HAJAR

{32..}

by @feenerhfeeche

Bappa ya ringa kallon Baba kafin yace "kace na daurawa Hajara aure da yaron da ba musan waye shiba?", Alhj Muktar yayi murmushin manya yace "naji daɗin wnn furuci naka, tabbas kanada gsky sosai, nima hkan zanyi idan na samu kaina a matsayinka na yanzu, kuma nima na taɓa shiga irin wnn yanayin da Adam ya shiga yanzu, na sake faɗa cewa ɗana nagartacce ne, amma idan zuciyarka ba ta aminta ba shknn ba damuwa", Baba ya dubi Bappa yace "A ɗaura mata aure da ɗan gidan Muktar, ba nida shakku ko kaɗan a kalamansa, na yarda dashi...", Bappa yayi ajiyar zuciya yace "tom, Allah ubangiji ya tabbatar da Alkairi" sai kuma ya dubi Alhj Muktar yace "fatan dai akwai sadaki a kusa", Alhj Muktar da walwala ta bayyana ƙarara a fuskarsa yace "akwai, bani minti uku", wayarsa ya ciro daga aljihu ya kira drivernsa, da sauri driver ya ɗauka, Alhj Muktar ya umarcesa da ya ɗakko masa kuɗi a mota, bayan minti bakwai driver ya bayyana a soron, ya durƙusa gaban Boss dinsa ya ciro wasu maƙudan kuɗi daga pocket ya ajiye, Alhj Muktar yace "zauna ka zama shaida", ba musu ya zauna ya tankwashe ƙafa, Alhj Muktar ya ɗauki uwar kuɗin ya ajiye gaban Bappa, Bappa ya dubi kuɗin ya girgiza kai yace "wnn kuɗin sunyi yawa", Alhj Muktar yace "ba suyi yawa ba, sadaki ai baya yawa saidai yayi kaɗan", ( Ehennnn a zamanin nan sai kaji mutane suna cewa wai ba a tsawwala sadaki ai ba siyar da yarinya za ai ba, to ga point of correction ba wani siyar da yarinya, shi fa sadakin aure baya yawa a musulunce, matuƙar kanada ikon bawa matarka zunzurutun dukiya mai yawa matsayin sadaki toh ba matsala, tauye sa shine matsala, wllh idan ma kanada arziƙin raba kano gida biyu ka bata rabi matsayin sadaki hakan daidai ne). An ɗaura auren Hajar da ɗan gidan Alhj Muktar bisa sadaki mai tsoka, ɗaurin auren ya samu shaidu masu yawa, Baba ya lumshe idonsa ya furta "alhmdllh", maroƙi ya ɗaga murya yana sanar da jama'a cewa ɗaurin aure ya kammala, muryarsa har cikin gida ta ratsa, wani mugun bugu zuciyar Maama tayi jin muryar maroƙi ta daki dodon kunnenta, ta juya ta kalli Balaraba da ta hangame baki har ƙuda na ƙoƙarin afkawa ciki, Wasila ta ɗaga zureren hancinta sama ta rangaɗa guɗa, murmushi mai kyau Umma tayi. Maama da idonta ya kisfe tsabar takaici tace "wllh sai malamin nan ya biya ni kuɗi na, kadan ba sai ya biya ba", Balaraba tace "abin fa da mamaki, tinda nake dashi bai taɓamin aiki baici ba, wllh a tarihin aikinsa ma baya faɗuwa, gaskiya akai abinda ya faru Rabii", Maama tace "Eh ai kam ga aiki nan na gani", Balaraba ta dafe kai tace "Rabii akwai lauje cikin naɗi, mu tsaya dai muyi kallo". Mu'azzam ne da Huzaifa suka ringa firfita da abinci, walima aka baje a soro ana kwasar dabge. Alhj Muktar da Baba suka fita daga soron zuwa can inda babu taron jama'a, godiya Alhj Muktar ya ringa yiwa Baba, shima Baban godiya yake masa domin kwa ya fitar dashi kunya, Alhj Muktar yace "insha Allah da yamma zasu zo", Baba yace "bana ganin ɗaukar yarinyar nan zai yiwu a yau, a bari zuwa gobe, kaga dai yadda lamarin ya jirkita, shima yaro ai sai an sanar dashi...", Alhj Muktar yace "toh ba damuwa da yau da gobe ai duk ɗaya ne, karka damu yaro a shirye yake", Baba yace "nagode fa, kaxo domin mu gana sai kuma wnn batu ya gifta bamu samu lokacin ganawarba", Alhj Muktar yace "daman nazo ne domin naga inda kake Adam", Baba yace "Allah sarki", Alhj Muktar ya miƙa masa hannu sukay sallama snn ya tafi. saida rurumar ƴar ɗaurin aure ta tsagaita snn Baba ya samu shiga gidan nasa, nan fa akay masa caa da gaisuwa da kuma fatan alkhairy, da sakakkiyar fuska ya ringa amsawa yana neman Umma da idanu, daga ɗakinta ta fito fuskarta ƙunshe da walwala, Baba ya dubeta yace "ɗakinsu Nasiru a buɗe yake?", tace "bari na duba", ta wuce ƙofar ɗakin ta tura taga a buɗe take, tace "Eh a buɗe take", ya ƙarasa ƙofar ɗakin yace "ina son ganinki" ya shiga ciki. afujajan Maama ta fito daga ɗakinta jin muryar Baba, wuwwurga idanu ta fara yi duk ta jiƙe da gumi, hangosa tayi lokacin da ya shiga ɗakinsu Huzaifa, da sauri ta wuce har tana ƙoƙarin bangaje Umma ta shiga ɗakin, kallonta Baba da yake shirin zama yayi, Umma dai ta shigo ta samu waje ta zauna, daga tsaye Maama tace "tin safe ka hana mu kudin abinci a gidan nan mal", yace "kuɗin abinci kuma Rabii?, ga abinci nan ku zuba kuci", tace "a ina yake abincin?, ni bangani ba", ya ciro 1k daga aljihun gaban rigarsa ya miƙa mata yace "gashi", amshewa tayi tace "yo da an barni da yunwa nida ƴaƴana", ta juya zata fita sai kuma ta dubi Umma tana yamutsa fuska, dawowa tayi ta zauna ta wani sha kunu, Baba yace "ba na baki kuɗin abincin ba", gefe ta kalla tace "Eh anan zan zauna", Baba yayi ajiyar zuciya baice komai ba, shiru ɗakin ya ɗauka babu wanda ya sake magana, bayan wani lokaci Umma tace "mal ko na tafi ne akwai baƙi da suke jirana", Baba ya girgiza kai yana kallonta yace "Faɗima", tace "na'am". kaf ya wassafa mata abinda ya faru akan auren ƴarta. wata katafariyar shewa Maama ta daka, ta miƙe da sauri ta fice tana gyara haɓar zaninta, saida ta shiga tsakiyar ƴan biki tace "ahayye riiiiiii, an yanka ta tashi, kowa ya baje an gama biki", ta afka ɗakinta domin ta sheƙawa Balaraba nasarar da suka samu, murna suka shiga ɓarkawa a ɗaki tamkar waɗanda akay wa bushara da gidan aljanna, sosai suka saki baki suna zance sbd su Nabilah sun fice daga gidan. Umma ta tuge ture kaga tsiyar kanta ta share zufar da ta tsattsafo mata tace "innalillah wa'inna ilayhirraji'un, mal dama baka ɗaura mata aure da wani ba...", katseta yayi yace "karki ɗaga hankalinki Faɗima, kiyi mata addu'a Allah yasa hakan shine alkhairy a gareta", tace "amma mal...", yace "idan kika ɗaga hankalinki waye zai kwantarwa da Hajara nata, itace wacca ya kamata a duba, idan kika samu nutsuwa itama hankalinta ba zai tashi sosaii ba, ƙaddararta ce, ko wane dan Adam da irin tasa, Allah ya rubuta ba Nura ne mijinta ba, ni kuma na gaya miki mutumin da na bawa auren Hajara bashi da matsala", Umma ta ajiye deep breathe tace "Allah yasa hakan shine alkhairy, amma taya ya zan sanar da ita?", Baba yace "she's your daughter fa, ki kiramin ita", ta gyara daurin dankwalinta ta miƙe ta fita da wani facial expression a fuskarta. ɗakin Baba ta nufa inda Hajar da muƙarrabanta ke zauna, a bakin ƙofa ta tsaya tana kallonsu, Umma ta dubi Hajar da tayi wani kyau wanda bata taɓa irinsa ba a rayuwa tace "kije inji Babanku yana ɗakinsu Mu'azzam", Hajar tace "tom", ta saka wayarta acikin handbag dinta, gyara yafen mayafinta da yake fitar da ainahin ƙamshin kabbasa tayi, ta saka takalminta flat mai kyau snn ta fita. Umma kam ɗakinta ta shige, ta matsar da kayan dake gefen gado ta zauna ta dafe kanta, a haka Anty ta shigo ta sameta tace "Adda, lfy kuwa?, ya da tagumi haka a lokacin farin ciki", Umma ta ajiye numfashi a hankali tace "Jamila", Anty ta samu guri ta zauna sbd yanayin ƴar uwarta ta, Umma tace "kin san kwa bada Nura aka ɗaurawa Hajara aure ba", Anty ta gwalo ido tace "ban fahimce ki ba Adda", Umma tace "uhmmm" ta labarta mata abinda Baba ya sanar da ita, shiru Anty tayi tana kallonta, kasa cewa komai tay kawai juya lamarin take a kwanyarta, can tace "kiyi haƙuri Adda amma sai naga kamar kun yiwa Hajar gaggawa, wai har nawa take har yanxu fa bata cike shekara 18 ba, dan ma tanada garun jiki amma wllh bata isa aure ba...", Umma tace "ba haka bane Jamila, muma ai bamu kaita ba aka kaimu gidan miji, kuma muka zauna", Anty tace "haka ne Adda, duk yadda zamani ya juya haka za a tafi dashi, a wnn zamanin aure yafi kyau idan yarinya ta kai shekaru 20, ta mallaki hankalinta...", Umma dai tayi shiru, Anty tace "Hajar ɗin ta sani?", Umma tace "Eh nasan yanzu ta sani, Mal ya sanar da ita". Hajar ta fito daga ɗakinsu Mu'azzam ƙafarta na harɗewa, da gudu ta shige ɗakin Umma ta zube a ƙasa snn ta fashe da wani matsanancin kuka mai ban tausayi, runtse ido Umma tayi tana jin itama kamar tayi kukan, Anty ta taso ta ɗagota ta rufe mata baki tace "shhhh, kiyi haƙuri kinji", kuka take kamar ranta zai fita.


★Mami ta murɗa handle ɗin ƙofar part ɗin Abba, da sallama ta shiga, Abba dake zaune kan kujera two sitter ya amsa mata, a gefensa ta zauna, ta ɗauke hularsa dake hannun kujerar ta ajiye bisa huge Centre table dake palourn, tace "gani yallabai, amma dai ba'a masallacin sarki kayi juma'a ba?", Abba ya sosa forehead dinsa yace "Eh, a can Masallacin Abubakar Siddiq nayi", tace "Ohk", yace "yau ce ranar da Uthman zai dawo ko?", tace "insha Allah, ɗazu na gama waya dashi sun ma taso, 9pm za suyi landing", ya gyaɗa kai yace "Alright, a yau da na fita ban dawo gida ba saida na ɗaurawa Nurain aure", cike da mamaki Mami ta dubesa har tana haɗe gira tace "aure kuma yallaɓai?", yace "yess, so start all the necessary preparations tommorow insha Allah za aje a ɗakko masa matarsa", Mami was speechless na kusan 1minute kafin tace "but without his consent aka ɗaura", yace "Do i need his consent, he is my son, he most respect my decision", Mami tace "this is a different case...", yace "i know, a da fa haka ake daura maka aure ba tare da kasan waye ka aura ba, iyaye ne kawai suke haɗinsu", Maami exhale heavily tace "wa ka aura masa?", yace "sunanta Hajar, ƴar wajen abokina ce", tace "Allah ya basu zaman lfy", yace "Ameen, key din gidansa na wajenki ko?", tace "Eh suna wajena", yace "ohk, sai a duba gidan nasa kafin Allah ya kaimu gobe", tace "sure, za ai komai". Mami na fitowa daga wajen Abba ta shiga kiran ƴar uwarta Zulaiha, tana picking Mami tace "idan ba damuwa ina son ganinki Zulaiha", Anty Zulaiha tace "ohk, when?", Mami tace "idan ma zaki taho yanxu to nafi son haka", Anty Zulaiha tace "is everything ok?", Mami tace "sure, komai lfy urgent abu ne ya taso", Anty Zulaiha tace "Shknn I'll be there right away", da haka Mami ta katse kiran thinking of another thing to do, After 40mins Anty Zulaiha ta iso tare da Khausar, direct palourn Mami suka wuce, Khausar ta sunkuya ta gaida Mami, amsawa Mami tayi tana tambayarta school, Noor ce ta fito daga bedroom din Mami sanye da english wears, gaisawa sukay da Anty Zulaiha snn taja hannun Khausar suka fita daga part din zuwa huge room ɗinta, Anty Zulaiha ta cire gyalenta ta gyara zama sosai bisa executive sofar palourn tace "wai mene ne abinda ya taso urgent?", Mami tace "ɗaxu Abba da ya dawo daga masallaci yake gayamin cewa wai ya ɗaurawa Nurain aure da ƴar abokinsa", Anty Zulaiha tace "ikon Allah, daman har yanzu ana irin wnn haɗin", Mami tace "nima dai haka nagani, saidai fatan alkhairy, wai sai gobe za a kawo amaryar, yanzu dai gidan Nurain din nake so aje a duba, an riga anyi furnishing dinsa amma kuma almost 8months ba shigesa ba, kinga za aje a dudduba abinda yayi damage, komai dai ya zama intact", Anty Zulaiha tace "toh ai wnn ba aikin mu bane, na dangin Amarya ne", Mami tace "yess nasu ne, Abba ne yace a buɗe gidan a gyara", Anty Zulaiha tace "toh shknn, ai sai a tura ma'aikata su gyara, su firfito da abinda yayi damage, mu kuma in Allah ya kaimu goben sai muje mu gani", Mami tace "nima haka nake tunani, kawai a tura masu aiki", Anty Zulaiha tace "toh kuma haka za a ajiye yarinyar a gidan babu mijinta", Mami tace "No, ai yau Nurain ɗin zai dawo", Anty Zulaiha tace "toh masha Allah abu yayi kyau kinga yana dawowa sai yayi Settling down, Allah yasa ta zame masa babban tukuici na abinda Ruqayyah tayi masa", Mami tace "Ameen". labourers aka tura katafaren gidan Nurain, tin daga sama har ƙasa aka shiga tsaftacesa, babu wani datti sai dust da dry falling leaves.


★Da misalin ƙarfe takwas da minti hamsin na dare ya parker luntsumemiyar motarsa a parking space da ke babban international airport na garin kano, waiting area ya nufa ya zauna yana kallon wajen da matafiya suke ɓullowa, yana jin announcement na saukar jirgin da ya iso daga India ya miƙe tsaye, few minutes kam suka fara fitowa, shine na biyar, sanye yake cikin ƙananan kaya da Pcap saman kansa kamar yadda ya bar 9ja, hannunsa daya na riƙe da trolley da yake ja yayinda ɗaya yake maƙale cikin black sweat pant nasa, Farooq na hango brother din nasa ya fara tafiya towards him, Nurain ya ciro hannunsa daga pocket ya dunƙulesa, shima Farooq dunƙule hannun nasa yayi, suna haɗewa suka haɗa hannayen nasu, Nurain yayi murmushi yace "hey dude", Farooq yayi masa side hug yace "barka da zuwa punk". saida aka gama checking luggage ɗin Nurain snn suka baro airport din, Farooq dake driving da mininum speed yace "ko dai wajen amaryata zamu wuce", Nurain yace "No, iron lady ban shirya facing dinta ba", slight smirk Farooq yayi yace "tsohuwa mai ran ƙarfe", Nurain yace "oh God look at how you're driving, ka take accelerator", Farooq yace "as in how na take accelerator, wai naga fa Doctors suna lallaɓa lafiyarsa amma look at you kana so ayi risking taka", Nurain yayi resting jikin kujera can ƙasan maƙoshi yace "hurry up". Farooq ya ƙara gudun motar kaɗan, slow down yayi kafin ya juya kan motar ya shiga street din gidan uncle ɗinsa, a bakin huge gate ɗin gidan ya danna horn, da sauri mai gadi ya zuge gate, ya danna motar ciki, parking lots ya isa yayi parking snn ya kashe motar, yana ciro key daga Ignition yace "did you just take a nap?", Nurain ya buɗe idonsa yana kallon environment ɗin ya yake ciki, buɗe motar yayi ya fita, yayi ajiyar zuciya yana stretching kansa yace "home sweet slum".......✍️