BABI NA UKU
by @billysfari
GS 3.
Murmushi yai yana hangosu tare da ajiye remote ɗin ya miƙe yana miƙa wa Jannat hannunsa ya riƙota yana cewa.
"Iyyee yarinyar Mommy wannan kwalliya haka, gyaran kai za'a je ko dai gasar kyau?." Dariya Mommyn tayi tana gyara mayafin jikinta take cewa,
"Duk wanda ka zaba Dady." Lokaci ɗaya kuma tana ƙwalawa Jauhar kira Jannat ko ta riƙe hannun mahaifin nata tana shigewa jikinsa cike da jin kunya. Mommyn bata rufe baki ba Jauhar dake kitchen ta ɗora abincin rana tafito da sauri ta duƙa gaban Hajja Maimoon tana cewa,
"Gani Mommy.." Tun kafin taƙarasa faɗa Hajja Maimoon ɗin ta buge mata bakin tana cewa,
"Uwar waye Mommyn taki? ban faɗa miki bana son kina kirana haka ba dan ubanki? Sannan waye kika barwa palourn nan ya gyara da kika tafi kika barshi haka baki kwashe waɗannan kayan da suka gama amfani dasu ba?" Cikin ruɗewa Jauhar take cewa,
"Kiyi haƙuri." Jauhar tafaɗa ɗage da bakinta dake mata raɗaɗi saboda zafin dukan data kai mata batare data sarar ba, dama tuni Alhaji Sha'aban Sada yayi gaba shi da yaransa zuwa katafaran compound ɗin gidan, dan haka Mommy taja tsaki cike da tsana tana kallon yarinyar kafin tabi bayansu. Da kallo Jauhar tabi ta har sai da ta dena ganin kyallinta kafin ta miƙe daga wajan jikinta duk a mace ta fara gyara parlorn.
A bakin wani katafaren wajen gyaran kai da suka saba zuwa Alhaji Sha'aban ya ajiyesu haɗe da juyowa ya kalli Hajja Maimoon yace,
"Ban sani ba ko akwai isassun kuɗi a hannunki, amma ga wannan ki riƙe ku ƙara kuyi amfani dashi." Ya mika mata rafar ƴan ɗari biyar sai sheƙi sukeyi. Amsa Hajja Maimoon tayi tana cewa,
"Kamar ka sani ba kuɗi a account ɗina Habiby gashi naso nima ayimun gyaran jiki, amma bari na bari sai bayan kwana biyu nayi nawa. Mungode Ya Habiby, Allah yaƙara maka buɗi."
"Amin, in sha Allah zan turo miki wasu ta account sai kema kije ayi miki koda zuwa jibi ne, yaushe kike tunanin zaku kammala nazo na ɗaukeku?" Ya tambaya cike da kulawa, dan yadda take kula da al'amransa kaɗai yakan tafiyar da ilaihirin tunaninsa.
"Eh zuwa la'asar dan Suhaila ma munyi waya daga school idan sun tashi lecture zata biyo tanan itama ayi mata, kasan halinta ita da ƙannen nata tamkar kishiyoyi suke."
"Eh to ina ga kuɗin nan baza su isheku ba, bari kawai nayi miki transfer ɗin yanzu." Ya faɗa cikin san ganin basu samu ko wacce irin tangarɗa ba da zata sa su wahala. Nan yaciro wayarsa yafara ƙoƙarin tura mata kuɗin, saurin dakatar dashi tayi tana cewa.
"Kabarshi tunda ni ba yau zanyi gyaran jikin nawa ba kaga sai idan katashi tura min ka haɗa min dana business ɗin da mukayi zancen dakai akan ina so nafara tunda dai yau hidimar tayi yawa ko kuwa?" Bai tanka mata ba har sai daya kammala tura kuɗin tunda dama yafara turawa sannan ya mayar da wayar cikin aljihu yana cewa,
"Ki duba na turo miki dubu ɗari uku da hamsin, dubu ɗari ukun naki ne na gyaran jikin da zakiyi, dubu hamsin ɗin ku ƙara na gyaran kan su Suhaila ɗin tunda har da kitso za ayi, alƙawarinki kuma ban manta ba zan baki ina sane dasu madam." Murmushi ta saki duk da ba haka taso ba a ranta idan ta tuna da tarin kuɗin da ɗazu aka kaiwa hajiyarsa, amma ko yanzu ba laifi tunda ta samu ta fazgi nata rabon ko banza yanzu account ɗinta ya ƙara yin nauyi. Sai data lumshe idanuwa cike da kissa sannan tace,
"Kuɗin nan fa Habiby sunyi yawa, duka nawa za'a kashe wajen gyaran kan nasu? Banda ma ba kuɗi a account ɗin nawa ai da ni ce nan zan biya." Kallanta ya yi itama shi take kallo cike da shagwaɓa ta kawar da kanta tana lumshe ido.
"Shiyasa ai naturo miki da ɗan dama ki samu kiyi saving wani abu a account ɗin, Iyalina kuma Gimbiyata ace account ɗinta empty yake?" Rolling eyes ɗinta tayi cike da jin daɗi dan Idan tana gabansa ji takeyi duk duniya babu wata macce sama da ita, haka ma tsintar kanta takeyi a yanayin ƙaunarsa marar misaltuwa a zuciyarta da bata taɓa yiwa wani mahaluki ita ba aduniya. Sanyaya muryarta tayi sosai haɗe da cewa,
"Godiya mukeyi Ya Habiby Allah ya saka da alkhairi ya tsare mana gabanka da baya ka."
"Amin." Ya amsa mata yana jin daɗin addu'ar tata kafin ya kamo hannunta ya sumbata sannan ta ɓalle murfin motar tafice tana ɗaga masa hannu haɗe da Allah ya kiyaye hanya bayan ta rufe masa ƙofar don tun ɗazu Jannat da Suhana suka wuce cikin shago saloon ɗin.
______
Jauhar kuwa basu daɗe da fita ba wani irin zazzaɓi ya rufeta, daƙyar tasamu ta kammala girkin tafito ta hau gyaran palourn tana yi tana tsayawa har ta kammala sannan ta hau sama ta gyara ɗakin Mommy da na su Jannat, tana sakkowa da niyar shiga nata ɗakin dake nan ƙasa gefen kitchen da ɗakin baƙi jiri ya ɗebeta tayi baya zata faɗi taji an tarota, jinta ajikin mutum yasa tayi saurin juyowa cikin ƙarfin hali tana ƙoƙarin ja ye jikinta. Cikin tsananin tausayawa Irfaan dake kallonta yace,
"Kiriƙa hutawa mana Jauhar, bakida lafiya ne?" Yayi maganar jin jikinta da zafi yana ƙoƙarin sake kai hannunsa a wuyanta don tabbatar da hakan, sai dai Jauhar tayi saurin janyewa dan bata saba da irin wannan kulawar ba.
"Sorry." Yafaɗa kafin yaci gaba da cewa,
"Ba kida lafiya ne Jauhar?" Yai maganar kamar zaiyi kuka dan ba ƙaramin tausayi ta bashi ba. Jauhar ta ɗaga masa kai hawaye na sakko mata a fuska dan ko magana ji tayi takasa yi. Juyawa ya yi yafice daga gidan yana cewa,
"Ina zuwa."
Bayan minti ashirin sai gashi ya dawo ya tadda ita anan bakin matattalkalar hawa sama zaune ta ɗora kanta a jikin karfen stairs ɗin hawaye na saukar mata a fuska. Ita kam Allah ma yasani ta gaji da wannan kangin bautar da take ciki, da ace akwai inda zata iya guduwa daya fi mata zaman gidan nan tayi tafiyarta ta huta, iyaye garkuwa ne kuma rahama amma bata san wane laifin tayiwa iyayenta ba takasa samun wannan garkuwa daga wajensu suka zabi takure rayuwarta a haka tun tana ƙarama har kawowa girmanta. Bata san meyasa aka haifeta ta cikin iyaye marasa tausayi ba. Irfaan ya kwashe mintuna uku yana kallon kyakkyawar fuskar tata wacce yake da yaƙinin idan har ta samu kwanciyar hankali da nutsuwa kyawunta sai yafi haka fitowa. Kallonta yake yi sosai da yake ganin gaba ɗaya bata cancanta da zama cikin irin wannan rayuwar ba kafin a hankali yakira sunanta,
"Jauhar." Ta ɗago kai ta kalleshi ba tare da ta iya cewa komai ba. Irafaan ya miƙa mata maganin hannunsa daya siyo mata yana cewa,
"Karɓi ga magani kisha zaki samu sauƙi kin ji ko?" Ba musu ta miƙa hannu ta karɓa don tasan idan ma bata karɓa tasha ba tofa ko ciwo zai kasheta agidan babu wanda zai bata magani tasha, gorar ruwan dake a ɗaya hannunsa ya buɗe ya miƙa mata takarɓa ta jefa maganin abaki tasha ruwan sosai har sai data shanyesu tas, tana gama sha amai ya taso mata saboda tun safe bata ci komai ba, da gudu ta wuce ɗakinta ta shiga toilet ta amaye maganin da ruwan da tasha tas, a kasalance tasamu ta wanko bakinta tafito ta zube akan katifarta tana fashewa da kuka. Anya rayuwa zata ci gaba da yimata lamunin da zata iya ganin wucewar wannan ƙuncin da take ciki? Anya zuciyarta zata iya ƙarfafa mata iya rayuwa da wannan matar da akullum take hango rashin imani da tausayinta acikin idanuwanta?
Tambayoyin data shiga jefowa kanta kenan cikin tsananin ciwo da damuwa kafin kuma ta samu bacci yayi awon gaba da ita. Irfaan daya kasa matsawa daga inda yake tsaye har yadena jin sautin fitar aman nata ya sauke ajiyar zuciya tare da ficewa daga gidan zuciyarsa cike da tausayinta.
_____
Mommy kuwa basu bar wajen gyaran kai ba har sai ƙarfe biyar na marece, cikin motar Suhaila suka nufi wajen kitso dan akwai matar dake yimusu shi yasa basu tsaya anan gidan saloon ɗin ba akayi kitson, wanda Jannat da Suhana kaɗai akayiwa dan Suhaila retouching tayi, sai bayan sallar magriba aka gama hi masu Mommy takira Alhaji Sha'aban ta sanar masa kamar yadda ya buƙata cewa idan angama takirasa. Ba'a jima ba ya iso wajen tunda dama ya san wajen kasancewarsa mutum mai kula da iyalinsa da ɓacin ran mahaifiyarsa bai haɗasu da komai ba shiyasa yake basu cikakken lokacinsa aduk sadda ya samu damar yin hakan. Da gudu Jannat tafito daga cikin gidan bayan ya iso tana nuna masa kitson da akayi mata hadda na gaba da jelolin suka fado mata a fuska kasancewarta mai tsawon gashi fiye da sauran ƴan uwan nata,
"Wow Masha Allah Mamana, anya wannan kitson basai naƙara kuɗi ba?" Nan su Mommy suka ƙaraso su Suhana suka gaisheshi Mommy ta gaishesa itama yana cewa,
"Mommy da yaranta an kammala ko?"
"Eh Dady." Ya kalli Jannat dake riƙe da hannunsa yace,
"Oya jeki wajensu Aunty zamu je gidan Hajiya." Sannan ya kalli Suhaila yace,
"Zamu fara tsayawa a ShopRite muyi siyayya kafin muwuce mu gaida Hajiya."
"OK Dad." Suhaila tafaɗa tana buɗe motarta suka shiga ita da Suhana. Jannat kuwa babu yadda Dady bai yi da ita ba taje wajensu Suhana amma taƙi hakan yasa Mommy yin dariya ta janyota ajikinta tana cewa,
"Barmun yarinyata Dady tunda bata son zuwa." Ta buɗe mata bayan mota ta shiga ita kuma ta buɗe gaba ta shiga. Juyowa Dady yai yana kallon Jannat data shige can cikin kujerar baya rike da wayar Mommy ta soma game yace,
"Mamana badai rigima ba ko?" Tayi murmushi kawai ba tare data amsa shi ba tana cigaba da latsar wayarta. Sai da Suhaila tayi reverse ta tada motar ta hau kan titi daidai sannan Dady yabi bayan motar tasu. Tafe suke Alhaji Sha'aban ya juyo yana cewa,
"Yau hidimar yaranki tasa kin manta dani ko abinci baki bani ba."
"Ayya Sorry, amma ina shegiyar yarinyar nan bata baka bane? Naboro ta fa ta ɗora abincin." Da yake yasan da wacce take dan ya saba da jin sunayenta kala-kala a bakin Hajja Maimoon ɗin.
"Ai ban koma gidan ba ne, nabiya campany ne acan nayi sallar magriba." Sai data ɗora hannunta saman nashi sannan tace,
"Sorry nasan muna isa gida ta kammala abincin dare sai muci ko?"
"Ba damuwa." Yafaɗa kafin su faɗa wata hirar har suka iso ShopRite ɗin. A gefen da Suhaila tayi parking motarta shima Dady ya yi suka fito gaba ɗayan su suka shiga yace kowa ya ɗauki abinda yake so. Kowacensu ta ja basket suka nufi ciki, ganin Mommyn tayi tsaye yasa ya kalleta yana cewa,
"Ya dai Mommyn Jannat?" Ta juya idanuwa tare da cewa,
"Kai nake jira muje tare na zaɓa mana namu." Murmushi ya sakar mata suka nufi wajen basket ɗin ta jawo ɗaya tana cewa su tafi. Ganin ya jawo ɗaya ya sata zuba mishi idanuwa tana cewa,
"Habiby wai ko ShopRite fin zaka saye mana ne? Wannan fa zai ishemu."
"Eh ke ki zaɓa mana, ni kuma zan zaɓawa Hajiya nata anan." Ya ƙarasa zancen yana wucewa gaba. Wani irin abu ne yazo ya tsaya mata a zuciya jin abinda yafaɗa kafin tayi saurin bin bayansa tana haɗiye abinda take ji adole. Turarukka masu matukar tsadar gaske agefen exclusive ya zabarwa Hajiyarsa da mayukan shafawa dana wanka, haka ɓangaren kayan ciye-ciye da yasan zata iya ci ko buƙata dan baiwa yara ko baƙi idan tayi duk sai daya kwasar mata. Ita dai Hajja Maimoon na biye dashi da idanuwa cikin wani matsanancin ɓacin rai wanda ita daƙyar ta iya haɗa musu nasu sannan suka wuce wajen payment ya biya inda kayan Hajiyarsa sai da suka kusan ninka duka kuɗin kayan da Suhaila, Suhana, Jannat da ita kanta Mommyn suka ɗauko. Juyowa yai bayan ya yi payment ɗin aka kwasar masu kayan su Suhaila sun wuce gaba an loda masu a mota yana kallon Mommy da tace,
"Waɗannan kayan da kika haɗa mana kina ganin sun isa bazaki ƙara wasu ba idan kina bukata?" Daƙyar ta danne zuciyarta ta ƙaƙaro murmushi haɗe da cewa,
"Sun isa Habiby kar kashe kuɗin suyi maka yawa, dubi bill ɗin da aka haɗa maka akayan Hajiya kaɗai ga kuma namu." Ta faɗa cike da kishi a cikin zuciyarta, gabaki ɗaya mantawa take da wacece Hajiya a wajansa.
"Karki damu, Hajiya ta ko nawa ne zan kashe mata banyi asara ba dan ta cancancesu, haka kuma babu faɗuwa ako nawa zan kashe muku saboda iyalina na kyautatama."
"Haka ne kuma. Muma in sha Allah sun isa Allah yaƙara buɗi." Ya amsa da amin sannan yawuce gaba tabi bayansa. Kamar yadda suka iso haka suka sake jerawa motar Suhaila na gaba ta Dady na bayanta har suka iso gidan Hajiya. Da gudu Jannat ta ɓalla marfin motar ta fice tun daga gate tana ƙwala mata kira.
"Kakata, Kakus.." Murmushi Hajiya dake zaune cikin wani katafaren palour daya gaji da haɗuwa ta saki lokacin da Jannat ta ƙaraso ta faɗo mata ajiki tana faɗin,
"Ja'ira ɗagani kada ki karya ni." Dariya Jannat ta saki haɗe da cewa,
"Kai gradma bani da nauyi fa." Bata rufe baki ba Alhaji Sha'aban Sada daya shigo ya ɗan kaimata ranƙwashi akai yana cewa,
"Ga Mommynki can je ki hau ƙafafuwanta kibarmun Hajiyata ta huta." Sai da Jannat ta ɗan turo baki kamar zatayi kuka kafin tace,
"Dady nima fa Mamanka ce ko Mommy?" Duk aka sa dariya kafin dukansu su shiga gaishe da kyakkyawar dattijuwar wacce da ka ganta zaka san hutu ya zauna mata ajiki bazaka taɓa cewa ita ta haifi Alhaji Sha'aban ɗin ba duk da kuwa ba shine ɗanta nafari ba. Da yake ƙasa take zaune ta mike ƙafafuwa Alhaji Sha'aban ya tankwashe nasa ƙafafuwan agabanta cikin girmamawa yana gaisheta yana mammatsa mata ƙafafuwan haɗe da cewa,
"Hajiya ya ƙarfin jikin?" Cikin kulawa ta amsa mashi da.
"Alhamdulillahi kafin tace,
"Ina kuka tafi Irfaan yace min gidan naku tsit ya isko yarinyar nan mai yimuku aiki ba lafiya?"
"Subhanallahi, bamu sani ba Hajiya ko dama batada lafiya ne Maimoon?" Dady tambaya haɗe da juyowa yana kallon Mommy. Mommy da jin hakan da tayi ko ajikinta yasa ta tace,
"Lafiya kalau muka barota Hajiya har ta ɗora girkin rana, bansan matsalar yarinyar nan sam bata son yin aiki ga shegiyar ƙarya da munafurci wallahi."
"Assha in haka ne kuwa bata kyautawa kanta ba Allah ya sawaƙe, ya ƙoƙari da yara Maimoon?"
"Alhamdulillah Hajiya ya jikin naki?" Mommy tafaɗa tana murmushi,
"Jiki alhamdulillah, Allah yai muku albarka yaƙara muku haƙurin zama da wannan rigimammiyar takwarar tawa, ga wata can miskila da bata son mutane itama." Hajiya ta ƙarasa zancen tana nuna Suhaila dake latsar wayarta tayi kamar bata jita ba. Hira suka ɗan taɓa tace mai aikinta takawo musu abinci duk suka ce sun ƙoshi, Dady ne kaɗai da Jannat suka ce zasu ci dan haka sai da mai aikin ta kawo musu abincin Hajiya takarɓa da kanta ta zuba masa ta tura masa gabansa da ruwan wanke hannu, tare da Jannat suka ci suka gama sannan Dady yamiƙe yana yimata sallama bayan tasa su Suhaila sun kwashe kwanuka sun kai mata kitchen. Har zata tashi Dady yace,
"Hajiya kiyi zamanki bari su Suhaila su kwaso maku sakonki su kawo maki, sai da safe."
"To Allah ya tashemu lafiya. Nagode Allah yayi albarka ya sake wadataka, yadda ka kula dani kaima Allah yasa naka ƴaƴan su kula dakai fiye da hakan." Ya amsa da amin sannan yafice suka bishi abaya.
"Sai da safe Hajiya." Hajja Maimoon tafaɗa itama sannan suka fice. Sai da su Suhana suka gama shigo mata da kayan sannan sukayi mata sai da safe tana sanya musu albarka suma tare da addu'ar Allah ya zaɓa masu mazaje nagari...
#A heart touching story
#Gonar Sharri..
#Hajja ce
#Billy s Fari
#Ƴan Tagwaye