BIYU
by @zeeeyybawa
*WATA ALAƘA*
*PAID BOOK*
*ƳAN TAGWAYE BIYAR*
Na
*STYLISH BCH*
da
*ZAYNAB BAWA*
*SHAFI NA BIYU*
Bayan whole class ɗin yayi shiru duka student ɗin sun bawa teacher attention ɗinsu cikin ƙanƙanin lokaci classroom teacher ɗin tayi introducing kanta cike da wasa da kuma barkwanci da iya sarrafa kalamai yanda zaiyi dai-dai da tunanin yaran yanayin yanda ya kamata teachern ƙananun yara ta kasance sai da ta tabbatar sun iya sunanta da sunan nanny's ɗin da suke kula dasu daga nan ta saka student kowa yafara introducing kansa/ta. Kusan rabi da kwata na student ɗin nickname nasu suke faɗa dan wasu ma basu san ainahin sunan su na gaskiya ba sai wanda ake kiransu a gida. Name-tag. dake jikin seat ɗinsu ne yake tabbatar da ainahin sunan yaran wanda dashi clasaroom teacher ɗin take amfani tana kiran yaran dashi. Da waƙa da dancing har sai da ta tabbatar da yawa sun gane sunayensu sannan aka duba record ɗin kowa shima cikin wasa da dancing kowa ke faɗar age ɗinsa, saboda a wannan stage ɗin ake son yaran su san information about their selfs, kamar su self-name, sex, age, complexion. Sai Kuma child's health records, height, weight and allergies. Sai Kuma sauran information dake jikin file na kowane student na parents, name of parents, parents phone numbers, occupation. Da Kuma garin ku da unguwar ku da dai sauran ƙananun abubuwan da ya dace. sosai Classroom teacher ta ƙware wajan iya sarrafa gabaki ɗaya yaran da cikin ƙanƙanin lokaci wasu suka saba da ita, classroom teacher tanada ilimi sosai akan harkar kula da yara, haka tayita bi dasu har zuwa lokacn lunch. Lokacin nayi aka basu break domin suyi lunch. Lunchbox's ɗinsu nannys suka fara cirowa a cikin lockers dake can bayan desks ɗin student din, da yawa daga cikinsu da lunchbox ɗinsu suka zo yayinda wasu daga ciki iyayen sun san tsarin makarantar na tanada wa yaro lunch kuma sun bada tsarin abincin da yaransu sukeci. Wajan lockers ɗin da aka ajiye musu lunchbox ɗin cike yake da tsari domin kowa da sunansa a jikin looker din. Nan da nan suka fara mikawa kowa nashi.
Hidaya ana miƙa mata nata tayi saurin amsa domin dama karɓan lunchbox dataga anyi yana daga cikin abunda ya ƙara mata kukan da tayi. Kallon yaron dake zaune next to ita tayi cikin yanayinsu na yarinta da wani irin sabon daya shiga tsakaninsu lokaci guda tace masa.
"Zakaci?" murmushi yayi a karo na babu adadi both side na kumatunsa suka lotsa abunda yake ƙara saka Hidaya nishadi kenan batareda yayi magana ba ya nuna mata Nanny ɗin da take ƙoƙarin ciro nasa lubchbox ɗin. Wani Luxury kuma hadaddan lunchbox aka fito dashi mai tambari wanda yafi kama dana masarauta ajiki daga ganin wannan lunchbox an san cewa ba a kowace gida ko stores za'a iya samun sa ba. yanayinsa yafi kama da wanda aka ƙirƙira purposely for wanda yake da mallakinsa. Nannyn tana cirowa ta ajiye gaban yaron da yake zaune next to Hidaya wanda aka rubuta HYDAR ALIYU TURAD jikin seat ɗinsa sunan dake jikin seat ɗin shine rubuce a jikin lunchbox din. Cikin yanayi mai haɗeda zallan yarinta Hidayata ta furta.
"Wow" tana son sanar dashi lunchbox ɗin tayi kyau amma maganar batayi ƙarfi sosai a bakinta ba.
Bayan sun kammala bawa yaran sannan sukayi musu jagora zuwa lubchroom da aka tanada domin yaran sannan anan duk wani yaro an tanada masa abincinsa harda wanda suka zo da lunchbox ɗin nasu kamar yanda doka da kuma tsarin school ɗin suka shar'anta.
Cikin hikima Nanny's din suka bi duk wanda bazai iya bude lunchbox dinsa ba suka bude masa, wanda zasu iya kuma sun bude kayansu. Cikin wanda suka bude harda Hydar Aliyu Turad wanda yake Allah Allah ya bude ya ɗaukowa Hidaya wata babbar chocolate dinsa dake ciki yana jin a ransa idan ya bata zatayi farin ciki. Matsowa yayi kusa da ita yana mika mata, ido ta bisa dashi tana kallonsa kamar bata gane me yake yi ba. Ganin ta kafeshi da ido yasa shi yi mata sanyayyan murmushin sa dake sa kumatunsa lotsawa. Hidaya ganin kumatunsa sun sake lotsawa yasata dariya irin tasu ta yara, hannu tasa ta amsa tana mai ture nata lunchbox din gefe. Jujjuya chocolate din ta shiga yi tamkar mai neman wani aibu a jiki already Nanny ta bude masa dama. A hankali ta saka cikin bakinta tahau sha hankali kwance, kamar wani babba Hydar Aliyu Turad ya mika mata tafin hannunsa alamar ta sammasa. Hidaya ta noke shoulder ya saki murmushi kawai shima yana zaro wata chocolate din ya dauka cikin sauran dake ciki yafara sha, yana sha yana kallon Hidaya wacce duk ta bata hannuta da bakinta da chocolate din, ko ta abinci ba sayi ballantana asa ran zasu ci. Bayan sun kammala nannys suka gyara musu jiki sannan aka maidasu classroom ɗinsu.
_________
Wajan 11:30 a get din makarantar tayiwa Mami saboda Abba dake gurin aiki, irin manya manyan motocin dake bakin gate din zai saka kara tabbatar da school din ta 'ya'yan manya ce masu ji da arzikin su. Mami na nan tana jira har 12 ta karasa, saboda daukin son daukar yarta da take cike da dinbin tausayin ta. Motocin school din ne suke ta fitowa daya bayan daya, yayinda masu daukar 'ya'yansu ke shiga dan dako nasu.
Mami itama bude kofar motar tayi bayan ta samu wajan parking ta adanar motar kafin tashiga cikin inda nan ne yara ke zaman jiran masu daukar su. A can nesa ta hango Hidayanta tare da sauran yara da nanny's dake tsatsaye suna jiran iyayen yaran da suke zuwa da kansu dan daukar 'ya'yansu. Hidaya murna tafara nan da nan ta shiga taɓarar da tayi niya bayan dauke Hydar da masu daukarsa sukayi aka wuce dashi gida. Dan duk saurin mami sai da aka dauki Hydar kafin ta karaso kasancewar shi masu ɗaukansa dama basu tafi ba ƙa'id ane zasu dinga jiransa kullum idan ya kammala su tafi tare. Yara wasu na wasa wasu na zaune suna jiran iyayensu dama already wadanda school bus take dauka sune suka fara fita daga school ɗin. Itama Mamin ganin dariyar yarta da murnar ganinta da taga Hidaya nayi yasata kara saurin tafiyarta dan karasawa gurinta.
"Oyo-yo Mamina, ga Mami ga Mami." Shine abinda Hidaya take ta fada tana murna. Hannu Mami tabata takama lunchbox dinta dake kusa da ita Mamin ta dauka tana gyara mata schoolbag dinta dake sakale a bayanta. Mami suka gaisa da nanny's din ta janyo hannun Hidaya suka fito. mamakk sosai Mami takeyi ganin yanda Hidaya ta saki jikinta bata taɓa ɗauka zatazo ta sameta a haka ba tunda ta koma gida tunaninta ya hanata sakat a tunaninta Hidaya tana can tanaci gaba da kukan da suka barta tanayi sai dai kuma yanzu taga akasin hakan. Seat din gaba ta ajiye Hidaya ta samata seatbelt lunchbag din kuma tasa shi a bayan motar. Itama ta shiga mazaunin gidan ta tada motar sukayi gida.
"Hidayan Mami ansha school, da dadi?" Mami tafada tana dan waigowa tana kallonta yarta ta cike da kulawa. Murmushi Hidaya tayi ta dago fararen idonta tana kallon Mamin nata.
"Mami ajina haka." Ta bude yatsun hannuwan ta uku tana nunawa mamin. Murmushi Mami tayi tana cewa.
"Woww har kinje aji uku kenan Hidaya? ashe da wuri zaki gama school din ban sani ba." Bata cewa komai ba akan maganar Mami sai cewa tayi.
"Kuma nayi aboki Mami yabani chocolate dinsa babba da alawa harda biscuit. Kuma Mami ko nawa ban ci ba bari ki gani." Ta juya tana neman lunchbox din nata dan ta nuna mata. Murmushi Mami tayi tace,
"No Hidaya yi zamanki idan mukaje gida sai ki nuna min. Ashe shi yasa Hidayan Mamin ta dena kuka saboda tayi aboki ya bata chocolate." Hidaya ta saki dariya tana kallon Mamin.
A bakin gate din gidan ta tsaya tare da danna horn har sau biyu kusan a jere, da sauri mai gadin ya leko ta ƙaramar ƙofar dan tabbatar da mai yin horn din. Ganin motar Hajiya ce yasa shi wangale mata gate din, hakan ne ya bata damar saka motarta cikin gidan tana sauke wata boyayyar ajiyar zuciya wacce take da tabbacin na jin dadin sun fita lafiya ne sun kuma dawo lafiya. Sai da ta tabbatar ta gama yin parking sannan ta fito, ta zagayo seat din mai zaman banza ta fito da Hidaya wacce take hango tsantsar walwala a saman fuskarta.
Dai dai wanan lokacin kuma wayar ta ta dauki sauti. Juya wayar tai dake hannunta dan tabbatar da mai kiran nata. Dr tare da emojis din heart tagani, picking tayi fuskarta na cika tab da ilahirin murmushi wanda yake nuna zallar farin ciki, da alama taji dadin kiran nan da akayi mata duba da yadda fuskarta ta gasgata.
"Abba." Ta fada tana sake sakin wani kyayataccen murmushin. Shima daga nasa bangaren murmushin ya saki yana mai cewa.
"An dakota kenan Mami?" Mami ta kalli inda Hidaya take tace,
"Eh mana gamu ma acikin gida kai kadai ne baka ciki." Murmushi yayi yana mai cewa.
"Daman nasan Mami bazatai wasa ba." Itama wani murmushin ta sakeyi tana mai kama hannun Hidaya daya don su shiga cikin gidan bayan ta dakko lunchbox din ta.
"Mami Abbana ne? Please bani Abbana Mami." Hidaya ta dinga fada tana mika dayan hannunta da Mamin bata rike ba,
"Bani yata na jiyo muryarta." Abba yace dan yana jiyo ihu ihun da Hidayan keyi na cewa bata Abbanta. Cike da farin ciki Hidaya ke yi masa magana tana cewa.
"Abba na dawo daga school." Abban nata da farin ciki ya cika shi shima musamman yadda yaji tana magana da wani irin nishadi a muryarta, sai yaji gabaki daya ragowar fargabarsa na ganin kamar ya kaita school da wuri ya ragu sosai. Tunda yaji muryarta yasan cewa ta ware kamar yadda yai expecting idan taga basa wajan kuma yaga yadda malamarsu da nanny's ke yi musu yasan zata saba kafin nan da one-week, sai gashi ma cikin yini daya tana neman basu mamaki.
"Abba nayi friend."
"Inye ya sunanta?" Ya tambayeta cike da kulawa.
"Namiji ne fa Abba." Ya ware ido tamkar yana gabanta, cike da salon muryar yara yake fadin.
"Friend namiji Hidaya? Duk matan dake class dinku babu wacce tayi miki sai shi?" Bata fahimci abinda yake nufi ba dan haka taci gabama da bashi labarinsa da abubuwan da ya bata kafin tace.
"Abba ka siyo min nima idan naje na bashi." Cikin dariyar da shi kansa baisan zatace hakan ba yake fadin.
"Zaki biyashi kenan?" Ta daga kai tamkar yana gabanta kafin tace,
"Abba guda ashirin." Daga shi har Mamin nata dake gefe tana jinsu suka saki dariya Mami na zare wayar daga kunnan Hidaya tana cewa.
"Kawo to tunda kin sanar dashi. Hello Abba bye sai ka dawo Allah ya dawo mana dakai lafiya." Amsa mata ya yi cike da kulawa daga haka duk suka ajiye, ta kamata suka karasa ciki. Uniform din ta cire mata suka nufi bathroom ta saka su cikin washing machine sannan ta tara ruwa cikin bathtub tare da tsoma Hidayan a ciki tana yi mata wanka. Bayan tagama wanke ta ta shiryata cikin kaya marassa nauyi wanda bazasu takura mata ba. Sai bayan ta kammala shirya Hidaya ta barta a palour tana kallo sannan ta shiga kitchen domin ƙarasa aikin data faro hankalinta yaƙi kwanciya ta tsaidashi ta tafi ɗauko ƴarta. Zuwa 1:30pm Mami ta kammala duk wani aikin da takeyi a kitchen ta shiryasu akan dining kamar yanda ta saba sannan ta dawo palour wajan Hidya ta zauna. Cike da kulawa take tambayar.
"Hidayam Mami zakiji abinci?" Girgiza kai Hidaya tayi cikin yanayi mai cike da yarinta tace.
"Mami tare da aydar zanje muci" Zaro ido Mamin tayi cike da mamakin yanda Hidaya tayi sabo da yaron nan lokaci guda kuma harta iya riƙe sunansa tace.
"Sunasa Hydar Hidaya?" Saurin jijjiga kanta tayi tace.
"Eh Mami tare zamuci" Cikin nuna tsantsar kulawa da dabara Mamin tace.
"Ai yanzu Hydar baya nan Hidaya yana gidansu kibari gobe idan Allah yakaimu idan zan haɗa miki lubchbox saina saka miki harda nasa" Cikin yanayi wanda yafi kama dana taɓara Hidaya ta noƙe kafaɗa tana shirin fara bori ita a lallai saida Hydar zataci abinci, dakyar Maminta ta rarrasheta da faɗin.
"Toh shikenan yanzu tashi muje sai kici harda nasa idan kikaci masa daga nan zaiji ya koshi" Hidaya cikin rashin wayo ta washe baki tana faɗin.
"Kawomin" murmushi Mami tayi ta miƙe ta nufi dining ɗam ƙaramin plate ta ɗauko tana zuba abincin tana mita ƙasa-ƙasa tana faɗin.
"Ƙarfi da yaji yara sai sun maida iyayensu maƙaryata yanzu ina zaman-zamana Hidaya ta sakani shirya ƙarya" tayi maganar a hankali yanda Hidaya bazata jiyota ha domin azabar wayao ne da ita, kaifin tunaninta da surutunta yafi karfin shekarunta tanaji zata akwai wata aƙasa game da maganar da mahaifiyarta ta faɗa mata. Kaɗan ta zuba abincin domin tasan idan Abbanta ma ya dawo saita sake ci ta kai mata palour yanda take zaune. Da sauri Hidaya ta amshi abincin tanaci tana surutai ita ala dole tanaci tana Hydar. Murmushi Mami tayi ta shafi kanta tana tunanin akwana atashi kuma wata rana za'a kai lokacin da Hidaya zata fahimci wani baya ciwa wani abinci har zata gane mahaifiyarta wayo kawai tayi mata. Bayan ta gama cin abincin ta tattara wajan dake hidaya nada nutsuwa sosai kusan komai nata neat yake shiyasa bata ɓata wajan sosai ba. dawowa tayi ta zauna Hidaya tacigaba da yimata hirar Hydar harda wani ramin dake fuskarsa. Mami tasha Dariya sosai bayan Hidaya tayi mata kwatance ramin dake fuskarsa ta gane Dimfull take nufi. Ahaka har bacci ya ɗauki Hidaya Mami ta ɗauketa taje ta kwantar da ita sannan ta dawo tashiga ɗakinta domin yin wanka saboda an fara kiraye-kirayen sallar la'asar."
"YAN TAGWAYE"