GONAR SHARRI...

BABI NA HUƊU

by @billysfari

GS 4.


Kwance Jauhar take ta rasa inda zata jefa ranta, duk da cewa yau masu takura mata basa gidan ta samu peace of mine, Sai dai zazzabin da tayi na yinin da kuma amai yasa jikin nata ya yi weak tun ɗazu bata iya ko motsawa daga inda take kwance ba bare ta iya mikewa. jin an buɗe gate yasa taji kirjinta ya wani irin bugawa tashin hankali ya shigeta har bata san lokacin da ta miƙe tsaye ta fito daga cikin ɗakin nata ba. Cikin sauri ta fice zuwa compound dai dai lokacin da suke ƙoƙarin yin parking ɗin motocin nasu. Ta cikin glass ɗin motar Hajja Maimoon ke hango Jauhar, tun kafin ta fito ta ɗaure fuska dan sai ran Jauhar ya ɓaci akan sanarwa Irfaan rashin lafiyarta, bataga dalilin da zai sa a dinga yi mata shisshigi a cikin al'amuranta ba. Rasa wanda zata fara tara tayi gashi ita ɗin ɗaya ce amma kowa a cikin su so yake ta bauta masa. Kai tsaye ta nufi motar su Hajja Maimoon kasancewar a dominta ne take tare da yaran gidan. 


"Baki ga kaya bane Jauhar?" Cewar Suhaila da take fito da kayan da sukayo shopping na motar ta ganin tana ƙoƙarin wuce su. Kallanta Jauhar tayi tana ƙarfafa zuciyarta dan ita kaɗai tasan irin yanayin da take ciki kafin tace.


"Yaya Suhaila bari na fara zuwa wajan Hajiya sai nazo na ɗauka." Suhaila ta riƙe ƙugunta cike da mamakin Jauhar ɗin, duk da taji yes ya kamata a fara zuwa wajan Mommyn tasu amma yadda takeji da isa akan Jauhar ɗin yasa ta juya tana tafiya take cewa. 


"Ke kika sani, idan kinga dama karki kwaso ki barsu anan wajan." Suka shige ciki ita da Suhana daga su sai handbag babu wacce ta ɗauki koda leda ɗaya a cikin su. Sauke numfashi Jauhar ɗin tayi tana kallon ledojin da suke jiranta kafin ta durkusa saitin ƙofar Hajja Maimoon tana jiran fitowarta. Jannat ce ta fito ta cillawa Jauhar ɗin handbag ɗinta batare da tace komai ba ta wuce abunta cikin wata isa. Cike da kasala Jauhar ta ɗauki handbag ɗin daga kan cinyarta ta riƙe a hannunta, babu abinda take jira sai fitowar Hajja Maimoon wacce ke cikin motar tana yiwa Alhaji Sha'aban rigima akan cewa idan suka shiga ciki karya ce zai yi wani aiki ko amsa waya, suna cikin motar tasa ya yi switch off ɗin wayoyinsa duka yana cewa, 


"A'a you wish Mommyn Jannat." ta sakar masa murmushi haɗe da rolling eyes ɗinta. Kusan a tare suka buɗe murfin, Hajja Maimoon har da buɗe ta gefenta duka ta yadda sai da ta bugarwa Jauhar a jiki wanda dama hakan ne burinta. Jauhar bata damu da sosa wajan ba ta shiga yi mata sannu da dawowa amma ko kallon inda take batayi ba tace. 


"Ki ɗebo kayan cikin motar." Daga haka ta ƙarasa wajan mijin nata suka jera zuwa ciki. Kallansu Jauhar tayi tana jin hawaye na shirin zuwa mata, tana mamakin yadda duk wani cin kashi da za'a yi mata a gaban mai gidan uffan baya cewa duk da cewa farko yakan ɗan tsawatar da yaran nasa amma daga baya kuma sai taga ya dena, ta kasa gane dalili duk da cewa zuciyarta na gaya mata ƙila Mommyn ce ta nuna masa rashin jin daɗinta akan sassauci da yake ganin ya dace a bawa Jauhar ɗin. Ganin tana ɓatawa kanta lokaci a wajan yasa ta mike tana riƙe da handbag ɗin ta zaro ledojin. Ganin kayan da yawa yasa ta rataya jakar Jannat a kafaɗarta ta ɗauki nasu Hajja Maimoon ta nufi ciki. Tana shiga parlorn idanun Jannat suka hango mata jakarta a jikin Jauhar. With so much shock ta ware ido tana buɗe baki cike da mamakin Jauhar ɗin. Kamar zatayi magana sai kuma ta fasa ta kumbura fuska ta wuce ɗakin su kai tsaye tana tunanin hukuncin yimata, wata zuciyar ce ke faɗa mata kama da wane ai bata wane, ko babu komai tasan Jauhar harta mutu bazata iya mallakar kwatankwacin irin abubuwan da ta ke dasu ba dan haka zata ƙyaleta for today. Jauhar kuwa sai da ta gama kwaso duka kayan ta shigo dasu sannan ta ɗauki na yaran ta kai musu har bedroom lokacin Suhana tana bathroom tana wanka itama Suhaila ta shiga ɗaya toilet din, Jannat ce kawai ta bararraje akan gado tana ta danna waya dan har lokacin wayar Mommyn tana a hannunta. 


Kallon kan Jannat Jauhar tayi, kitson ya yi kyau sosai har bata san lokacin da tasa hannunta ta shafo kanta ba. Tunawa kawai tayi rabonta da kitso irin haka na mutunci ba zata iya tunawa ba, zata iya rantsuwa tunda ta taso ta fara ganinta cikin duniya ba'a taɓa yi mata kitso mai kyau ba. Lokacin da ta fara girma ne take wanke kanta idan ta samu an bata damar yin wanka sai ta haɗa da kan ta wanke. Lokacin da ta fara sanin kanta a hannun Hajja Maimoon tana tunawa bata taɓa bar mata gashinta a kanta ba, yana fitowa zata sanya reza ta kwashe mata shi tasss sai ta maida kan tamkar saɗal sannan take barinta. 


"Idan ke mayyace Jauhar haka zaki gama ki rabu dani." Jauhar taji Jannat ta faɗa wacce still idanunta yana kan game ɗin da take bugawa. Kanta ta ɗauke daga kallon dake shiga tsakaninta da Jannat ɗin kafin ta buɗe bakinta da kyar wanda ya yi mata mugun nauyi tace. 


"Sorry kitson ne naga yayi kyau, ya burgeni sosai."


"Kinga kuwa har ki mutu bazaki taba ganin irinsa akanki ba koda a mafarki ne." jauhar tasan gaskiya Jannat ta faɗa dan haka ta basar da maganar ta hanyar cewa.


"Ga kayan na kawo." 


"Okay handbag ɗina fa kin gama ɗanawa?" Jannat tayi maganar tana juyowa ta kalli Jauhar ɗin a yatsine kamar taga kashi. 


"Ya za'a yi na ɗana jakarki Jannat? Kawai kaya ne suka yimani yawa shiyasa har kika ga..." Ƙasa ƙara sawa tayi ganin wani kallo da Jannat ɗin ta watso mata, dan yarinyar akwai tsaurin ido ta raina Jauhar da gaske ba kaɗan ba, ta ɗauketa tsantsar mai aiki shiyasa batayi mata komai da sauƙi. Gyara kwanciyarta tayi tana haɗe fuska take cewa. 


"Ai zaki ƙara idan halinki ne, village girl, sannan wai ba zaki dena kiran sunana gatsal ba ko?" Yadda tayi maganar tamkar wata babba yafi komai bawa Jauhar haushi sai dai ko a fuska bata nuna ba gudun abinda zai je yazo. 


"Mekike so nace miki?" Jauhar ta tambayeta tana kallonta. 


"Hajiya ƙarama, karki sake kirana da Jannat saboda sisters ɗina ba zasu kirani da hakan ba kema kice zaki kira." Jauhar ta buɗe baki cike da mamakinta tana ɗan zaro idanuwa, wato tunda taji Mommy na kafa mata doka akan yadda take kiran sunanta itama kafa mata zatayi? Lallai ma to bazata saɓuba, Jauhar ta faɗa cikin zuciyarta don sam bata ji zata iya kiranta haka ba, babu sunan da zata canza mata bare ta kirata da Hajiya ƙarama. Ba tare da ta kulata ba ta juya zata bar ɗakin. Jannat da nata ran ya ɓaci jin shirun da Jauhar ɗin tayi dake tabbatar mata da cewa ba zatayi abinda take so ba ta bita da kallo. Sai da ta kusa fita dan har ta kusa rufe ƙofar Jannat ɗin ta kirata. 


"Ke..!" Kamar ba zata amsa mata ba sai kuma ta dawo ciki tana jiran taji me zata ce. 


"Faɗi muji." Da rashin fahimtar inda ta nufa Jauhar ɗin tace, 


"Mene?" 


"Kice Hajiya ƙarama." 


"Bazan iya ba." Jauhar ta faɗa ba tare da ta sani ba, kawai dai tasan zuciyarta a toshe take ba komai zata iya bari ba a wannan lokacin. Suhana ta fito daure da towel a jikinta daidai lokacin kuma da Jannat ta tsaya gaban Jauhar wacce kansu ɗaya dan rashin kwanciyar hankali da tsangwama yasa sam bata wani girma shi yasa Jannat ke ganinta kamar wata sa'arta. Suhaila ma a lokacin ta fito dan tun tana cikin toilet take jiyo maganganunsu ƙasa. Kafin suyi wani abun dan a cikin su ba zasu ce ga wacce ta fara kaiwa ɗaya hannu ba kawai gani sukayi an hau kokawa. Maimakon su rabasu sai duka suka rufarwa Jauhar kamar dama haushinta sukeji. Ana cewa sarkin yawa yafi sarkin karfi hakan yasa suka riƙa jibgarta duk da tana samu ta ɗan rama akan Jannat data saki wata irin ƙara. Hajja Maimoon ta shigo ɗakin da sauri dan yadda sauttin ƙarar Jannat ɗin yakai mata a kunnuwa yasa ta kasa shiga wankan da take shirin yi a rufe ta ƙaraso ciki ɗakin nasu. Ganin yadda Jauhar ke ƙoƙarin ƙwatar kanta a yanzu ta hanyar kai duka ga duk wanda ta samu acikinsu dan tuni Jannat ta gudu yasa ta ƙarasa da sauri ta wani irin fizgota da karfi ta kira mata mafita har biyu masu kyau tare da hankaɗata gefe. Jannat ta rugo tana kuka ta shige jikin Mommyn tana ɓoye fuskarta. 


"Meye nake gani haka a cikin gidan nan?" Tayi maganar tana kafe Jauhar wacce ta buge da jikin bango da ko zafi bataji ba kamar yadda taji zafin abinda Hajja Maimoon ɗin tayi mata yanzu da idanuwanta da suka gama ƙanƙancewa tsabar masifa. Cikin kuka wanda da kyar muryarta take fitowa tace. 


"Meye nayi da ba za'a soni kamar kowa ba? Me yasa ake son ganin na zama wahalalliya marar galihu acikin gidannan ake bautar dani? Bazan iya ba nagaji da hakan, Mommy ki maidani wajan Babana na zauna a gidansa kamar yadda suma suke zaune da nasu Baban." Habawa tamkar ta kunnawa Hajja Maimoon wuta a cikin zuciyarta, cikin sauri ta isa wajan da Jauhar ɗin take tare da fisgota, fita sukayi daga cikin ɗakin tana janta tamkar ba ƴar Adam ba. A kitchen ta direta tare da zuwa ta zaro wuƙa da ashana ta dawo wajan Jauhar ɗin dake yashe a ƙasa tana kuka. Cikin wani irin fushi da ɓacin rai Hajja Maimoon ɗin ta kyasta ashanar tana kai wutar saiti fuskar Jauhar, muryarta a kausashe take faɗin bayan ta saka mata wukar a wajen wuyanta. 


"Maimata min ki sake gaya min cewa na maidake wajan Babanki ki gani idan ban ƙonaki da ranki ba. Dan ubanki ni zaki kalla kice na maidake? Waye uban naki a duniyar nan Jauhar? Waye shi? Nace wanene shi..!" Ta faɗa a tsawace tamkar kitchen ɗin zai tsage saboda tsananin masifa. Cikin tashin hankali ganin yadda take sake kai wutar wajan fuskarta yasa Jauhar ɗin fara bata haƙuri cike da tashin hankali tana cewa.


"Na dena Hajiya kiyi haƙuri dan Allah bazan sake ba, na tuba bazan koma cewa ki maidani ba wallahi." Cilli Hajja Maimoon tayi da tsinken ashanar ganin ya kusa laso mata yatsun hannu da take riƙe dashi sannan ta koma kai wuƙar wajen wuyan Jauhar ɗin tana ci gaba da cewa. 


"Ubanki ba komai bane Jauhar shi yasa bakya gabansa, ni kuma da aka jonawa ke bana ƙaunarki bare na buɗe ido na ganki a inda nake rayuwata bisa baƙar ƙaddara nake zama dake dan babu yadda zanyi, kin zame min masifa, kin zame min bala'i a cikin rayuwata, dole ce ƙanwar naƙi yasa nake tare dake. Amma banda haka Jauhar da tuni ban sanki ba bare nasan inda kike. Karki sake kai ni bango irin haka idan ba haka ba zaki sha mamaki na wallahi tallahi. Banza kawai, ƙazama, sakarai shashasha. Sannan idan kika sake ɗaga wannan ƙazamin hannun naki akan ɗaya daga cikin yaran gidan nan kisan mezai biyo baya." Ta ƙarasa maganar tana wurgar da wuƙar hannunta gefe. Har zata fita daga kitchen ɗin taji Jannat na cewa. 


"Mommy kice karta sake kiran sunana idan ba zata ce min Hajiya Ƙarama ba." Hajja Maimoon ta kalli Jauhar cikin ƙasƙantarwa tace da ita. 


"Kinji abinda take so ko bakiji ba?" Da sauri Jauhar ta ɗaga kai tana kuma amsawa da bakinta. 


"Toh Hajiya." Daga haka ta fice tabar Jauhar zaune a wajan tana kuka mai cike da ɗacin zuciya. Jannat ta zabga mata harara cike da jin haushinta take cewa. 


"Kina zaune a gidan mu kina cinye mana abubuwa kice ba zaki yi abinda nake so ba? Toh Allah sai kinyi ko mu koreki mu sake wata." Tana kaiwa nan itama ta fice. Jauhar ta kuma fashewa da kuka tana tunanin wannan wane irin masifa ne? Me yasa Mommy takeyi mata haka? Shin da Babanta ya tashi bar mata ita cewa ya yi kar ta gatanta ta? Shin meyasa ma aka barta a wajanta sai kace ita kaɗai ce a cikin danginsu. Wani kukan ta sake fashewa dashi saboda rashin amsar tambayoyin nata da duk duniya babu inda zata iya zuwa ta samesu in ba abakin Mommyn ba, wanda ta tabbatar da yin hakan a wajenta tamkar gayyato ranar mutuwarta ne, Kasa tashi tayi daga wajan bare ta koma ɗakin da yake a matsayin nata. Kusan a kitchen ɗin ta kwana saboda yadda jikinta ya sake rikicewa, haka ta kwana tana masassara babu wanda ya sani daga ita sai Allahn da yasan manufar zamanta tare dasu..

________


Kwance yake akan gado hannunsa waya ce yana ta danne-dannensa, yadda cikinsa yake ta zafi yasan yunwa yakeji amma wayar ta hanashi zuwa ya samarwa kansa abinda zai ci. Kafin kace menene tuni cikin nashi ya wani irin murɗawa hakan yasa yai saurin kifawa kan gadon har wayar tashi tana sabulewa daga hannunsa. Murkusu ya somayi yana riƙe gefen cikinsa. Shigowar ɗan uwansa ɗakin yaga halin da yake ciki ne da sauri ya nufe shi yana kiran sunansa. 


"Zain..! Zain..!!" Shiru ya kasa amsawa dan ko taɓashi ma da ake yi baya so." 


"Mama.. Mama Zain zai mutu." Cewar Al'amin da yake ta kiran Maman tasu. Tana parlor suna cin gyaɗa tajiyo kiran, da gudu suka nufi ɗakin Zain ɗin dan ganin abinda yake faruwa. Ganin yadda yake a kife yasa tayi saurin nufarsa tare da ɗagoshi tana tambayar. 


"Menene Zain?" Ya shiga girgiza kai yana sake dafe wajan da yake masa zafin. 


"Cikin ka ne?" Ya ɗaga kai yana sake lasar lips ɗinsa. 


"Kaci abinci kuwa?" Ta sake tambayarsa a karo na biyu tana ɗago fuskarsa. 


"A'a Mama please ku kyaleni kawai." Ya faɗa a wahale yana son koma durkushewa. 


"Wai me yasa kake neman janyowa kanka masifa ne Zain? Wannan ciwon naka bazai wuce ace ulcer ba ce, so kake sai kaje kayiwa kanka illah sannan hankalinka ya kwanta?." Ta faɗa tana ɗagowa tare da kallo ɗaya daga cikin ƴan matan nata tana cewa. 


"Husnah oya jeki haɗo masa abinci yanzun nan, ke kuma Baby haɗo masa tea." Duk suka juya hankalinsu a tashe ganin ɗan uwan nasu a cikin wani yanayi zuwa aiken na mahaifiyarsu. Kusan a tare suka dawo kowa ɗauke da abinda aka ce ya kawo. A gaba ta saka shi ya ɗan sha tea sannan ya ci abincin suna ta yi masa sannu. 


"Ka fito parlorn mana ayi hira dakai." Maman ta faɗa tana daukar cup ɗin da ya gama shan tea ɗin.


"Mama bari na huta." Ya faɗa yana zamewa ya kwanta. 


"Nasan ba fitowa zaka yi ba Zain, Allah ya kyauta maka sai kace wata mace kullum kana ɗaki." Bai ce komai ba ganin haka yasa ta fito daga ɗakin tana ɗan korafinta wanda inda da sabo yaci ace ta saba da wannan halin ɗan nata...




#A heart touching story

#Gonar Sharri..

#Hajja ce

#Billy s Fari

#Ƴan Tagwaye