SHAFI NA 7
A razane su ka mike tsaye sabo da firgici, ganin azzalumai zagaye a gabansu dauke da bindigu.
Cikin tashin hankali su ka mimmike tsaye, wasu kuma anan wajen zuciyoyin su, suka buga sabo da tsananin tsoro.
Haka aka tasasu gaba, sai ma'ajiyar barayi.
San nan suka nemi ba'asi akan wanda ya kawo shawarar guduwa.
Cikin dakewa irin na mazajen farko, Lukman ya mike tsaye ya ce shine.
Da sauri ta daga kai tana kallonsa, jin abun da yake fada.
"Idan har nabar hakan ta faru, banyi mishi adalci ba, dole na karbi laifin da ni ce silar aikata shi. Sai kuma gabanta ya dinga faduwa. Ba tasan irin hukuncin da zasu yanke akanta ba.
Tunowa tayi da iyayenta tamkar yanzu abun ya faru haka take gani a idonta.
"Tsoro ba naki bane Joɗa, jarumi shike kafa tarihi a kundin rayuwarsa. Ja da baya ga abokan gaba, ci bayane, Allah na tare dake Joɗar Baffa."
Wannan ita ce maganar karshe wadda Hamma Gidado ya furta mata, a lokacin da yake kan gangara.
Kafin ta dawo duniyar mutane, har an fito da Lukman za ayi mishi hukunci.
"Ba shi ya aikata ba, Ni ce." suka tsinkayi muryarta
Kan bindiga suka kwadawa Lukman, san nan suka ce, "Zaka fada mana gaskiya ko sai mun kashe ka?
Har sun fasa mishi goshi.
Cikin dakewa ya ce , "Ni ne ba ita ba ce.
Ganin sun seta bindiga akansa, zasu harbe shi, ya sa tayi saurin ce,
"Wallahi Ni ce, shi babu ruwansa a ciki.
Tura shi gefe suka yi, su ka damko gashin kanta su na ja, sai a tsakiyar fili.
Cikin harshen fulatanci daya daga cikin su ya tambaye ta, "ina kika samo Aska?
"Lokacin da akazo kwance Ni zanyi fitsari, anan Aska ta fado daga aljihu na dauka."
Kafin ta rife baki har wani ya kai mata wawan mari a fuska.
San nan suka rirriketa aka yi mata bulala dari,tare da horon yunwa5
Tun da aka fara yi mata bulala Lukman kanshi na kasa.
Mutanan wajen duk sun tausaya mata, wasu kuma tsoro ya kara shigarsu, duk da sun sha ganin an kashe rayuka a gabansu.
Amma wannan kuma, wani abu ne na daban.
#YAR MUTAN ARGUNGU