawarta da take cewa.
_"Kinsan fa ƴan kasuwa basu sakarwa matansu kuɗi haka kawai dole sai da dalili, ki dinga yi masa dabara kina kwakular rabonki idan ba haka ba babu abinda zaki tara a tare dashi."_
Murmushi ta sakeyi zuciyarta cike da tunanin yadda zata fisge rabonta kafin ta bari a fitar da su daga gidan. Yadda ta sauke numfashi a saitin kunnansa sai da yasanya Alhaji Sha'aban lumshe idanunsa yana jin wani irin abu a jikinsa zummm. Ta lura da yanayin da ya shiga dan haka ta sakar masa hannayensa tana jingina bayanta jikin kujerar da suke, da tsantsar kulawa take masa magana.
"Ya Habiby yauma aikin ladan za'a yi kenan?" Yace,
"Wannan aikin na wajibi ne Hajiya za'a kaiwa." Wani abu mai zafi ne ya daki cikin zuciyarta dama tun kafin ya faɗa tasan cewa Hajiyarsa za'a kaiwa, haushi da bakin ciki suka cika mata zuciya. A duniyar nan tana matukar kishi da matar nan saboda irin kulawar da Alhaji Sha'aban yake bawa Hajiyarsa a wajan Hajja Maimoon tayi yawa, gabaki ɗaya idanunta kullewa sukeyi ta manta da matsayin matar a wajan mijin nata. Shi kuma baya haɗa komai da mahaifiyarsa dan wani irin girma da soyayya mai matukar burgewa ce tsakanin su. Kasa haɗiye bakin cikin nata tayi, sai dai bata yi magana ta yadda zai gano akwai wani bad thing a maganarta ba tace.
"Ya Habiby kenan, Allah ya rabaka da Hajiya lafiya. Kana ji da ita matukar ji dan ni kam ban taɓa ganin namiji irinka mai ji da mahaifiyarsa ba. Amma Ya Habiby sai naga kamar kana cikawa Hajiya kuɗi bayan kuma baka barta da rashin ci ko sha ko sutura ba, ni sai naga kamar kuɗin da kike aika mata dashi is too much, kasan kuma ba wai ita ke amfani dasu ba." Tayi shiru tana fatan samun nasarar maganganunta suyi tasiri a gurinsa. Sai da ya juyo ya kalleta tare da sanya tausassun hannayensa ya kamota zuwa jikinsa yana sake shaƙar ƙamahinta da yake saukar masa da wata irin kasala yake faɗin.
"Basu yi yawa ba Madam, waɗannan ba komai bane da zan bawa Hajiyata, duk wani abunda zan bata bazan iya biyanta da abubuwan da tayi min ba. Za'a kai mata idan tace sunyi kaɗan Madam dole zan ƙara mata saboda komenene na zama a yanzu itace mutum ta farko da ta bani gudummawa ba tare da gajiyawa ko gori ba." Tunda ya furta idan Hajiya ta nemi ƙarin wasu kuɗin akan wannan na gabanta da za'a akaiwa Hajiyan, gabaki ɗaya hankalin Hajja Maimoon ya sake tashi. Ƙanƙance idanuwa ta shiga yi tana jin zuciyarta tamkar zata fito. Karan hancinta taji yaja tare da sumbatar saman hannunta da yake riƙe dashi yana cewa.
"Ko duka arzikin da Allah ya yi min Hajiya tace na bar mata su zan bata babu gaddama bare kuma ɓata rai." Duk yadda Hajja Maimoon take jin kamar zata mutu saboda yadda yake nuna kamar mahaifiyarsa tafi ta, sai kawai ta daure sosai tana sake shige masa take cewa.
"Masha Allah haka ake so ai Ya Habiby." Tayi shiru bata ƙarasa abinda ke ranta ba saboda tana son tayi amfani da damar itama ya wawuro wani abun a cikin kuɗin ya bata. Ta buɗe baki zatayi magana Irfaan ya fara knocking, Alhaji Sha'aban ya ɗan saisaita kansa yana kallan ƙofar tare da bada izinin a shigo. Cikin girmamawa ya gaishe su suka amsa Hajja Maimoon sai hararasa takeyi tana miƙewa tsaye, zuwan Irfaan tasan ba zata samu ko naira biyar ba, idan kuma an bata Irfaan yana komawa gida zai gayawa mahaifiyarsu. Ficewa tayi bayan ta ƙudiri aniyar karɓar nata dan ba zata taɓa hakura ba.
_____
Iya karfin ta take amfani tana dirzar tiles ɗin dake jikin bangon bathroom ɗin, gabaki ɗaya ta haɗa zufa tana yi hawaye masu zafi suna gangarowa saman fuskarta. Sai da ta tabbatar da cewa ya fita yadda duk bala'i ba za'a iya dawo da ita baya ba sai idan suna son kuma bata wahala, sannan ta saka bayan hannunta tana sharce gumin da yake tsatso mata a saman goshinta. Handshower ta janyo bayan ta kunna ruwa ya fito ta shiga ɗauraye tiles ɗin kafin ta sake ɗakko sosan da ruwan da ta haɗa kumfar taje tana sake dirzar cikin standard jacuzzi ɗin wanda yake fari ƙal dashi. Yadda taji an buɗe ƙofar an shigo ne yasa ta juyowa a firgice dan ba ƙaramin tsora taji ba. Wani kallo da take yi mata ne yasa ta sauke kanta ƙasa tana jin wani irin tashin hankali yana shigarta dan bata san laifin da za'a ce tayi ba yanzu. Cike da wulakanci da ƙaskanci take kallonta tana sake ƙarewa bathroom ɗin kallo.
"Yauma sai da kika sa na taso ko? Wai Jauhar me yasa baki da tunani ne na tashi da wuri kiyi mana abunda yakamata? Mtwww dallah can ki ɗauraye zan shigo nayi wanka ƴar ƙauye kawai." Tana gama maganar ta juya tana banko ƙofar. Da kallo Jauhar tabi Suhana wacce zata iya cewa kaf cikin yaran gidan tafi su saukin kai a hakan. Sauri tayi ta shiga wankewa tana sake wanke sink da shower tare da duk abin ya dace a wanke a cikin ɓanɗakin. Sai da ta gama sannan ta ɗakko towel ɗin da ake goge bathroom ɗin nan ma ta goge ko'ina ta saka bathroom freshener. Sai da ta kusan fitowa daga ciki tana riƙe da handle ɗin ƙofar ta sake kallon ko'ina, ita kanta sai da tayi murmushi ganin ya yi kyau sannan ta rufe. Jikinta ciwo yake sosai burinta ta zauna ta huta, kallon gadaje guda ukun dake jere a cikin ɗakin tayi tana kallan masu yin bacci akai. Ina ma ace itama tana da gatan ta zata ganta tana bacci so compartable koda ba a irin wannan gidan ba. Jiki babu karfi taje zata fita harta murɗa handle taji an kirata da sigar da tafi tsana wato.
"Ke..!" Ras kirjin Jauhar ya wani irin bugawa, zuciyarta ta harba tamkar zata yo waje. Ta daɗe tana kokawa da numfashinta yadda zata samu karfin zuciyar da zata jurewa abinda wacce ta kiratan zata yi mata. A hankali ta juyo tana kallon wacce take kwance a kan gadon tsakiya, yadda take haka ta juyo ta ganta bata motsa ba idanunta kawai ta buɗe.
"Zoki yi min tausa jikina ciwo yake mun." Jannat ta faɗa tana sake maida idanunta a hankali ta rufe tamkar ba ita tayi maganar ba tana sake bajewa akan ƙawataccen gadon nata. Hawaye Jauhar taji sun zubo mata wanda tana da tabbacin na bakin ciki ne, a girme tasan ta girmi Jannata dan ta bata shekaru biyu suna gidan akaiwa Jannat birthday ɗin 12 da 13years ita kuma yanzu haka 15years take dashi. Amma yadda ta rainata take kuma wahalar da ita tare da kyamatarta kaf gidan babu mai yi mata kalar na Jannat ɗin. Ƙarasawa tayi wajan gadon tasa hannunta akan ƙafafuwan Jannat ɗin zata fara matsa mata kawai taji tana.
"Ahhh." Tare da ɗagowa ta hankaɗa Jauhar ɗin. Gabaki ɗaya tayi baya ta faɗa ƙeyarta ta buge da gadon Suhana. A gigice Jannat ta shiga cukuikuyewa a duvert tana sake sakin ihu tamkar wata wacce take ganin abin tsoro.
"Menene wai Jannat? Me tayi miki?" Sohana ta shiga tambayarta ganin yadda ta gigice. Kafin tayi magana Hajja Maimoon ta shigo cikin ɗakin.
"Meya faru?" Ta tambaya tana nufar Jannat dake takure. Jikinta ta janyo ta a ruɗe tana duddubawa ko zataga wani abun, ganin babu komai yasa ta sake tambaya.
"Jannat menene?" Cikin kuka Jannat ta fara magana.
"Gatacen daga cewa ta matsa min ƙafafuwa na kawai tazo tana shafa min ruwan hannunta, gashi hannun da mugun sanyi." Ta ƙarasa faɗa tana shigewa jikin Hajja Maimoon wacce tsabar ɓacin rai har kamanninta sun soma canzawa. Furucin Jannat yasa Jauhar saurin kallon inda suke zaune tana ware idanuwa jin sharrin da Jannat keyi mata. Yadda taga Hajja Maimoon ta ɗora Jannat a jikinta tana lallashi ne yasa Jauhar kasa yin magana sai hawaye da yake zubowa daga idanunta tasan yau kam ta shiga uku saboda ta saka shalelen gidan kuka. Suhana ce ta dafe kirji tana yin wulli da duvert ɗinta, sakkowa tayi daga kan gadonta ta nufi inda Jauhar ke duƙe a ƙasa ta fisgota da karfi. Jauhar ta kalli Hajja Maimoon dan ganin reaction ɗin ta, ga mamakin ta sai taga ta ɗauke kai tana kwantar da Jannat a hankali tamkar wata kwai da ba'a fatan ya samu matsala.
"Gaya mana muji aiki kika zo ko kuma kashe mana ƴar uwa? Kinsan ai tana fama da limoniya shine kika zo zaki ƙarasa ta ko?" Ko kafin Jauhar tace wani abun tuni taji an wanke fuskarta da wani gigitacen mari wanda yasa ta manta da kanta na tsawon sakanni. Muryar Hajja Maimoon ce ta dawo da ita cikin duniya da kuma hayyacinta inda taji tana cewa.
"Da alama bakin cikin ganinsu kike yi ko?" Kuka ya kwacewa Jauhar tayi saurin toshe bakinta da tafukan hannunta tana girgiza kai.
"Ƙarya kikeyi shegiya mayyar yarinya, to ina faɗa maki idanunki ya fita daga kan mutanan gidan nan domin su ba watsatsu bane ba kamar ke dan nasan ke kanki kinga alamar hakan. Idan kuwa kika sake ɓatawa wani rai a gidan nan ina tausaya miki Jauhar domin sai na lahira ya fiki jin daɗi. Kije kiyi warming hannunki sannan kizo ki mata abinda takeso kafin kiga ɓacin raina, ƙazama kawai." Ta faɗa tana yi mata kallo mai cike da tsana. Gabaɗaya tazame mata kadangare bakin tulu ta rasa yadda zatayi da ita, Banda kaddara ita kam bataga dalilin da zai sa taci gaba da ganin yarinyar nan a cikin gidanta ba. Da gudu Jauhar ta fice daga ɗakin, kitchen ta shiga tare da fashewa da wani irin kuka mai sosa zuciya. Gudun kada ta sake janyowa kanta yasa tayi saurin ƙarasawa ta kunna cooker gas, jikinta yana rawa bata dena kukan ba ta fara gasa hannunta, saboda hankalinta baya jikinta yasa ko zafin wutar bataji, kalmar watsattsiya yafi komai taɓa mata zuciya. Sam bataji motsi ba sai ji tayi an saukar da hannunta daga wajan wutar, tayi saurin ɗago fuska tana ɗora jajayen idanunta akan fuskarsa. Waigawa tayi ta kalli ƙofar shigowa ganin babu kowa yasa tayi saurin durƙusawa har ƙasa tana gaishe dashi. Kallanta yake cike da mamakinta kafin ya miƙa mata hannu alamar ta bashi nata ya ɗago da ita amma taki yadda.
"Bakya tsoron ki ƙone?" Taji ya faɗa cikin tattausar muryarsa.
"Ina son busar da hannu na ne." Jauhar ta faɗa tana fatan ya fita daga kitchen ɗin kafin azo a ganshi a ciki. Kallanta ya yi sosai yana son ya gano wani abun a tattare da ita. Ganin zai bawa kansa wahala yasa shi janye hannun yana zuba su cikin aljihunansa.
"Aikin gidan nan ya miki yawa ke kaɗai Jauhar." Ya faɗa cike da nuna kulawarsa agareta. Lumshe ido tayi tana jin muryarsa tana ratsa mata cikin kai, tunani ta shigayi ina ma ace yana da iko akanta tasan tabbas zai kaita duniyar da tafi ta yaran gidan nan, sai dai sanin hakan bazai faru ba yasa tayi saurin miƙewa dan kada tayi laifi, bata kalleshi ba kanta yana ƙasa tace.
"Zanje na ƙarasa aiki." Tana faɗa ta juya zata fita Suhana da ta shigo kitchen ɗin ganin wanda yake ciki yasa ta saki murmushi tana ƙarasawa wajansa.
"Uncle Irfaan." Tausassar ajiyar zuciya ya sauke bayan ya ɗauke idanuwansa daga kan Jauhar da yabi da kallo har ta fice yana cewa Suhana.
"Doughter kin taso baccin?"
"Eh Uncle Irfaan Ina kwana?"
"Lafiya kalau ina sarkin rigimar gidannan Jannat?"
Yaƙare zancen yana ficewa daga kitchen ɗin ba tare daya tsaya jiran jin amsa daga gareta ba.
#A heart touching story
#Gonar Sharri..
#Hajja ce
#Billy s Fari
#Ƴan Tagwaye