{40..}
💛 HAJAR 💛
Hajiya tabi ƙofar da Nurain yayi banging da kallo tace "ikon mai duka, cewa nayi fa zanyi magana da kai shine zaka zo ka nunamin wata fuskarka da na rasa dalilin sauyawarta ka fita", Hajar ta runtse idonta tana haɗiyar wani kwallo da ya tsaya mata a throat, ta wutsiyar ido ta gansa shine ta maze, gaba ɗaya taji ta tsani zaman nan en so take ta koma inda ta fito, a hankali ta miƙe tana jan fingers, Hajiya ta dena sababin da take ta ɗaga kai tana kallon Hajar tace "lafiya kika miƙe sai kace wacca aka zubawa mugun mintsili?..", Hajar tayi kasa da idonta tace "zanyi sallah ne..", Hajiya ta nuna mata qibla tace "buzun tsaftatacce ne, kiyi sallar ki", Hajar dai tayi shiru don ba haka taso ba, ita so take ta bar nan din kawai, Hajiya tayi kasaƙe tana kallonta ganin bata kalli qiblar ba kuma ba tada niyyar kabbara sallar da tace za tay, Hajiya ta dubi Noor tace "ƴar nan, kee", ina Noor sai blushing take tana tura coconut macaroons a baki, gaba ɗaya mind dinta na kan TV, Hajiya ta ɗauki trow pillow ta wurga mata, sai a snn Noor ta juyo tana wuri wuri da ido tace "mene ne iron lady?", Hajiya ta mata daƙuwa tace "wnn wane irin masifar kallo kike ne, nayi ta miki magana amma kin saki baki da hanci kin zubawa wasu ƙodaddu idanuwa a talabijin", Noor ta ajiye coconut macaroons da take ci tayi folding hands tace "Allah ya baki haƙuri, banji bane", Hajiya tayi tsaki tace "kinga ƴar nan matar Usuman tace zatay sallah nace tayi anan tinda buzun tsaftatacce ne amma taƙi yi, toh inajin dai tsaftarsa ba tay mata ba, ki tashi ki ɗakko mata wani acikin ɗaka sai ta ɗora akan wnn tayi sallar", Hajar tayi ƙasa da murya kanta a ƙasa tace "A'a zan koma can din ne sai nayi sallar a can", Noor ta tashi tace "alright muje na rakaki..", da haka Noor ta nufi door Hajar tabi bayanta walking slowly, Hajiya ta bisu da kallo tana taɓe baki tace "Au wnn aka aurawa Usuman, da gani bata son mutane, ta zauna a cikin mutane amma taƙi ta gwammace ta ƙurmusa a ɗaki, Allah dai ya kyauta...". har sun kama hanyar part din Mami sai kuma Noor ta dakata, ta juyo tana ƙarewa main palourn kallo, taji scent dinsa amma kuma bata gansa ba, yana zaune a edge of executive two seater yana operating Mac phone, Noor ta buɗewa Hajar ƙofar shiga part en Mami tace "go ahead am coming", Hajar ta shige ciki, Noor ta koma main palourn ta isa kusa dashi ta tsaya daga gefen kujerar tace "Yaya ina yini?", ciki ciki ya amsa mata ba tare da ya kalleta ba kawai danne dannesa yake jikin Mac phone, tace "Yaya don Allah zan turo maka da project dina ka duba min kafin nayi submitting na gama..", sai a lokacin ya ɗaga kai ya kalleta kafin ya mayar da idonsa kan abinda yake yace "Ohk, Allah yasa ba shirme kike rubuta ba, don naga yanzu ba kya karatu sai kallon shirme kika iya, keep this in front of your mind idan shirme kika rubuta am going to punish you", ta sosa forehead dinta tace "shknn ma, yaya Farooq zan turawa ma kar nayi stressing dinka", yace "kafin 9pm naga mail dinki in my inbox Noory", ta gyaɗa kai a hankali tace "Sure Yaya" ta bar wajen ƙirjinta na bugawa, tasan dai bata rubuta shirme ba cause saida tayi research kafin ta rubuta komai, amma dai dole sai an mata gyara, ta shiga part en Mami, a tsaye ta tarar da Hajar a corridor ta jigina da bango, Hajar tayi saurin juyar da kanta gefe tana goge cheeks dinta, Noor taso ta fahimci cewa kuka take amma kuma demon en gabanta shine ya kwashe mata tunani, har ɗaki ta raka Hajar kafin ta fito, direct kuma room dinta ta wuce tayi plugging Lap top dinta a charge. Hajar ta idar da sallah, kwanciya tayi kan carpet ta lulluɓe da babban hijab din da tayi sallar, tara da rabi Mami ta shigo dubata, Mami ta dafa forehead dinta to feel her temperature, Hajar ta buɗe idonta don ba bacci take ba, tunani ne iri iri ya cunkushe mata a brain, Mami tace "ki dena kwanciya kan carpet ga bed nan, ko headache en ne?", Hajar ta tashi zaune tana girgiza kai tace "A'a ya dena ciwo", Mami tace "toh alhmdllh, ya baki ci abincin da aka kawo miki ba, ko ba kya son sa?", Hajar tace "na ƙoshi, naci da yamma", Mami tace "Okay, toh kisha drugs enki sai ki kwanta ko, if you need anything just let me know kinji", Hajar ta gyaɗa kai a hankali, Mami na fita Hajar ta shiga bathroom, tayi wanka ta fito ta saka kayan baccin da Noor ta bata, like yesterday night wnn ma ba tayi bacci ba, saidai wnn daren lafiyar ta lou kawai dai ta kasa rintsawa.
★Hajiya ce zaune bisa 3 sitter a great room din Abba, tayi shirinta tsaf da shigar asun da asun na atamfa, ga ɗaurin kallabi irin na tsofaffin nan mai santi, ta zubawa Abba dattijon idanunta da suka sha farin kwalli tace "Muntari nidai ban fahimci zaman Usuman a gidan nan ba, ya ɗauki matarsa su koma gidansu tinda ta warke sumul abinta, tinda dai waraka ta sauka to banga amfanin zama a nan ba, su koma gidan su kar aje a ƙuma musu sata, don wnn uwar dukiyar da aka laftawa gidan ɓarayi sai su shigar musu tinda banga alamar mai gadi ba, amma kuma dai naga wayar shokin zagaye da gidan, ɓarayi ba zasu iya shiga ba gsky..", Abba yace "insha Allah this week zasu koma..", Hajiya ta katsesa da fadin "toh mai zai hana yau su tattara su tafi, nifa yau zan rugungunta na tafi, kamata yayi ma mu fita gidan nan tare dasu, nasan yanzu ma Umaru yana kan hanyar zuwa ɗaukata", da taushin murya Abba yace "Hajiya ku dan sake zama mana zuwa wani lokaci ko sati fa ba kiyi ba..", Hajiya ta girgiza kai tace "A'a A'a Muntari kasan dai ni adala ce, shekarata biyu a gidan nan banje gidan Salisusu ba ina nan, shima saina jingine masa shekaru biyu kafin na juyo nan idan Allah ya ara min lokacin". knocking door akay kafin aka buɗe aka shigo, Mami ta shigo da sallama, ta sanar da Hajiya cewa breakfast dinta is ready, Hajiya tace a kawo mata abincin nan anan zata ci, Mami ta juya ta fita, babu jimawa ta dawo da tray a hannunta, tayi serving Hajiya creamy groundnut pap with yummy beans cake. Mami na gama serving dinta ta tashi zata fita, Hajiya ta ajiye cup en pap tace "Khadijah...", Mami ta juyo tace "Na'am Hajiya", Hajiya tace "naga jikin ƴar taki da sauƙi toh shine nace me zai hana yau su tattara su koma gidansu..", Mami tace "Eh Alhmdllh ta samu sauqi sosai, amma dai bata gama shan drugs dinta ba, da sai nan da sati mai zuwa sai a mayar da ita ɗakinta lokacin insha Allah ta gama shan drugs en, amma yadda kika ce ai haka za ai Hajiya", Hajiya ta rausayar da kai tana cin ƙosai tace "ai shknn tinda kin kawo batun magani, shima mijin naki haka yace sai sati mai zuwa da yake bakinku ɗaya". kwanan Hajar hudu a gidansu Nurain, tin ranar da suka je wajen Hajiya bata sake fita daga part en Mami ba, everytime tana ɗakin da aka ajiyeta, tana dai fita palourn Mami ta gaisheta sai kuma ta koma ɗaki, Sosai suka saba da Noor sbd tare suke kwana, da rana kuma ta zauna ita kadai idan Noor ta tafi schl, ƙarfe biyar da minti huɗu Noor ta shiga ɗakin da Hajar take, dawowarta daga schl knn, wanka kawai tayi ta canza kaya, Noor tayi murmushi tace "masha Allah, waoh gsky kayan nan sun miki kyau", Hajar ta dubi kanta, straight skirt ne na english wears da shirt dinsa masu kyau, Noor din ce ta kawo mata su tinda daman kayanta take sawa, duk yawancin kayan da ta bata ƙanana ne amma decent, don Noor ta fi son su sbd tafi zama comfortable dasu, Noor ta ringa yaba kyan Hajar da kayan, sun fi yiwa Hajar din ma kyau don ita data saka sau ɗaya basu mata kyan haka ba, Hajar tayi murmushi tace "an dawo schl lfy?", Noor tace "lfy alhmdllh, za kici Noodles?'', Hajar ta gyaɗa kai tace "Eh zan ci", daman kaɗan taci lunch da aka kawo mata, Noor tace "Ohk, let's prepare it together", Hajar tace "together?", Noor tace "yhap", ƙin yarda Hajar tayi wai ita bazata fita ba, daga ƙarshe ma tace ta ƙoshi, da kyar Noor tayi convincing dinta ta yarda, zumbulelan Hijab din da take sallah ta kirma, Noor ta bita da kallo tace "keda zaki kitchen meye kuma na saka hijab", Hajar tace "in ba dashi ba na fasa zuwa", tare suka fito main palour suka shiga huge luxury kitchen din gidan mai shegen kyau, kitchen island ma wani irin makeke, ga cupboards da drawers suma manya wanda suka zagaye girman kitchen din, Noor ta ɗakko pot kafin ta fara harhaɗo ingredients, Hajar daga gefe ta tsaya tana kallonta, within 15mins Noor ta gama dafa wata shaɗananniyar Noodles, ga fried egg with sausage, A babban plate ta juyo musu, Noor ta buɗe fridge ta ɗakko lemon kwali da ruwa ta bawa Hajar ta riƙe musu ita kuma ta ɗakko plate en Noodles en, a Main palour suka zauna wanda Hajar ba taso hakan ba, Still Hajar tayi tana kallon Noor ganin abinda ta ajiye musu a maimakon fork, Hajar ta ringa kallon tsinkayen tace "meye kuma wnn?", Noor ta ɗauki chopsticks din ta fara ci dashi, sosai ta iya amfani da Chopsticks, saida Noor taci loma uku amma Hajar ko attempting ɗaukar sticks en ma ba tay ba, Noor tace "ya naga ba kya ci?", Hajar ta ɗauki Chopsticks en gabanta ta fara ƙoƙarin ɗebo Noodles din, daga ta ɗiba sai ta zame, Noor ta ringa mata dariya kafin ta tashi ta shiga kitchen ta ɗakko mata fork, Hajar tace "tayi daɗi sosai", Noor tace "really, da fatan dai kin riƙe recipe din cause it's one of yaya Nurain's favorite", suna gama ci Hajar ta ɗauki plate din ta shiga kitchen dashi, Noor ta juya tana kallon stairs jin footsteps, tini ta ajiye cup din lemon da take sha ta tashi da sauri ta ruga ɗakinta, tsoron haɗuwarsu take sbd wata red cancel ya turo mata akan project dinta da ta tura masa hakan yana nufin shirme tayi kenan, gashi yace sai yayi punishing dinta idan shirme tayi, shiyasa take avoiding dinsa kar ya kamata, Nurain ya ƙarasa sakkowa downstairs yana kallon ƙofar part din Mami, kitchen ya nufa da cup din Coffee da ya gama sha, yana shirin murɗa handle kawai yaji an murɗa ta ciki kafin aka buɗe ƙofar, kanta a ƙasa tana tattare ƙasan hijab dinta da yake sharar floor, ji tay tayi karo da abu, ta ja baya da sauri ta ɗago kanta, girarsa a matuƙar haɗe yake kallonta, Hajar ta zuba masa lulu eyes dinta zuciyarta na bugawa, ita tsorata ma tayi shiyasa take masa wnn kallon, da sauri ta janye idonta tabi ta gefensa zata wuce tinda akwai space sosai da yake ƙofar babba ce, ( mu bawa juna haƙuri daii ) shine abinda ya amsa a brain din Nurain within 1sec, this time around din ma junan zasu bawa haƙuri ko kuma ita zata basa, hannu yasa ya fixgota baya ya mayar da ita kitchen din, yace "kee are you mad?, dutse kika bige ne?..", Hajar ta yamutsa fuska tace "wa ya sani ko dutsen ne".....✍️