GONAR SHARRI...

BABI NA BAKWAI

by @billysfari

GS 7.


Tabbacin data samu akan zai sai mata wani gold ɗin yasa zuciyarta yin wani irin sanyi, da haka ya riƙo hannunta suka sakko suna hira tamkar ba itace ta gama kuka ba har yana tsokanarta wai itama zata koma kamar Baby Jannat tafara saka mashi ciwon kai da rigimarta. Su Suhana dama sun wuce ɗakin su, kallonta yai tare da cewa,


"Muje kici abincin ki dan na lura baki ci komai ba."


"Na ƙoshi, bari nayi mata magana kawai tazo ta gyara wajen." Ta ƙarasa zancen tana nufar ɗakin Jauhar ɗin. Kwance ta hangota wani baƙin ciki ya sake tokareta na ganinta kaɗai da tayi kwance, gani tayi tamkar jin daɗi ne yasa ta kwanciyar saboda idan son samunta ne kawai ta buɗe idanuwa taga Jauhar cikin wahala da kuma aikin bauta da babu ranar tsayawa a huta aciki, 


"Ki tashi kije ki gyara wurin can, amma ki sani bawai na kyaleki bane, inhar banga zinarina ba bazan taɓa bari kihutawa rayuwarki ba acikin gidan nan, saboda na dinga jefaki a masifa kala-kala har sai kin gaji kin fito dashi, nonesense!"


Daga haka ta wuce part ɗin Alhaji Sha'aban tana tunanin kalar ukubar da zata tanadar mata gobe. Jauhar kuwa miƙewa tayi da kyar tafito palourn don dama wata irin masifaffiyar yunwa take ji ta kwashe kayan takai kitchen ta dawo ta gyara wajen, abincin da aka rage ta tattara ta hau ci har sai data canyesu tas sannan ta wanke kayan ta gyara kitchen ɗin, tana fitowa Suhaila na sakkowa, tana ganinta tace, 


"Ke.!" Lokacin Jauhar na ƙoƙarin shiga ɗakinta ta juyo tana kallonta ba tare data amsa ba, 


"Ki haɗo min coffee ki kawo mun." Jauhar da jikinta ke tsami taji kamar ta fashe da kuka amma ba damar yin hakan sai kawai ta amsa mata da,


"Toh." Tana juyawa tare da komawa cikin kitchen ɗin ita kuma Suhaila ta juya takoma ɗakinsu. bayan mintuna biyar Jauhar ta kammala haɗa coffee ɗin ta nufi ɗakinsu ta kai mata, har zata juya tafita Suhana tace,


"Ki shiga toilet akwai undies ɗina cikin washing machine ki ƙara wankemun ki shanya." Jauhar ta amsa mata da, 


"Toh." Tana sake ɗan tattaro karfin jikinta ta nufi toilet ɗin ta shiga wankin undies ɗin Suhana. Ba ita ta gama ba sai kusan ƙarfe sha biyu ta wanke toilet ɗin tas sannan tafito ta wuce ɗakinta, wanka ta shiga tafara yi ko jikinta zai saki sannan tasha ragowar maganin da Uncle Irfaan ya taɓa bata daga nan ta kwanta, kamar jira akeyi ta kwanta wani irin zazzaɓi ya taso ya rufeta, take tafara rawar sanyi ta ja zannuwanta duka ta lulluɓa hawaye na sakko mata, bata san lokacin data fara kuka ba tana kiran sunan Abbanta ba dako kasheta za ayi bata san inda yake ba yanzu, kuma bata san duniyar da zata shiga wajen nemansa ba.


Yadda taga dare haka taga safiya ba tare data runtsa ba saboda yadda zazzaɓi ya rufeta. Tun tana jurewa har takasa tafara kuka ƙasa-ƙasa, duniya ta sake yi mata zafi wacce dama ba wai ta taɓa yi mata bane, haka ta taso bata san wani abu farin ciki ba ko kaɗan. Alhaji Sha'aban Sada ne da asuba daya fito zai tafi masallaci yaji kukan nata can ƙasa-ƙasa amma da yake har an tada sallah bai tsaya bi takai ba ya wuce masallaci, da kuma ya dawo sai ya manta ya shige part ɗinsa ba tare da ya tuna cewa yaji kuka kafin ya fita ba. Hajja Maimoon na zaune ta idar da sallah tana duba wasu kaya a wayarta da take son fara business ɗin su, kai ta ɗago ta gaishe shi ya amsa yana faɗin, 


"Yau da wuri nake son fita saboda akwai bakin da zan gani ƙarfe bakwai, saboda haka ina tunanin bazan tsaya karyawa ba kawai haɗa min ruwan wanka dan bana so asamu matsala, mutanene masu muhimmanci da nake sakaran idan Allah ya daidaita tsakaninmu zan cika miki alkawarinki a cikin satin nan."


"Kamar kasan kayan da nake son fara business ɗin sune nake dubawa a wani group dana shiga na masu campany, duba kaga kalar designers ɗinsu." Ta miƙa masa wayar haɗe da tashi ta shiga toilet ta haɗa masa ruwan wankan tafito. Wayarta ya bata sannan ya miƙe yana cewa,


"Kayan sunyi kyau sosai idan har naga business ɗin ya karɓeki to nima zan saka hannun jari aciki sai na buɗe miki shago." Tana murmushi ta karɓi wayar tare da cewa, 


"Zai ma karbeni in sha Allah, ai sana'ar kayan yara da turarukka da jakunkuna da kake gani ba ƙaramin samu akeyi ba, matsalar kawai idan mutum baida kuɗi da kuma isasshen jari, hala ka manta a cikin harkar ka ganni ka ƙyasa?" Ta kasara maganar cike da zolaya. Ya yi murmushi yana cewa. 


"To ki ɗauka ba kida wannan matsalar gimbiya ta, bari na shiga wankan kar na makara." Alhaji Sha'aban ya faɗa yana ƙarasa shigewa cikin toilet ɗin ba tare da ya jira taje ta haɗa masa ba. Mintuna ashirin yafito ta taimaka masa ya shirya, tana cikin fesa masa turare wayarsa ta ɗauki ƙara lokaci ɗaya kuma sukaji ana buga musu ƙofa da ƙarfi ana kiran su, 


"Dady..!, Mommy..! kufito Jannat zata mutu." Suhana dake buga ƙofar da ƙarfi tafaɗa cikin tsanani tashin hankali, kusan atare suka ƙaraso bakin ƙofar Mommy na faɗin, 


"Me ya samu Jannat ɗin?" 


"Ciwonta ne ya tashi." Tafaɗa hawaye na sauko mata dan tunda asuba da suka tada ita suka ga ta sake shigewa cikin bargo wai sanyi take ji, shine fa yanzu ko da suka ga lokacin zuwa school na ƙoƙarin yi bata tashi ba suka janye bargon suka ga ta kakkame a cikin bargon, shine Suhaila ta tallabota zuwa jikinta tasa Suhana ɗin tazo takira su Mommyn. Already Dady ya riga da ya saba da ciwon Jannat dan haka cikin nutsuwa bayan yaje yaga yanayin da take ciki ya kira Irfaan a waya, bugu ɗaya ya ɗaga suka gaisa kafin yace yayi maza yazo gidan yana nemansa, dama jiya ba'a gidan ya kwana ba gidan Hajiya yayi tafiyarsa ya kwana acan saboda ɓacin ran abinda Mommy tayi masa da rashin iya jurewa ganin halin da Jauhar ke ciki da bazai iya ba.


Bayan mintuna goma sai gashi ya iso, lokacin an fito da Jannat nan palour, kallonsa Dady yai haɗe da cewa,


"Yanzu aka kirani akwai mutunen da zan gani urgent, ka ɗauki Jannat ka kaita asibiti ciwonta ne ya tashi, duk yadda ake ciki ka kirani kafin nazo.


"To Yaya." Irfaan yafaɗa tare da ɗaukar Jannat Mommy tabi bayansa ita dasu Suhaila da gaba ɗaya hankalinsu ya tashi. Har Alhaji Sha'aban ya shiga motarsa ya tayar suma sun shiga wacce zasu wuce asibitin ya saukar da glass ɗin motarsa yana cewa Irfaan. 


"Yauwa Irfaan da kun dawo yarinyar nan ku dubata ku gani idan lafiya take saboda da asuba da na fito zanje sallah naji kukanta ƙasa-ƙasa na manta bamuyi maganar da Maimoon ba." Yana ƙarasa faɗar hakan yafice daga gidan bayan mai gadi ya buɗe masa gate. Irfaan kuwa yana Jin haka ya kashe motar, har yakai hannunsa zai buɗe murfin ƙofar Hajja Maimoon ta dakatar dashi, 


"Ina kuma zaka je baka ga halin da yarinyar nan take ciki ba ne? Kana ganin fa yanda take kokuwa da numfashinta."


"Ita waccan ta cikin gidan ba mutum ba ce? Bazai yiyu abarta ita kaɗai ba har sai mun dawo tunda ba'a san halin da take ciki ba, ki je ki dubota in lafiya take sai mu tafi, I know Jannat will be ok in sha Allah ba abunda zai faru da ita." Tsabar ɓacin rai kasa magana Hajja Maimoon tayi ta ɗauke kai kawai zuwa can gefe, ganin haka yasa Irfaan ya ɓalle murfin motar yafita zuwa cikin gidan zuciyarsa duk babu daɗi. Kai tsaye bakin ƙofar ɗakin Jauhar ya nufa ya kwankwasa mata, jin shiru bata amsa ba ya sashi tura ƙofar a hankali. Adunkule ya ganta cikin zannuwan data rufa dasu har lokacin jikinta na rawar sanyi, sai kukan da takeyi wanda dan tsabar wahala ko fita baya yi sosai dan tayi kukan har ta gaji.


"Subhanallahi." Yafaɗa yana takowa cikin ɗakin tare da jaye zannuwan jikin nata, halin ɗaya ganta aciki ba ƙaramin tsorata yai ba yaciro wayarsa da sauri yakira Suhaila da itama ta cika tayi fam ganin yadda uncle ɗin nasu yake ƙoƙarin fifita mai aiki akan ƴar uwarsu. Kamar bazata ɗauka ba sai kuma ta ɗaga tana turo baki take cewa, 


"Uncle ko naja motar kawai mutafi ne?" Tayi maganar cikin nuna shi tunda yana da uzuri bari su tafi. 


"Short up Suhaila bake zaki sani yin abinda ya kamata ba, ai Yayan yasan kun iya mota amma ya taso dani nazo. Kuyi sauri ku shigo ke da Suhana ina jiran ku, ki faɗawa Mommy yarinyar nan batada lafiya sosai." Ya ƙarasa maganar yana kashe kiran tare da kiran sunan Jauhar ɗin har sau biyu amma takasa amsawa. Cike da ɓacin rai Suhaila ke faɗin. 


"Mommy wai kinji Uncle Irfaan yace Jauhar batada lafiya sosai."


"Wannan ba damuwar mu bace Suhaila, kije kifaɗa masa idan bazai kaimu asibitin nan ba ke ki dakko makullin motarki kizo mutafi kawai, ina ruwanmu da matsalarta? ta mutu mana."


"Mtss Allah Uncle Irfaan yacika matsala." Suhana tafaɗa tana balle murfin motar suka nufi cikin gidan. Saka su yai suka tallabo Jauhar wacce da daƙyar take iya tafiya suna faman kumbura fuska tare da riƙe numfashin su kamar sun riƙo kashi suna kauda kai suka shiga da ita cikin motar, dama Hajja Maimoon na gaba ta runtse idanuwa zuciyarta na tafarfasa haɗe da juyar da kanta gefe. Babu yadda zatayi ne amma da ba za'a taɓa yin tafiyar nan da Jauhar ba, kawai dan bata son a ɓata lokaci ne ba'a kai Jannat ɗin ba wani abun yazo ya sameta tasan sai tafi kowa damuwa saboda ta shaƙu da yarinyar fiye da sauran yaran. 


Ba tare da Irfaan ya kulasu ba ya dakawa Suhaila tsawa data yi tsaye a bakin ƙofar motar ita a dole bazata shiga motar ba yana cewa, 


"Suhaila karki bari na saɓa maki da sanyin safiyar nan, karki kai ni bango wallahi." Tana turo baki ta shiga cikin motar ganin yanayin yadda yai maganar ba wasa a fuskarsa ta ja murfin da ƙarfi ta rufe sannan ya buɗe ya shiga shima ya fizgi motar aguje suka nufi Fedral Medical center. Suna zuwa ya yi parking, Jannat kawai suka fitar dama tun a ciki sukayi ta mintsinin Jauhar wacce hawaye kawai take ta kasa bayyana kukan nata a fili. Ciki suka shige ganin haka yasa Irfaan yiwa ma'aikata mata dake cikin asibitin magana suka karaso wajan motar suka taimakawa Jauhar aka shiga da ita ciki emargancy dan gabaki ɗaya tafi Jannat wahala. Ƙoƙarin yadda za'a duba Jauhar kawai Irfaan keyi hakan yasa ran Hajja Maimoon sake ɓaci tayi saurin ƙarasawa inda yake cikin fushi take faɗin. 


"Irfaan hala ka manta wacce tayi sanadin fitowar mu ko? Naga gabaki ɗaya hankalinka yana kan wacce babu wata alaka tsakaninka da ita. Kaje kaji da Jannat ka tsaya nan wajan. Ni wani lokacin sai na kasa gane manufarka akan Jauhar wallahi." Jin kalmarta na ƙarshe-ƙarshe yasa Irfaan saurin kallanta ta jinjina masa kai alamar tabbatar da abinda yaji ta faɗa. Yaja ɗan guntun tsaki yadda ba zataji ba. Yana mamakin yadda take yi masa abubuwa bayan a girme ya girmeta dan shi yana da talatin da uku ita kuma tana da talatin. Gudun ɓacin rai yasa shi juyawa ya yi settling case ɗin Jannat aka bata ɗaki sannan ya koma kan Jauhar wacce fitowar Zain kenan wata nurse tana nuna masa inda Jauhar take a kwance kan bancin dake ajiye a reciption. Wajan ya ƙarasa tare da buɗe baki da kyar ya furta. 


"HI." Jauhar dake kwance taji tsayuwar mutum a kanta ta buɗe idanunta da kyar suka sauka akan ƙafafuwansa dake sanye cikin black cover shoe ta kasa ɗaga kai ta kalli fuskarsa saboda yadda idanunta sukai mata nauyi. Durƙusawa ya yi saitin fuskarta tare da leƙawa suka yi ido huɗu da juna. Da sauri ya miƙe tsaye ganin idanunta biyu yace. 


"Tashi zaune." Jauhar ta shiga ƙoƙarin tashi amma ta kasa, sai dai tana karfafawa zuciyarta guiwa tana ta kokawar miƙewa sanin cewa jiranta ake yi. Hannunta da take dafa bancin ne ya goce tazo zata faɗi cikin sauri Zain yasa hannu zai taro ta Irfaan da isowarsa kenan ya tare ta. Da sauri dukkan su suka kalli juna ido cikin ido kafin Irfaan ya juya yana taimaka mata ta zauna sosai akan bancin, daga shi har Zain kallanta suka yi yadda albarkatun kirjinta da suka fara tasowa suka tsaya a cikin rigarta wacce babu bra a jiki. Da sauri Irfaan ya kauda kansa Zain rintsa ido wani mugun takaici yana taso masa tun daga can ƙasan ransa har zuwa saman harshensa...




#A heart touching story

#Gonar Sharri..

#Hajja ce

#Billy s Fari

#Ƴan Tagwaye