HAJAR

{26..}

by @feenerhfeeche

Wannan time ɗin ma dai Ruqayyah a ciki ta ji bugun zuciyarta, har wani darkness ne ya rufe mata sight, sama sama taji muryar Dr Marwan, a firgice tace "Dr, kamar dai banji me kace ba..", yace "i said kinyi shiru..." da sauri ta katsesa tace "No ba wnn ba", kallonta ya ringa yi ganin she isn't herself yace "ohk, which one?", tace "you said something like Boss yana India, this Friday ya tafi", he can't help it dole yayi blushing yace "Ohh you heard it, am jet serious baya nan, sai nanda 8months insha Allah zamu gansa", ƙirjinta ta dafe tace "8months..", katseta yayi yace "A Nurse i thought you are here for something serious, but i have patients waiting outside", tamkar wacca aka zarewa spine haka ta miƙe tace "Alright, thank you for the little time" da haka ta nufi door ta buɗe ta fita, da kyar ta isa Nurse station cause har yanzu darkness ɗin da yayi mending sight ɗinta bai gama fading ba. room ɗin dake station ɗin ta shiga, tsaye tayi tamkar wata statue, a tare ƙafafuwanta da hannayenta suka fara karkarwa sai kace wnda aka jona musu shocking machine, ta dubi Mug ɗin hannunta mai ɗauke da coffeen da ya zama tap water tsabar hucewar da yayi, tasss Cup din ya faɗi ya tawarwatse, two seconds da faɗuwarsa itama ta bisa ƙasan. kuka take son yi amma ta kasa, tears sun ƙafe a idanunta, kawai mgnar Dr Marwan ce take amsa ƙuwwa a kwanyarta, she spent 15 good minutes durƙushe tana kukan zuci, ta lumshe idonta da ƙarfi, she wish this is nothing but a nightmare, ita kanta tasan she was just fooling herself babu wani nightmare. wata colleague ɗinta ce ta shigo, kallonta ta tsaya yi kafin ta dubi broken cup ɗin dake ƙasa tace "Ruqayyah are you okay", Ruqayyah ta miƙe tana murje idonta wanda take fatan hawaye ya cikosa tace "partially, kai na ke ciwo Amina", Amina tace "ohh sorry bari na kawo miki drug", tsugunnawa Ruqayyah tayi ta fara picking pieces ɗin broken cup ɗin tace "don't burder I'm going home", Amina tace "Okay lemmi help you", Ruqayyah ta tashi ta dafe kanta tace "thank you", tarkacenta ta ɗauka ta bar asibitin da ya zame mata one living hell, a wani book shop ta tsaya ta siyi plain sheet da envelope snn ta fito ta tari Napep ta wuce gida, kafin taje gida ciwon kan da ta kirawa kanta ya lulluɓeta, a ɗan madaidaicin compound ɗin gidan nasu ta tsaya, ta zauna akan dakalin shiga main building ɗin, jakarta ta buɗe ta ɗakko pen da plain sheet ɗin da ta siya ta ɗora akan jotter, tana ɗora pen kan papern hannunta ya ringa rawa, da kyar ta gama rubuta umarnin da Daddy ya bata, tayi folding papern ta saka cikin envelope amma bata liƙe ba, tashi tayi ta shiga ciki da sallama, Momy dake zaune palour ta amsa, Ruqayyah da kanta ya fara juya mata tace "Momy barka da gida, na dawo", Momy ta kalli agogon dake palourn tace "da wuri haka", Ruqayyah ba tace komai ba, Momy ta taɓe baki tace "ina resignation lettern?", Ruqayyah ta miƙe mata white envelope dake hannunta, amsa Momy tayi ta ajiye hannun kujera, Ruqayyah tace "Momy na shiga ciki" ta wuce room ɗinta, da ido Momy ta bita ganin yadda ta dawo odd, she looks disturb and weak. wunin yau Ruqayyah bata ji daɗinsa ba, tama rasa meke damunta, gaba ɗaya ta kasa figuring out what is happening to her, abinci ma saida Momy ta kirata tace mata taci snn taci kaɗan, that was bayan sallar la'asar, tinda taci ta koma ɗakinta har akay sallar magrib da isha bata fito ba, tana kwance kan tiles tana juye juye Momy ta shigo, kallonta ta ringa yi kafin tace "ke me yake damunki ne waii?", zaune Ruqayyah ta miƙe tace "ba komai Momy", ai ko karen hauka ne ya cijeta bazata iya faɗin damuwarta ba, daman Momy ba haƙura ta gama yi ba tasan tsaf za tace mata Allah shi ƙara or something that will add salt to her fresh wound. Momy tace "ki sameni a palourn Daddy yanxun nan, kuma in kinje karki ce komai haquri kawai zaki basa", Ruqayyah ta gyaɗa kai, Momy ta juya ta fita. Ruqayyah ta ɗauki hijab ɗin da tayi sallah ta saka ta fita, zuciyarta na lugude ta shiga palourn Daddy, rakuɓewa tayi gefe saman carpet ta zauna, Daddy ya ɗauki envelope da ke gefensa ya wurga mata yace "ni zaki kawowa ko ni na baki aikin?", Ruqayyah dai kanta a ƙasa tace "sorry Daddy, dan girman Allah kayi haƙuri, wllh i learn my mistakes", keenly yace "wane mistake?", kuka ta ringa yi kamar ranta zai fita tace "kayi haƙuri dan Allah..", wani ɓoyayyen ajiyar zuciya yayi baice komai ba, sai a lokacin Momy dake zaune palour itama tace "ayi mata afuwa Alhaji, wnn shine first time da tayi wronging namu amma kuma she won't go free ayi mata wani hukuncin dan Allah", shiru Daddy yayi na wani lokaci kafin yace "da farko ma dai ina yarinyar taje?", Momy ta kalli Ruqayyah tace "talk", Ruqayyah ta sharce hawayen idonta tace "Egypt naje", baki buɗe Momy tace "Ruqayyah me ya kaiki Egypt?", Ruqayyah tace "kuyi haƙuri dan Allah..", wani tsawa Momy ta daka mata tace "wnn ba zancen haƙuri bane magana za kiyi malama", Ruqayyah ta kwantar da murya tana shessheƙa tace "wani aiki naje nema amma ban samu ba...", Momy tace "karki bari na sake tambayarki Ruqayyah, I'm giving you this last warning, ki gaya min komai", Ruqayyah ta share zufar dake keto mata tace "few months kafin a kawo kuɗin aurena na cike wani form online na wani aiki da ƙasar Egypt take bayarwa na waɗan da suke da karatu a fannin lafiya, aikine na shekara ɗaya mai kyau, bayan na tura musu form ɗin suka turomin da saƙon cewa zasu nemeni domin yin interview, ban sake samun wani message ba har sai ranar wata alhamis ranar mother's eve ɗina, tsakar dare na ga message cewa anyi hiring ɗina don haka kafin ranar Monday na kasance a garin Cairo, ban tafi haka ba saida na ajiye muku latter ai kuma shima Nurain na tura masa saƙon cewa ya jirani zan dawo, ranar juma'a na hau jirgi zuwa Abuja kamar yadda suka ce nan ne meeting point ɗin da zamu taru kafin mu wuce Egypt, A Cairo Monday ta riskeni, akay mana interview amma ni banci ba, don haka suka ce na ƙara gaba baza a ɗaukeni ba, da kyar na samu aikin da nayi na samu kuɗin ticket din jirgi na dawo Nigeria, Momy Daddy wnn shine gaskiyar dan Allah kuyi haƙuri na ɓoye muku da nayi, ina tsoron ku hanani shiyasa ban gaya muku ba...", Daddy ya jinjina kai ya kalli Momy yace "barin aikin shine hukuncin da ya dace da ita...", Momy dai tayi tagumi takaicin ƴarta ta ya gama cikata, ajiyar zuciya tayi tace "get out Ruqayyah", Ruqayyah na sharɓe hawaye ta miƙe ta fita, Momy tace "Alhaji karka yanke hukunci cikin fishi, ka tsaya kayi nazari dan Allah, yaran yanxu sai a hankali idan ka biye musu sai ka bata musu rayuwa da baki ko kuma ka tagayyara su da wani action ɗin, Allah ya huci zuciyarka, plxx think twice kafin ka zartar da hukunci...". ajiyar zuciya yayi yace "toh aurar da ita zanyi daman har yanzu Dauda na ciki", Momy tace "Eh ba damuwa gara ayi mata auren" da haka ta tashi ta fita.


★Tinda aka mayar da Sa'adatu da Maimuna makaranta shegun suka samu babban lasisin tsula tsiyarsu, yau sati uku kenan sau ɗaya suka taɓa zuwa, a kullum zasu shirya cikin uniform harda jaka snn su fita, daga sun fita sai ko wacca ta kama hanyarta, Maimuna ta wuce yawonta daga wnn hotel ɗin zuwa wani, Sa'adatu kam gidansu Mabaruka take wucewarta su sheƙa ayarsu san ransu, daga lokacin tashi daga makaranta yayi sai su dawo gida, hakan ba ƙaramin daɗi yake musu ba, su a ganinsu da baƙi ƙirin gwara baƙi baƙi. A fanin Hajar kam babu abinda ya shalleta dasu, a kwandon shara ta wurga su, ita gani take ma kamar babu su a gidan, koda sun takaleta saidai ta yamutsa fuska tayi banza dasu ko kuma ta shige ɗaki. ta kwantar da hankalinta ta zubawa idonta toka bama ta gani ba bare ta tanka, ta tushe kunnenta bama ta ji ba bare ta tanka, ranar Alhamis da daddare Hajar na zaune a soro tare da Nura, firar su suke cike da shauƙi da kaunar juna, rufe fuskarta tayi da hijab tana tiƙar dariya sbd abin dariyar da ya fada, shima dariyar yake yace "insha Allah gobe zasu kawo min kuɗina wajen Baba..", ta bude fuskarta tace "kuɗin me?", yace "kuɗin da zan ɗauki hanyar mallakarki..", turo baki tayi tace "kaji ka ko, toh wai haka ake yi, nifa har yanzu ba sanka nake ba, kuma ni ƴar yarinya ce ban isa aure ba" ta murguɗa masa baki childishly, murmushi mai sauti yayi yace "Ohh really, ai naga alama shiyasa yau kika takura sai naxo kin ganni hakan ma ai duk cikin rashin so ne, snn kuma very soon zaki zama mother kinga ba maganar yarinta..", ta juya manyan idanunta tace "Au nice ma nace maka kaxo ko?", kafaɗa ya ɗaga yace "Eh mana, kin ga you inform your parent kinji", wani gwalo ido waje tayi tace "chabb ai kwa ba za a kawo kuɗin ba indai ni zan gaya musu", dariya ta basa sosai na expression dinta yace "toh meye aciki?", yana kwaikwayon muryarta yace "haka fa kawai zaki ce, Umma Baba gobe za a kawo kuɗin", turo baki tayi tace "ni gida zan shiga", ya kalli agogon wayarsa yace "Okay, sai munyi waya don ban gaji da jin muryarki ba", ledar da yazo da ita ya miƙa mata, ƙin amsa tayi tace "A'a nagode", haɗe gira yayi yace "amshi mana ko so kike mu ɓata", a hankali ta amsa tace "nagode", ya tashi ya nannaɗe darduman da ya zauna ya naɗe wacca Hajar ta zauna ma, amsar darduman tayi tace "nace maka fa ka ringa bar min zan naɗe fa", yace "naƙi ɗin..", ya ringa kallonta har saida ta gaji ta juya masa baya tana turo baki tace "Allah nace maka fa banaso", yace "toh me nayi miki", tace "saida safe" ta shige gida. tinda ta shigo Maama da Sa'adatu dake zaune bakin ƙofar ɗaki suke binta dana mujiya, Maama tayi tsaki tana kallon ledar hannunta, Sa'adatu tace "kullum sai a shigo da wata mitsiyaciyar leda, uhmm Maama za kiji zuwan da dawowar wllh, a banza ake zaman soro harda su leda, ai nasha ganin blue film na zahiri a soron nan...", Maama tace "barewa tayi gudu ɗanta yayi rarrafe, ai muna ganin jalala a wnn gidan...", Hajar dai ta wuce ɗaki abinta. washe gari Juma'a, bayan Sallahr la'asar aka kawo kuɗin Hajar, Baba ya shigo gida da uban kuɗin a hannunsa yana kabbara yace "alhmdllh", yaye labule Maama tayi tace "wnn kabbara haka malam sai kace wanda akay wa bushara da gidan aljanna..", yace "ki fito ki saka albarka kuɗin auren Hajara aka kawo", Maama ta buga wata shegiyar guɗa ta fito tace "Au haba, ƙwandala nawa aka kawo?", ƙanƙance ido yayi yace "wace irin ƙwandala kuma Rabii?, ke me yasa ba a abin arziƙi ne dake", tace "ai gani nai ƙwandalar ce ta dace da ita", Baba ya girgiza kai yace "kiyi fatan Allah ya bawa ƴaƴanki ko da rabin nata ne..", da sauri Sa'adatu da Maimuna suka matso jikin window suka kasa kunne suji nawa aka kawo, Nabilah kam taɓe baki tayi, Maama tace "nawa ne", Baba baice komai ba ya kunce ledar uwar kuɗin ya fito dasu, zaro ido Maama tayi ganin yawansu, tinda take bata taɓa ganin kuɗi masu kaurin haka ba, Baba ya mayar da kuɗin yace "ƙwandala goma ne" ya wuce ɗakinsa ya barta nan tsaye da sakakken baki, wani tuƙuƙin baƙin ciki da hassada ne ya turnuƙeta, tamkar kububu haka ta afka ɗakinta, ta dubi Maimuna da ke jikin window tace "wai mahaukaciya kuka mayar dani ko me?", Maimuna ta turɓune fuska cike da rashin ɗa'a tace "toh wai ke Maama me mukay miki ne?", wata muguwar ashariya Maama ta lafta mata tace "uban ki kikai min, ji nake cemin kukai faƙiri ne ke neman auren Hajara, toh ba kuga uban kuɗin da aka kawo ba na aure", Sa'adatu tace "wai uban kuɗi naji fa Baba yace ƙwandala goma", Maama da zuciyarta ke tafarfasa tace "toh wasu dunƙulallun kuɗi ne ƴan dubu dubu, kaurinsu da aukinsu inajin sun doshi miliyan...", baki suka haɗa sukace "Aaaaaa Maama haba dai", cike da takaici ta shiga kutuntuma musu ashar tace "ƙarya nake knn?", Nabilah ta fashe da dariya tace "A haba dai Maama ya zai kiyi ƙarya ai saidai ki faɗa ba daidai ba ko Maimu", Maimuna tace "kwarai kuwa, Maama na rasa me yasa kika ɗaga hankalinki a kan wanda waccar matsiyaciyar zata aura", Maama ta gasa mata harara tace "yo ba dole hankalina ya tashi ba, ha kurum sai taci gaba kuna zaune jaɓar kuna kallonta..", Sa'adatu tace "Maama nifa kinsan ba aure zanyi ba, indai cigaba na aure kike magana toh na yarda Hajara ta fini a wnn fannin", Maama ta saki baki tana kallonta tace "Au haka zaki zauna a gidan ba xaki gidan mijinki ba...", Nabilah ta taɓe baki tace "Ayyah Maama ai ki saka Sa'adatu a addu'ar ki ta koda yaushe, dan na gaya miki irin alfashar da nake tunanin suna aikatawa da tumakan ƙawayenta amma kin ƙi yarda", Sa'adatu tace "dalla malama ban kasafta dake ba bare ki dauka..", Nabilah tace "kinyi kaɗan bari kiji in gaya miki, toh baki kai nan....", Maama tace "ya ishesku, zaku fara raba halin naku knn", Maimuna tace "dama kin rabu dasu yauma nasha kallo, ai sun iya bawa hammata iska" ta fashe dariya. Da misalin tara da rabi na dare wayar Hajar tay ringing, yamutsa fuska tayi snn ta sakata a silent, yau dai baza tay picking ba, gado ta hau tayi kwanciyarta zuciyarta wasai, an kawo kuɗin aurenta da ya sayyadi, washe gari ta tashi ta gama komai na gyaran gida da ta saba, har waken kulele saida ta wanke, bayan ta gama komai ta shiga wanka, tana shafa mai Umma ta shigo ɗakin, gaban wardrobe ta tsaya ta ciro kuɗi snn ta koma gefen gado ta zauna tace "idan kin shirya zan aikeki gidan Jamila", Hajar tace "tom" ta cigaba da rubbing cream a fatarta, doguwar rigar atamfa ta saka, ta sanya hijab da ya tsaya mata a guiwa tace "Umma na gama", Umma ta miƙa mata kuɗin hannunta tace "ki kai mata wnn, za muyi waya da ita", Hajar ta amshi kuɗin ta saka a jakarta tace "na tafi", Umma tace "karki kai yamma", tace "tom" ta ɗauki flat shoe a ƙarƙashin gado ta fita, a soro ta tarar da Naseer da yazo jiya, ta sunkuya tace "yaya ina yini", yana kallonta yace "lfy lou, ina zaki haka?", tace "Umma ce ta aiken gidan Anty Jamilah", gyaɗa kai yayi yace "Okay" ya wuce ciki ita kuma ta fita, cike da nutsuwa take tafiya har ta isa bakin titi, cikin sa'a kam ta samu Napep da wuri, tana zuwa gidan ta tsaya bakin gate tayi knocking, Hafsa ce ta buɗe tana ganinta ta zaro ido tace "the bride to be wnn bazata hka", Hajar ta shiga gidan tace "ina Tahfeez din, yau naga asabar..", Hafsa tace "ba nida lafiya". da haka suka shiga ciki, Hajar ta durƙusa ta gaida Anty, Anty tace "lfy lou, ya mutan gidan", Hajar tace "suna lfy", Anty tace "madallah", Hajar ta zuge jakarta ta ciro aiken ta mikawa Anty tace "gashi inji Umma".......✍️