BABI NA UKU
by @ummasghar
A cikin wannan yanayi na tunani da take yi bacci mai nauyi ya ɗauketa, cikin bacci taji ringing na wayarta, a hankali ta buɗe idonta da suka yi mata nauyi saboda bacci ta janyo wayar, ganin number Yaya Suwaiba yasa ta ɗauka da sauri tare da sallama. "Batula ina kika shiga sai kiran wayarki nake yi amma baki ɗauka ba har kusan sau biyar?"
"Kiyi haƙuri Yaya bacci nake yi ban san kin kira wayar ba, farkawa ta kenan."
"Shima Mijin naki haka nayi ta kiranshi bai ɗauka ba."
"Allah sarki Yaya na tabbata bai ga kiran bane, dake lokacin aiki ne, sai can zaki ga ya kiraki."
"Dama Baba ne bai gane ma jikin shi ba, jiya haka suka kwana ko rintsawa basu yi ba, Inna ta kirani da sassafe yanzu haka muna asibiti muna layin ganin likita."
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un," Batulu ta ambata gami da da dafa ƙirji, gani nan zuwa yanzu in sha Allah Yaya kuna wani Asibiti ne?" "Muna nan ɗan masara." Tana jin sunan asibitin ta datse kiran bata jira me Yaya zata sake cewa ba, a gaggauce hannunta na rawa ta soma neman layin Suleiman, haka ta riƙa ringing tana yankewa amma bai ɗauka ba, ba taji komai cikin ranta ba don idan da sabo ta saba da sabbin halayen Sulaiman, hankalinta da tunaninta kaf ya karkata zuwa Asibiti don haka cikin sauri ta rubuta mishi message ta shaida mishi zancen rashin lafiyar Baba, ta nufi ɗaki da hanzari ta ɗauki kuɗi tasa mayafi ta fita.
Sulaiman duk kiran da Batulu take yi mishi yana gani sai dai sam bai ji zai iya amsawa ba, ganin ta dame shi gashi yana cike wasu files yasa ya kashe wayar ya cigaba da aikin shi hankali kwance duk da yasan haka nan baza ta dame shi da kira ba sai idan da wani ƙwaƙƙwaran dalili.
A cikin Napep banda kuka da sauke ajiyar zuciya babu abinda Batulu take yi, a haka har suka iso asibiti. Kiran Yaya Suwaiba tayi ta shaida mata inda zata samesu, tun a waje taci karo da kannen ta Aliyu da Mus'ab cikin tashin hankali ta fara tambayarsu "Ina Baban? Meye ya sameshi?" Kafin su bata amsa idonta ya kai inda Baban ke kwance Yaya Suwaiba nayi mishi fifita, da sauri ta ƙarasa ta faɗa jikin Baba ta fashe da kuka. "Menene haka Batulu? ba kya ganin yanayin da yake ciki ne? Amma kin zube mishi a jiki kuma kina kuka?" Inna tayi maganar tana binta da kallo, share ƙwalla tayi ta tashi daga jikin nashi tare da furta "Allah ya baka lafiya Baba." Ta koma gefen Inna tana tambayarta ya abun ya soma. Kusan hour daya da rabi suka ɗauka a gaban likita kafin aka turasu gado, takardan magani likita ya bayar Inna taba Aliyu yaje pharmacy yaji kuɗin, da isarshi aka yi mishi jimlar kuɗin naira dubu arba'in da uku. Babban magana wai ɗan sanda yaga gawar soja, shiru suka yi sun yi cirko cirko a ƙofar ɗakin suna tunanin meye mafita irin wannan maƙudan kuɗaɗe a ina zasu je su samo su. Batula ba tare da tunanin komai ba ta fito da wayarta cikin ƙaramar jakarta ta cire sim ɗinta ta miƙawa Mus'ab. "Kaje ka kaita container inda za'a sayeta da daraja, idan har kudin da ake bukata ya samu har zan iya samun karamar waya kazo min da ita."
"Allah ya saka da alkairi". Suka ambata gaba ɗaya farin ciki na yalwatuwa a fuskarsu.
Sulaiman sai da ya kammala duk abinda yake yi kafin ya kunna wayarshi, har yayi yunƙurin bin bayan kiran Batulu zuciyarshi ta haneshi da yin hakan, ganin time ɗin tashin su Fahad yayi yasa ya ajiye duk abinda yake yi ya tafi makarantar tasu don ya ɗauke shi su wuce gida. Mamaki sosai ya bayyana kan fuskar Sulaiman shigowarsu gida babu Batula, kuma da alama ta jima da fita ganin yadda wajen yake babu gyara, take zuciyarshi ta soma zafi, idonshi har baya gani saboda tsananin ɓacin rai ya soma kiran number ta, amma is not reachable ake ce mishi, ciza leɓe yayi ya furzar da iska mai zafi ya kama hanun Fahad suka fito.
Batula sai da taga komai yayi dai-dai magani ya isa hannun nurses har sun ɗaura wa Baba ruwa hankalinta ya dawo jikinta, sai a sannan ta tuna da Sulaiman da fitowar da tayi bai sani ba, da sauri ta kalli agogon bango ƙarfe daya da kwata, kanta ne taji yayi wani irin sarawa, sim dinta ta ciro ta mayar cikin karamar wayar ta fara neman layinshi.
Ikon Allah shi ya isar dashi gidan Hajiya, a yanda yake fisgar motar duk wanda ya ganshi zai ce baya da hankali ne, Hajiya kallo ɗaya tayi mishi ta hango tsantsar ɓacin rai tattare dashi, tura Fahad tayi ciki wajen Amina ta maida dubanta gareshi, "Sule lafiya ka shigo haka meke faruwa?" Tamkar zai yi kuka saboda takaici ya dubi Hajiya "Ina roƙonki Hajiya ki ƙyaleni wannan karon na gwada ma Batula kasawarta, wallahi na gaji Hajiya na gaji, akan me sai kace ita kaɗai ce mace? Ko idan bana tare da ita ba zan yi rayuwa bane? Wallahi na tsaneta Hajiya ba zan iya cigaba da zama da ita ba, kawai ki ƙyaleni na saketa". Ya ƙarasa maganar yana ciza leɓe numfashin shi na hawa yana sauka, murmushi Hajiya tayi, "To Sulaimanu na ni dai tunda ka zauna bayani ɗaya kake yi baka sanar dani meye Batular tayi maka ba? Sai faman zaka saketa ka gaji da zama da ita?" Shiru yayi na wani ɗan lokaci kafin ya kwashe komai ya sanar da ita.
Girgiza kai Hajiyar tayi tana jinjina wannan al'amari kafin tace "ita kuwa Batula me yasa take haka ne bayan tasan baka son yawan fitar da take yi ba tare data sanar maka ba? amma ta kasa dainawa." Ƙwafa yayi yana jin ƙarin baƙin ciki da takaicin abinda Batula take yi mishi idan yayi magana Hajiya ta hanashi ɗaukar mataki in banda haka da tuni wani zancen ake yi ba wannan ba. "Kuma ka kirata ta faɗa maka inda ta tafi ko kuwa?" Kamar daga sama yaji tambayar Hajiya a kanshi. Siririn tsaki yayi yace "Ni ban kirata ba Hajiya don babu abinda zata faɗa mini da zai hanani ɗaukar mummunan mataki a kanta wannan karon don dai wallahi na gaji."
"Ka dai bi komai a hankali baka san uzurin daya fitar da ita ba nima kuma zan je gidan nayi mata faɗa amma kayi haƙuri ka bar batun rabuwar nan ko don Fahad dake tsakanin ku ba zaka so ya taso iyayenshi basa tare ba." Haka dai Hajiya tayi ta tausarshi don fa Suleiman ya hau dokin zuciya har wani tafasa yake ji zuciyarshi nayi idan ya tuna da Batula da abinda taje yi mishi. Bai bar gidan Hajiya ba sai da la'asar sannan ya kama hannun Fahad suka koma gidan don yayi mishi shirin islamiyya ya kai shi.
*****
Ita kuwa Batula sai sauri take yi ta samu ta koma gida kada Suleiman ya dawo bai tarar da ita ba. Wata wawuyar ajiyar zuciya ta sauke lokacin da ta shiga taga gidan na nan kamar yadda ta barshi babu alamun Suleiman ya dawo da bata nan. Mayafinta kawai ta ajiye ta hau gyaran gidan da bata samu tayi ba kafin ta fita, a gaggauce ta gama komai ta faɗa kitchen ta ɗora musu jollof ɗin taliya don ta samu ta gama komai kafin ya dawo, yadda hankalinta ya ɗauku da son ganin ta hattama komai kafin ya dawo yasa bata lura da cewa lokacin dawowar tashi tuni ya wuce ba ita dai ƙoƙarinta tayi ta gama komai akan lokaci don kada ya kamata da wani laifin kuma.
Cikin hukuncin Allah har ta gama komai bai dawo ba don haka tayi sauri ta faɗa banɗaki tayi wanka haɗi da ɗauro alwala sannan tazo ta shirya cikin sassauƙar shigar doguwar rigar material da yabi jikinta ya kwanta luf ya fitar da kyakkyawar surar jikinta ta ɗiya mace. Har tayi sallah ta idar Suleiman bai shigo ba don haka ta tashi ta koma parlour ta zauna. Wayarta ta ɗauka ta danna mishi kira don taji a ina ya tsaya duk da ma dai tasan baya wuce gidan Hajiya suka wuce tunda tasan dole zuwa yanzu ya ɗauki Fahad daga makaranta. Har wayar ta ƙari ɓurarinta ta gama bai ɗauka ba, haka tayi ta gwada kiranshi wayar na tsinkewa amma bai ɗaga ba, ita tasan da gangan yake ƙin ɗaukar wayarta. Ta rasa me take yiwa Suleiman haka da zafi da ya canja mata gaba ɗaya tamkar ba shine wannan Suleiman ɗin mai yawan ƙaunarta da tattalin farin cikinta ba.
Tana zaune a wurin tana tunani har bata ji ƙarar shigowarsu ba sai dai jin muryar Fahad tayi yana cewa "Ammie ina kika je muka dawo ba kya nan sai gidan Hajiya Daddy ya kai ni acan naci abinci aka yi mini wanka." Wata irin faɗuwa taji gabanta yayi, ashe dai Suleiman ya dawo ya tarar bata nan ita ce bata lura ba. A hankali ta ɗago kai ta kalleshi murya a sanyaye tace "Abban Fahad sannu da zuw..." Hararar daya watsa mata ce tasa sauran maganar ta maƙale a maƙogwaronta. A fusace yace "gidan ubanwa kika je na dawo ba kya nan." Sai da hantar cikinta ta kaɗa tsabar tsoron Suleiman da taji ya kamata, murya na rawa tace "nayi ta kiranka a waya baka ɗauka ba idan ka duba zaka ga har saƙon text na tura maka, Baba ne aka kwantar a asibiti baya da lafiya."
"Baban ubanki," yace haɗe da ɗauke fuskarta da wani irin mari da sai da taga tartsatsin wuta tsabar azaba, ta tafi ta hantsila ta buge da center tabke a take goshinta ya fashe ya fara zubar da jini. A gigice ta saka ƙara haɗe da dafe kuncin daya mareta. Ɗago kai tayi ta kalleshi sai dai babu shiri ta mayar da kanta ƙasa ta sauke saboda wani mummunan kallo da yake jifanta dashi. Kafin tayi wani yunƙuri har ya cire belt ɗin dake ɗaure a ƙugunshi ya shiga lafta mata yana haɗawa da kai mata harbi da ƙafa. Gaba ɗaya haushinta yake ji don yaso Hajiya ta bar shi ya danƙara mata saki ta koma wahalalliyar rayuwar gidansu da talauci yabi yayi musu ɗaurin goro inda abincin da zata saka a bakinta ma sai ya gagareta samu. Dukanta yake yi babu ji babu gani tun tana ihun ceton rai har ta gaji tayi shiru ganin babu mai shigowa don ya kawo mata ɗauki.
Fahad ne da yaga dukan da Abban nashi yake yiwa Amminshi yayi yawa ya ruga da gudu ya kwanta a jikinta yana kuka yana tayata bawa Baban nashi haƙuri, sai sannan Suleiman ya sassauta dukan da yake yi mata don kada yaje ya samu ɗan shi. Gaba ɗaya jikinta yayi tsami ga goshinta da har lokacin yake zubar da jini, shesheƙar kukanta ne kawai yake tashi amma koda wasa Suleiman bai ji tausayinta ba sai ma nunata da yayi da yatsa yace "rashin ɗaukar wayarki ba shi zai baki damar ficewa yawon banzarki ba a duk lokacin data raya miki, idan kuka kin ƙi ji ba kya ƙi gani ba don kuwa jikinki ne zai faɗa miki, banza ƴar matsiyata kawai." Yasa kai yayi ficewarshi ko bi ta kan Fahad dake taya uwarshi kuka bai yi ba bare ya tuna da zai kai shi makarantar islamiyya.
Ta jima a kwance a wurin tana kukan da bata da mai rarrashinta, sai da tayi iya yinta sannan ta bawa kanta haƙuri ta tashi taje ta wanke goshinta da har lokacin yake zubar da jini. Zama tayi a bakin gadonta idanunta na tsiyayar hawayen baƙin ciki da takaicin halayen Suleiman da baya jin komai don ya kai hannunshi jikinta. Zuwa Fahad yayi ya kwanta a jikinta, shi kanshi yaron sai ya zama abun tausayi gaba ɗaya jikinshi yayi sanyi da dukan da yaga mahaifin shi ya yiwa Amminshi ga kuma wani tsoron mahaifin daya shige shi. Hannu tasa ta janyo yaron jikinta, wani irin tausayin kansu ne taji ya kamata, ji take yi tamkar bata da kowa a duniya face tilon ɗanta Fahad.
#SADIYANASIRDAN
#UMMASGHAR