GONAR SHARRI...

BABI NA SHIDA

by @billysfari

GS 6.


Kallon yadda jikinta ke rawa Irfaan ɗin yai kafin ya maido da kallonsa wajan Hajja Maimoon dake fitowa daga ɗakin. Tana ganin Irfaan ɗin ta ƙaraso ƙasa da sauri tana cewa. 


"Alhamdulillah kazo a dai-dai Irfaan, kai da kake ɗaurewa shegiyar yarinyar nan ƙugu, ka faɗa min duk gidan nan waye zai shiga har ɗakina ya kwashe min gold idan ba ita ba? toh wallahi yau ko ni ko ke Jauhar agidan nan sai kin fito dashi duk gidan uban da kika kai shi." Kasa cewa komai Irfaan yai yana kallon Hajja Maimoon har ta dasa aya sannan ya juya ga Jauhar da har lokacin jikinta be dena rawa ba yana cewa, 


"Jauhar ke kika ɗaukar mata?" Yanayin irin kallon da yake yi mata ya tabbatar mata da ɓacin ran dake cikin zuciyarsa, wanda shi bana komai bane illa na zallar bakin cikin ganin halin da ako yaushe idan ya shigo gidan yake ganinta aciki. Cike da tausayinta a zuciyarsa yake jin ina ma yana da inda zai kai ta da ya ɗauke ta daga cikin bala'in nan na gidan ɗan uwansa. Ita kuwa wani kukan ta fashe dashi tana ji aranta cewa shikenan shima ɗin dake ɗan tausaya mata ya yarda cewa tayi sata, jin bata ce komai ba yasa a ɗan hasale Irfaan yake cewa, 


"Ba magana nake yi miki ba?" Wata irin zabura ta sakeyi cike da tsoro ta shiga girgiza masa kai alamun ba ita ta ɗauka ba. Juyowa yai yana kallon Hajja Maimoon yace, 


"Kin ji Hajiya ba ita ce ta ɗauka ba. Mai yiyuwa kin sauya mishi waje ne baki sani ba." 


"Ahhhh lalai Irfaan! Karya zan yiwa Jauhar ko me kake nufi?" Gyara tsayuwarsa yai cike da gundura da kukan Jauhar ɗin da yake ji yace,


"Bance karya kike yi ba Hajiya amma kiyi tunani tukunna, me Jauhar zatayi da gold idan ta ɗauka tunda babu inda take zuwa? Kuma ga alama kin duba cikin kayanta baki gani ba kinga kuwa idan har ta ɗauka dole zaki gansa a ciki tunda ko nan da gate ba zuwa take yi ba." Wani mugun kallo Hajja Maimoon ta watsa masa haɗe da cewa, 


"Yanzu ma dole zan ganshi idan taji ajikinta, idan kina son zaman lafiya acikin gidannan kizo ki faɗa min inda kika kai shi ko wanda kika ba ya ɓoye miki." Hajja Maimoon taƙarasa zancen tana ɗora ƙafarta ɗaya akan ɗaya daga kan kujerar da take zaune tare da ɗauke kanta gefe ganin irin kallon da Irfaan ɗin keyi mata dan dama da biyu tafaɗi hakan. Kallonta sosai yai tare da sakin murmushin takaici ya maida kallonsa ga Jauhar sannan ya juya yabar gidan zuciyarsa kamar zata fito.


"Zaki zo ne ko sai na sameki a wajen nan?" Jauhar dake tsoron ƙarasawa tuni ta shiga tittirjewa ta shiga haɗa hannuwa waje ɗaya tana cewa, 


"Kiyi haƙuri Mommy wallahi ba nice na ɗaukar miki ba." Cike da jin zafin Mommyn data sake kiranta dashi Hajja Maimoon ɗin ta runtse idanuwa tana jin tamkar ta watsa mata wuta a fuska, ta taso a hasale tayo kanta ta shiga naɗa mata duka, bata ƙyaleta ba sai da taga bata motsi alamun ta suma sannan ta koma saman kujera tana haki tamkar wacce tayi tseren gudu, ganin mintuna biyar ba alamun Jauhar zata motsa yasa ta mike ta ɗauki ruwa mai shegen sanyi dan har ya soma sanyi a fridge ta tuttule mata a jikinta, duk da zata so a ce Jauhar ɗin ta mutu sai dai tasan za'a tuhumeta tunda Irfaan ya san halin da suke ciki. tamkar an fizgo numfashin Jauhar ta saukewa lokaci ɗaya tana sakin wata irin ƙara dake nuni da a firgice take tana ja da baya tana cewa. 


"Bani ce na ɗauka ba wallahi Hajiya ban ɗaukar miki ba." Ta sake faɗa tana ƙoƙarin barin falon don tsira da ranta, don a yanzu kam ta yarda cewa tabbas Hajja Maimoon zata iya kasheta kamar yadda akoda yaushe take faɗa. Tasowa Hajja Maimoon ɗin tayi tana jan ƙafafuwan Jauhar ɗin har zuwa cikin ɗakin nata ta jefata tare da ciro key ɗin ta ciki ta kulleta ta waje tana cewa. 


"Na fiki taurin kai Jauhar, ubanki ɗan iskan banza ke kuma ɓarauniya ko? indai baza ki faɗa min inda kika kai min gold ɗina ba babu inda zaki je koda kuwa mutuwa zakiyi." Daga haka tawuce ɗakinta rai aɓace taci gaba da neman gold ɗin nata data ajiye bata gansa ba.


Jauhar kam tsabar kuka gaba ɗaya fuskarta ta suntule tayi jajir, tayi kuka tayi na bakin cikin haɗata da Hajja Maimoon, da haka bacci yazo ya ɗauketa saboda tsabar wahala, A ɓangaren Hajja Maimoon ko dole ita tafito ta ƙarasa girkin da kanta cikin rashin walwala ta jere akan dining don ta ɗau alwashin sai Jauhar ta fito mata da gold ɗinta ko da zata buɗeta.


Kasancewar ba wani damuwa da ita yaran gidan sukayi ba yasa koda suka dawo daga school babu wanda ya nemeta, musamman da duk wani abu da zasu buƙata Mommy ta tanadar musu shi, shi yasa har dare babu wanda ya nemeta acikin gidan, girkin dare da Mommyn ta ɗora da kanta ma Jannat na gani ta soma murna yau Mommy ce zata yi musu special abinci ba sai sunci jagwalgwalen Jauhar ba. Murmushi kawai Mommy ta sakar mata taci gaba da aikin kafin Suhaila data dawo daga school tafito ta sameta aciki, 


"Sannu Mommy, Wai yau meke damunki ne?" Sai da Hajja Maimoon ta juye kayan miyanta a blender da zata markaɗa ta kunna sannan ta kalli Suhaila data ciro crackers daga cikin loka ɗin dake kitchen ɗin ta haye carbinant tana ci tace, 


"Ba lafiya kam Suhaila, gold ɗina na nema acikin gidannan na rasa!"


"What!" Suhaila tafaɗa tana zaro idanuwa, sai data tura crackers ɗin acikin bakinta sannan ta sake cewa,


"Mommy are joking? Toh waye zai ɗaukar maki gold har cikin dakinki?"


"Tambayar da nayiwa kaina kenan Suhaila saboda Jauhar tace ba ita ta ɗauka ba, kuma kinga ita kaɗai ke shiga ɗakin nawa." 


"Maganar banza, wallahi ita ta ɗauka Mommy kawai tafito miki da abunki ko taci ubanta acikin gidan nan, dama da ɓarauniya muke zaune Mommy?"


"Abunda nake tunani kenan, shiyasa na rufeta cikin ɗaki har sai ta gaji ta fito min da abuna." Hajja Maimoon tafaɗa tana kashe blender ɗin dan kayan miyan sun markaɗu, da haka kuma Mommy ta kammala aikin suna tayata fira. Tana gamawa tasa suka kwashe abincin suka kai kan dining ita kuma ta gyara kitchen ɗin sannan ta haye sama, wanka tayi tai sallar magriba sannan ta sakko ta samu yaran a palour zaune suna kallo, Jannat ce ta ɗago kai tana cewa.


"Mommy wai gold ɗinki aka ɗauke?" Shafa kanta kawai Mommy tayi haɗe da neman kujera ta zauna don gaba ɗaya ƙarfin halin yin komai takeyi, ɓatan gold ɗin ba ƙaramin tashin hankali ya sakata aciki ba daurewa kawai takeyi tana yin abubuwa. Kusa da ita Jannat ta koma ta zauna tare da ɗago kanta tana kallon fuskar Hajja Maimoon tace, 


"Mommy sorry, Jauhar ce ta ɗauke miki ko?"


Kafin ta tankata sai ga Daddy ya shigo, da gudu tamiƙe ta nufi wajensa tana yi masa oyoyo ya rike hannunta suka ƙaraso ciki, sannu da zuwa Suhana da Suhaila suka yi masa ya amsa cike da farin ciki kafin yakai kallonsa ga Hajja Maimoon dake yi masa sannu da zuwa yana cewa, 


"Yawwa Mommyn Jannat, yau nasan nayi laifi ayimun afuwa." Ya faɗi hakan saboda rashin dawowa gida dawuri da baiyi ba dan ba irin wannan lokacin yake dawowa ba, kullum ana gama sallar la'asar yake dawowa gida amma yau wani aiki ya riƙesa bai dawo ba sai yanzu. Murmushi ta sakar masa kafin tamiƙe ta nufi sashensa, tana jin Jannat na faɗa masa cewa Jauhar ta ɗaukewa Mommy gold, bata dawo baya ba tayi gaba abunta. Bai bi takan zancen ba har sai bayan ta haɗa masa ruwa yayi wanka ya saka doguwar jalabiya ya wuce masallaci yayo sallar isha'i ya dawo sun zauna cin abinci sannan ya kalli Jannat yana cewa, 


"Jannat kika ce me? Me Jauhar tayi?"


"Gold ɗin Mommy ta ɗauke." Juyowa yai ya kalli Mommy dake ɗan tsakurar abincin dake gabanta dan ba da ɗinsa take ji ba yace, 


"Mommyn Jannat wai da gaske ne?" Ajiyar zuciya ta sauke haɗe da cewa,


"To na nemesa na rasa Habiby, waye zai ɗauka idan ba ita ba tunda ita kadai ke shiga ɗakin?"


"Kin duba da kyau kuwa? kuma kin tambayeta ko ta sauya mishi wajen zama ne data je gyaran ɗakin?." Ranta a ɗan ɓace take magana, 


"Na duba ko'ina fa Ya Habiby, na kuma tambayeta amma ta tsaya tana yi min musu wai bata ɗauka ba, dan haka wallahi ko mutuwa zatayi a gidan nan sai ta fito min da gold ɗina kafin na sake barinta ta shaƙi iskar wajen nan." Hannunsa ya miƙa ya ɗora saman nata ganin yadda ɓacin rai ya taso mata lokaci ɗaya haɗe da cewa. 


"Calmdown Mommyn Jannat, Jauhar ɗin tana ina yanzu?" Sai data haɗiye wasu yawun bakin ciki da tun ɗazu suka tsaya mata a maƙoshi hawaye na sakko mata tunawa da makudan kuɗin data saka ta sayi gold ɗin da tsada dan shiga tsara amma wai ace yanzu ya ɓata sannan tace, 


"Tana ɗakinta na rufe ta dan babu inda zata je ban sani ba kota haɗa kai da wani taje ta bayar a sayar min da abu." 


"Kamar ya? Wai tun yaushe hakan tafaru ban sani ba?" Yafaɗa cike da mamaki jin wai ta rufeta a ɗaki sai kace wata dabba, 


"Tun da kafita." Ta bashi amsa a takaice tana wani turo baki,


"Subhanallahi shine kuma kika rufeta? Haba Mommyn Jannat mutunce fa kuma ki tuna muna da ƴaƴa, zaki ji daɗi idan aka yiwa Jannat, ko Suhana ko Suhaila hakan? Look koma meye kiyi hakuri ki buɗeta abi abun a hankali kada azo a samu matsala yarinyar mutane tazo ta mutu a hannun mu." Kuka Hajja Maimoon ta saka tare da miƙewa tana cewa, 


"Wallahi ni bazan buɗeta ba sai tafito min da gold ɗina, kasan nawa nasa na siyashi?" Goshinsa ya dafe haɗe da cewa, 


"Oh my God! Kije ki buɗeta nace zamu yi magana daga baya Maimoon." Yadda yai maganar ya alamta mata cewa ransa ya ɓaci, ba dan ranta ya so ba ta shiga kitchen ta ɗakko key ɗin taje ta buɗe ɗakin Jauhar tana barin wajen aguje tana kuka. Da idanuwa Alhaji Sha'aban Sada ya bita yana kallo kafin ya maido kallonsa wajansu Suhana da ransu ya ɓaci ganin Mommyn na kuka yana cewa, 


"Suhaila je ki kira yarinyar." Yafaɗa cike da damuwa shima. Wani kallon wulakanci Suhaila tayiwa Jauhar da tana jin motsin buɗe kofar a tsorace ta tashi ta takure waje ɗaya tana ƙanƙame jikinta acan kusuwar ɗakin, 


"Munafuka, ki taso Dady nakira kuma sai kin fitowa da Mommyn mu gold ɗinta ko bakya so ɓarauniya kawai." 


Jiki ba ƙwari Jauhar tamiƙe wani irin jiri na ɗibarta saboda yunwa da halin da take ciki tafito tana rabewa ajikin bango, tausayinta ne ya rufe Alhaji Sha'aban ganin yadda ta koma yace,


"Ƙaraso nan Jauhar." Sai data dudduba palourn taga Hajja Maimoon bata nan sannan ta saki jikinta ta iya ƙarasawa wajen ta duƙa ƙasa yaran sai harara suke aika mata da ita tamkar idanunsu zai faɗo. Cikin sigar rarrashi Alhaji Sha'aban yace da ita,


"A ina kika ajiyewa Mommynku gold ɗinta har tayita nema bata gani ba?" Ba tare data ɗago kanta ba tace, 


"Ban ganshi ba Dady kuma wallahi bani na ɗaukar mata ba." Taƙarasa zancen hawaye na sakko mata akan fuskarta.


"A'a Jauhar kiyi tunani tunda kinga ke kaɗai ke shiga ɗakin yi mata gyara ko kin gansa kin sauya masa waje?." Sai alokacin ta ɗago kai tana kallon Dady har lokacin hawaye basu daina sakkowa akan koɗaɗiyar fuskar tata ba da gaba ɗaya tayi kama kalar aljanu saboda rashin kulawa duk ta dushe in ba ga wanda ya santa ba tun farko tana cewa.


"Allah Dady ban ganshi ba, za'a iya sake cajeni agani ko a sake duba ɗakina, wallahi ko kashe ni idan za'ayi Dady bansan inda Mommy ke ajiye gold ɗinta ba idan ba nagani a wuyanta ta saka ba."


"Shikenan, tashi kije." Dady yafaɗa tare da miƙewa ya nufi sama wajen Hajja Maimoon ɗin. Wani irin mugun ranƙwashi Jauhar taji Suhaila ta sakar mata da zata wuce akai tana cewa,


"Barauniya kin dai ji kunya wallahi." Suhana ta bangajeta ita kuma daga inda take ta faɗi tare da wucewa abin ta. Jannat na zuwa itama tasa kafa ta takata ta wuce tana cewa, 


"Beranya.."


Zuwa yanzu hawayen Jauhar sun fara ƙarewa, haka ma zuciyarta ta bushe da sam babu sanyin dazai sata tausasa har taba idanuwan nata damar zubo da ƙwalla, hakan yasa ta miƙe ta wuce ɗakinta ta rufo tana addu'ar Allah ya kawo mata mafitar barin gidan kota samu ƴancin rayuwa data rasa tun tana ƙarama.


Alhaji Sha'aban Sada kuwa a hankali ya tura ƙofar ɗakin Mommy ya shiga, tana zaune gefen gado ya ƙarasa ciki tare da tsayawa agaban madubi ya ɗan jingina yana kallonta yake cewa. 


"Yanzu meye abun kuka Maimoon da har zaki bari waɗannan tsadaddun hawayen naki su zuba kuma agaban ƴaƴan ki? Ina gold ne dai ko? Toh kibari zan siya miki wani, kiyi hakuri kibi abun a hankali tare da saka mata idanuwa, idan har yana wajenta na tabbata zaki ganoshi amma to me I don't think yarinyar nan ita ta ɗaukar miki abu saboda na sake tambayarta ta tabbatar min da batasan ma inda kike ajiyewa ba, a yanda kuma nasan kina daraja duk abinda kike so bana tunanin zaki ajiyesa inda zata iya ganinsa." Ɗago kai tayi tana tsaresa da idanuwa kafin tace.


"Me kake nufi? kenan kana goya mata baya kenan ko? bayan ni da kai da kowa ma na gidan nan munsan ita kadai ce zata iya ɗaukarsa. Jannat, Suhana da Suhaila duka nasan wannan ba halinsu bane, be side ba abunda suka rasa daga wajen mahaifinsu balle suyi negative thinking irin wannan, but Jauhar fa? I don't trust her at all, bana tunanin zata wadata da abinda take dashi tunda ba tada gata irin nasu, asali ma da ita da babu duka ɗaya ne a wajen mahaifanta me zai hana tafara tunanin ɗauke-ɗauke." Iska Alhaji Sha'aban Sada ya ja ya furzar ta baki haɗe da cewa, 


"Ba goyon bayanta nakeyi ba, nasan itama baki taɓa cewa kin nemi abunki kin rasa acikin gidan nan ba, zancen gata da kikeyi Allah fa shike gatanta wanda yaso, koda wannan ɗabi'ar ta Jauhar ce zan so ki ajiye duk abinda kike ji a zuciyarki da iyayenta suka yi ba dai-dai ba, ki janyota ajikinki tamkar ƴarki ki gatanta itama, hakan zai iya sa ta sauya kuma ta amfaneki nan gaba ta hanyar mayar da alkhairi agareki akan sharrin da iyayenta sukayi miki, ƙaramar yarinya ce ita Maimoon, mai yiyuwa bata masan abinda sukayi miki ba amma kina sauke fushinki akanta which is wrong, very very wrong." Wani kallo take jifan Alhaji Sha'aban ɗin dashi haɗe da miƙewa tana kallonsa.


"Over my died body Habiby bazan taɓa ɗaukar Jauhar a matsayin ƴa ba a wajena balle har na gatanta, yadda na tsani mutuwata haka na tsaneta da duk wani abu daya shafi rayuwarta, halinta kuwa idan zaifi haka muni Allah ya tabbatar mata dashi ya sake lunka mata da wanda yafisa, ni kuma akwai nau'ukan azaba kala-kala da zan tanadar mata har zuwa lokacin da zata gudu da kanta tafice cikin rayuwata nima na huta." A yanzu ko kaɗan Alhaji Sha'aban Sada baya mamakin duk wasu munanan kalamai da zasu fito daga bakin Hajja Maimoon akan Jauhar, wanda hakan ke tabbatar masa da koma meye tsakaninta da iyayen yarinyar to baƙaramin abu bane, sai dai hakan bazai zama hujjar da zata sa ta ɗauki fansa akanta ba. 


"Shikenan, what ever dai wannan damuwar ta wuce please in sha Allah gobe zamu je na siya miki wani gold ɗin kiyi hakuri kin ji ko?" Ya faɗa yana ƙarasawa yariƙota tare da janyota zuwa jikinsa....... 




#A heart touching story

#Gonar Sharri..

#Hajja ce

#Billy s Fari

#Ƴan Tagwaye