HUƊU
by @zeeeyybawa
*WATA ALAKA*
*PAID BOOK*
*ƳAN TAGWAYE BIYAR*
Na
ZAYNAB BAWA
&
STYLISH BCH
*SHAFI NA HUƊU*
Bayan Mami ta idar da sallar la'asar ta sake komawa ɗakin Hidaya don dubata har lokacin bacci Hidaya takeyi, palour Mami ta koma ta zauna don hutawa, Hidaya bata frk ba sai yamma liƙis lokacin Mami ta fara harhaɗa kayan yin meatpia wanda Hidaya zata tafi school dashi washe gari domin sunyi deciding da kansu zasuna haɗa mata lunch ɗinta tunda school ɗin tabada zaɓi akan iyayen yara zasu iya kawo yaransu da lunch ɗinsu, ta yanke shawarar sucigaba da kaita da lunch ɗinta kamar yanda suka fara don Hidaya ba komai take iya ciba ba lallai abincin school ɗin yazo dai-dai da taste ɗinta ba. tunda Hidaya ta fahimci abunda Maminta zatayi ta dameta a yi harda na Hydar shima zata kai masa idan taje makaranta. Murmushi kawai Mami ke yi mata tana mamakin rashin mantuwar ƴar tata, yaci ace ta manta da lamarin yaron nan amma motsi kaɗan sai tace abokin ta Hydar, idan ta tsamo meatpie din daga cikin mai sai ta fara murna tana fadin hadda wannan da wancan za'a bata ta kai masa. Har Mami ta kammala Hidaya batayi shiru ba tana ta sanarwa gobe dole abata da yawa.
________
Cikin Babban palourn mai martaba suka nufa bayan anyi musu iso cewar magaji ya iso. Idanun maimartaba yana wajan kofar ya kagu yaga yaron nashi da yake jin zuciyarsa a wannan lokacin tamkar ya budeta koda yaron zai iso kawai ya shige cikinta ya kulle. Suna isowa bakin ƙofa chak Hydar Aliyu Turad ya tsaya daga bakin kofar shiga, shi bai shiga ba sannan kuma bai juya ya koma ba. Bafaden dake gefen maimartaba dake hannun hagu ne ya russuna cike da biyayya yace.
"Ran sarki ya dade bari aje a karaso da magaji ciki." Da hannu maimartaba ya dakatar dashi yana mikewa tsaye. Ba tare da yace komai ba maimartabar ya nufi inda Hydar din yake tsaye ya harde hannunsa a saman kirji kansa yana kallan gefe da alama akwai abinda aka yi masa. Cak maimartaba ya daukeshi tare da rungumeshi kamar zai hadiyeshi saboda yadda yake jin kauna da soyayyar yaron tana sake huda masa jini da tsokar dake jikinsa.
"Abbana meke faruwa?" Mai martaba yayi magana cikin sanyayyen murya. Shiru Hydar yayi sai kwantar da kansa da ya yi saman kafadar mahaifin nashi.
"Gaya min ko Ummi ce?" Ya girgiza kai yana sake rungumeshi.
"Okay ni ne ko?" Sake girgiza kai Hydar din yayi har suka nufi wata yar rumfa dake cikin parlorn, iya tsaruwa wajan ya tsaru sai sam barka. Cikin kujera mai kama da gado suka zauna still maimartaba bai ajiye Hydar din ba. Saman cinyarsa ya zaunar dashi yana kallonsa soyayyar shi na shiga jikinsa yace.
"Menene?"
"Hidaya." Hydar yafaɗa yana kwantar da murya.
"Who's she?"
"Abie Hidaya zanje." Hydar din ya fada yana shirin yin kuka.
"A ina take Abbana? Gaya min."
"School." Hydar ya bashi amsa cikin zakuwa.
"O my God, Abbana ai yanzu ta tafi gida, ko kasan gidan nasu ne?" Hydar ya girgiza kai kawai sai hawaye ya cika masa ido, maimartaba na shirin magana suka gangaro. Hankalinsa ne ya yi masifar tashi ganin tilon dan nasa yana kuka, cike da tashin hankali ya mike yana jijjiga shi yake fadin.
"Zakaje wajan Hidaya gobe kaji ko Abbana? Amma yanzu dai kayi shiru kaci abinci idan ba haka ba nace bazaka ganta ba." Jin ance za shi kawai ya faranta masa rai har bema gane sai an kwana an tashi za'a kaishi ba. Murmushi ya sakarwa maimartaba yana fadin.
"Abbie zanje?"
"Yes of course." Mai martaba ya faɗa yana dariya domin yaga ɗan nasa yafara sakewa. Uwamrni yayi a kawo abinci da Hydar zaici sannan bayan sun kawo ya sallami gabaki ɗaya mutanen da suke cikin palourn don kasancewa da yaronsa shi kaɗai.
Isowarta sashin mai martaba kenan taci karo da gabaki ɗaya ma'aikatan sashin mai martaba a waje, hakan ya tabbatar mata da Hydar ko mahaifiyarsa acikinsu akwai wanda yake tare da mai martaba a wannan lokacin domin duk lokacin daya kasance da ɗaya a cikinsu yakan sallemi kowa a plaourn sa, wani irin tuƙuƙi takeji a ranta daƙyar ta daure ta sanarwa Jakadiyar mai martaba tayi mata iso. Juyawa jakadiya tayi ta nufi palour mai martaba duk kuwa tasan baison abunda zaiyi interrupting ɗinsa idan yana tare da Hydar sai dai azabar tsoron Uwargidan mai martaba Hajiya zulaiha da takeyi yazama kamar dole ta isar da saƙonta a wannan lokaci, Hajiya zulaiha kuwa a tsaye take ranta yana mata azabar ƙuna Allah-Allah takeyi ya kasance mahifiyar Hydar ce a cikin falon mai martaba ta gwada mata iyakarta a ranar yau ɗinnan. Jakadiya tana fitowa ta shaida mata yabata umarnin shigowa tayi wuff ta shige palourn. Tun daga ƙofar palourn take jiyo dariyar mai martaba kamar bashi ba harta ƙarasa ciki, zuwanta yayi daidai da lokacin da mai martaba ya rungume Hydar a jikinsa yana dariya ganin mijin nata ya manne Hydar a cikin kirjinsa yasa taji wani mugun ɓacin ran da take ciki ya ƙaru sai dai babu yanda ta'iya domin mai martaba bai ɗaukan duk wani wargi akan ɗansa da ace mahaifiyarsa ta samu zatayi borinta yanda ranta yakeso akan ta shigo sashin ba ranar da take da mai martaba ba sai kuma akasamu akasi Hydar Aliyu ne wanda baida shamaki da kasancewa da mai martaba a kowane irin lokaci. Wani abu taji yana mata yawo cikin zuciyarta wanda tasan kishi ne ba wani abu ba.
Zama tayi gefe tana yiwa mai martaba barka da warhaka batareda ya kalleta ba ya amsa domin hankalinsa yana ga abincin daya ɗebo ya bawa Hydar. Tsuke baki Hydar yayi yafara nuna alamun abincin ya isheshi, cikin sigar lallashi mai martaba yace.
"Haba Aliyu ɗan Aliyu jikan Aliyu magajin gari yaron Mama da Ummi buɗe bakin kaji?" Kafaɗa Hydar ya maƙe alamun bazai buɗe ba dabara ce ta faɗowa Mai martaba cikin sauri yace.
"Kuma abokin Hidaya maza buɗe kaci gobe idan kaje wajan Hidaya taga ka ƙara girma" da sauri Hydar ya buɗe bakinsa mahaifin ya saka masa abinci. Baki buɗe Hajiya Zulaiha take kallonsu ganin yanda mai martaba ya maida kansa a gaban yaron kamar ba shine wanda magana ma da hannu yake yinta ba sai dai bafadai su fassara abunda yake nufi. A halin yanzu babu wanda zaiji wannan kalaman yayi tunanin daga bakin sarki suke fitowa. Kasa haƙuri tayi tace.
"Haba Takawa Haba ranka shi daɗe kaida kanka? Da kanka kake bawa Hydar Abinci? Ina mahaifiyarsa take?" Murmushi mai martaba yayi sai a lokacin ya juya ya kalleta ya sake juyawa wajan Hydar yace.
"Abbana yau da fitina yakeji yaƙi cin abinci"
"Wannan dai ba aikinka bane ina mahaifiyarsa?" Murmushi mai martaba yayi sannan yace.
"Yau a matsayin mahaifi nake yanzu ba'a matsayin mai martaba ba" ya faɗa yana sake maida hankalinsa kan Hydar. Hajiya zulaiha bataji daɗi ba amma haka ta daure ta miƙe zata tafi domin bazata iya cigaba da ganin kayan baƙin cikin ba, mai martaba ne ya tsareta da faɗin.
"Ba wani wani bane ya kawoki? Naga har zaki fita batareda kince komai ba" Yaƙe Hajiya Zulaiha tayi cikin yanayi na makirci wanda taga alamu idan bada shiba bazataci riba akan alaƙar Hydar da mai martaba ba tace.
"A'a dama Hydar nazo dubawa, naji yatafi school ba'a kawoshi yamin sallama ba haka kuma ya dawo ban ganshi ba bansan halin da yake ciki ba shiyasa nakasa hakuri na aika wajan mahaifiyarsa aka ce yana wajanka shine nazo ganinsa" ta ƙarashe maganar tana mirmushin yaƙe, fara'ar fuskar mai martana ne ta faɗaɗa wanda har ita kanta Hajiya zulaiha sai da tayi mamaki bata taɓa tunanin abun zaiyi tasiri a zuciyarsa haka ba, cike da jin daɗi mai martaba yace.
"Allah ya huci zuciyarki Maman Hydar zanyiwa Umminsa magana daga yau koda yaushe zaije makaranta zaizo ya miki sallama idan ya dawo bayan ya huta zan yiwa Umminsa magana ana kai miki shi kiga lafiyarsa hankalinki ya kwanta ki tabbatar ya'iso lafiya" Duk da Hajiya zulaiha taji zafin yanayin yanda mai martaba yayi maganar cike da kulawa akan Hydar bai hanata jin daɗi yanda ya nuna muhimmanci sosai kuma ya ɗauki maganarta da muhimmanci ba, bata taɓa sanin makirci da kisisna yanada tasiri haka ba kasancewarta mace mai zuciya wacce bata iya ɓoye fushinta.
"Abbana maza gaishe da mamanka" mai martaba yafaɗa yana juya Hydar yana facing Hajiya zulaiha, murmushin yaƙe tayi batareda tajira gaisuwar ba tace."Ai naga lafiyarsa barina wuce Takawa ranka shi daɗe" cike da jin daɗin yanda Hajiya zulaiha ta nuna kulawa akan Hydar mai martaba yayi mata sallama.
Sai dare sosai kafin mai martaba ya maida Hydar wajan mahifiyarsa lokacin bacci yafara kamashi.
Mai martaba ba don ransa yaso ba ya bada Hydar aka miƙashi baiƙi ace su kwana tare ba."
Lokacin da aka kai Hydar bacci yaci ƙarfinsa sosai wanka kawai aka masa a daddafe ya kwanta.
_______
Washe gari tunda safe kamar time din da ta saba tashi Mami ta tashi ta nufi kitchen ta fara aikin haɗa breakfast. Mami irin matan nan ne masu saurin aiki, shiyasa nan da nan ta gama aikinta cikin kankanin lokaci kuma kasancewar yau ba kamar jiya. Jiya tayi aikin cike da zullumi da fargabar yanda Hidaya zata kasance a school kuma tayi aikinne ranta a sake domin ta tabbatar a halin yanzu Hidaya tafison zuwa school ɗin fiye da zaman gida domin tun jiya batada magana saita school. Mami tana gamawa ta fara jera abincin a dining table. Kai tsaye ta wuce dakin Hidaya dan har lokacin bacci take yi saboda daren jiya bata kwanta da wuri ba sai da sukayi mata da gaske sannan tayi. Cike da kulawa bayan Mamin ta zauna agefenta tayi mata addu'o'i kamar yadda ta sabayi mata, sannan tasa hannu tana shafa kan Hidaya.
"Princess kitashi hakan nan ko kin manta yau akwai school ne?" Cikin bacci Hidaya ta bude manya idanuwanta tare da zuba su cikin na Mami. Sake maida idanunta tayi da alama baccin bai gama isar ta ba, da sauri Mamin ta kuma dago ta tana cewa.
"Okay da alama yau ba zakiga Hydar ba ko?" Hidaya jin maganar Mami yasa tayi saurin buɗe ido tana tashi zaune tace.
"Mami na tashi." Mami tayi murmushi tana fadin.
"Da alama Hydar din nan zai yi mana amfani tunda gashi daga ambato sunansa kin tashi." Hidaya bata fahimci abinda take nufi ba kawai ta fara sakowa daga kan gadonta irin na yara. Cikin sauri tanata mutseka fuska dan kar a kuma cewa ko ba zata je ba tana fadin.
"Ban manta ba fa Mami, ai inaso naga Hydar na bashi meatpie din da kikayi mana." Mamaki ne ya cika Mami ganin har lokacin Hidayan bata manta cewa zata kai masa meatpia din ba.
"Eh sosai ma zaki ganshi kuma ki bashi. Oya toh muje toilet ayi wanka da alwala." Kayan barcinta dake sanye a jikinta riga da wando masu santsi ta cire mata suka shiga bathroom din ta sanya kayan cikin washing mashing dake cikin toilet din sannan tafara yi mata wanka. Ko a cikin toilet din ma Hidaya bata da wata magana sai ta Hydar, Mami dai ta lura yanzu babu abinda zasu dinga ji daga bakin Hidaya sai maganar Hydar abokinta. Nan da nan tai mata wankan, tasata tayi brush tare da daura alwala suka fito tasa mata wata doguwar riga da hijab tace tayi sallah. Tana idarwa ta fara shiryata cikin uniform dinta da suke a wanke kuma a goge tas. Tsaf Mami ta gama shiryata ta ja hannu ta suka fito, kai tsaye suka nufi dining area. Tun da suka fito daga dakin Hidaya tafara hango Abbanta shima yana shirin zama a daya daga cikin kujerun dining din, dan shima yau sauri yake ya isa asibiti akwai Surgery da zaiyi, wasu dayawa daga cikinsu sai jiya aka saka date ɗin surgeryn bayan ya bawa kowane dokokin abinda zai yi da wanda ba zai yi ba har ayi aikin. Da sauri Hidaya ta saki hannun Mami tayi gurin Abbanta, dan dama har tayi barci bai dawo ba, shiyasa dama take Allah Allah ta gansa tafara basa labarin new friend dinta da tayi a school wato Hydar duk da cewa ta bashi labari a waya.
"Good morning Abba." Hidaya ta kamo hannun Abban nata tare da juyawa ta kama hannun Mami ma da ta iso gurin fuskarta cike da murmushi.
"Ohh Good morning Mami." Ta fada tana washe musu baki tunawa da ita bata gaishe da ita ba.
"Good morning too little princess." Duk suka fada suma a tare. Suna kallon juna suka sakarwa kansu murmushi. Abba hannuta ya kama ya dagata ya daura akan daya daga cikin kujerun dining din dake kusa da tasa. Sannan Suka fara cin abincin bayan Mami ta zubawa kowannensu. Ita kam Hidaya babu abinda takeyi sai bawa Abbanta labarin Hydar wanda tai ta jiran dawowar shi ta basa a zahiri saboda gani take kamar wanda tayi masa a waya bazai fahimci abinda take nufi sosai na.
"Hidaya kina yin wannan sabon friend din naki ko?" Abban nata ya fada yana jan hancin ta yana murmushi. Duk cikin zuciyoyinsu kuwa cike take da mamakin yarda Hidayan take ta maganar Hydar din tun daga jiya har zuwa yau, bayan sunsan ko cikin yan uwa tana da matukar wuyar sabawa. Breakfast dinsu suka cigaba dayi hankalin su a kwance har suka gama. Sai a sanan Abba ya juyo yana kallon Mami tare da fadin.
"Mami yau kema naga hankalinki a kwance ba damuwar tafiyar Hidaya school a tatare dake, ko har kunsaba?" Idanuwan ta tadago ta zuba masa tana murmushi take cewa.
"Abba baka ga diyar taka yau tafi kowa daukin a tafi ba? Ni ai sai dai nace alhamdulillahi tunda naga ta kwantar da hankalinta." Ai kuwa kamar ana zungurata ta diro daga kujerar tana fadin.
"Abba mu tafi." Yana ajiye cup yake cewa,
"Wai meke damunki ne yau princess dita?" Ya faɗa yana dora mata Idanuwansa yana kallonta. Sannan cikin kulawa ya kamo hannuta ya jawota gabansa yana fadin,
"Hidayan Mami duk daukin tafiya school din ne haka?" Murmushi Hidaya tayi tana kara sakala hannuta don ta dai dai ta zaman rikon nasu take fadin.
"Abba ai Hydar ma zai je school, gobe ma yaje, rannan ma yace zai zo." (Jiya da yau) kenan a lissafin su na yara. Jinjina kai Abban nata yayi gabaki daya Hidaya sakashi nishadi takeyi, yama kasa gane karatun takeson zuwa yi ko kuma dai ganin abokinta? Ya mike still hannunsa yana cikin nata suka baro wajan dining zuwa kan kujera inda lunchbox da schoolbag din ta suke ajiye. Ya dauki schoolbag din ya goya mata wacce babu komai sai pencil da color a Ciki ba a fara basu book ba tukunna. Tana sakala hannayenta hankalinta yana kan lunchbag din tace.
"Mami nida Hydar kika sakawa?" Cike da gajiya dajin tambayar tace,
"Eh idan kinje sai ki bashi shima." Farin ciki ya lullubeta wanda su kansu sai da suka hango hakan a saman fuskarta. Ita ta rike lunchbox din suka fito zuwa mota Mami sai dariya takeyi. Har suka shiga motar suka tafi Mami na tsaye sai da taga an rufe gate sannan ta juya ciki zuciyarta tana yi musu fatan sauka lafiya da addu'ar samun abinda aka fita nema.
*****
#Love & Destiny
#Wata Alaka
#Zee Bawa
#Stylish Bch
#Yan Tagwaye