GONAR SHARRI...

BABI N BIYU

by @billysfari

GS 2.


Da sauri Jauhar ta nufi cikin ɗakin tana gudan karta sakeyin wani laifin, sai dai duk da hakan sai da ta tarar da wani ɓacin ran dan tana shiga ta tarar da Hajja Maimoon tana yiwa Jannat tausa da kanta sai wani shafa mata gashi take tana yi mata hira. Nan da nan Jauhar taji wani abu ya taso mata tun daga ƙasan zuciyarta har saman harshenta, tsayawa kawai tayi tana kallon su kuka na shirin zuwa mata. Idan tace zuciyarta bata sosu ba tabbas tayi ƙarya, tana son ganin itama ana treating ɗinta kamar yadda ake yiwa ƴaƴa sai dai bata da wannan gatan, gatan ta ɗaya shine ta zauna a gidan nan taci gaba da bauta kamar yadda ta taso tun tana ƴar ƙaramar yarinya. Da sauri ta ƙarasa wajan ta durƙusa saitin kafafun Jannat tana ƙoƙarin yin abinda aka umarce ta, jikinta yana kyarma zuciyarya na rawa tace. 


"Mommy kawo naci gaba da yi mata." Hajja Maimoon ta watsa mata wani banzan kallo ranta a matukar ɓace tace. 


"Menace miki akan kirana Mommy?" Tasa hannu ta shaƙu wuyan Jauhar kamar zata kasheta dan ta tsani taji itama ta kirata da Mommy ji takeyi kamar ta kasheta. Jauhar ta shiga kakarin amai tana kuma ƙoƙarin kwacewa amma ta kasa. Hajja Maimoon kamar zata haɗiye zuciya tsabar ɓacin rai da yarinyar ke sakata ta, da kallon ki shiga taitayinki ta bita tana faɗin. 


"Idan na sake jin wannan ƙazamin bakin naki ya kuma kirana da Mommy sai na fasa shi, sannan ki tashi kije kitchen Jannat zata wainar fulawa ta man gyaɗa." Jauhar ta mike jiki babu kwari tana haɗiye kukan da yake neman kwace mata. Idan tace bata nadamar zama tare da mutanan gidan nan tayi ƙarya, ji takeyi gwara rayuwar da ta baro dan ko babu komai wahalar da take sha a nan bata kai tacan ba. Kafin zuwanta gidan takan samu hutu tayi bacci da sauran wasu abubuwan na rayuwarta da takeyi. Amma nan ta rasa a wane situation zata saka kanta. Sohana ce tare da Uncle Irfaan a tsaye bakin kitchen ɗin hakan yasa ta kasa ƙarasawa, bata da matsala da Irfaan amma idan taje zata ratsa su tasan tabbas sai Sohana tayi mata abinda zai taɓa mata zuwa. Gefe guda kuma tsoran kar lokacin kiranta ta kawo wainar ya yi take, idan tace bata gama ba case, idan tane farawarta kenan shime ya zama case. Irfaan yana hangota ya kirata ta isa wajan cikin sanyin jiki. Shi fa yana mamakin yadda yarinyar take gidan nan amma bata gaba bata baya kullum jiya iyau, idan ya lura ma kamar kayanta kala uku ne dan sune zagaka tana ta sakawa. Sai da ta ƙaraso wajan ta durkusa har kasa kanta yana kallan tiles ɗin dake malale a wajan, ji tayi yana yiwa Sohana magana. 


"Wai babu kayan da zaku iya bawa Jauhar ne a cikin naku?" Kallonta Sohana tayi kafin tace,


"Mommy ce take kyauta da tsofaffin kayanmu idan muka cire." 


"To me yasa ba'a bata? Gida bai ƙoshi ba za'a kai waje? Ko kece bakya so Jauhar?" Yayi maganar yana kallon Jauhar da har lokacin kanta ke ƙasa. Da sauri ta girgiza masa kai, ita gaba ɗaya wannan tsare tan da yayi ba ƙaramin ɗaga mata hankali yake yi ba, sam zuciyarya taki nutsuwa a wajan bare har ta fahimci irin karamcin da Irfaan ɗin yake shirin yi mata. Ganin kamar uzuri takeson yi a kitchen ɗin yasa ya bata hanyar da zata wuce, Jauhar tamiƙe jiki a sanyaye ta shige cikin kitchen ɗin ta soma haɗa kayan haɗin wainar fulawa ɗin wacce gabaki ɗaya hankalinta yana kan ganin ta shiga ta fara. Shi kuma palour suka nemi waje suka zauna da Sohana suna cigaba da firarsu wanda ko mintuna goma ba'a yi ba ta ƙwalawa Jauhar ɗin da har ta soma soya wainar fulawar kira. Da sauri Jauhar tafito taƙaraso wajen tana ɗan sinne kai take cewa.


"Gani." Ba tare da Sohana takalleta ba tace, 


"Ki wanko mana fruit ki kawo mana ni da Uncle." Jin wani aikin take son bata yasa kirjin Jauhar ya shiga bugawa, ta rasa me suka ɗauketa tamkar wata inji kowa ya tashi bata aiki sai ya rufe ido ya kasa hango wanda takeyi a lokacin. Duk da tasan abinda zata furta bai zama lallai a karɓi uzurin nata ba, duk da hakan ta daure tace, 


"Amma Jannat nake soyawa wainar fulawa kada ta ƙone, bari na ɗan ƙarasa sai na wanko nakawo maku." Da sauri Suhana tayi mata wani mugun kallo tace,


"Mene? Ni zan saki aiki ki tsaya kawomun excuse? Ke wace? har kin isa Jauhar?"


"Kiyi haƙuri." Jauhar tafaɗa tana juyawa tabar wajen. Suhana ta bita da tsaki ranta a ɓace. Kallonta Uncle Irfaan yai yace,


"Sohana me yasa ke bazaki tashi kije ki wanko fruit ɗin kisha ba idan kina ra'ayin sha? ko ni kinji nace miki inada ra'ayi ne? Wai neyasa bazaku ji tausayin yarinyar nan ba Sohana? Ko kun manta kuma mata ne za'a iya yi muku duk abinda kuka yimata ko yiwa ƴaƴan ku?."


"Tufar da yawun bakinka Irfaan, in sha Allah hakan bazata faru ga yarana ba, ko ka manta ba matsayinsu ɗaya da ita ba? Sannan kuma bazasu taɓa zama ɗaya ba saboda su suna da gata." Irfan yajiyo muryar Hajja Maimoon dake sakkowa daga stairs riƙe da hannun Jannat, Hajja Maimoon na faɗa ta bayansa. Juyowa yai yana kallonsu fuskarsa ba yabo ba fallasa har suka ƙarasa sakkowa daga stairs ɗin suka ƙaraso cikin palourn, Jannat ta taho da sauri tana shigewa jikinsa tana faɗin, 


"Uncle Irfaan welcome yaushe kazo ban sani ba?" Sai da ya saki murmushi yana riƙe da ita yake cewa, 


"Taya zaki sani kina can kina zubawa Mommynki sangarta, kar dai nace sai yanzu kika tashi daga baccin?" Dariya ta sakar masa tare da kallon Mommy dake zaune ta ɗora ƙafa ɗaya akan ɗaya tana wurgawa Irfaan ɗin wani mugun kallo mai cike da tsana wanda ba kowa ne zai iya fahimtar hakan ba. 


"Mommy wai yanzu na tashi?" Jannat tafaɗa aɗan shagwaɓe tana turo baki. Murmushi Mommy ta saki tana cewa,


"Ƙyale Uncle kin riga kowa tashi a gidan nan ciki kuwa har dashi." Dai-dai lokacin Jauhar tafito ɗauke da wani kyakkyawan tray daya ƙawatu da kalar gold sai ƙyalli yakeyi da fruit aciki ta kawo gaban Suhana ta ajiye ta juya gabanta na wani irin faɗuwa ganin Mommy da Jannat a wajen kasancewar bata kammala aikin da suka saka ta ba, 


"Ke!" Taji Muryar Jannat tafaɗa cikin tsiwa. Jauhar tayi saurin rufe idanuwanta ɓacin rai yana sake wanzuwa cikin zuciyarta, 


"Ina wainar fulawata baki soya mun ba ko?" Sanin Mommy na wajan, sannan Sohana ma tana nan yasa Jauhar sanyaya murya tace. 


"Kiyi haƙuri saura kaɗan naƙarasa." Jauhar tabata amsa cikin marairaicewa tamkar mai yin magana da babba lokacin datake juyowa. Kuka Jannat ta saka tana buga ƙafafuwan ta nufi wajen Mommyn tasu tana cewa, 


"Mommy zan mutu yunwa fa nake ji." Wata uwar tsawa Mommyn ta dakawa Jauhar da tayi tsaye tana kallon ikon Allah. Hajja Maimoon ranta a ɓace tare da jan Jannat ajiki take cewa, 


"Uwar me kika tsaya yi da bazaki je ki ƙarasa ba yanzunnan ki kawo mata?" Sum-sum Jauhar taja ƙafafuwanta tabar wajen tana share ƙwallor da suka zubo mata, Mommy tayi tsaki tana cewa, 


"Shashashar yarinya kawai, sorry my Baby yanzunan zata kawo miki kici kinji ko?" Taƙarasa zancen tana ɗago fuskar Jannat ɗin tana share mata ƙwallar da ta fara ɓata mata fuska. Ƴar ajiyar zuciya Irfan ya sauke tare da kallon Mommy yace, 


"Abunda yaran nan naki sukeyi yayi yawa fa, ke Sohana ina jin ke kika sata aiki amma kina ji anayi mata faɗa bazaki iya faɗar ke kika sa ta ajiye aikin da aka sakata ba tayi naki?" Yayi maganar yana kallon Sohana da take turo baki. 


"Look Irfaan koma meye yakamata tasan aikinta da yadda zata iya aiwatar da kowane aka sata cikin lokaci, zata zauna gidan ubansu ne tana ci da sha mai kyau taki yimusu abinda suke buƙata? Impossible dole takoyi yin komai in time yadda ake buƙata koda kuwa duk yaran gidan sun sakata yin wani abun." Mamaki ya kusa kashe Irfaan jin abinda matar Yayan nashi take faɗa. Cike da ɗaurewar kai na kalaman ta yake cewa. 


"Amma aikin ne naga kamar yayi mata yawa, suma mata ne is good ace suna koyar yin wasu abubuwan da kansu ba tare da anyi musu ba." Ran Hajja Maimoon ya soma ɓaci da yadda Irfaan ke nuna mata kamar bata iya wasu abubuwan ba, cike da isa da kuma iko take cewa. 


"Me kake so kace min ne Irfaan? Nabar yaran nawa marayun Allah su shiga kitchen saboda ita? Na kalli Habiby da wace fuska kenan bayan ga wacce ke aikin? Impossible wallahi dole kafahimci wutsiyar raƙumi tayi nesa da ƙasa domin akwai tarin banbanci sosai tsakaninsu da ita."


"Allah ya kyauta, amma hakan ba so bane, dan na tabbata idan mahaifiyarsu na raye wannan iskancin baza suyi ba kuma ta ɗaure musu ƙugun yin rashin mutunci." 


Irfan yafaɗa yana jin ba daɗi aransa tare da miƙewa tsaye, hakan yayi daidai da fitowar Jauhar ɗauke da tray data ɗora plate ɗin wainar fulawa akai tare da yaji agefe da kayan miya da albasa data yayyanka akai. Cike da tausayinta yabita da kallo har ta ajiye plate ɗin akan side table ta janyoshi zuwa gaban Jannat dake zaune kusa da Hajja Maimoon ɗin da kalaman Irfan ɗin suka gama ƙona mata zuciya ta cika tayi fam kamar zata fashe. Yana ƙoƙarin fita muryarta ta dakatar dashi da take cewa, 


"Me kace Irfan? Da mahaifiyarsu na raye kenan so kake ka nuna musu duk abinda nake musu bana sonsu tunda bani na haifesu ba?." Kamar ba zai waigo ba sai yaji yana so ya bata amsa, dan haka ya ɗan juyo yana kallanta yadda zatafi fahimtarsa yace, 


"Ko ɗaya ban faɗi haka ba, yadda kike kula dasu tare da basu gata nasan zai yi wahala yaya yasamu matar da zatayi musu hakan, sannan kar hakan yasa kiriƙa mantawa da cewa ƴaƴa mata ne su kuma gidan wani zasu je, bawai ki ɗaure musu ƙugun ba ana wulakanta yarinya tare da bautar da ita sai wacce a girme sun girmeta idan aka ɗauke Jannat." Sallamar Yayan nasa Alhaji Sha'aban daya shigo cikin palourn yasa yakasa ƙarasa maganarsa haɗe da ɗan rissinar dakai yana yi masa sannu da shigowa. Kukan da yaji Hajja Maimoon tafashe dashi ya sashi kasa amsa gaisuwar ɗan uwan nasa tare da ƙarasawa ciki wajenta da sauri ya janyota zuwa jikinsa yana kallon Irfan ɗin yake cewa,


"Irfaan meke faruwa? Me akayi take kuka haka?" Har Irfaan ya buɗe baki zaiyi magana yaji Jannat na cewa,


"Dady Uncle ne yasa Mommy kuka wai ba itace ta haife mu ba shi yasa bata samu aiki."


"What?" Alhaji Sha'aban yafaɗa da karfi yana ɗago kansa daga kallon Jannat da yakeyi ya maida wajan Irfaan. Ransa a ɗan ɓace yake magana, 


"Irfaan wannan wane irin shashancin ne kayi haka? Na ɗauka kana da hankali ashe sam ba kada wayau? Meye Maimoon bata yiwa yaran nan? Wallahi ko Hajiya Maryam mahaifiyarsu ke raye iya gata da soyayyar da zata nuna musu kenan! Bana son tashin hankali da damuwa acikin gidana kada kasake yin hakan kuma maza kabata haƙuri yanzun nan." Mamakin yadda Yayan nasa ya rufe ido yake faɗa ba tare da yaji ta bakinsa ba yake, cikin son kara kansa yace, 


"Yaya nifa ba.." Bai ƙarasa ba Alhaji Sha'aban ya dakatar dashi, 


"Bana son jin komai daga gareka kabata haƙuri nace maka." Alhaji Sha'aban ya yi maganar cikin ɓaci ran daya bayyana ƙarara akan fuskarsa, dan idan har yace kalaman ɗan uwan nasa basu ɓata masa rai ba to tabbas yayi ƙarya don bashi kadai ba hatta ƴan uwa da mutanen gari shaida ne akan soyayyar da Hajja Maimoon ta ke nunawa yaran nasa ta gaskiya. Ba tare da Irfaan ya ɗago kai ya kalleta ba yace, 


"Kiyi haƙuri." Sannan yafice yabar gidan yana mamakin makirci irin na mace. Alhaji Sha'aban kuwa ɗakinsa yaja Mommy suka shiga ya zaunar da ita bakin gado ya shiga rarrashinta, daƙyar ya samu ta tsayar da hawayen dake fita daga cikin idanuwanta, reƙa fuskarta ya yi yakai hannunsa yana ɗauke mata ƙwallar yake cewa, 


"Haba gimbiya keda ke fama da irin Jannat baki taɓa gajiyawa ba balle har zuciyarki tayi raunin da zakiyi kuka sai Irfaan? Shima fa har yanzu yaro ne bai kamata ace kin kula da maganganunsa ba." Lafewa tayi a jikinsa tana faman sauke ajiyar zuciya tamkar wacce aka ɓatawa rai da gaske, cikin sanyaya murya tare da son sake shiga cikin zuciyarsa take faɗin. 


"Haba Habiby taya zai ce wai idan mahaifiyarsu Sohana na raye bazata barsu haka basa aiki ba, meye amfanin mai aikin da muke da ita da kuma arzikin da kake dashi idan har baza a tausayawa yaran nan ba su huta?."


"Kiyi haƙuri, nasan halin Irfaan bai faɗi hakan dan ya ɓata miki rai ba, shi da kansa yana faɗa min cewa ba ƙaramin sa'a nayi ba da Allah ya bani mata kamarki ba saboda yadda kike son yaran nan bakya nuna musu banbancin cewa yaron wata ne kin riƙe su da amana."


"Amma kuma gashi yana ganin laifina yanzu, ni dama nasan kawai baya sona sun riga sun tsaneni." 


"Kidena wannan zancen babu wanda ya tsaneki acikin ƴan uwana duka suna sonki kamar yadda kike son su." Wayarsa ce dake gaban aljihu ta ɗauki ƙara ya fiddo ta tare da saurin ɗagawa ganin mai kiran, cikin girmamawa haɗe da russunar da kai tamkar yana agaban mai kiran yake cewa,


"Barka da rana Hajiya ya ƙarfin jikin?" Ta daga can ɓangaren ta amsa masa cikin kulawa da girmamawa, 


"lafiya ƙalau alhamdulillah Ɗan albarka naga saƙo Irfaan yakawo. Nagode Allah yayi albarka ya ƙara buɗa maka."


"Amin Hajiya duk dai lafiya kuke ko?" 


"Lafiyarmu ƙalau ya iyalin naka da sarakunan jin magana?" Ɗan murmushi ya saki tare da cewa, 


"Duk lafiya ƙalau muke Hajiya, in sha Allahu anjima zamu shigo su gaisheki tunda yau weekend ɗin ke ƙarewa gobe kuma sai makaranta." 


"To ba laifi Allah ya kaimu agaishesu."  


"Zasu ji Hajiya, in akwai wani abu da kike buƙata kiyi magana da Irfan zai kawo muku." Cikin jin daɗi mahaifiyar tasa da ako yaushe takeyiwa Allah godiya daya bata ɗa tamkar da dubu da baya da buri irin yaga ya kyautata mata tare da sakata farin ciki tace, 


"Bana buƙatar komai yanzu, amma idan hakan ta taso zan sanar masa." Da haka sukayi sallama fuskarsa ɗauke da murmushi ya ɗago kai yana kallon Hajja Maimoon data lula duniyar tunani jin duk uban kuɗin daya narkawa Hajiyar tasa ɗazu har sake tambayarta yakeyi ko akwai wani abu, iskan bakinsa ya hura mata fuska cike da kulawa dan Alhaji Sha'aban wayayyen mutum ne dake da son soyayya da kuma iya tattalin macce yace, 


"Me kuma Gimbiya ke tunani?" Yaƙarasa zancen cike da kulawa. Murmushi ta ƙaƙaro zuciyarta cike da baƙin ciki tace,


"Ba komai Habiby, bari naje nasa su shirya muje wajen wankin kai da kitso." 


"Muje sai na kaiku ko?" Ya faɗa yana miƙewa tare da riƙo hannunta suka fito palourn. 


"Suhana, Jannat kuje ku shirya muje wajen wankin kan nan da wuri asamu ayi kitson ko? Oya a yi sauri muje da wuri karmu tarar da layi." Tayi maganar tana ɗaga Jannat dake kwance suka nufi sama dan su shiryo su fito su tafi tunda su kaɗai yake jira. Shi kuma ya zauna tare da ɗaukar remote yana canza channel ɗin cartoon da suke kallo zuwa ta labarai. Bayan kamar mintuna goma sai gasu sun fito gwanin burgewa suna sakkowa tana gyarawa Jannat ƙaramin mayafin dake kanta, idan kaga Hajja Maimoon da yaran bazaka taɓa cewa ba ita ta haifesu ba saboda yadda take basu tsantsar kulawa ta zahiri da kuma haɗini, da yawa mutane suna kallon kulawar tata ga yaran da wata manufa amma har ga Allah iya gaskiyarta take son su da kuma kaunarsu saboda soyayyar da take tsananin yiwa mahaifinsu..




#A heart touching story

#Gonar Sharri..

#Hajja ce

#Billy s Fari

#Ƴan Tagwaye