GONAR SHARRI...

BABI NA BIYAR

by @billysfari

GS. 5


Haka Zain ya wuni a cikin ɗaki har mahaifin nasu ya dawo gaba ɗaya yaran suka tarbesa da murna da farin ciki. Bayan Mama ta kawo masa abinci da ruwa yaci ne ya kammala yake tambayarta, 


"Ina yaron nan ne?"


"Al-amin?." Mama ta tambaya tana ƙoƙarin kwashe kayan abincin dake gabansa, 


"A'a Zain dai, wane Al'amin daya bar wajen nan yanzu.!" 


"Ai kasan halinsa da zaman ɗaki sai kace sabuwar amarya, yana ɗakinsa yau da ciwon ciki ma ya wuni duk da ina ganin ulcer ce."


"Subhanallahi bai fita wajen aikinsa ba kenan!?" Abban ya tambaya da ɗan ɓaci rai a fuskarsa. Sallamar Zain ɗin tasa shi ɗago kai yana ɗaure fuska, dan idan akwai abinda ya tsana aduniya bai fi yaji ance ɗan nasa bai fita wajen aikinsa ba. Ƙasa Zain ya samu waje ya zauna yana gaida Abban nasu, bai amsa masa ba sai dai yaji ya jeho masa tambaya cikin ɓacin rai.


"Wai me kake son zama ne Zain? Yanzu duk makudan kuɗin dana kashe wajen sama maka aikin nan baza ka tsaya ka maida hankalinka akai ba sai kayi sanadiyar da aka koroka kayi zaman gidan mai dalili? Menene amfanin wannan rayuwar idan mutum ya rasa madogara? Kar ka manta kai ne madubina kuma madogarar ƴan uwanka tunda kana gani ba wani abinyi ne da ni ba da zan iya ci gaba da riƙeku kafin ta Allah yazo kaina, shi yasa na tsaya tsayin daka wajen ganin ka samu ilimin nan da kuma aiki dan kariƙa taimaka min, Shikenan kuma sai kazo kana wasa bayan kasan kuɗin upper ɗin aikin nan da muka ara aka siya har yau ba'a gama biya ba ko? Wannan wace irin rayuwa ce haka? So kake na fara surutai ni kaɗai ko ya ya?" Jiki babu kwari Zain ɗin yace, 


"Kayi haƙuri Abba yau off muke shi yasa."


"Off kuma? Hmmm wai Off..! Shi wannan Off ɗin wai koda yaushe cikin zuwansa ake? Bafa nason ƙarya Zain." 


Murmushi Zain yai yana ganin duk wannan faɗan da mahaifin nasa keyi laifinsa ne da bai zauna ya fahimtar dashi yanayin yadda aikin nasu na nurses yake ba, a yadda kuma mahaifin nasu ya wahala kafin sama masa upper dan fara aikin daya haɗa ƙaddarorinsa ya siyar har gonarsa ta gado daya gada iyaye da kakanni ko shine matsayinsa abunda zai yi kenan koma yayi fiye da yadda yakeyi masa faɗan, saboda kusan dubu ɗari da hamsin mahaifin nasu ya siya masa upper kafin ya samu gurbin fara aiki a asibitin fedral medical center dake nan garin duk da kyan da result ɗinsa ya yi da zamaworsa overall best student of the year, haka yayita zama gidan har na tsawon shekara bai samu aiki ba saboda lalacewar ƙasar tamu har sai da mahaifinsa ya sai masa upper ɗin da kansa. Sanin dalilin yin faɗan Abban nasu yasa Zain sake sanyaya murya akan wacce yake da ita yana cewa. 


"Abba ba karya nakeyi ba, ka'idar aikin mu na nurses idan ka kwana biyar kana aikin safe ko rana koma fiye da kwana biyar ɗin to za'a baka hutun kwana biyu kaje ka huta kafin ka ɗauki wani aikin, idan kuma kayi aikin dare na sati ɗaya ko kwana biyar shi kuma hutun sati ɗaya za'a baka batare da kaje aiki ba saboda ka samu karinka baccin da bakayi ba da sauran ƴan abubuwa da kake buƙatar yi, bayan wannan hutun kuma akwai anual leave shima duk shekara muke samunsa sau ɗaya, akwai kuma casual leave da un expected yake zowarwa mutum, kamar rashin lafiya tazo ma mutum ko kuma wani nashi da yazama dole ana buƙatarshi awajen, ko wani abun daban da zai jawo mutum yabar wajen aikinsa bisa dole ba tare da saninsa ba, sai abashi hutun da bazai wuce sati ɗaya zuwa biyu ba. Sai kuma maternity leave, shi kuma nurses mata kaɗai ake bawa shi, wannan yasa zaka ji akai akai ko nace duk sati sai nace maka off nake." Kalaman Zain ɗin sun sanyaya kusan kaso tamanin na zafin da Abban ya ɗauka, dan haka yace. 


"Ikon Allah, to ai bayani kake mani tun farko Zain, yanzu inna fahimceka hutun sati ɗayan ne ka samu tunda kwanaki naga aikin dare kayi ko?"


"Eh Abba." Zain ya amsa masa yana murmushi ganin yadda fuskar Abban nasi ta washe. Murmushi Abban shima yai yana sauke ajiyar zuciya haɗe da cewa.


"Alhamdulillah ba laifi Allah ya taimaka yabada sa'a."


"Amin ya rabbi Abba nagode da, kulawa."


"To ya jikin naka naji ance bakaji daɗi ba? Gashi dai kasan illar ciwo amma sai kariƙa wasa da lafiyata, kullum kana ɗaki riƙe da waya kana latsawa, Allah yasa ba haka kakeyi wajen aikin naka ba?" Sai da Zain ya gyara zamansa sannan ya kalli mahaifin nasa yana cewa, 


"Alhamdulillah naji sauƙi Abba, ai wajen aiki daban lokacin latsar waya kuma daban saboda bazai yiwu na haɗasu lokaci ɗaya ba, kuma latsar wayar da nakeyi Abba shima wata hanya ce ta samun kuɗi nake amfani da ita, amma dai sai abun ya tabbata tukuna zanyi maka bayaninsa." Daɗi Abban yaji a ƙallah yaji farin ciki tunda riƙe wayar ma ashe kuɗi zai kawo. 


"Allah to ya tabbatar da alkhairi."  


"Amin Abba." Zain ya faɗa kafin su faɗa wata firar shi da Abban nashi. Zain shine babba awajen mahaifinsa malam Abdallah, shekarar data wuce ya kammala karatunsa na school of nursing, mahaifinsu ɗan kasuwa ne dake sana'ar kayan cosmetic acan cikin kasuwa yake da ɗan ƙaramin shagonsa wanda shine sana'arsa tun ƙurciya har zuwa yanzu da girma ya kamashi, kuma da haka yake ɗaukar lalurar duka iyalansa da kuma karatun ƴaƴansa ta yadda idan kaga family ɗin sai sun baka sha'awa. Husnah ke bi masa dake matakin karshe a Sakandire, sai Al'amin dake SS 1, sannan Khadija, Baby da yanzu ta shiga secondary aji ɗaya. Mahaifinsu mutum ne mai jajircewa akan yaransa haɗe da tarbiya daidai gwargwado kuma iya ƙarfinsa, duk da bashi da tarin arziƙi baza kuma akirasa cikin marasa ƙarfi ba kasancewarsa mutum ne mai zuciyar yi da kuma wadatar zuci. Wannan kenan.

_______


Sati ɗaya Jauhar ta kwashe tana zazzaɓi a tsaitsaye wanda hakan baya hana Mommy sata duka aikin gidan kamar yadda ta saba, gabaki ɗaya bata ganin irin yadda ta rame ta fita hayyacinta, idan ma ta lura toh ta shafawa idanunta toka bata mata uzuri kamar koda yaushe. Yau ma tunda asuba take tsaye akan aikace aikacen gidan idan tayi wannan tayi wancan ta gama wannan ta haɗa waccan saboda zuwan yaran gidan makaranta kasancewar yau monday kowacensu da abinda zata ce tana buƙatar tayi mata. Ba ita ta samu ta zauna ba sai karfe tara dai-dai bayan ta tabbatar da kowacensu ta wuce school da abinda fa buƙata. Mintuna uku da zamanta taji sakkowar Hajja Maimoon da maigidan nata daga ɓangarensa sanadiyar firar da sukeyi suna dariya. Da sauri ta miƙe don gaba ɗaya ta manta data kammala haɗa breakfast bata kai kan dining table ta shirya ba. Kayan abincin ta shiga haɗawa a gurguje akan ƙaton tray tafice da sauri ta nufi wajen dining ɗin dasu tun kafin su ƙaraso, tana gama jerasu suna isowa ta koma gefe ta tsaya tana sunkuyar da kanta ƙasa tace.


"Barka da fitowa Mommy ina kwana?" Tafaɗa har lokacin kanta na ƙasa, Hajja Maimoon dake ji tamkar ta hamɓareta ta maka mata harara tana cewa, 


"Ke zo nan." Ba tare data amsa gaisuwar tata ba. Gaban Jauhar is a ne yai wata irin faɗuwa ta ɗaga ƙafafuwanta daƙyar ta tako zuwa gabanta. Jawo ta tayi ta duƙar da ita haɗe da sakar mata wani mugun dundu a bayanta lokaci ɗaya tana kai mata ranƙwashi akai tare da riƙe kunnenta ta murɗe tana cewa, 


"Wai ke wace irin mayya ce da bakya jin magana? Ban hanaki kirana Mommy ba?" Jauhar da tuni azaba ta gauraye mata jiki hawaye na sauko mata tace, 


"Kiyi haƙuri Hajiya mantawa nakeyi."


"Ashe kuwa kin ɗaura aure da wahala dan kuwa daga yau zan fara fasa miki wannan mugun bakin naki mai kama da na munafukai, tashi ki fice min da gani kafin na sauya miki." Jiki na rawa Jauhar tamiƙe zata bar wajen Hajja Maimoon ta daka mata wata uwar tsawa wacce tasa Jauhar ɗin tsayawa cak. 


"Wai ke wace irin daƙiƙiyar yarinya ce ne Jauhar da bazaki iya gaida mutane ba idan kin gansu? Ko ni kaɗai kika gani awajen?" 


"Dady ina kwana?" Jauhar tafaɗa cikin rawar murya har tana tsittsinkewa saboda kuka. Tsaki Hajja Maimoon ta ja shi kuma Alhaji Sha'aban Sada ya amsa da, 


"Lafiya lau, ina yaran sun wuce school ne?" 


"Eh." Ta bashi amsa cikin sanyin murya haɗe da juyawa tabar wajen tana jin haushin yadda suke hanata kiran sunayen su kamar yadda kowa keyi, abin nan yana bata haushi matuka. Sai da Hajja Maimoon ta zuba masa abinda zai ci ya wuce office ta turo masa agabansa ya soma ci sannan ya ɗago kai yana kallonta.


"Wai menene matsalar yarinyar nan ne Mommyn Jannat? Naga keda ita sam bakwa jituwa waje ɗaya ko zaki canja ƴar aikin nan ne?" Sai d Hajja Maimoon takai haɗin yankan soyayyen bread a bakinta ta gutsura sannan ta kalli mijin nata cike da so tana cewa, 


"Zan so haka Ya Habiby, but karka manta labarin yarinyar nan dana baka, ba tada iyaye garin nan kuma kasan ba ƴan garin nan bane kamar yadda na faɗa maka, matsalata ɗaya itace ina zata tafi idan na koreta daga gidannan? Na tabbatar komai daren daɗewa waɗanda suka tilasta min zama da ita zasu dawo su nemeta, wallahi Ya Habiby na tsani yarinyar nan fiye da tsammaninka, kallonta kaɗai idan nayi sai ya haifar min da damuwa saboda kwata-kwata bana son ganinta, shiyasa nace maka in har kana so na kadena tausayinta zai iya saka nima nazo nafara tausaya mata saboda soyayyar da nakeyi maka tafi komai a cikin zuciyar nan tawa. Kuma wallahi bata cancanci hakan daga wajena ba takowace irin fuska dan mahaifinta bashi da mutunci ɗan akuya ne da bai san darajar ɗan Adam ba." Taƙarasa zancen idanuwanta na kawo hawaye. Damuwa shima Alhaji Sha'aban Dada ya shiga ganin Hajja Maimoon ɗin acikin wannan yanayi saboda ba kaɗan yake jinta aransa ba, tun mutuwar matarsa data barmasa ƴaƴa yayi tsammanin yai bankwana da farin ciki, amma shigowar Hajja Maimoon rayuwarsa da yadda ta riƙe masa ƴaƴansa yasa ya manta da duk wani raɗaɗin baƙin ciki daya shiga zuwa farin ciki kamar yadda ta ɗora shi, ta haska masa rayuwarsa shi da ƴaƴansa ta kuma basu farin ciki da kulawa marar misaltuwa, shi yasa baya son abinda zai taɓa mata zuciya ko kaɗan. Cike da kulawa yake cewa, 


"Sorry Mommyn Jannat, a iya tunanina tunda hannunki ta taso yakamata ko meye kiyimanta kiyi hakuri ba dan iyayenta zaki yi ba please kiyi haƙuri.." Saurin ɗaga masa hannu tayi haɗe da cewa, 


"Dan Allah kaima kada ka soma tursasa zuciyata abinda bazata iya ba akan yarinyar nan Habiby, zan so ko Irfaan kayi masa magana yadena shiga shirginta bana so, hakan ne kawai ke sa ina jin sassauci a zuciyata idan ina ganinta cikin kunci da damuwa, domin ta sanadiyarta nima na shiga fiye da irin wannan damuwa da ƙuncin da kuke ganin kamar tana ciki."


"Is ok." Yafaɗa yana ɗan sakata ajikinsa tare da bubbuga bayanta alamar lallashi. Sai da yaga ta koma masa yadda yake so sannan ya ɗauki spoon ɗin dake gabanta ya yanko omalet egg ya kaimata a baki yana cewa, 


"Have your food sai ki rakani kada na makara." Ta buɗe baki yasaka mata soyayyen ƙwan yana jan karan hancinta. Sai da ta kammala ta rakashi har bakin mota ya buɗe ya shiga ya tayar yafice sannan ta dawo ta haye sama abunta ba tare da tabi takan Jauhar ba, don da gaske dole ke sa tana jurar kallonta ba dangantakar so ba.


Jauhar na ganin Hajja Maimoon ta haye sama ta dawo ta kwashe kayan takai kitchen ta tatattara sauran abincin da suka rage ta canye ta wanke kayan ta maida kowane inda yake, dama ta gyara kitchen ɗin dan haka ta ɗora girkin rana sannan ta wuce palourn ta gyara ko'ina, tana kammalawa ta haye sama ta gyara ɗakinsu Suhana ta wanke toilet ɗin, sai da ko'ina yayi tsaf sannan ta rufe ƙofar ta koma kitchen tana jiran Hajja Maimoon ta sakko dan ta samu ta shiga gyara mata nata ɗakin. Tana cikin soya miya taji Hajja Maimoon na kwalo mata kira kamar wacce ta rasa idanu cikin wata irin hargatsattsiyar murya dake cike da tashin hankali. Spoon ɗin dake hannunta ne data gama juya miyar ya suɓule ya faɗi ƙasa saboda gigicewa takai hannunta daƙyar ta rage wutar don kar ta kone ta sake shiga wani tashin hankalin sannan da sauri ta fice ta nufi stairs ɗin da Hajja Maimoon ke tsaye ta cika tayi fam sai wani hayaƙi ke tashi akan fuskarta tamkar haɗuwar baƙin hadari tsabar masifa. A gabanta Jauhar ta zube ƙirjinta naci gaba da faɗuwa duk da batasan abinda ke faruwa ba. 


"Ina kika kai min gold ɗina?" Hajja Maimoon tafaɗa cikin kakkausar murya tana zare mata idanuwa, wanda hakan yayi daidai da ɗaukewar ji da ganin Jauhar na wasu mintuna kanta na juyawa haɗe da sara mata lokaci ɗaya jin kalaman na Hajja Maimoon da daidai suke da saukar aradu acikin kanta.


"Gold kuma Hajiya! Wane irin gold kuma?" Jauhar tafaɗa cike da ruɗewa tana juya lamarin a ƙwaƙwalwarta, dan a iya saninta ko inda gold yake ajiye bata taɓa bi ta wuce ba in ba a wuyan Hajiyar ta gansa ba koma yaran gidan, to meye hadinta da shi da za'a tambayeta? fisgota ɗin da taji Hajja Maimoon tayi ta taso ƙeyarta zuwa gaba suna sakkowa ƙasa ya maido da ita daga tunanin da ta shiga yi, 


"Na rantse da Allah sai kin fito min da gold ɗina ko nasa kiyi nadamar haihuwarki aduniya yau Jauhar dan bazan taɓa kyaleki ba ɓarauniya mai halin ɓeraye." Wasu zafafan hawaye ne suka samkowa Jauhar tana kallon Hajja Maimoon dake faman turota ƙasa take cewa, 


"Wallahi ban ɗaukar miki gold ba Mommy, ban san ma inda kike ajiyewa ba in ba a jikinki na gashi ba.." Kafin ta rufe baki Hajja Maimoon ta kai mata wani wannan bugu a baki tana cewa.


"Ƙarya kikeyi munafukar yarinya duk gidan nan waye ke shiga ɗakunan idan ba ke ba? To wallahi nafison gold ɗin nan akanki dan haka maza muje ki fitomun da kayana." Taƙarasa zancen tana turota da ƙarfi har sai da taga ta shiga gangarowa daga stairs ɗin daya rage musu sauran hawa bakwai su sakko. Tuni goshin Jauhar ya fashe lokacin data ƙaraso ƙasa kanta ya bugi karfen dake jikin stairs ɗin wajen hawa. Cikin rashin nuna damuwa Hajja Maimoon ta sake fisgota daga ƙasan ta turata zuwa ɗakinta, kayanta tasa ta shiga ɗakko mata tana watsa mata su ɗaya bayan ɗaya tana neman gold ɗinta aciki amma bata samu ba, hakan yasa ta nufi wajen ƴar ƙaramar wardrobe ɗin dake jikin ginin ɗakin tana watso sauran kayan Jauhar ɗin da undies, nan ma bata samu komai ba tayo kanta tana faɗin.


"Ina kika je kika ɓoye shi? Muje ki fito da shi tun muna mu biyu Jauhar ko kuma na lahira yafiki jin daɗi acikin gidannan."


"Mommy wallahi ban ɗaukar miki ba.." 


"Toh uban waye ya ɗauka Jauhar? ina ke kaɗai ce ke shiga dakina agidannan ko gold ɗin zai dauki kansa ne?" Hajja Maimoon ta katseta a hasale tana yowa kanta wanda hakan yasa Jauhar ficewa daga ɗakin aguje dan ta tabbata komai zata iya yi mata idan tariƙeta acikin gidan nan da suke daga ita sai ita kaɗai. Tana kawowa palour Irfaan na shigowa jikin Jauhar na rawa ta ruga ta ɓuya a bayansa tana neman ceto..



#A heart touching story

#Gonar Sharri..

#Hajja ce

#Billy s Fari

#Ƴan Tagwaye