HAJAR

{21..}

by @feenerhfeeche


A hankali Nurain yayi knocking ƙofar ɗakin Hajiya, da ga cike akace "waye ne?". Nurain ya haɗe gira snn ya murɗa ya shiga. tinda ya shigo Hajiya da ke zaune bisa lallausar rug ɗin ɗakin take kallonsa har ya zauna a ɗaya daga cikin kujerun ɗakin. Hajiya ta gwalo ido cikin ƙwamemen glasses ɗinta tace "O oho ashe Usuman ne, ai daman tinda naga abu kamar fel waya nasan kaine, angona ba sangameme bane irinka, ni ko yaushe ma zai dawo daga ƙasar can mai ƙanƙanra karfa ya daskare na shiga uku....", Nurain yace "su duk mutanen da suke rayuwa a ƙasar basu daskare ba sai shi", tace "A'a bar wannan zance ai su daman can ƙanƙarar ta gama musu illa sun saba", yace "shima ya saba aii", tace "inafa zai saba, shi da ba jinsin su ba, mutane kamar an bursuna musu garin filawa, angona da yake baƙi ai sam ba gami tsakaninsu, da zan samu jirgin da zai kai masa saƙo ai da na bada maganin sanyi an kai masa..", Nurain yace "toh ki kwantar da hankalin ki next week zai dawo", ta kallesa ta saman glasses ɗinta tace "Au shi Umarun ne zai dawo?, eh ai gara ya dawo kar ya daskare gsky, to kai wa ya gaya maka zai dawo?", Nurain yace "A waya mu kay magana", tace "Oh ni, babu yadda banyi da yarinyar nan Shatu akan ta kira min shi ba amma ta ƙi, yaufa wajen wata guda kenan ina fama da ja'irar yarinyar nan, yanzu kam tinda kazo maza kamo min shi na gansa..", yace "ki bari nan da mako mai zuwa zaki gansa a zahiri yanzu dare ne a can", kafa masa dattijan idanunta tayi ta saman glasses tace "Auu, kaima ja'irin ne kenan?", hade gira yayi yana pointing kansa yace "nine ja'iri Hajiya?", tace "yo ba gashi na gani ba, nace ka kiramin mijina kace min wai dare yayi sbd ka iya lafto ƙarya, ga rana gatsal-gatsal amma kana kiran dare..", gyada kai yayi yace "toh shknn, ni daman zuwa nayi muyi sallama jibi zan bar ƙasar", zaro ido tayi tace "zaka bar ƙasar kamar ya?, kaima garin arnan zaka koma?", yace "Eh", tace "amma dai ban taɓa sanin notin kan Muntari ya kunce ba sai yanzu, shine ya barka ka koma ƙasar arnan, har itama Khadijan notin kanta ya kwance wllh. kamar abin arziƙi ka doshi hanyar zama cikakken mutum sai kuma ka koma baya, da tini kaima da iyalinka dan ma yarinyar ta kasa ka, au koda yake ba jikana ta kasa ba wllh kanta ta kasa, eh shegiya ita taga duhu wllh dan har abada ta rasa nagartacce kamar jikana....", Nurain ya haɗiyi wani yawu cause his wound is still fresh yace "bari na kira miki angon naki", wayarsa ya ciro daga pocket ya kunna data ya shiga kiran Farooq video call. ba ta daɗe tana ringing ba Farooq ya ɗaga. Nurain yayi waving hannunsa a screen ɗin wayar yace "ba fa na ganinka, ka kunna haske Iron Lady ke son magana da kai", Farooq yace "Ohh really, seee yaah My bride" ya miƙe daga kan table ɗin karatunsa ya kunna Light, fuskarsa ta bayyana raɗau sbd haske, yau ma dai jibgegiyar sweater ce ajikinsa, Farooq yace "tana ina?", Nurain ya haska masa fuskar Hajiya, Hajiya na ganin Farooq tace "innalillah wa'inna ilayhirraji'un me ya kumbura ka haka sai kace wanda aka buga masa iska?", Farooq yayi murmushi sbd ba abinda yake gani sai fuskarta da kantamemen glasses ɗinta sun cika screen ɗin wayar. Hajiya tace "ka yiwa Allah da manzon sa ka dawo gida", Farooq yace "next week zan dawo amaryata", tace "Atoh ya dai kamata wnn kumburi haka..", Farooq yace "ba fa kumbura nayi ba rigar sanyi ce, bari na cire ki ga", da sauri ta katsesa tace "A'a karka cire ka daskare, tinda dai baka kumbura ba shknn", Farooq yace "toh shknn". tace "kaga wnn fel wayar wai shima ƙasar arnan zai koma sbd shegiyar yarinyar da zai aura ta gudu ta barsa shine ba zai nemi wata ba", Farooq was shocked da abinda ta faɗa amma yace "ni kam ina dawowa zan miki kishiya", tace "Eh maza ka dawo kayi min ai kishiya alheri ce indai ta gari ce..", yace "Au ba kya kishi na kenan?", tace "kaji wani zance yo wnn ai shine kishin", Farooq ya murtuke fuska kamar gaske yace "ni bani ɗan uwana", Nurain ya karɓi wayar don yanajin komai da suke faɗa. Farooq yace "so that's why you said until your heart heal?", Nurain ya gyaɗa kai yace "sure, and now it's healing..", Farooq yace "wish you all the best bro", Nurain yace "thank you i will call you tomorrow" ya katse kiran. ganin magrib na dosowa yasa Nurain ya yiwa grandmother ɗin tasa sallama, Hajiya tace "toh yanzu sai yaushe Usuman?, kaima shekarun zaka ɗauka kamar Umaru ko?", yace "A'a Hajiya, wata takwas zan yi insha Allah na dawo gida", tace "O oho har wata takwas ɗan nan, Allah ya tsare...", ta miƙe tana dogara sandarta ta shiga bedroom ɗinta, bayan wani lokaci ta fito da ƴar leda tace "ungo na kane kai kaɗai, karka tsamma kowa", ya karbi ledar yana leƙa cikinta yace "wai har takwarar taki?", tace "A'a ni ba takwarata bace, ni ba sunana Noor ba", yace "ai ɓoyewa akai, to Hajiyarmu khairan", Hajiya ta fara matsar kwalla tace "to Usuman ka kula da addininka don Allah", yace "insha Allah" da haka ya nufi door ya fita, saida sukay sallama da Ummi snn ya wuce. 


★Tin safe Hajar take neman hanyar da zata sanar da Anty zuwan Nura, sau biyu tana attempting amma saita kasa, a zaune take akan stairs ɗin varendern palour, wayarta ce ta fara ringing, yamutsa fuska tayi ganin numbern dake kiranta, a fili tace "na shiga uku wai wnn wane irin naci ne", tana kallon wayar har kiran ya katse wani ya sake shigowa, 20+ missed call yayi mata daga safe zuwa yanxu, da kyar ta ɗauka ta wani sha kunu, daga ɗaya ɓangaren Ahmad yace "Assalamu alaikum", a wani daƙile tace "wslm", yace "how are you?", tace "fine", yace "alhmdllh, Hajar plxx just give me a chance to show my feelings", tayi gathering courage tace "don't you have anything else better to do?, I'll pretend that I didn't hear that", ya sauke ajiyar zuciya a hankali yace "you heard everything, you can't pretend that you didn't", ta ciji lower lip ɗinta painlessly dan sosai maganarsa ta shigeta, tace "i have to hang up....", pleadingly yace "plxx answer me before you hang up", kasa cewa komai tayi, shiru ne ya dauka har hakan yasa su ke jin breathing din juna, tayi twinking lulu eyes dinta tace "aiki nake yi", after few seconds yace "alright...", da sauri ta katse kiran ba ta jira sauran cewarsa ba. blocking numbernsa tayi snn ta goge call log ɗinsa gaba ɗaya, murya can ciki tace "Allah ya baka gaba Ahmad". bata da wani space a zuciyarta, Nura has already filled everywhere. knocking gate aka yi ta miƙe ta buɗe, su Hafsa ne suka dawo daga school, Hajar ta matsa musu hanya tace "barka da dawowa yan bokoko", Hafsa tace "na dai kusa gamawa", ƴar autar Anty kam tini ta wuce ciki tana fige hijab ɗinta. bayan Sallahr la'asar Hafsa ta shiga ɗakinsu tana dafe kai, Hajar da ke nannaɗe darduman da tayi sallah tace "lafiya?", Hafsa ta yamutsa fuska tace "kaina ke ciwo", Hajar tace "sannu kinsha magani?", Hafsa tace "A'a yanzu dai zan je wajen Anty na amso paracetamol", Hajar tace "okay, zauna na kama miki kan sai kuma kisha magana za kiji sauƙi sosai", Hafsa tace "tom" ta zaune gefen gado, gefenta Hajar ta tsaya snn ta fara kama mata kan tana hura mata addu'a, tana gamawa ta matsa thick vein ɗin goshin ta yarfe tace "toh ya kika ji?", Hafsa tace "wllh har ya lafa sosai" ta mike zata fita a ɗakin, Hajar tace "wajen Antyn zaki amso magani?", Hafsa ta gyaɗa mata kai, Hajar tace "dan Allah kice mata anjima zanyi baƙo", Hafsa tace "Au haba mutumin jiya ne zai zo?", Hajar tace "kinji ki da wani zance wai mutumin jiya toh bashi bane", Hafsa tace "toh waye?", twinking eyes Hajar tayi tace "Ya sayyadi na ne zai zo", Hafsa tace "wai daman har yanzu kuna tare da Nura?", Hajar tace "Eh, ai iyayensa ma sunje wajen Baba", Hafsa tace "kaiii amma shine baki fadamin ba, da yaushe zai zo?", Hajar tace "da yamma", Hafsa ta fita daga ɗakin ta shiga kitchen ta ɗauki pure water snn ta shiga room ɗin Anty, motsin ruwa taji a toilet, bedside drawer ta janyo ta fara neman Panadol tinda anan suke ajiye first aid drugs, ta dauke panadol ta ɓalli two tablets ta mayar da sachet ɗin. da kyar ta haɗiye maganin tana yamutsa fuska, Anty ta fito daga toilet tana gyara hular kanta tace "ku shirya ke da Hajar muje barkar Fauziyya", Hafsa tace "yanzu zamu?", Anty tace "Eh", Hafsa ta ɗaga ragowar pure watern da ta sha drug tace "Anty wllh kaina ke ciwo yanzu ma nasha magani, ko na bari ranar suna naje da yamma", Anty tace "tom shknn, kyaje ranar suna dama ba zuwa zanyi ba", Hafsa tace "tom, Hajar tace anjima za tay baƙo", Anty ta ciro kayan da zata saka daga wardrobe tace "ke ta aiko knn?", Hafsa tace "A'a wai bazata iya gaya miki ba", Anty tace "toh shknn, sai ta saukesa a sitting room, akwai semosa a fridge", Hafsa tace "tom" ta miƙe ta fita. Anty tana gama shiryawa ta ɗauki handbag dinta ta fita, ɗakinsu Hafsa ta shiga tace "toh sai Allah ya dawo dani", Hajar tace "Allah ya tsare", Hafsa tace "sai kin dawo". Biyar da rabi na yamma Hajar ta fito daga wanka, ta shafe jikinta da sabon cream ɗinta mai daɗin ƙamshi, riga da skirt ta saka na atamfa ta tsaya gaban mirror tana cakare ɗauri, Hafsa ta shigo tace "uhmm kinyi kyau, na gama soya semosan", Hajar na zizara kwalli a fatar manyan idanunta farare ƙal tamkar madara tace "nagode". wayarta dake tsuwwa ta ɗauka ganin me kira tayi murmushi tace "ina jin ma ya iso", kara wayar tayi a kunne tace "okay, gani nan fitowa", mayafin da ta fitar ta ɗauka ta yafa, Hafsa tace "laa ya naga kinsa mayafi ba Hijab ba, ko ba ustaz bane?", Hajar ta zabga mata harara tace "chab wai dan yana malamin islamiyya shine zai zama ustaz, wllh ba ruwansa indai zaki saka abinda zai rufe miki jiki to shi bashi da damuwa", Hafsa ta kalleta sama da ƙasa taga dai ruf mayafin da ta saka ya rufe mata jiki kuma ba shara shara bane, Hafsa tace "Eh, kinsan mazan ma kowa da ra'ayinsa, wani yafi son Hijab wani kuma mayafi wani kuma duka, wani kuma babu ruwansa indai za kiyi decent dressing is okay", Hajar tace "that's my Man shima decent kawai yake so", Hafsa tace "yana fa jira", Hajar tayi wasa da kwayar idonta tace "ai ya saba" ta ɗauki turare ta fesa sama sama. slowly Hajar ta fito compound ta nufi gate, ta bude ƙofa ta fita, yana tsaye jikin fillelen sabon motorbike dinsa yana danna wayarsa, yana ganinta yayi murmushi ya mayar da wayar aljihu, kallonta ya ringa yi ba ƙiftawa har ta ƙaraso, sosai silent kwalliyar da tayi da kuma decent dressing ɗinta ya tafi da imaninsa, sunkuyar da kanta tayi tace "sannu da zuwa", baice komai ba kawai kallonta yake, shirun da taji ne yasa ta ɗago kanta ai kam sukay ido huɗu, tayi sauri ta sunkuyar da nata tace "Bismillah ka shigo", yace "A'a nidae bazan shiga gidan mutane ba", tace "toh nan fa kan hanya ne", ya dubi street ɗin yaga akwai mutane yace "toh amma dai ansan da zuwa na dai ko?", childishly ta hararesa tace "Bismillah" ta juya ta koma ciki ba tare da ta jira cewarsa ba. bayanta yabi har suka shiga gidan tayi leading ɗinsa har sitting room. a kujera one seater ya zauna ita kuma ta zauna a two seater dake gefensa, Calmly tace "ina yini", ya ringa kallonta, ɗago kanta tayi jin bai amsa ba sukay ido huɗu, tayi pouting lips ta rufe fuskarta da palms ɗinta tace "dan Allah ka barii", murmushi mai sauti yayi yace "me fa?", tace "why are you staring at me?", yace "because i missed you so much and you look beautiful", murmushi tayi tana wasa da yatsun ƙafarta, yace "ba ki rubuta Jamb ba ko?", ta gyaɗa masa kai tace "Eh neco kawai na zana", yace "Ohk, suma yanxu school of Nursing suna amfani da jamb, gashi baki rubuta ba amma ba damuwa saiki rubuta next year ko?", tace "Admission din bazai samu ba saida Jamb result knn?", yace "Eh, ai da nasan sun canja tsari da sai kin zana jamb, kamar yanxu ne zaki ji an fara registration, and you're still young kinada enough time", tace "Ahh I'm not young", yace "ohk sai ki gayawa wanda bai sanki ba to me you're a little girl kuma you know akwai certificate of birth ɗinki a wajena", sallama akai a bakin ƙofa Hajar ta amsa, Hafsa ce ta shigo tana sanye da hijab hannunta riƙe da tray mai dauke da bottle water da drinks sai kuma plate ɗin semosa, a hankali ta ajiye trayn akan Centre table ta zauna kusa da Hajar, Hafsa tace "sannu da zuwa, ina yini", Nura yace "mun yini lfy?", tace "alhmdllh", yace "masha Allah, ya karatu?", Hafsa tace "alhmdllh", a hankali Hafsa ta miƙe ta basu waje tana fita ɗakin akay knocking gate, bakin gate ɗin ta wuce ta buɗe ƙofa, ita tasha ma Humaira ce ta dawo daga islamiyya amma me sai taga wani yaro, tace "ya akai?", yaron yace "wani mutum ne yace wai ana sallama da Hajar", tace "yana ina?", yaron yayi nuni da wata jugunanniyar mota dake gefen titi a parke, Hafsa ta kalli mutumin da ya fito daga cikin motar, zaro ido tayi sbd ta ganesa, shine mutumin da suka hadu jiya a supermarket, Ahmad ya ƙaraso bakin gate ɗin yana kallon Hafsa da itama take kallonsa cike da mamaki.......✍️