HAJAR

{15..}

by @feenerhfeeche

đź’› HAJAR đź’›


Wani ihu Sa'adatu ta kurma tace "Hajar kashe ni za kiyi?, nifa ƴar uwarki ce", Hajar ta kasa cewa komai sbd kallon da Baba yake mata, Sa'adatu ta miƙe tana dafe bayanta tace "wllh ta karya min ƙashin baya", Baba baice komai ba ya wuce cikin gida, Umma ce tayo hanyar soro sbd ihun da ta jiyo, kaciɓus sukay da Baba tace "sannu da zuwa Malam", Baba yace "yawwa", ya wuce ƙofar ɗakinsa, ya ciro keys a aljihunsa, ya buɗe padlock ɗin ya shiga, Sa'adatu ta cafki wuyar Hajar tana ƙunduma mata ashar, Hajar tace "wllh badai nawa ba, dalla malama sakeni niba jaka bace da zan haɗa ƙashi dake", Sa'adatu tace "keee anƙi a sake kin, kiyi abinda za kiyi", zainab dai sai raba idanu take tana cewa Hajar kyaleta dan Allah, Umma tana zuwa ta tarar da Sa'adatu ta cakumi Hajar, ta fara ƙoƙarin ɓanɓare hannun Sa'adatu dake wuyan Hajar tace "me ya haɗaku?", Sa'adatu ta cakumo Umma sannan ta danna ihu da ƙarfi tace "Maama ku fito, gasu nan sunyi min rubdugu zasu hallakani", Nabilah ce ta fito tana wuwwurga idanu sai kuma ta riƙe baki tace "Maama fito ki gani", Maama tana fitowa ta ɗauki takalmin roba ta rufe Umma da duka, Nabilah da Maimuna kuma suka taru akan Hajar, Sa'adatu kam har lokacin tana riƙe da Umma gam, Hajar ta kufce daga riƙon da Maimuna tayi mata ta gallarawa Sa'adatu cizo a hannun, Sa'adatu ta saki Umma tana lailayo ashar, Zainab dai jikinta sai rawa yake tana kallon ikon Allah, Sabra ta shigo da ɗan gudunta jikinta sanye da Kayan islamiyya, gefe ta koma ta rushe da kuka, hayaniyar da taƙi tsayawa ce tasa Baba ya fito, tsaye yayi yana kallonsu zuciyarsa na tafarfasa, Maimuna da Nabilah suna ganinsa suka saki Hajar suna huci, Baba ya rungume hannu yana kallon yadda Maama ke laftawa Umma takalmi, Maama tana ankara da Baba ta wurgar da takalmin tace "mal baka ga yadda muka fito muka tarar da faɗima da ƴarta sun rufarwa Sa'adatu ba", Umma ta juya ta tsinkawa Hajar marii, Hajar ta riƙe kuncinta ta fashe da kuka, Umma ta daka mata tsawa tace "wuce ɗaki", da sauri Hajar ta shiga ɗaki tana shessheƙa, Sabra tabi bayanta itama tana kukan, Zainab dai ta ɗauki jakarta ta fita daga gidan. Umma ta shiga ɗakinta zuciyarta na tafarfasa, har lokacin Hajar bata dena kuka ba, Umma bata ce mata uffan ba sai haushinta da take ji. kiran sallar magrib akai Hajar ta miƙe da lulu eyes ɗinta da sukay jajur, ta fita tsakar gida tayi alwala ta dawo tayi sallah, bayan ta idar da sallar ta jingina da jikin wardrobe, Umma na zaune kan darduna bayan ta idar da sallah, Mu'azzam yayi sallama ya shigo, ya durƙusa a gaban Umma yace "Umma ina yini", tace "lafiya, an taso lafiya", yace "eh lafiya alhmdllh", tace "toh Allah ya temaka", yace "Ameen", Hajar da dasasshiyar muryarta tace "yaya sannu da dawowa", ya ringa kallonta snn yace "yawwa", ya ciro biscuits daga pocket ɗinsa ya bawa Sabra da take homework, Umma ta kallesa tace "idan ka fita Sallahr isha'i ka tahomin da Ghana most go", yace "tohm, wane size?", tace "medium", yace "tom" ya tashi ya fita. ƙarfe takwas da rabi Mu'azzam ya dawo da Ghana most go a hannunsa, ya miƙawa Umma yace "wnn tayi?", ta karɓa tace "Eh, ga abincinka", ya ɗauki medium warmern abincinsa ya fita, Umma ta ɗauki Ghana most go ɗin ta wurgawa Hajar tace "haɗa kayanki", Hajar ta ringa kallonta bata dai ɗauka ba, a hasale Umma tace "ba kiji me nace miki ba?", Hajar ta janyo Ghana most gon tace "Umma kayan me zan haɗa?", Umma tace "kayan sawarki zaki haɗa", a sanyaye Hajar tace "tom", ta tashi ta buɗe wardrobe side ɗin da kayanta yake, ta ringa ciro kayan tana ɗorawa akan gado, sai kuma ta dawo ta zuba su a Ghana most go, tana gama zubawa ta zuge zip ɗin, Umma ta taso ta kalli wardrobe din tace "waɗan nan kuma fa?", Hajar ta kwaso su ta zuge zip ta zuba, Umma duk tana kallonta, Sabra tace "Umma ina Adda zata?", Umma tace "ba kin gama homewark ɗinki ba, maza hau gado ki kwanta, karna sake jin bakinki", Sabra ta haye gado bata sake magana ba. Hajar dai tayi ta sa ran kiran Baba amma har bacci ɓarawo ya ɗauketa bai kirata ba. ƙarfe bakwai na safe Hajar ta fita tsakar gida tayi brush, tana so ta shiga ta gaishe da Baba amma kuma shakkar hakan take, ɗaki ta koma taga Umma tana shafawa Sabra Vaseline, tana gama shafa mata ta saka uniform ɗinta, Umma tace "ki shiga ki gaishe da Baba kafin ki tafi makarantar", Sabra ta goya jakarta tace "tom" ta fita, sai kuma gata ta dawo tace "Baban bacci yake", Umma dai tayi mamaki sbd da wuya ne kaga Baba yana baccin safe, Umma tace "toh maza ki tafi karki makara". Sabra tayi tafiyarta makaranta, Hajar tace "Umma ina wake yake zan tsince", Umma tace "A'a ba tsintar wake za kiyi ba, zoki shirya fita za muyi", Hajar dai zuciyarta bata yarda da fitar nan ba, haka ta shirya a sanyaye, Umma ta zauna gefen gado bayan ta saka Hijab dinta tace "kiyi sauri kar ki ɓatamin lokaci", Umma ta ɗauki wayarta tayi kira, wayar kare a kunnenta tace "Jamila insha Allah gani nan zuwa gidanki", bayan few seconds Umma ta katse kiran tana kallon Hajar da ta taƙune fuska, Umma ta miƙe ta ɗauki ƴar purse ɗinta tace "wuce muje", Hajar tace "tom" ta wuce zata fita, Umma ta dakatar da ita tace "zo ki ɗauki kayanki da kika haɗa", Hajar ta kalli Umma ganin babu sauƙi a fuskarta ta fara jan Ghana most go ɗin data fi ƙarfinta, Umma ta rufe ɗakin da padlock, ruwa ya cicciko idanun Hajar, Umma na ankare da ita tace "muje mana", ta goge hawayen da ya zubo mata tace "Umma ban gaisa da Baba ba", Umma tace "bacci yake, ko baki ji abinda Sabra ta faɗa ba, ki ɗauki kayanki ki wuce malama, kina ɓatamin lokaci", Hajar ta fara kuka a hankali tace "bazan iya ɗauka ba", Umma ta haɗe rai tace "ƙoƙarta ki kaisu soro", ta fara jan kayan a hankali, Nabilah da ta fito bayi ta bita da harara tana taɓe baki. bayan Hajar ta kai kayan soro Umma ta saka almajiri ya ɗauka ya fitar musu dasu bakin titi, Umma ta tari Napep, ta kalli Hajar tace "shiga", bayan me napep ya saka Ghana most gon a boot Umma ma ta shiga, few minutes suka isa gidan Anty Jamila, Hajar ta ɗan ji relief ganin inda suka zo, Bayan sun shiga gidan, Hajar ta ajiye kayanta a ƙofar palour, Umma ta zauna akan kujera suna gaisawa da Anty Jamila, Hajar ta zauna kan carpet tace "Anty ina kwana", Anty Jamila tace "lafiya lou Hajar", Umma tace "yara sun tafi makaranta ko?", Anty tace "Eh suna makaranta", Umma tace "Jamila dan Allah wata alfarma nake nema a wajenki", Anty tace "tom Adda", Umma tace "dan Allah ina son Hajara ta zauna a wajenki na ɗan lokaci", Anty tace "Adda wnn ai ba damuwa bace ni me riƙe Hajara ce", Hajar dai duk tana jinsu, Anty ta kalli Hajar tace "tashi ki shigo da kayanki ki kai ɗakinsu Hafsa", Hajar ta miƙe a sanyaye wani kuka yana taho mata, yanzu anan Umma zata barta knn, tasan dai Anty bata da wata damuwa, amma ita tanada kwakwar Uwa, ko kaɗan bata so tayi nesa da Umma shiyasa ma babu inda take zuwa. Anty tabi Hajar da kallo, Umma tace "tashin hankali akai jiya a gidan, kuma Hajar ce a gaba gaba wajen assasa hakan", Anty tace "garin yaya?", Umma ta taɓe baki ta gaya ma Anty iya abinda ta sani, Anty tace "Subhanallah, gaskiya Adda haƙurin ki yayi yawa, shine kika tsaya kishiya ta ringa dukanki da takalmi", Umma tayi ajiyar zuciya tace "duk Hajara ce ta jawo, nayi nayi da ita ta dena shiga harkar yaran can amma taƙi ji", Anty tace "toh ai baki san me ya haɗasu ba da har ta biye mata, kika sani cutar da ita tazo yi ita kuma tayi ƙoƙarin kare kanta", Umma ta miƙe tace "da tayi haƙuri ai da yafi, ba zama zanyi ba, daman cewa nai bari na kawota da kaina", Anty ta raka Umma har ƙofar gida, Hajar na fitowa daga ɗakinsu Hafsa taga babu kowa a palour, ai kam ta fita waje da Sauri, har Umma ta tsare nepep tana shirin shiga, Hajar ta riƙe ƙarfen Napep ɗin tace "Umma dan girman Allah kiyi haƙuri..", Umma ta harɗe rai sai kace bata jin zafin rabuwa da ƴar tata tace "ai bakya son zama dani Hajara", Umma na faɗin haka ta shige napep ɗin, mai nepep ya burgi babur ɗinsa, Hajar ta rufe fuskarta da hijab tana kuka ta koma gida, Anty da take bakin gate ta bata hanya ta wuce snn ta rufe ƙofa. Anty dai bata ce mata komai ba, Hajar taci kukanta ta more snn tayi shiru, Anty ta fito daga ɗakinta tace "kinci abinci ma kuwa?", Hajar ta girgiza kai tace "na ƙoshi", Anty tace "shknn" ta shiga kitchen. Umma tana komawa gida ta leƙa ɗakin Baba, a kwance ta ganshi har lokacin, ta tsaya tana kallonsa na 5second snn ta juya, keys ta ciro daga ƴar purse ɗinta ta buɗe ɗakinta, Hijab kawai ta cire ta fito tsakar gida ta fara aikace-aikace, da Hajar tana nan da tuni ta gama, Umma ta dasa kujera a tsakar gida ta zauna tana tsince wake, Maama ta fito da ɗaurin ƙirji da doya guda ɗaya hannunta, zama tayi ta fara yanka doyar, tana yankawa taga doyar gaba ɗayanta ta ruɓe, ta ja wani dogon tsaki ta tashi ta shiga ɗaki ta ɗakko wata, itama dai tana yankawa ta ganta ta ruɓe, Maama tayi wurgi da wuƙar hannunta ta miƙe ta shiga ɗaki, Umma dai tabi ruɓaɓɓiyar doyar da ke zube anan tsakar gida da kallo ta girgiza kai, Umma tana ta kallon ɗakin Baba taga ya fito amma shiru, a hankali tace "A'a wai yau malam lfy yake wnn baccin", ta janyo latsinetarta ta duba lokaci taga har tara da rabi ta gota, miƙewa tayi ta shiga ɗakin Baba, tayi sallama yafi sau uku amma shiru, ta ƙarasa inda yake kwance, sai taga nunfashinsa ya canza, ta taɓa goshin taji kamar tasa akan wuta sbd zafi, ta ɗan jijjigasa tace "malam!!, malam!, malam".............✍️