HAJAR

{16..}

by @feenerhfeeche

💛 HAJAR 💛


Umma ganin Baba bai amsa ba, ga kuma yadda numfashinsa yake fita sama sama yasa ta fita tsakar gida da sauri, salati da sallallami ta zabga snn tace "Rabi ku fito malam ba lafiya", Maama tana ɗaki tana jinta amma tayi mursisi, ita baƙin cikin doyarta da ta ruɓe ne ya turnuƙeta, ƴaƴanta kam suna kwance suna baccin asara, Nabilah ce kawai tayi sallar asuba itama da rana gatsal-gatsal, Umma ta matsa bakin ƙofar ɗakin Maama tace "ku fito mu kai malam asibiti, bashi da lfy", Maama ta gyara ɗaurin ƙirjinta ta fito ta yiwa Umma kallon hadarin kaji tace "Malama lfy kike mana ihu sai kace daga dawanau", Umma dai a rikice take tace "malam nefa ba lafiya", Maama ta tafa hannaye tace "innalillah wa'inna ilayhirraji'un, kika ce kin kashe malam", sai kuma ta rushe da kuka, Umma da take a rikice saida tayi sak jin abinda Maama ta faɗa, Maama ta koma ɗaki cikin sauri ta shiga ɗalawa ƴaƴanta duka a cinya, faɗi take "ƴaƴan nan ku tashi, faɗima ta kashe muku uba", Nabilah da ita baccin nata beyi nauyi ba ta miƙe tana zabga hamma, Maama tace "tashi ƴan uwanki, faɗima ta kashe malam", Nabilah ta zaro ido ta dafe ƙirji tace "Baba". Umma dai tinda taga haukan da Maama take shirin ƙullawa bata sake bi takanta ba, wayarta ta ɗauka ta kira Mu'azzam, tana fara ringing ya ɗauka, Umma tace "Mu'azzam kana ina?", yace "ina wajen mai shayi", tace "taho gida yanzun nan", yace "Tom", ta katse wayar ta ɗauki hijab ɗinta ta fita, bayan minti biyar ta dawo tare da Munkaila makwabcinsu, Umma ta nuna ɗakin Baba tace "Bismillah". Munkaila ya shiga ɗakin tabi bayansa. Maama da ƴaƴanta sun rufa akan Baba sai kuka suke, Nabilah tace "wllh ai na gansu da sassafe da wata ƙatuwar bakko zasu gudu", Maama ta fyace majina tace "Ta kashe min miji", Umma ta harɗe rai tace "kiga mutuwa akanki, ni ba ce miki nayi ya mutu ba, dan Allah ku fita kun cika masa kunne da haushi, karku ƙara masa zafin ciwo", Maama ta wangale baki tace "haushi fa kika ce faɗima?", Umma ta bawa shara ajiyarta ta dubi Munkaila tace "dan Allah Munkaila temaka min mu fita dashi", Munkaila da Umma suka fito da Baba tsakar gida, a lokacin kuma Mu'azzam ya shigo, Umma tace masa ya taro napep, Ta uwa ta uba Maama ta ringa zage Umma tamkar zogale, Umma dai bata biye mata ba, da taimakon Munkaila aka fita da Baba aka sakasa a Napep ɗinda Mu'azzam ya taro, Munkaila da Mu'azzam ne riƙe da Baba, Umma ta tari wani Napep din tabi bayansu zuwa asibiti, da yake ranar Monday ne akwai doctors, Emergency aka wuce da Baba, doctor yana dubasa ya rubuta allurai da za a masa a takarda, Mu'azzam ya amshi takardar yaje ya siyo da ƴan kuɗin da suke aljihunsa, Saida Baba ya zama stable snn aka basa gado sbd kwantar dashi akai, blood pressure dinsa ne yayi mugun high gashi kuma akwai heart attack da ake zargin ya samu, Umma dai bata kira kowa daga dangin Baba ba sbd ba ƴan Kano bane, ainahin garinsu Baba Yola, Umma tana zaune gefen gadon Baba da yake bacci sbd alluran da akay masa Mu'azzam ya matso kusa da ita da takarda a hannunsa, a hankali yace "Umma kinga likita ya rubuta tests da drugs da kuma allurai, kuɗin hannuna bazasu isa ba", tace "tom, ka kira Naseer ka gaya masa", yace "bari na kira saina baki wayar kiyi masa magana", ta gyaɗa kai, ya ciro wayarsa daga aljihu ya kira Naseer, Naseer na ɗagawa Mu'azzam yace "Yaya ga Umma za kuyi magana", Umma ta karɓi wayar ta kara a kunne, Naseer yace "ina kwana Umma", tace "lafiya lou, ya aiki?", yace "alhmdllh", tace "toh Allah ya temaka, Baba ne aka kawosa asibiti ba lfy, toh kuɗin hannun mu sun yanke, gashi kuma ba a gama siyan drugs ba", yace "me yake damunsa?", tace "jininsa ne ya hau", yace "toh Allah ya basa lafiya, Insha Allah gobe zan dawo, yanzu dai Mu'azzam ya turomin da account number ɗinsa saina turo muku kuɗi", tace "toh shknn". Mu'azzam ya turawa Naseer account number ɗinsa, babu jimawa saiga alert ya shigo wayar na kudin da Naseer ya turo. Munkaila ne ya shigo ward ɗin ya yiwa Umma sallama, Umma tayi masa godiya Sosai.


★Through out the day Hajar was so Moody, har saida su Hafsa suka dawo daga schl snn ta ɗan sake, Hafsa ta fige hijab ɗin jikinta na uniform tana kallon Hajar tace "yau sai ga ki a gidan nan", Hajar tace "Eh mna", Hafsa tace "kice ƴan ziyarar sun motsa ta kanmu", Hajar ta nasa mata harara tace "kya ji dashi, naga kema ba zumuncin kike ba", Hafsa tace "Tahfeez", Hajar tace "Tahfeez ɗin ce ta hanaki fita knn?", Hafsa tace "yesso, bari na cire uniform" da haka ta shiga ɗakinsu, saida tayi wanka snn ta fito, Hajar ta ɗaga kai ta kalleta, Hafsa tace "ina Anty ne?", Hajar tace "tana ɗakinta", Hafsa tace "kinci abinci?", Hajar ta girgiza mata kai, Hafsa ta wuce hanyar kitchen tace "bari na zubo mana", ta zubo musu abincin a plate ɗaya, ta kawo ta ajiye akan carpet ta koma kitchen ta ɗakko musu pure water da gaseous drink, ta zauna ta janyo plate ɗin abincin ta saka spoon tace "toh sakko hajiya ta", Hajar ta zamo daga kan kujerar da take ta ɗauki spoon ta fara cin abincin, Anty ce ta fito daga corridorn ɗakinta, zama tayi a palourn tace "yanzu kinga damar cin abincin knn?", Hajar tace "daman Hafsa nake jira". suna gama cin abincin Hajar ta ɗauki plate ɗin ta kai kitchen ta dawo ta zauna tana shan drink. da yamma Anty ta shiga room ɗinsu Hafsa, Hafsa na latsa wayarta, Hajar kuma na durƙushe gaban Ghana most go ɗin kayanta, Anty tace "Hafsa ki bata space a press ɗinku ta jera kayanta", Hafsa tace "tom, wai daman da gaske kwana za tay?", Anty tace "kun shigo ɗaki kunyi gurgumi sai kace wasu ƴan matan Amarya, wa zai girka muku abincin dare?", Hafsa tace "wai da sai daren sai muyi jollof spaghetti", Anty tace "A'a tuwo zaku yi, Hajar tayi tuwo ke kiyi dry okra soup", Hafsa tace "tom, semovita ko?", Anty tace "Eh" ta fita ɗakin. Hajar ce ta haɗa duka tayi, da tuwan da miyar duk ita tayi su, kuma kafin a kira Sallahr magrib ta gama, Hafsa aikin fito mata da ingredients da jajjage kawai tayi, bayan sun idar da sallahr magrib sukay zamansu a palour, Abdallah ne ya shigo palourn first born ɗin Anty, ya kalli Hafsa da take bawa Hajar lbri yace "an gama dinner?", Hafsa tace "Eh", ya shiga kitchen, sai kuma ya fito empty hand, ya haɗe rai yace "wai tuwo aka dafa?", Hafsa tace "Eh", yayi slight hiss ya ɗauki remote ya canza channel daga American zuwa channel ɗin da ake ball, ya zauna kan kujera, Hafsa ta kallesa tace "ka turo min 2GB, yanzu na tashi na dafa maka indomie sharp sharp", yace "toh sleepy thief, saidai 1GB", tace "Eh naji, turo min naga dahir", ya ciro wayarsa ya tura mata Data 1GB, ta kalli wayarta da ke hannun kujera tace "yawwa sun shigo, Hajar ina zuwa", ta miƙe ta shiga kitchen da wayarta a hannu, Abdallah yace "Hajar ki koyamin yadda ake dafa abar nan mna, waccan muguwar taƙi koyan kullum sai taci kuɗina kafin ta dafamin", Hajar tayi murmushi tace "tom shknn, karka damu, kafin nabar gidan nan saika zama expert wajen dahuwar indomie", yace "yawwa, ina autar Umma?". tace "Sabra, tana nan lfy". Anty ta fito daga ɗakinta itama ta zauna tana kallon TV tace "meye wnn?, Abdallah idan za kayi kallon Ball dinka ka ringa tafiya can ɗakinka, kazo nan ka cika mu da hayaniya", yace "toh" sai kuma ya miƙe ya shiga kitchen, Hafsa ta jingina da cabinet sai latsa waya take, ga tukunya nan akan gas wacca take dafa indomien, yace "ai daman na sani, kiyi sauri malama, kin tsaya danna waya, I'm hungry", tace "tafa dahu, yanzu zan kawo maka", ya miƙa mata plate yace "juye min haka", ta amshi plate ɗin ta kashe gas, ta kama plastic handle ɗin tukunyar ta juye masa, wayarta ta ɗauka ta fita, saida ya ɗauki drink a fridge snn ya fita da plate ɗinsa na indomie, room ɗinsa ya wuce direct. Humaira ce ta rugo da gudu ta miƙawa Anty wayar hannunta tace "Ana kira", Anty tayi saurin ɗagawa ganin wacca take kiran nata, Hajar ta ringa kallonta sbd ta fahimci da wa take waya, Anty tace "toh Allah ya basa lfy, ya sa kaffara ne" ta katse kiran tana kallon Hajar da ta kura mata na mujiya, washe gari da misalin ƙarfe 11 na safe Hajar ta fito wanka, ta shafa man da ta gani kan mirror snn ta saka doguwar rigar atamfa, tana fita palour ta ga Anty ta fito daga kitchen da basket mai ɗauke da warmers, daman tin ɗazu suka gaisa, Hajar tace "Anty me za ai?", Anty tace "ba komai Hajar, ki ɗakko gyalenki fita za muyi, za muje asibiti mu duba Baba", zuciyarta ce buga da ƙarfi tace "Baban ne bashi da lfy, dan Allah Anty me yake damunsa?", Anty tace "yafa ji sauƙi, kawai dai jininsa ne ya hau, kuma yanzu ma sallamarsa za aii", Hajar ta sauke ajiyar zuciya ta shiga ɗaki, Ghana most go ɗinta ta buɗe ta ɗakko ironed Hijab maroon, tare da wayarta da tin jiya da bata bi takanta ba, hijab ɗin ta zumbula ta fito palour ta zauna tana jiran Anty, babu jimawa saiga Antyn nan ta fito daga room ɗinta. Hajar ta miƙe da sauri, Anty ta kalleta tace "toh ɗauki abincin muje", Hajar ta ɗauki basket ɗin ta fita compound, saida Anty ta rufe ko ina snn ta fito, Anty ta rufe ƙofar gate bayan sun fito ta zuba keys ɗin a hand bag, Hajar dai ta ƙagu kafin ma Anty ta gama rufe gida harta tsare Napep. Anty ta gayawa mai Napep asibitin da zai kaisu snn ta shiga, Hajar ma ta shiga. hankalin Hajar bai kwanta ba saida taga sun iso asibitin, Anty ta kira Umma a waya tayi mata kwatancen ward ɗin da aka kwantar da Baba, Anty ce ta fara shiga ward ɗin snn Hajar dake biye da ita, gadon da yake kusa da ƙofa anan Baba yake, Umma Maama sai Nabilah ne a asibitin, Anty ko kallon direction dinda Maama take ba tayi ba ta matsa kusa da Umma da take bawa Baba Youghurt, Hajar ta ajiye basket ɗin hannunta ta isa kusa da Baba da yake jingine da allon gado, a sanyaye tace "Baba sannu, Allah ya baka lafiya", Baba ya gyaɗa mata kai yace "Ameen Hajara", Hajar ta kalli Umma tace "Umma ina kwana, ya me jiki?", keenly Umma tace "lfy, jiki da sauqi", Anty ma suka gaisa da Baba da kuma Umma, saida Anty ta zauna snn tace "sannu Rabii, ya me jiki?", Maama ta taɓe baki ta juyar da kai tana girgiza ƙafa, Anty a zuciyarta tace kinyi da ƴar halak, Umma ta kalli Hajar tace "Hajara idan kika fita ɗakin nan saiki bi hannun hagu, idan kika bi hagu saiki tambayi Nurse station, saiki tambayi Nurse ɗin wajen ya baki takardar test ki kawomin, tin ɗazu yace aje a ƙarba sbd dashi za mu ga likita anjima", Hajar ta miƙe tace "tom", walking slowly ta fita daga ward ɗin. perfectly tabi kwatance da Umma tay mata ta isa Nurse station, Sallama ta yiwa Nurse ɗin dake zaune kan white plastic chair tace "nazo amsar test ne", yace "name?", Hajar tace "Adam Muhd Gini", Nurse ɗin yace "Okay" ya buɗe wata drawer ya ciro paper ya miƙa mata, Hajar ta amshi paper snn ta juya tabar wajen da papern riƙe a hannunta.


★ƙarfe tara da rabi Nurain ya fito daga room ɗinsa, car key da briefcase ne riƙe a hannunsa, down stairs ya sauka, Noor ya tarar a kan dining tana breakfast, ta yi shirin fita schl shine ta tsaya yin breakfast, Noor ta kallesa tace "good morning", yace "morning lil sis", tace "ga breakfast", yace "enjoy it alone, idan kin gama help me with a cup of coffee", tace "Tom", yace "zan shiga wajen Abba, make it kafin na dawo", ya ajiye briefcase ɗin hannunsa a kan kujera snn ya wuce part ɗin Abbansa, da sallama Nurain ya murɗa tsadadden handle ɗin ƙofar palourn kana ya shiga, ya ji daɗin ganin Mami itama a palourn tare da Abba, kan carpet ya zauna ya gaishesu, Abba ya amsa yana nuna masa kujara yace "sit", Nurain ya koma kan kujera ya zauna yana shafa kansa, a zuciyarsa addu'a yake Allah yasa parent ɗinsa su yarda da maganar da yazo musu da ita yanzu, Abba yace "is there any problem Uthman?", Nurain yace "yeah, but it is not a problem", Abba yace "then?", Mami ta ringa kallon Nurain tana jiran taji abinda zai ce, Calmly Nurain ya fara magana yace "Akan maganar course ɗin da 1yr back nace zanyi a India sai kuma na canza decision, yanzu kuma am ready to take it if i get your approval", Abba yace "for how long?", Nurain yace "six to eight months", da wani expression Mami ta kalli Nurain sai kuma ta girgiza kai tace "No", Abba ya kalleta yace "why ?", Mami tace "sai ya bar aikinsa da business ɗinsa da ya fara kafasa yanzu ya tafi wani karatu, gaskiya nidae bada yawuna ba", Abba yace "wnn ma ai zaiyi boosting qualifications ɗinsa snn kuma he need a rest, kinsan da hakan ko?", Mami ta kalli Nurain tace "tom shknn Allah ya bada sa'a", Nurain yace "Ameen, nagode Mami", Abba yace "saika fara shirye-shirye", Nurain yace "yeah, idan komai ya tafi normal ina jin ma ranar Friday zan tafi", Mami tace "this Friday?", Nurain yace "yeah", Abba yace "Ohk, Allah ya bada sa'a", Nurain yace "Ameen, yanzu ma zan wuce hospital nayi signing". Abba ya gyaɗa kai, Nurain yayi musu sallama ya fita. Main palour ya koma, a lokacin Noor ta fito da Mug ɗin coffeen da ta haɗa masa, tace "in time?" ta miƙa masa, ya karɓa yace "thank you" ya zauna kan kujera kusa da briefcase ɗinsa ya fara sipping, Noor ta rataya jakarta zata fita dan already driver na jiranta, yace "muga wayarki", tayi sak sai kuma ta zuge bag ɗinta ta ɗakko wayarta ta miƙa masa, jujjuyata kawai yayi bai kunna ba ya mayar mata da kayarta. ta mayar da ita bag snn tayi masa sallama ta fita. saida ya gama shan coffeen snn ya ɗauki car key da briefcase ɗinsa ya fita compound, parking space ya nufa ya buɗe motarsa, bayan yayi warming ya fita daga compound ɗin ya hau kwaltar street ɗin gidansu dake a mulmule, with a minimum speed ya isa Hospital, wajen da aka tanada dominsa na parking anan ya paka motarsa, ya kashe motar ya fito hannunsa riƙe da briefcase, Majestically yake tafiya har yaje office ɗinsa, secretaryn sa Halima ta miƙe cike da girmamawa tace "welcome Dr, good morning", yace "Morning" ya wuce katafaren office ɗinsa, ajiyar zuciya ya sauke yana ƙarewa Office ɗin kallo sai kuma ya buɗe briefcase ɗin da ya shigo da ita ya ɗakko wani file, da file ɗin a hannunsa ya fito, Haleema ta miƙe da sauri tace "Sir aike ne?", yace "No, continue what you're doing", ya fita. wani corridor yabi yana shan kwana sukay karo da juna, kanta ya bugu da ƙirjinsa ta shaƙi ƙamshisa, hannunta kuma mai riƙe da papern da ta kwarɓo wajen Nurse ya bige file ɗin hannunsa, a take takardun file ɗin suka baje a ƙasa, itama takardar hannunta ta faɗa cikin takardun, Hajar ta ɗago da nufin basa haƙuri amma suna yin ido huɗu saita murtuke fuska taja da baya..........✍️