FreeArewaPen original
BISHIYAR TSIYA....
- 1views
- 90chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · BABI NA ƊAYA
01:28pmIdonta ya sauƙa kan agogon dake manne jikin bango. "Hasbunallah wani'imal wakil, na shiga uku". Shine kalmar data furta ta miƙe jiki duk babu kuzari sakamakon rashin wadataccen hutu da bata samu ba, kitchen ta nufa ta samu ta ɗaura lunch a gaggauce, tasan duk in da Suleiman yake yanzu yana gaf da dawowa gida, ganin babu kayan miyar da zai wadaceta yin girki yasa ta dawo palo ta ɗauki wayarta tayi dialing number shi ko zai shigo mata da kayan miyar tunda yayi mata kashedin fita idan baya nan, sau shida tana kiran wayar amma ɗauka ba, ajiyar zuciya ta sauƙe ta ajiye wayar gefe ta soma lissafi cikin ƙwaƙwalwarta, matuƙar Suleiman ya dawo ya iske ba tayi abinci ba wulaƙancin da zai biyo baya bashi misaltuwa, mayafi da kuɗi ta ɗauka ta rufe gidan ta gangara ƙasan layinsu ko zata samu kayan miyar.Yana driving yana kallon duk kiran da Batulu take yi mishi, haka ya riƙa jan tsaki har ya isa gate din makarantar, tun daga nesa Fahad ya hango Daddyn shi, nan fara'a ta yalwatu kan fuskarshi ya nufo motar da gudu, Suleiman na ganinshi yayi saurin buɗe mishi gaban motar yana mai mayar masa da murmushi, "Daddy yau ba kazo da wuri ba, saura kaɗan nayi kuka". Shafa kanshi Suleiman yayi, "Sorry Fahad na tsaya sallamar baƙi ne a office, rufo ƙofar mu ƙarasa gida nasan kana jin yunwa." Kaɗa kai Fahad yayi ya janyo murfin motar ya rufe suka ɗauki hanya.Layi sosai ta samu a wurin dattijon, waje ta nema ta zauna ta zuba tagumi cikin zuciyarta tunani take yi na irin badaƙalar da zata wanzu tsakaninta da Suleiman matuƙar ya dawo gidan bata kammala abinci ba, "Baiwar Allah meye za'a baki?". Dattijon yayi magana da ɗan ƙarfi don ya lura hankalinta yayi wani wajen, A ɗan zabure ta waigo, nan taga har jama'ar dake wurin sun watse saura tsiraru, kuɗin ta miƙa mishi ta sanar dashi abinda zai bata, tana karɓa tasa sauri har tana harɗe kafafu don ta samu ta isa gida akan lokaci kada Suleiman ya dawo bai sameta ba.Horn Suleiman ya soma amma shiru babu alamar Batulu za tazo ta buɗe mishi gate, ƙwafa yayi ya fito daga motar ya buɗe gate din da key din hannunshi, da shigarshi ko rufe motar bai tsaya yayi ba ya faɗa gidan yana ƙwala kiranta sunanta."Batulu! Batulu," ganin bata amsa ba kuma bata fito ba yasa ya nemi waje ya zauna ya janyo Fahad jikinshi yana jin zuciyarshi na zafi, "Daddy yunwa nake ji". Ajiyar zuciya ya sauke ya kama hannun Fahad zuwa kitchen, sosai yaji ranshi ya ƙara ɓaci ganin babu alamar tayi abincin, kama hannun Fahad yayi suka dawo palo ya janyo wayarshi ya danna kiranta.Batulu tana yankowa layin gidan kiran Sulaiman na shigowa wayarta, sosai ƙirjinta ya soma bugawa ganin number shi, gudun kada ta ɗauka yaji alamar tana waje yasa ta ƙara sauri ta shiga gida. "Ni Batulu yau tawa ta sameni," ta furta idonta na canza kala zuwa ja ganin motar...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.